A D U N I Y A TA COMPLT BY HUGUMA
A D U N I Y A TA COMPLT BY HUGUMA
*_H U G U M A_*
*Arewabook:Huguma*
__________________________
*_Amintaccen guri kuma muhalli na siyayyar ingantattun suturu na alfarma,siyayya cikin aminci,farashi
na musamman da babu irinsa_*
*lace*
*mayafai*
*lafaya*
*sarqoqi da agoguna*
*under wears*
*_Akwai group na musamnan saboda nasu buqatar kayan kitchen HUGUMA UTENSILS UNIVERSE_*
https://chat.whatsapp.com/EzM8Qst8A2XAevw3akx5ub
*_me kikeyi tuntuni bakiyi joining group dinnan ba?,sallah tana matsowa,azumi na tunkarowa?_*
https://chat.whatsapp.com/DT97XBDyEfyEwniN0a09Cz
__________________________
Page 01
*_The gateway_*
"Maaaam.......don Allah maama,abbee bashi da lafiya sosai kin sani maama......idan kika tafi waye zai
kula damu?,idan kika tafi maama waye zai kula da abbeee?" Muryar yaron da gaba daya bazai haura
shekara goma sha uku ba kenan take fita cikin wani irin sanyi da matsanancin rauni wanda koda ba'a
gaya maka ba.....koda kuma baka kalli fuskarsan nan dake jiqe da hawaye ba.....koda baka kalli
hannuwansa dake rawa ba wanda ke tallafe da mujinyacin dake zaune tsakanin cinyoyinsa ba zaka
fahimci yana cikin matuqar kaduwa razani tare da zallar firgici.
"Na fasa tafiya" daga bakinta,duk kuwa da cewa ba wani abu guda daya tal da ya bashi alama komai
qanqantarta da take nuni da zata iya janyewar. A maimakon haka ma,sai sake gyara yafen mayafinta
dake saman kanta tayi,ta duqa tana cusa ragowar kayanta da basu samu gurbi ba cikin baqar jakar
gabanta.
"Don Allah mariya.......ba don ni ba......ko don yaran nan,kiyi haquri......ki zauna ki rungumesu,ni tawa me
sauqi ce,ina da tabbacin kwanaki qalilan ne suka ragemin,su din dai sune abun dubawar......" Mutumin
da rashin lafiya da kuma talauci sukayi gamayya da matsin rayuwa suka yiwa kowanne sashe na halittar
jikinsa illa. Yayi maganar da qyar yana fidda numfarfashi kaman numfashin nasa zaya qwace daga
tsakanin qirjinsa zuwa hunhunsa.
Dauke dubansa yayi daga kan fuskar mutumin da yake MAHAIFI a gareshi ya maida kanta
zuciyarsa na narkewa da wani irin tausayin kansu gaba daya idan ka debe ITA!. Bugun zuciyarsa na sake
daduwa da tsananin tashin hankali da tausayin na daban kamar zai fasa zuciyarsa ta tsage. Ya jima yana
begen jin fitar wasu kalmomi daga bakin mahaifinsu wanda a qalla yau kusan kwanaki goma cif kenan
baya um baya um um. Ya kashe darare masu yawa yana kasa kunnen yaji wani abu daga bakinsa.....sai
gashi a yau bakin ya budu,amma kuma sun budu ne saboda tsananin bala'i da firgici da take shirin jefa
rayuwarsu,bawai ya budu bane da zummar musu magana da kyawawan kalmomin nan da baya rabo
dasu a kansu.
Idanunsa cike da fatan zuciyarta zata rusuna daga kalaman mahaifinsu.....kodon kalmar mutuwa
daya ambatarwa kansa wadda ta zama daya daga cikin dalilan da ya sanya yaji inama baiyi maganar
ba,inama shuru yayi da bakinsa duk da tarin buri da begen yaji yayi maganar wanda ya cika zuciyarsa.
Yana tsaka da wannan shawagin cikin zuciyar zato da fata ya sake jin busashiyar muryar mahaifin nasa
mara amon sauti yana sake tattara dukka juriyarsa yana fadin
"Mariya......idan kika tafi waye zai kula dasu?" A fusace ta waiwayo ta watsa masa wani irin kallo tana
rataya jakarta bisa kafadarta
"Dasu nazo?,ai dama a nan na samesu kuma a nan din zan barsu,dan da uwarsa ke mutuwa ma randa ta
haifeshi yanzu haka suna rayuwa sunfi miliyan bare wadanda suka kai shekara sha uku da takwas" tana
kaiwa nan ta soma daga qafafunta tana baiwa dakin takun bankwana,abinda ya bashi tabbacin da gaske
fa take!
Baisan wanne tunani ya kamata yayi ba,don a sannan qwaqwalwarsa tayi qanqanta da daukan
dukka wadannan abubuwan bare har ya rarrabe hukuncin daya dace da wanda bai dace ba,sai ya
tsinceshi a gabanta,riqe da qafafunta yana qaramin kuka da iya dukka qarfinsa a shekarunsa.
Dubansa tayi kaman zata qwace qafar,sai kuma ta saka hannu ya dagoshi ta maidashi ta zaunar
tana cewa
"Nan din shine dolenku,a nan zaku zauna da dadi ba dadi,da wuya ko babu,idan nace nima zanci gaba da
zama,dukkanmu ni daku za'a yi haihuwar guzuma ne ni kwance ku kwance babankun ma haka,gwara na
matsa kadan,wataqila rabon yana a gaba".
Cak maganar ta yiwa zuciyarsa tsaiwar mashi. Idanuwansa suna iya hangen mahaifinsa yana
runtse idanunsa. Sai ya zare nasa idanun yana maidawa kan yaron daya yunqura zaibi bayanta bayan
fitarta qofar dakin.
Yadda ta zare idanunta daga kanshi haka ya zare nasa. Sai ya maida dukka yunqurinsa wajen
qoqarin kwantar da mahaifinsa yadda zayaji dadin kwanciyar. Jikinsa ya qara nauyi ya kuma sake sosai.
Saidai duk da haka numfashi na fita ta qofofin hancinsa,abinda ya sanya sam tunaninsa bai kai kan komai
ba.
Bashi da wani sauran FATA a kanta......amma kuma hankalinsa ya gaza daukewa daga
kanta,yana lissafe da takun takalminta sanda take ficewa daga cikin gidan nasu. Fitar da har yanxu ta
kasa barin qwaqwalwarsa. Fitar da har yanxu take masa matsanancin ciwo......fitar daya alaqantata da
sila kuma MABUDIN afkuwar kowanne irin tsanani da matsin rayuwa.
*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*
*ZAFAFA BIYAR*
*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA
ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*
_K'ALBIM Mamuhghee_
_DUNIYATA Huguma_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
_YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_
*09033181070*
89825722
1000cf
*D U N I Y A T A*🌍
*_H U G U M A_*
*Arewabooks:Huguma*
Page 02
Idanunsa da suka qanqance suka kuma sake shigewa ciki saboda tsananin kuka tashin hankali da firgici
ya bude. Ya jefa idanunsa gefansa hannun hagunsa,ya kuma aza idanunsa saman shimfidaddiyar
lamusashiyar shimfidar. Shimfidar da kwanaki uku kenan da matuwar mamallakiyarta, shimfidar da
kwanaki uku da suka gabata iwar haka suna tare da me shimfidar. Kaka a garesu,mahaifiya ga mahaifinsu
wadda ta zame musu bango jigo kuma majingina a garesu bayan rasuwar mahaifinsu.
Har yau ya kasa sanya hannu ya tattare shimfidar,hakanan babu wanda ya damu ya dauke ta.
Yo ina aka damu dasu ma ballantana abinda ke cikin gidan?. Su din ba wasu bane,basu da abinda zasu
bawa jama'ar zaman makoki,basu da gata basu da wani tsayayye da zai tsaya ya tayasu jimamin rasa
kakar tasu da suka zauna da ita shekaru uku cikin tsanani da kuma zazzafar gwagwarmaya irin wadda ke
xamantoww tsere ne tsakanin tsanani da kuma sassauci cikin tsananin.
Hawayen nan daya kasa yankewa daga idanunsa ne suka sake bullowa. Har yau gani yakeyi
wasa ne,har yanxun gani yake JADDA zata dawo. Shudewarta ya dawo masa da mikin rasuwar
mahaifinsa,sai yakejin kamar yau ne ya rasu,kamar a yau ne yayi bankwana da duniyar,kamar a yaune
MAAMA ta sanya qafafu ta fice ta barsu,tafiyar data xama wani yanki na tunzura yanayin rashin lafiyar
abbee......tafiyar kuma data zaman kamar ta tafi da ruhi da kuma rayuwarsa. Hannunsa daya ya sanya ya
riqe wuyansa da kyau kamar yana shirin shaqe kansa. Wasu murtuka murtukan jijiyoyi suka fito bisa
saman kansa da goshinsa sukayi layi rad'a rad'a. Kalar da idanunsa yayi ya sake ninkuwa da kalar jaa
ainun,kuka da hawaye me zafi ya sake yanke masa,matuqar maqurar qiyayyar jinin mahaifiyarsa yana
tsartuwa cikin kowanne sashe da lungu na gangar jiki da zuciyarsa.
"Hamma.....ham" yaron daya fado dakin ya dakata da kiran da yake jera masa. Cikin wannan yanayin ya
waiwayo yana kallonsa,sai yaron ya dan ja da baya,don ya tsorata ainun da yadda yaga fuskarshi ta
sauya. Yanayi ne dake sanya masa tsoron hamman nasa sosai da sosai,duk sanda ya ganshi a irin haka
sai ya dinga ganin kamar ba hamma dinsa ba.
Ya lura da hakan shima,wannan ya sakashi zare hannunsa daga wuyansa yana tattaro wani
irin yawu me tauri da kauri yana hadiyewa da qyar kamar me hadiyar duwatsu. Yakai zuciyarsa cen
nesa,ya kuma gyara harshensa sannan ya jefa masa tambaya
"Abba ne......abbansu farouq ne yace kazo yana soro" idanunsa ya sauke yana jin wani kaso na rahama
da sassauci suna sauka a zuciyarsa. Mutum qwaya daya tak a duniya da ganinsa ko jin kiransa yake
shaida masa zuwan alkhairi sauqi sassauci ko rangwame daga dukkan wani hali da suke ciki.
Yana tafe amma yana jin kaman ba'a kan qafafunsa yake tafiya ba,yana tafe yana jin kamar
tsakanin sama da qasa yake,saboda tashin hankali yunwa harma da qishi. Ko sau daya bayan rasuwar ya
gaza kai qwayar abinci bakinsa daga abincin da maqota ke saka musu jifa jifa. Yana daddafe da bango
yana wulga idanunsa ga sararin tsakar gidan nasu daya zama kamar filin sukuwa......ya zama fetal ya sake
fadi,abinda ke alamta masa cewa lallai sun sake rasa wani bangon kuma madaafa.
******Dattijo me cikar kamala wanda duka duka shekarun haihuwarsa a duniya ba zasu haura arba'in
da biyar ba. Amma alamu sun nuna muraran shi din me ginanne kuma lafiyayyen jiki ne dake iya cinye
shekaru.
Yana sanye da yadin kufta da yasha aikin hannu wanda ya qara masa cikar kamala. Ya tura
hularsa baya,qafarsa sanye da slipper dan madina,wanda ke zamantowa daya daga cikin dabi'unsa a
lokuta da dama idan zaya fito guraren da bai wuce masallacin cikin unguwa ba ko wata unguwata
kurkusa a cikin abun hawansa ko a qafa.
A raunane suke kallon juna shi da shi,ganinsa sai ya sake sakawa zuciyarsa wani raunin,yana
shirin duqawa ya gaidashi ya tallabeshi
"Tashi tashi......sannu da qoqari,sannu da haquri......akwai wai abu da kuke buqatar dauka ta cikin
gidan?" Ya tambayeshi yana dubansa. Bai gane komai abban yakeson fada ba,don haka ya dubeshi sosai.
"Gida na zan wuce daku,ba za'a barku ku dinga kwana kuna tashi gidan da ba kowa a cikinsa ba saiku
kadai"
"Dauko abinda ya sawwaqa a kulle gidan" yayi maganar yana kama hannun qaramin qanin nasa dake
kusa dashi.
Sanda yake hada kayan kudu da yamma gabas da arewa na zuciyarsa a cakude yake da tunani.
Zasu koma gidan abba?. Gidansu farouq?. Tabbas su farouq 'yan gata ne gaba da baya,saidai wani irin
gata suke samu dake da wani wawakeken gibi da kuma naqasu. Gatan daya rasa wani bango kuma jigo a
cikinsa,gatan da wani lokacin yakan juya musu da wani irin launi mara armashi. Wani gata da bai amsa
sunansa ba a lokuta masu yawa,su din sukan zama har sun darasu samun wani abu guda daya,duk da
tarin nasu naqasun rashin wadata da sukunin rayuwa. Sun darasu samun 'YANCI SAKEWA DA KUMA
WALWALA. kenan zasu rayu tare da momy?,zasu zama qarqashin inuwa da mulkinta kamar sauran
yaran?.
Sakin ragowar kayan hannunsa yayi ya sulale ya zauna a qasa. Iya wannan tunanin kadai ya karya
duka sauran guntun karsashinsa.
Tunaninsa ya dinga rarrabuwa,a haka dai gatane suka sameshi saboda abban wani irin dattijo ne
me fafutukar taimakawa da tallafawa sukkan me rauni. Tun zamanin da mahaifi da mahaifiyarsu ke
rayuwa tare hannuwansa da aljihunsa harma da lokacin cikin hidimta musu suke. Shudewar uba a garesu
ya sanyashi sake ninka alkhairinsa. Ya sanya hannu bibbiyu ya tallafi rayuwarsu data jadda,a yanzun
kuma yana shirin maida nauyin kacokam bisa wuyansa.
"Idan ba zaka iya shirya kayan ba fito hakanan a barsu zuwa gobe ko?" Muryar abban ta baqunci
kunnensa,wanda dole ta sanyashi miqewa ya debi iyakar abinda zai iya. Ya janyo qafafunsa yana fita
daga dakin,idanunsa na rarrabuwa a sassannin da suka qaraci dabdalar rayuwarsu suda jadda bayan
shekaru uku da rasuwar mahaifinsu. Abinda ya dunqule waje guda ya bashi adadin shekaru SHA BIYAR a
duniya.
*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*
*ZAFAFA BIYAR*
*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA
ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*
_DUNIYATA Huguma_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
*09033181070*
89825722
1000cf
*D U N I Y A T A*🌍
*_H U G U M A_*
*Arewabooks:Huguma*
Page 03
https://chat.whatsapp.com/CKY0xZDtpby6MTkGrPkXLr
______________________________
Yana riqe da hannunsa tsam cikin nasa cikin tausayi da nuna kulawa. Yayin da yake biye dasu a
baya,rungume da kayansu jikin qirjinsa, wanda ke dauri a wani yalolon mayafi.
Duk taku daya yana yinsa ne tare da bugawar zuciyarsa,wani irin shakkun shigarsu gidan yana
mamayar zuciyarsa,dukkan sarewa da kuma rauni tare da rashin tabbas suna cikashi. Daidai sanda abban
ya waiwayo a nutse,lokacin da suka kawo bakin gate din gidan.
Murmushi ya sakar masa a hankali da mufin kwantar masa da hankali,ya fahimci akwai anunuwa
da yawa dake kai komo a zuciyar yarin game da shigarsa gidan. Shigarsa gida wani tsohon labari ne daya
jima da shudewa,a qalla shekaru kusan biyu cur kenan yanzu ake magana.
"Ka saki jikinka,hakan shine zai sanya dan uwanka shima ya saki jikinsa,ka dauka a ranka tamkar
mahaifinku ne ya dawo,zan zame muku uba bango kuma majingina muddin numfashi yana yawo a
gangar jikina,kasa a ranka a yanzun baku da sauran matsala ko maraici kaji?" Abba ya furta yana dora
hannunsa saman kanshi,qauna da tausayinsa yana ratsashi.
Ya jima yana kallon yaron a mabanbantan ranaku lokutta da kuma gurare cikin unguwar. Ya
jima da sanin cewa yaron ya fita daban cikin sauran yara,komai nasa na dabanne,nutsuwa da hangen
nesansa kawao zai sanya kayi tunanin ya girmewa shekarunsa. Bai taba ji ba,bazai kuma taba iya tuna
wani lokaci da yaji wani yayi kusa dashi cikin unguwar bisa rashin gaskiyarsa ba,muddin kaji wani koke a
kansa to lallai ba shakka taboshi akayi,an shiga gona ko huruminsa.
Duk sanda ake irin wannan case din a mafi yawan lokuta yana tare da mahaifinsa,yakance
"Ka barni nayi masa hukunci koda shine da gaskiya,ya cika zafin rai,ya fiya taurin kai da kafiya,wannan
duka ba dabi'u bane masu kyau,ya kamata ya sauya saboda rayuwa".
Murmushi abban yakan saki,ya kuma maida dubansa ga fuskar yaron kafin ya bawa mahaifinsa
amsa
"Ka godewa Allah,ba'a taba kawo maka qararsa akan rashin gaskiyarsa ba,koda kuwa an kawo qarar zaka
sameshi ne ame gaskiya,shin me kake nema ko fata sama da haka?". Mahaifinsu mutum ne me tsananin
kawaici,kanshi kawai yake kawarwa yana murmushi. Abban ya wuce komai a wajensa,maqoci ne me
nagartar da samun irinsa yake wahala,don haka ne yake bashi dukkan girma,ba kuma wai don arziqi ko
dukiyan daya mallaka ba,a'ah,don kawai ya cancanci hakan.
"Kana jina?" Abba ya sake fada don maido hankalinsa kansa,sai ya gyada kansa a nutse shima yana
duban abban
"Yauwa,muje ciki,dukka su saddiq ma suna ciki na tabbatar yanxu" Bai musa ba yayi gaban abban yana
biye dashi yana tsokanar dan uwan nasa daya sake sosai,farinciki ne ma kwance akan fuskarsa,da alama
quruciya da rashin sanin cikakken ciwon kai ya sanya ko kusa ko alama baya hasashe ko hangen abinda
kan iya faruwa,ko a kusa ko a nesa,me kyau ko akasinsa a kansu da rayuwarsu dama DUNUYARSU gaba
daya.
Ci gaba sukayi da tattaki cikin harabar gidan,yalwatacciyar haraba dake shimfide da interlock. Kana
ma gidan kallo daya zakasan akwai sukunin rayuwa a cikinsu,duk da ba zaka kirayeshi da wani
MAHAUKACIN ME KUDI BA amma tabbas yana cikin jerin MASU KUDI ARZIQI DA WADATAr daya tserema
neman komai na biyan buqatar rayuwa,kamar yadda ya tserema RASHI ya masa tazara irinta HAIHATA
HAIHATA.
"Bude mana" Abban ya furta sanda yaga yaja ya tsaya ba tare daya buda qofar falon da zata sadaka da
ainihin cikin gidan gaba daya ba. Matsawa yayi gaba kadan,ya murda qofar ya kuma tura,sannan ya saka
qafafunsa cikin falon dake gauraye da sanyin Ac.
Ita dince dai,itace mace ta farko da idanunsa suka fara tozali da ita. Bai sani ba,tsabar yadda ya
washeta ne,yake kuma qyamatar shiga cikin dukkan lamuranta ne kamar yadda take nuna qyamata da
qin jininsu qarara a fili?,wannan shi ya sanya ta zama mutum na farko daya fara gani?.
"Kai dakata!,ina zaka je?,wajen wa kazo?,wai ban hanaku shigowa gidan nan haka gaba gadi ba kamar
gidan tsohonku?,me ma ya kawowa da wasu tsummokara a hannu?"
"Nine na kawoshi" Abba dake bayansa ransa na quna da jin kalamanta ya furta. Sak ta danyi,duk da
bawai ta razana bane da jinsa,sai tsabar baqinciki da kuma zato daya soma zuwa ranta
"Lallai kawai bala'i cikin gidan nan" Ta raya a ranta tana sake tattara dukka girarta waje daya ta
hade,babu rahama ko qanqani saman fuskarta.
Yaron dake zaune a rakube daga qasan carfet din ya sake tattare jikinsa waje daya,alamu dake
bayyana lallai ya shiga taitayinsa da sauyawar yanayin nata.
"Laaaaa......kaine kuma yau?ashe zaka sake shigo mana?" Yaron dake fitowa daga kitchen din gidan ya
furta,fuskarsa na juna tsantsar farinciki,kamar yadda ya bada dukka hankalinsa akan wanda ya jefawa
tambayar,hannunsa dauke da tray,daga hannun nasa har zuwa qafafunsa ya tattare bakin wando da
kima rigar tasa.
"Kai me yasa baka da hamkali ne?,zaka zo ka ajjiyemin ko kuwa?" Hamshaqiyar matar dake zaune saman
kujerun falon ta sake ma yaron tsawa,wanda tamkar ma ya manta da abinda ya fito dashi daga kitchen
din,kaf hankalinsa ya tafi ga baqon yaron daya shigo din,wanda a idanu shekarunsu tamkar daya suke.
Juyawa yayi xuwa gareta don aje mata tray din,hakan bai isheta ba ta bishi da wani mummunan
kallo,idanunta kamar zasu ciro su fado qasa
"Shashasha,kamar wani wanda yaga qanin ubansa,sai nayi maganinku" Ta furta cikin fushi. Daga baya
baya kadan ya ajiye tray din yana fatan kada hannuwanta yakai kansa,duk da yasan hakan zaiyi wuya,ko
don wanzuwar mahaifinsu a wajen
"Musaddiq......maza karbi kayan hannunsa ku wuce dakinku dukkanku" Zumbur yaron dake a zaune
rakube tsakanin kujerun ya miqe. Bai jira kowa ba a cikinsu yayi hanyar dakinsu,saidai yana tafe yana
dan waiwaye.
A sanyaye ya sakarwa musaddiq kayan hannun nasa,yana qoqarin maida masa martanin
murmushin da yaketa faman yi masa tunda sanda yayi tozali dasu
Bai musa ba ya soma bin bayansa,don zamansa a falon yayi imanin sam bazai yiwu ba koda abba
bai basu umarnin wucewa ciki ba.
Zazzafa kuma tozartaccen kallo take binsu dashi,zuciyarta na mata wani irin suya,bacin rai da
takeji kamar zata yi aman zuciyarta.
Debe idanuwanta tayi daga kansu tana jan qaramar qwafa qasan zuciyarta,ita daidai take
dasu,babu wanda ta shirya bari ya takura rayuwarta ko ya quntata ta.
Duk wani motsi nata yana karance da ita,har zuwa sanda ya daidaita zamansa saman kujerar
sannan ya dubeta yana kiran sunanta
"Ga yara nan na kawosu,yara ne kuma da kin sansu bawai baqi bane a wajenki,kin kuma san basu da
wata matsala ko aibu ko wani abun fada cikin unguwar nan......alqawari ne da na yiwa kaina tsakanina da
ubangijina,na kuma cika alhamdulillah,ina fatan zaki tayani riqesu bisa amana ko don maraicinsu".
Wani kallo takeyi masa ranta cike fal da mamaki,ta karkace tana dubanss tare da tattara abinda
zata ce masa
"Yanzu bayan naka yaran har yaran maqota kakeyimin kalensu?" Ta aje maganar tana jin zafi cikin ranta
da zuciyarta. Tana jin ta quna bata tsoron qauri,ta soma gajiya ta kuma soma qosawa tare da debe haso
hadi da tsammani na samun shimfidaddiyar rayuwar data jima tana mafarki gami da shimfidawa cewa
zata samu cikin gidan.....
*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*
*ZAFAFA BIYAR*
*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA
ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*
_DUNIYATA Huguma_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
*09033181070*
89825722
1000cf
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
*Arewabooks:Huguma*
*PAGE 04*
A nutse ya daga kai ya watsa mata wani irin kallo. Yau ta fara fadin hakan,amma kuma ya dade
yana karantar hakan daga dukka ayyukanta da motsinta.
"Nayi tunanin akwai dattako fahimta da kuma qaunar juna a tsakaninmu da har yarana sukafi qarfin kice
riqonsu kikeyi,na zaci cewa kina ji a jikinki da zuciyarki kina rainkn 'ya'yan da kika haifa ne a cikinki?"
Wani abu ne yazo yayi mata tsaye a wuya,ta juya kanta gefe guda tana tattaunawa da zuciyarta kan
"Har abada 'ya'yan riqo ba 'ya'ya na bane,'ya'yan wasu ba zasu taba zama 'ya'yana ba.....banda qaddara
me zai hadani da riqon 'ya'yan wasu?" . Idanunsa a zube fes a kanta,ya gyara zamansa sosai yana sake ci
gaba da kallonta
"Inaso ki cire a ranki riqo kikeyi.....ba 'ya'yana na cikina bama.......hatta yaran dana kawo yanzu,inaso ki ji
a ranki Tamkar suna rayuwa ne cikin gidan mahaifinsu a gaban uwa da kuma ubansu". Dukka haqurinta
ya qare,ya tuqeta ta kuma kai bango,tana jin ba zata iya ci gaba da zama tana sauraronsa ba,don haka ta
miqe tsam,ta kuma gegara ta gabansa tana barin falon.
Da ido ya bita har zuwa sanda take shirin bacewa ganinsa. Ya jima yana ganin alamun da suke
alamta masa akwai matsaloli masu yawa cikin rayuwar su farouq,amma yayita qaryata hakan gudun
kawo damuwa da matsala cikin zaman uwar wani da d'an wani wanda keda wuyar sha'ani,sai gashi a
qanqanin lokaci komai yana bayyana kansa daki daki.
Numfashi ya zuqa ya fesar yana rufe idanunsa,qoqari yake ya saita kansa yana tunanin hanyar
da zai daidaita komai.
Tray din da faruqee ya ajjiye yabi da kallo,a dawowarsa daga lagos wannan karon ya fahimci
kamar ma suke yiwa kansu girki harma su hada da ita idan ta kama,babu sakewa babu walwala sam
tattare dasu. Ya lura da raguwar kuzarinsu kyara da kuma hantara daga gareta,saidai dukka ya kauda kai
don bai kamaci a karon farko ya fidda soyayyar yaransa kai tsaye daga zuciyarsa har haka ba,bayaso
yabar wani tabo ko targaden da zai kasa gyaruwa tunda wurwuri haka.
Da idanu kawai yake bin dakin da kallo sanda Faruqee yaketa masa bayani zuciya da fuskarsa cike
da zumudi da farinciki.
"Kayi shuru?,ka tsaya a bakin qofa,ko dakin baiyi bane na gayawa abba a qaro wasu abun?" Faruqee ya
fada jikinsa yana sanyaya da yadda yaga fuskarshi. Don a yadda ya zata zayaga farinciki sosai a fuskarsa
kaman kwatankwacin nasa farincikin na dawowarsa cikin gidansu,farincikin samun aboki me hankali
irinsa,farincikin samun aboki da yayi daidai da shekru da hankalinsa,ba aboli irin qaninsa ba da sam.baya
gane wsu abubuwan saboda sabanin mizanin hankali da fahimta dake tsakaninsu.
Karon farko yayi qoqarin sake fuskarsa da kyau yana kallon faruqee. Dakin gata kuma dakin yaran
gata irin wannan da shi din bai taba samun kwatankwacinsa ba ta yaya zaice baiyi masa ba?. Dukka alatu
da yayi saura a dakin bashi yake daukarsa ba.......duk da qarancin shekarun daka iya dakusar da tunanin
yaro a sannan......amma shi sun bawa qwaqwalwarsa damar budewa da yin tunani me nisan zango akan
"Wacce irin rayuwa zasu fuskanta a matsayinsu na agola bayan su kansu tsatson gidan basu tsira
ba?,mene ne makomarsu?,meye farko da kuma qarshensu?" Tarin tambayoyin da baisan ta ina zaa fara
sauke masa su ba
"Nayi murna farouq" Ya furta a sanyaye,sunan da shi daya yake furtashi daidai yadda yake,don har yau
bai taba kiransa da faruqee ba.
Yadda qanin nashi ya zuba masa idanu ya sanyashi qoqarin sakewa,ya qaraso ainihin cikin dakin
kamar yadda sauran suka kai ga shigowar.
Qoqarin kauda komai ya dinga yi daga zuciyarsa,yana zaune daga falon yana iya jiyo muryoyinsu
sama sama,saidai har yanzun baiji tashi muryar ba. Baiyi mamaki ba,don ya sani,yadda komai nasa ya fita
daban daga cikinsu,haka dabi''arsa da halayyarsa ma ta zama daban.
Abincin yaja ya soma ci bawai don cin abincin yana masa dadi ko yana burgeshi ba. Tunaninsa
yayi zurfin da har ba komai dake wakana cikin falon yake ganewa ba,bai taba zata ba,bai kuma taba
kawowa rabuwa da rabi'atu zai iya zame masa qalubale ba sai yanzun da dukkan alamu suka fara
bayyana kansu. A karon farko har yaji ya fara tuhumar kansa da kansa,tare da nacin son gano meye
ainihin laifin rabi'atu ne har ta cancanci a saketa?.
Baici da yawa ba ya ture,ya miqe yana irgen lokaci,sai ya juya ya fara takawa zuwa dakin yaran.
Dukkansu sunyi shirin bacci amma bandashi,yana zaune gefe daya na gadon farouq,ya goye
hannayensa a qirjinsa tamkar wani babba da yayi nisa cikin nazarin wani abu.
Motsin abban ya sanyashi waiwayowa,da sauri ya sauke hannayensa yayi qasa da kansa yana
niyyar zamowa daga saman gadon
"Yi zamanka me babban suna......tunanin me ka zauna kana yi?,duk 'yan uwanka sunyi shirin kwanciya
banda kai?" Farouq dake zaune tsakiyar gadon yayi hanzarin karbar maganar dama tana damunsa tun
dazu
"Abba yaqi ya canza kaya,na bashi kayan bacci yaqi ya saka tun dazu" Hannu kawai abban ya miqawa
farouq din,sai ya saka masa kayan baccin dake gefansa.
Kayan abban yabi da kallo yana jujjyasu a hannunsa,sannan ya maida dubansa zuwa jikinsu
dukka su ukun dake sanye da wasu kalolin kayan.
"Amma faruqee ban gaya muku a bada kayan nan ba dukansu?,ina kayan dana kawo muku wancan
tafiyar da nayi?" Ya qarasa tambayar yana maida idanunsa kan saddiq qaninsa.
Har wani juyawa saida cikin saddiq din yayi,saboda tunawa da yayi da kakkaifan warning din da
suka samu daga wajen matar gidan akan batun.
"Abba,dukka mama ta karbesu,ta kuma gargademu kada mu sake mu sanar dakai,idan ba haka ba saita
tsoma kawunanmu a ruwan zafi" Ba abba kawai ba,hatta me babban sunan saida maganar ta ratsashi
duk da qananun shekarunsa,amma zuwa yanzu ya dade da yiwa kansa karatun qalubalen da suke shirin
fuskanta
"Ruwan zafi?" Abba ya furta cikin tsananin kaduwa da mamaki,sai faruqee ya gyadawa abban kai.
Maganar ta ladabtar d abba ta sanyashi samun waje ya zauna. Yana tsoron ci gaba da wannan tafiyar
tasu......yana tsoron garin neman lada ya rufta ya buge d wucewa jahannama,ya debo marayun Allah da
nufin basu rayuwa me inganci,muddin Mariya bata goya masa baya ba meye makomar yaran?,ya
gobensu zata kasance?. Tambayoyin da suka dinga karafkiya kenan a kansa.
Indai haka ne ya zama dole yayi jan ido,ya zama dole yayi wuta wuta akan gidansa da iyalinsa. Ya
sauke dukka nauye nauye haqqunan da suka zama wajibi dama wadanda basu zama wajibi bs,ya zama
dole to itama ta bishi yadda ya kamata.
"Ba komai,tashi me babban suna ka shirya,idan kun kammala ku kashe kayan wuta gaba daya kuyi addua
ku kwanta" Yayi maganar ne yana sake nazartar dakin tare da kallon guraben da ga siya ma yaran
abubuwa da dama ya ajjiye saboda jin dadin Rayuwarsu a yanzu ba komai a wajen sai gurbinsu.
Sai daya kammala komai daga ainihin dakinsa sannan ya zarce dakin mariya. Ta gama shirin
kwanciya tsaf tayi rub da ciki tsakiyar gado tana latse latsen waya. Fuska a hade ta daga kai ta kalleshi
sau daya saita dauke kan nata ta maida ga wayarta tana sake tsuke fuska.
"Tashi zamuyi magana" Ya fada cikin yanayin dake tabbatar mata da gaske yake,da kuma zafinsa ya
shigo. Sai da tayi kamar ba zata tashi ba sannan ta miqe ta zauna sosai tana gyara wuyan rigar baccinta
tare da tsuke fuska da kyau.
*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*
*ZAFAFA BIYAR*
*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA
ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*
_K'ALBIM Mamuhghee_
_DUNIYATA Huguma_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
*09033181070*
89825722
1000cf
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
*Arewabooks:Huguma*
"Asama'u" Ya kirayi sunanta da wani irin yanayi da har cikin zuciyarta ta tabbatar cewa......dukka
maganar da zata gita yanzu haka daga bakinsa ,yankakkiyar magana ce wadda babu janyewa a cikinta ko
kuma wani sauyi bare sassauci
"Ban rabu da mariya ba don na auro wata matar tazo ta azabtar min da 'ya'ya ba,ina tsananin qaunar
'ya'yana fiye da soyayyar da nake yiwa kaina,duk soyayar da zaki gwadamin bata da alfanu rana ko kuma
fa'ida a gareni muddin ba zaki so 'ya'yana ba......asama'u,na rantse da Allah,dai dai da rana guda na samu
wulaqanci cin amana ko tsanantawa diyoyina bisa ganganci bawai kuskure ko ajizanci irin na dan adam
ba bazan raga miki ba"..... Wani dum taji har tsakiyar kabta,batabtaba kawowa dukka maganganunsa
zasu kai har wannan iyakar ba,bata tana tsammanin abun yayi zurfi haka haka ba,da ake gaya mata yana
da son yara batabtaba kawowa yakai har wannan bigiren ba.
Zuwa sanda zatakai qarshen tunaninta shi din ya jima da miqewa yana kallonta
"Bazan fasa tafiye tafiye na wajen neman halak da neman abinda zan rufawa kaina da iyalina asiri
ba......ba kuma zan kwashe diyoyina na kaisu wanin guri ba,gaki gasu nan asamau,dukkan abinda kika
qudirta yi kada ki fasa koki sauya ra'ayi" Ya qarashe fadi yanajin wani irin daci saman harshensa,bai
kuma dakata ya saurareta ba ya juya a nutse yana barin dakin nata.
Har sanda ya bacewa ganinta bata dauke dubanta daga bakin qofar dakin ba,ta qanqance idanu
tana kallon qofar tare da jin dacin kalamansa suna gauraya kowanne sashe na jikinta. A taqaice dukka
bayanansa suna auna mizani da kuma adadin iya matsayinta kenan a wajensa?. Bata shigo gidansa don
ta fita ba,don muhallin dame muhallin duka sunyi mata,amma kuma bata shigo bautar d'an kowa
ba,hakanan bata shigo don a takata ko aci mata zarafi ba bare kuma a hanata sakewa.
Shawara take buqata kawai a yanzu hala,don gaba kura ne baya sayaki,ta kula dasu ko ta barsu
komai ta fanjama fanjam?,to amma fisabilillahi zai yiwu kuwa ace ta buge da bautar d'iyoyin da ba ita
tayi Jigilar daukar ciki da kuma rainonsu ba?.
Matsawa tayi kusa da wayar landline dake gefan gadonta,ta latsa lambobi tana fatan sashen
kamfanin sadarwar ya sadata da matar data kira take mararin magana da ita. Ba'a dauki dogon lokaci ba
sukayi mata hakan,saita qarasa sauke dayar qafar tata qasa tana zama sosai yadda zatafi jin dadin
amayar da abinda ke cikinta.
Yanayin yadda suka gaisa kadai zai gaya maka akwai shaquwa me zurfi da tsohuwar sanayya a
junansu.
"Ya nake jinki haka sama sama?" Daga saya bangaren ta tambayeta. Sai data aje dogon tsaki sannan ta
fara magana,zuciyarta cike da wannan bacin ran da batasan ranar da zai wanke daga zuciyarta ba
"Barni kawai......dukka shirina har yanzun bai tafi a yadda na jima ina tsarawa ba"
"Wani abunne kuma?" Kai ta rausayar tana jin kamar ta qifta idanuwanta ta budesu ta tarar babu kowa
tsakiya da gefannin rayuwarta da mijinta,daga ita saishi
"Yarannan haleema......bayansu ya sake kwasomin riqon marayu,bayan wadannan din har yanzu ban
gama da matsalarsu ba......" Daki daki ba tare data rage komai a abinda yake faruwa ba ta shimfida
mata,sannan ta dora da fadin
"Inajin kamar naje gurinsa ayita ta qare haleema,na meye zaa dinga doramin nauyin da bai zama wajibi a
kaina ba?" Ajiyar zuciya haleeman ta sauke
"Ashe qarya kikeyi,baki shirya zaman auren ba" Haleema ta katsi numfashinta sanda taji tana shirin sake
dorawa da wata mitar
"Kamar yaya?,ya zakice haka bayan kinsan komai?" Ta tambayeta tana tsuke gira tare da mamakin
amsar data bata
"Eh to ai dole nace haka,wani lokaci sam baki da wayo asama'u,yaransa biyu da yake mutuwar so ki gaza
riqesu?,bakisan ta hanyar riqon da zaki musu bane zaki samu fiye da abinda kike hange ko hasashe daga
jikinsa?" Ta qarashe maganar da sigar tambaya,tambayar data dauki dukka tunanin asama'u ta jefashi
wani guri me nisa
"Amma haleema,saina zama baiwar yara har hudu?" Ta yiwa haleema tambayar tana jinjina girman
abun,tamkar wadda aka dorawa nauyin wanke kashinsu da fitsarinsu gami da ci dasu tsahon kowacce
rana da wuni na rayuwarta
"Bance haka ba,ban kuma goyi bayan hakan ba,yaransa sune dolensa,su zaki kama ki riqe,saura kuwa
wannan baida hurumin tilasta miki zama dasu,idan ma baki riqesu ba bakiyi laifi ba,kedai yaransa su
zama makamin zamanki a gidan,yo asama'u kona ganin ido ne ke ba zaki iya ba?.......".
Dadewar da sukayi saman waya sa haleema iya adadin karatun data samu daga gareta,ta kwanta
ne tana juyawa tare da tauna yadda zata dauki shawarwarin haleema tayi aiki dasu,ta yaya zata danne
zuciyarta da dukka wani abu da takeji tayi yadda haleema ta kwatanta mata?.
*_W A S H E G A R I_*
Dukka su hudun suna zaune a gabanshi,yana jansu da hira cikin yanayin da zakayi tsammanin shi
din wani babban yayane a garesu bawai uba ba.
Da idanu yake karantarsa,har yanzu dai bai sake ba kamar yadda ragowar 'yan uwansa uku suke
a sake. Har yanzu a darare yake,dararewar data sanyashi yaji a ransa akwai abinda ya hanashi sakewar.
Har cikin rai da gangar jikinsa a yanzun da suke gabansa yake jin kamar dukka su hudun
mallakinsa ne,shine ya haifesu. Inda yana da iko tabbas zai maida agogon rayuwarsu baya ya mantar da
al'ummar da suka sanshi dama na unguwar cewa shi din ba shine ya haifesu su biyun ba.
Tun daga nesa da take takowa cikin falon idanuwanta yake kansu. Sunyi wanka dukkaninsu sun
kuma shirya cikin shaddodinsu masu kyau,wadanda tayi imani cikin sabbin kayan daya saba tahowa da
yaranne. Sake maida idonta tayi a kansu,a nutse yake qwarai fiye da dan uwansa,ba wani karsashi a tare
dashi ko kuma rawar kai,saidai kuma haka siddan takejin muguwar matsananciyar tsanarsa shi da dan
uwansa.
Ta yaya tun bata aje nata yaran ba ace wasu yaran sun shigo sun sake cinye gurbi da muhallin
mutum biyu bayan gurbin mutum biyun da yaran gidan suka cinye?. A yanzun idan har ta soma aje nata
yaran kenan saidai su tashi daga na biyar?,ya za'ayi ta bari haka ta kasance?.
Sai data iso dab dasu sannan ta iya controlling kanta tayi sallama. Dukkansu suka daga kai suna
dubanta banda abba da ya kauda nasa kan kadan gefe don da haushinta ya kwana.
Qoqarin gaidata sukayi,ta amsa tana binsu da kallo daya bayan daya,wannan ya sanya kowa ya
sake kama kanshi a cikinsu,bansa me babban suna wanda tun daga kallon farko bai sake daga kansa ba
bangaren da take.
"Ina kwana abba?" Ta gaidashi cikin matuqar qoqarin daidaita kanta idanunta zube kan kayan breakfast
dake gabansu.
"Lafiya lau" Ya amsa mata a taqaice yana rufe plate din fried egg din daya gama ci.
"Yau nayi bacci me nauyi ban samu tashi na hada abincin safe ba"
"Eh laraba tayi.......don dama fita nakeso muyi" Ya amsa mata yana miqewa.
"Ina haka da safiyar nan?" Tayi masa tambayar cikin son sanin komai
"Makarantarsu Faruqee,inason na yiwa su me babban suna registration,next week idan Allah ya kaimu
su koma tare baki daya" maganar tayi mata kama da almara ko kuma ba zata. Tana tantamar akwai
hikima ko hankali kuwa cikin maganganun abban?,ta yaya zai dauki yaran maqota ya kaisu makaranta
me kudade masu ciwo haka?,makarantar dako yaran cikinsa da taji nawa ne school fees dinsu saida taji
kishi da baqincikin abun?,ta kuma bashi shawara a fakaice ya kusa sau biyar akan ya sauya musu da
wadda bata kaita ba.... Ko don yadda shima wani lokaci ta lura kaman yawan school fees din yana dan
takurasa?.
Abinda ya darsu a ranta me girma ne,tana da abubuwan da takeson ta fadi masa amma girman
bacin rai da kuma abinda ya tsaya mata a wuya ya hanata cewa komai har suka tarkata suka fice daga
falon.
Idan nace ta samu nutsuwa tun daga fitarsu har dawowarsu to zance ne kawai. Sanda suka tashi
dawowa din kuma sun dawo da dukka tarkacen kayan amfani na buqatar rayuwa na yau da kullum.
Komai hurhudu ya siya,amma kaf cikin siyayyar bataga tsinke nata ba
"Somin tabi kenan hatsin gara a buta......tun yanzu?" Wani sashe na zuciyarta ya ayyana mata. Ai juma'ar
da zatayi kyau tun daga laraba ake ganeta. Tun a rana ta farko ta soma karantar iyakokinta?,dukka kuma
akan yaran da suka kasance tamkar wata tsintacciyar mage?. Yaran da basu da GATA ASALI ko wani
GALIHU?. Ita kuwa asama'u yaushe?,yaushe zatayi wannan SAKEN?. Muddin bata bazama su ba lallai
anyi asarar haihuwarta,muddin bata ganar dasu kuskuren maida UBAN WANI NASU BA bata cika MACE
BA....
*_GWANA KUMA QWARARRIYA WAJEN SACE ZUKATA DA ALJIHUN MAZAJE DAMA ASUSUNSU GABA
DAYA_*
*DUNIYATA(MUHAMMAD JADDA)*
*DUNIYATA(SABREEN)*
_GA HANYA MAFI SAUQI DA ZAKI KASANCE DA ZAFAFABIYAR FAMILY IN SHA ALLAH_👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾
*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*
*ZAFAFA BIYAR*
*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA
ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*
_K'ALBIM Mamuhghee_
_DUNIYATA Huguma_
_Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
*09033181070*
1000cf
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
*Arewabooks:Huguma*
Page 06
___________________________
*_TURQASHI_*
*_TURAREN WUTAR DA ZAKI SANYAWA DAKI AMMA HATTA DA LABULAYE KAYAN SAWAN DAKE SAQALE
A DAKIN SU KAMA DA QAMSHI?_*
Khumra
Turaren wuta
Kulaccam
Lablab
Oil perfumes
Multipurpose spray
*karki kuskura kada kiyi ganganci ayi babu ke,kai tsaye tuntubeta ta wannan number*
08032119803
Ko ki lalubeta ta nan👇🏾👇🏾👇🏾
*Facebook_kabo daughter*
*Twitter_kabo daughter*
__________________________
Tayi zaune kawai saman kujerar falon tana duban kowa d'ai d'ai da yadda yaran keta walwalarsu
da sabgoginsu. Ta yita juya zancan haleema a ranta,anya zata iya kuwa?,zata iya jurewa?,daga bisani
data tabbatar muddin taci gaba da zama a wajen zata karya dukka tsarinta saita yunqura kawai ta miqe
tana bar musu falon.
Cikin satin ya tabbatar yayi musu dukkan abinda ya dace,ya kuma sauke duk wani abu da uba zai
saukewa 'ya'yansa,tun daga suturunsu xuwa takalmansu,kayan makaranta hadi da jaka takalmi da duk
wani abu daya zama dole ga dan makaranta.
Zai iya cewa Kansa da kansa sauyi ne na dare daya yazo cikin rayuwarsu,duk kuwa da cewa har
yanzun.....daidai da second dayahasashe,koda da wasa irin na qwaqwalwa zuciyarsa bata taba hasashen
ta manta da abubuwa guda ukun nan da suka shafi rayuwarsa ba......suka shigeta da wani irin
yanayi,yanayin daya tilasta canzawar zubi da kuma tsari na dukkan feeling na zuciyarsa da gangar jikinsa.
Abbansa
Jadda
Da kuma uwa uba mahaifiyarsa da zuciyarsa ke mata wani irin bahagon kallo.
Halitta mafi girma da daraja cikin rayuwarsa......amma kuma dukkan wani matsayi da girman suna
da halittar ta mallaka baya jinsa ko dis cikin jininsa da zuciyarsa.
Eh tabbas......a tsukin kwanakin rayuwarsu tayi wani wawan sauyi,saidai nashi sauyin ya tsayane
cak iya zahirinsa. Darare da yawa suna wucewa cikin idanunsa. Alfijir dake cikin kowacce asubahi da
Ubangiji ya halittama kwanakinmu sun sha ketowa ta cikin qwayar idanunsa. Ta tsakiyar qwaqwalwarsa
yana jin kamar an tsatssagarta da wani abu me kaifin tsini
"Me yasa maama taqi zama damu?,me yasa ta kasa jurewa lalurar Abbey?"
"Saboda bashi da komai yanzun,saboda shi talaka ne" Amsar da kullum yakeji ana rada masa kenan cikin
kunnuwansa. Sau tari yakan sanya dukka tafukan hannayensa ya toshe qofofin kunnuwansa wai ko zasu
daina jiyo masa wannan amsar......waiko amsar tambayarsa zata iya sauyawa?.....saidai aah,koda wasa
bai taba jin amsar nan ta sauya ba. Tun baya daukar gaskiya ake rada masa ana kuma sake jaddada masa
har zuciyarsa ta gamsu da hakan.
"Indai haka ne maama ita tayi silar mutuwar Abbey......indai haka ne maama itace tayi ajalin jadda"
Abinda yake gayawa kansa kenan a duk sanda ya kalli fuskarsa dake dauke da qananun shekaru
"Amma ta yaya ta kashesu?" Tambayar da daya kasa lalubo amsarta,saidai yasan koda duniya zata taru
ta hanashi wannan tunanin bazai taba kankaruwa daga qwaqwalwarsa ba har ABADA.
*******
Safiyar litinin ce dake dauke da yawaitar hazo da kuma lullumin sanyi daya soma tun a daren
shekaran jiya. Cikin dakin nasu a cikin su hudun kowanne shirin tafiya makaranta yake yiwa kansa don ba
wanda baya iya yiwa kansa da komai da komai a cikinsu,daga su Faruqee da suke 'yan gidan,har su da
suke baqi ko kuma ace 'YAN RIQO. Kusan za'a iya cewa banbancinsu dasu Faruqee din shine,mamarsu da
babansu dukkansu suna a raye,sannan komai tsanani suna da gatan dangi da kuma muhallin da zasu
kwana a ciki. Amma ta fuskar samun cikakken gata da kulawa na iyaye,sun tashi kusan a mizani guda,don
sun rasa kaso tamanin a cikin dari sanadiyyar RABUWAR AUREn mahaifansu.
"Ya kamata kayi ka gama,wannan laqai laqai din naka ba abinda zai haifar mana sai bata lokaci,kasan dai
abba ya koma a motan haya zamu je yau" Faruqee dake saba school bag dinsa yace da saddeq dake
kurba shayin da Faruqee ya hado musu dukkansu suka gasa cikinsu.
Kusan ya zame musu jiki,duk randa mahaifinsu ya sanya qafa ya koma Lagos lunch box dinsu
yakan koma hoto,zancan breakfast kuwa saidai da tsananin rabo Faruqee ya faki idanunta ya hada musu
tea susha su wuce kaman yau. Tasha kamashi bayan anyi hakan,tasha gargadarsa amma a banza wai
man kare,gobe ma sai ya qara. Tun tana hukuntashi ta hanyar duka har yakai shekaru sha biyar. Tayi
niyyar masa wani wawan duka,amma da yake ance qashin namiji dana mace ba daya bane saita samu
targade a hannun nata madadin shi yaji rauni.
"Alhakina ne". Hakanan taji jiyyar hannun nata ba tare da kowa ya sani ba. Tun daga ranar ta canza kalar
horo,saita hadashi da aiki me tsanani,kota hanasu abinci a ranar gaba daya. Irin wannan horon yafi mata
dadi idan ya zamana abba baya gari,idan kuwa yana nan abubuwa da dama saidai tayi haqurin dole ta
tarasu sai randa ya wuce.
Ba wanda gabansa bai fadi ba cikin su ukun bayan ratsowarsu ta falo da zummar fita daga gidan
idan ka dauke me babban suna da ya dauke idanunsa daga kanta tuntuni.
Qafarta daya saman daya tana karkadata a hankali,kamar yadda ta zube musu idanunta tana
binsu da kallo kamar qwayar idanun nata zasu zuba a waje.
A darare dukkansu suka gaidata,saidai idanunta suna kanshi ganin yadda ya gaidata hankali
kwance,sam kuma kwata kwata babu wannan razani da kuma d'ar d'ar dake kwance a fuskokin 'yan
uwansa dake takawa cikin sanda suna fatan wucewa daga falon lafiya.
"Zo nan dan qaruna!" Ta furta da wata kakkausar murya tana sake jin haushi da tsanar yaron. Dukkansu
suka waiwayo,ta sake binsu da ido
Ba wanda ya musa mata suka tako dai dai da dai dai suka zube saman carfet din
"Kai don ubanka waye yace ka shiga kitchen ka taba madarar gidan nan?" Ta jefawa Faruqee tambayar
tana watsa masa zagi da hannayenta.
Kiran uban da tayi shi ya sauka har tsakiyar zuciyarsa ya sosata. UBA wani abu mafi daraja da
yake ganin kimarsa cikin DUNIYARSA fiye da uwa,ubansa da kuma ABBAN Faruqee mutane biyu da basu
da tamkar da bayajin zai iya jurewa zaginsu. Idanunsa ya maida ya lumshe yakuma yi qas da kansa yana
hadiyar wani abu me tauri da zafi tamkar shi mama ke tambaya. Wai haka iyaye mata suke ne marasa
tausayi?,marasa imani?,me yasa iyaye maza yaketa gani da tambari da dukka wani tabo na tausayawa
'ya'ya?,me yasa kalmominsu suke tsauri akan 'ya'ya cikin rashin tausayi da kyautatawa?.
"Makaranta zamuje,kuma yunwa mukeji"
"Ubanka nace......saboda ubanka ne ya kawo madarar shine kake ganin kana da right na shigarmin
kitchen yadda kakeso?"
*_kusa kurai da zaa gani a ciki ajizanci ne irin na dan adam,da fatan za'ayi afuwa a kau da kai_*
*_Don Allah don Allah ina roqo da fatan zaku zama masu uzuri a gareni,saboda yanayin sabgogin
rayuwa,kowa ya sani yau da gobe tana iya sauya bawa daga ainihin yadda aka sanshi_*
*_duk sanda kuka samu wani sauyi tattare dani game da tsaiko na posting,tsahon pages da sauransi,ina
kyautata muku zaton soyayyarku gareni zata sanya ku zama masu yimin uzuri_*
*_ina godiya qwarai game da yadda bakwa gajiya da bibiyata,da bibiyar zafafa biyar gaba daya_*
*_alkhairin Allah yakai muku a duk inda kuke,tare da fatan ubangiji zai tsareku kuma daga dukkan
abunqi_*
*_na gode qwarai,kuma in sha Allah a duk sanda dama ta samu zaku samu komai fiye da yadda kuke so
ma cikin wannan tafiya ta DUNIYATA_*
*_LABARIN ZAI TABO BOYAYYAR MATSALAR DA MUKE FAMA DA ITA,na muku alkawarin nishadi da
sassanyar soyayya kan bigiren salon da kukafi so😍_*
*HUGUMANKU CE*
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
*Arewabooks:Huguma*
________________________
Page 07
Dif sukayi dukkansu,ba wanda ya iya tanka mata a cikinsu. Daga can qasan zuciyarsa yake jin wani
irin zugi fushi da kuma radadi,don meye zata dinga zagin iyaye a gaban 'ya'yansu?,shi abban me yayi da
har ya cancanci a zageshi?.
"Badai makaranta zaku ba?,ku tashi ku bacemin da gani". Kaman dama suna jiran wannan umarnin ne
daga gareta dukkansu suka miqe din kusan lokaci guda,kowa yana yunqurin barin gabanta kamar yadda
ta buqata
" Harda su kaza a cin danqo?" Ta furta tana kama haba idanuwanta a kansa
"Kai dan qaruna ina zakaje?"
"Na manta uban masu gida,saika karanta min,don ubanka da can makarantar suka damu da zuwa?,shine
yanzu saboda wuce gona da iri da samun waje har suke rawar jikin tafiya?.to wallahi kuda makaranta
saidai idan anfi qarfina" Ta fada tana kada hannu da kyau cikin hargagi tana nunasu da yatsa.
Hukuncin nata yazo masa a bazata,don bai taba tsammanin zatayi hukunci me tsauri har irin
haka ba. Yaji abun ya taba ransa qwarai,domin a yanzun bashi da wani buri daya rage masa saina
KARATU. KARATU shine cikar burinsa qwaya daya tal daya rage bai qarasa mutuwa daga zuciyarsa
ba,yana jin zai iya bada kominsa don yayi karatu,zai kuma iya jure dukkan wata wahala tsanani ko
tsangwama saboda karatu. Ko a yanzun yana daya daga cikin abinda ya sanya zuciyarsa ke qarfafa,tana
sake jadda masa zai dauki komai ya kuma jure komai din saboda ingantaccen ilimin da yake hangowa
zaya samu. Dole ya daga idanunsa da suka fara sauya launi ya kalleta dasu
"Kalleni da kyau......ba wani karatu da zakuyi cikin gidan da ba na ubanku ba,idan kuma kallon mamaki
kake yimin ai uwarka yafi kamata ka yiwa wannan kallon,ita kanta ta kasa jurewa zama daku sai ni da
bani da galihu akeson hadani da alaqaqai,to wallahi yadda ban samu yadda nakeso ba,haka kuma ba
zaku samu ba......."
"Me kikeso ayi mama?" Ya furta tana aje numfashinta daga tijarar da takeyi. Tsananin mamakin yaron
takeyi yadda yakeyin komai cikin dakiya da taurin rai dana zuciya
"Ko baka tambaya ba ai zan gaya maka kuma dole kabi,ka sauke wannan munafukar jakar ku wuce
ciki,sudai da babu yadda zanyi dasu gidan ubansu ne saisun dawo,a sauka lafiya" Ta fadi tana nunawa su
Faruqee hanya da yatsa.
"Mama.....amma" Zakayimin shuru ko sai ka jawo kuma na hanaku?" Wani dunqulallen abu ya hadiye
can qasan ransa yana jin kamar ana masa suya
"Kudin mota"
"Kudin ubanka dai,sayyadarku zaku taka sisi bazan bayar ba" Ya fada tana zazzare masa idanu hadi da
dukan hannun kujerar da take kai
"Ku tafi Faruqee don girman Allah" Ya furta da rinannun idanunsa da kuma muryarsa da tayi laushi
qwarai yana duban Faruqee din,don kunnuwansa sun soma gajiya da jin zagin da take nausawa bawan
Allahn da baisan hawa ba baisan sauka ba.
Kallon kallo suke ma juna shida Faruqee din,kowanne cikinsu zuciyarsa cike take fal da zallar
bacin rai daya haurawa shekarunsu. A zahiri tausayin me babban suna shi yafi rinjaye a zuciyar Faruqee.
Ba yau ba ba kuma jiya ba ya sani......muddin ka ambaci kalmar UWA ko mahaifiya a gabansa takan zame
masa kamar tabo ko kuma ciwo koda ba dashi kake ba,ballantana a yanzun da aka kirata muraran.
Abun ya jima da zame masa kamar wani ciwo,tunda zancan ya bulla cikin unguwa sai ya zama
abun yamadidi da magana tsakanin maqota da mazauna unguwar. Sam baa tallafi rayuwarsu ba,ba'a
agajesu ba,ba wanda ya waiwaya ya dubi tsanani bayan tsananin da suke ciki,ba wanda ya bawa
rayuwarsu tallafin da zai rage musu radadin da sukeji,a maimakon haka,sai suka debo DAFI na cecekucen
maganganu akan rayuwarsu suka sake watsawa ciwuka da raunukan dake ciki zukatansu shi da d'an
uwansa.
"Kaje Faruqee" Ya sake maimaita masa yana tsareshi da ido. Ya karanci komai ta cikin idanunsa,ya
karanci abinda yake nufi da maganarsa,don haka bai qara koda minti daya ba ya kama hannun musaddiq
suka suma takawa suna barin falon.
"Na dawo gareka" Ta furta cikin izza da dagawa tare da jinta can saman qololuwar isa da kuma 'yanci
"Ka koma ka zare wadannan kayan,don basu dace da agola irinka ba,tabbas da 'ya'yan da mahaifiya zata
wofantar dasu,ta tsallakesu ta gudu ta barsu to ba'a banza ba......don haka banga dalilin da uwar data
haifeku bata tausaya muku ta zauna daku ba ni zan tausaya muku ba......tunda kun iso inaga ya kamata
me mana wanki da guga ya tafi hutu hakanan,ka shiga dakin ajiyar kayan wanki ka debo duk kayan da ka
gani ka fita dasu bayan gida wajen fanfunan can ka wankesu......wallahi wallahi kace zaka saka iskanci a
aikin kaga ikon Allah,banaso kuma azahar tayi maka baka kammala ba". Baice komai ba yakau da kai ya
soma takawa yana komawa dakinsu ranshi yana wani irin tafasa da suya. Tsanar maama tana sake wani
mahaukacin tasiri cikin ransa. Inda bata tafi ta barsu ba duk tsanani duk wuya,komai girman talaucinsu
sunfi gaban a goranta musu,don da iyaye ake ado,sune abun adon diyoyinsu.
Me yasa ta aikata hakan?,me yasa ta kasa jurewa?,tsabar son kai ne irin na jinsin DIYA MACE da
ya tabbatar a yanzun haka halittarsu take?.ko kuma son duniya da qyale qyalen cikinta ne ya rudeta?.
Me yasa batayi haquri ba kaman yadda Abbie ya dinga kira mata?. Har yau har kwanan gobe sashen
qwaqwalwarsa da ya nadi muryar Abbie ta qarshe.....magiyar Abbie ta qarshe akan roqarta ta zauna ya
gaza goge su......ya gaza goge wannan rarraunan sautin nasa daga nemory dinsa. Abinda ke sake aza
masa wata mahaukaciyar wuta,tare da dasa masa fara kallon halittar diya MACE a baibai.
Yana cire kayan saddiq yana kallonsa,a duk sanda zuciyar dan uwansa ta motsu shine mutum na
farko dake fara fahimtar hakan. Ya kammala cire kayan tsaf ya musanya dana gida sannan ya juya ya
adana na makaranta yana musu kallon tsanaki,dukka ruhinsa da zuciyarsa tana makarantar,yana wassafa
malami na farko ya fita zuwa yanzu,malami na biyu kuma na dab da shiga ajin komai yana ciki.
Hannu ya sanya ya share fuskarsa yana qoqarin lanqwasa zuciyarsa. Farat daya qaunar da
yakewa karatu ya ninku a zuciyarsa ganin abba ya bashi dukkan wata dama da zaiyi karatun,sai gashi
farat daya tana nema ta zama silar da zaiyi nisa sosai da MAFARKINSA?.
_________________
*_YA SUBHANALLAHI_*
*_IDAN KINA DA MATSALA KINA NEMAN TURARE ME KAMA WAJE,KINASON SAKEWA OGA SABON
QAMSHIN DAKI DA PARLOR,KE KANKI KINASO KI SHIGA WAJE A DINGA TAMBAYAR WACE TA ISO NE?_*
_________________
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*
_K'ALBIM Mamuhghee_
_DUNIYATA Huguma_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
*09033181070*
89825722
1000cf
*_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_*
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 08
__________________________
*_YA SUBHANALLAHI_*
*_IDAN KINA DA MATSALA KINA NEMAN TURARE ME KAMA WAJE,KINASON SAKEWA OGA SABON
QAMSHIN DAKI DA PARLOR,KE KANKI KINASO KI SHIGA WAJE A DINGA TAMBAYAR WACE TA ISO NE?_*
___________________________
"Hamma" Ya tsinkayi muryar saddiq tana kiransa,sai ya waiwaya ya zubawa qanin nasa ido
"Wai sai yaushe maama zata dawo?,yaushe za'a daina yi mana gori?" Tambayar ta tsinka zuciyarsa sosai
ta kuma sake yi masa tabo. Ya zuba masa idanu sosai,kamar bazai ce komai ba sai ya motsa labbansa
"Duk tsanani duk wahala.....kada ka sake zancanta sadiq,ta tafi kenam,ba kuma zata sake waiwayomu
ba.....ni zan tsaya dakai a kowanne yanayi da.mataki na rayuwa,bazan bari kasha wahala ba in sha
Allahu,bazan bari ka zubda hawaye irin wanda na zubar ba.....kayimin alqawari ba zaka sake zancan
maama ba?" Ya qarashe maganar yana ritsashi da idanu.
Kai ya jinjina a sanyaye yana maida jikina ga bango ya jingina,wani abu sosai yaron yakeji da
baisan yadda zai fasalta shi ba
"Ka cire uniform din" Ya bashi umarni ya sanya kai yana nufar qofa bayan muryar mama ta karade
ilahirin gidan ta cimmasa har dakin nasu
Tun daga wannan rana ta sauya lokutan zuwansu makaranta zuwa lokuta na bauta da wahalar
ayyukan gidan da basu ratayu a wuyansu ba. Duk wani aiki ta kallafa masa,har takai ta bawa ainihin
masu gudanar da aikin hutu tace saita nemesu,hutu ba tare da an yanke musu albashi ba.
Dukka yawa da azabar aikin aikin banza ne a garesa idan aka kwatantashi da maganganu masu
dafi da take jifansu dashi. Duk kalmarta guda daya me tsananin guba ce tana kuma same zuba masa dafi
da guba me daci ne cikin zuciyarsa. Rashin ko inkula dinta a kansu da dukka dabi'unta basi fiya bashi
mamaki ba,saboda ya riga da ya yiwa mata kudin goro gaba daya,tunda ya fara ganin sample daga kan
mahaifiyar data tsugunna ta kawoshi duniya kuma. MATA BASU DA IMANI,BASU DA KIRKI,BASU DA
TAUSAYI,BUQATAR KANSU CE A GABA DATA KOWA.
Wannan shine rubutaccen abu daya zauna radam cikin kwanyarsa da zuciyarsa,wanda baya jin
akwai lokacin da zaizo wanda wannan zai wanke daga cikin kundinsa.
Duk yadda Faruqee ke cikin tsananin fushi da daukar alwashin sai ya gayawa abba idan ya
dawo,in yaso ta kamashi ta gutstsira namansa ta kacalcala amma me babban suna ya danneshi ya kuma
haneshi
"Maama ma data haifemu ta gujemu,ta gaza tausaya mana?,ta kasa haquri damu?,ina ga mama......mu
din ba dolenta bane Faruqee,iya abinci da take sawa ana bamu da gurin kwana ma kawai tayi qoqari"
"Abincin nata ne?,ko gurin kwanan nata ne?,sannan shi kansa abincin waye yake qoshi?,bayan store din
gidan nan cike yake da kayan abinci?" Qaramin murmushi ya saki. Duk da qarancin shekarunsa amma
kwanyarsa tana aiki yadda ya kamata. Dukka wannan bai cika masa ciwo bafa,abinda maama tayi ya
danne dukka wadannan ciwo da zafi da kuma tsaiwa a zuciya. Abu daya ne yakejin yana dab da kasa
jureshi,hanashi zuwa makaranta......yana qaunarta yana qaunarta yana qaunarta har baisan iya adadi ba.
Abu na biyu indai saddiq dinsa yana lafiya to komai me sauqi ne.
A haka suka debi wata guda cur babu abinda ya sauya. Yadda kowacce safiya da ubangiji zai
bullo da ranarsa haka zata fidda wani sabuwar muguntar don quntatawa cuzgunawa a garesu. Duk fushi
zafin zuciya da rashin daukar raini irin nashi bai taba daga kai ya kalleta bare ya tanka mata ba,yana duba
cewa ta girme masa,gaba take dashi,a qalla ta ninka shekarunsa sau biyu. Duka duka shekarunsa sha
shida basu kai adadin shekarun da zai tsaya yana jayayya da babba ba.
Wanda ya rigaka kwana zai rigaka tashi. Sanda ya sanar da dawowarsa kaf ta hadasu ta musu
mummunar jankunne data tsoratasu ainun. Saidai ko kadan shi bai tsorata ba,don ba komai yake bashi
tsoron ba,bare a yanzun da zuciyarsa ke qarasa bushewa da qeqashewa akan komai na rayuwa.
Yadda aka saba haka ta sakar musu,sukaci gaba da zuwa makaranta abba yana kaisu da kanshi
kamar yadda yakeyi idan har yana gari.
Ya tsumu sosai,zuciyarsa kuma ta cika da takaici da bacin rai me yawan gaske sanda ya isa class
dinsu yaga yadda aka tsere masa a karatu. Kusan ranar duka ya qarar da ita wajen bibiyar dame dame
akayi da baya nan?,ya karbi note books na classmate dinsa da dama ya taho dasu gida .
Da yake abba yana nan akwai isashen lokaci 'yanci da kuma hutu,babu tarin aikace aikacen nan
marasa dalili marasa kuma tushe ballantana makama,sai ya zauna ya qarar da dukka wuninsa a daki
wajen ganin ya daidaita karatunsa dana 'yan uwansa.
Bashi da matsala da saddiq,don ajinsu daya da musaddiq,kuma duk sanda suka dawo gida
Faruqee yana hadasu su sake maimaicin karatu tare ta yadda zai zamana ba'a wuce saddiq din ba.
Yana da wata irin baiwar basira ta gasken gasken,sharp brain dake da saurin koyo da kuma riqe
abu tun yana dan mitsitsinsa ballantana a yanzun da yake shirin fara shiga shingen samartaka,danyan jini
yana zagayawa da gudu a jikinsa. Wannan ya taimaka cikin sati gudan da abba ya musu hutu ya gama
kammala komai,ya kuma tarar dasu tamkar dama dashi ake karatun. Sai a sannan ya samu sukuni ya
soma dawowa daidai. Saidai kuma a satinne qarshen satin,a yammacin juma'a abban ya tattara ya koma
lagos,abu guda daya dake alamta musu zasu koma RAYUWAR GIDAN JIYA kenan cikin gidan.
*********
*_MONDAY_*
Tushen aiki,bai sare ba ya shirya tsaf kamar yadda su Faruqee ke shiryawar,yana shirin Faruqee na
rantse rantse da cewar ba abinda zai hanasu fita a makaranta yau din. Ya lallaba kitchen ya hada musu
tea kaman yadda ya saba ya dawo ya bawa kowa,saidai ya tsallake me babban suna don yasan bazai sha
ba,don kuwa tun daga wancan ranar data zagi abban bai sake ci ko shan wani abu da Faruqee zai dauko
musu ba,ya tsani zagin iyaye matuqa,mutum ne kuma me fushi da gudun zuciya,wannan ya sanya yake
takatsantsan,akan komai bai fiya zura jikinsa ba.
Fitowa sukayi kamar wancan karon,saidai a yauma sun sameta hakimce a falon. Idonsa yadan
lumshe yana addua daga qasan zuciyarsa. Ya tabbatar wannan zaman ta yishi ne saboda su,son a lokutan
da abba yake gari kwata kwata nasa ganin qyallinta sai kusan shada zuwa sha biyu na rana.
"Eh......wato akuyar daure an samu sake,to kuzo nan" Faruqee ne na farko daya fara cakewa guri
daya,amma ya kama hannunsa ya jashi suka qarasa wajen.
"Me zakuyimin ku?,tunda kuna da uba ya daure muku gindi?,ku tashi kuban waje,ku kuma ku koma ta
inda kuka fito a cire uniform azo a kama aiki ko?" Cikin tsananin bacin rai Faruqee ya miqe yana nufar
hanyar fita yana kuma qananun maganganu qasa qasa
"Zagina kekeyi farouqu?,ka kuskura ka zageni ubanka zanci wallahi la'ada waje" Ta furta da hargagi tana
nunashi da yatsa sanda suke kusa da ficewa daga falon. Abinda ya sanya me babban suna miqewa yana
jin nauyi da kuma zafin zaginnan. Ko meye zatayi me ya gamo da iyayensu?,me su sukayi mata idan su
din masu laifi ne a gareta?.
"Don Allah mama ki barmu muje muma,idan mun dawo zamuyi miki duk aikin da kikeso"
"Kai.....wasa nakeyi dakai?,zaka tashi ka bani waje ko sai na zagi uwarka mara daraja da ubanka dake
qarqashin qasa?" Kamar saukar mashi haka kalamanta suka soki zuciyarsa,har sai daya kasa jurewa ya
waiwayo yana dubanta.
"Don Allah mama ko meye,ko meye mukayi miki ki mana hukunci ba tare da zagin iyaye ba......"
"Ubanka da uwarka,shegen yaro me tsaurin ido,kaci ubanka" Ta fada har tana zullo tare da watsa masa
daquwa. Ta jima da tsanar dama wannan kamewar tasa,ta jima da tsanar yadda yake da dauke kai da
rashin hayaniya akan komai da zatayi masa,duk yadda takai ga tama masa wajen bashi baqin kashi da
baqar wahala don ya magantu dukka ya shanye sai a yau din.
Cikin qasa da minti guda launukan idanunsa suka sauya,baice qala ba amma kunnuwansa suna
suna iya jin zafafan muggan kalaman da take jifanshi dasu. Ya tako a nutse ya iso gaban saddiq dake
durqushe a gabanta ya sanya hannu ya damqi hannunsa ya tasheshi tsaye,abun sai ya masa
kamanceceniya da sanda saddiq din ke tsananin roqon mahaifiyarsu akan kada ta tafi ta barsu.
Bai waiwayeta ba,bai kuma dakata ba ya durfafi qofar fita daga falon kanshi tsaye,ba tsoro ba
shakka ba kuma shayi
"Ina zakaje,bance ba zakuje makaranta ba?" Ta furta da qaqqarfan sauti. Bai dakata ba bai kuma
waiwayo ba ko ya nuna yasan tanayi har ya fice daga falon. A yau ta rushe dukkan wani ragowar kara da
dagin qafa da yakeyi mata. Baya wasa da kalmar UBA sam a rayuwarsa,IYAYEN MA guda biyu,abba da
Abbey.
https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997
________________________
_QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_
_K'ALBIM Mamuhghee_
_DUNIYATA Huguma_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
*09033181070*
*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*
89825722
1000cf
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
*Arewabooks:Huguma*
https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997
PAGE 09
Har a sannan ranshi a jagule yake,bacin rai kowanne second yana sake motsa zuciyarsa. Faruqee ya
sameshi daga bayan makarantar zaune qasan bishiya saman rairayin dake wajen,hannunsa riqe da
busashen siririn reshen bishiyar yana tona qasa dashi,ya kafe qasar da idanu kamar me nazarin samar da
wani abun amfani daga gareta. Ta gefansa ya zauna,yayi masa tambayar duniya akan ya akayi ya taho
makarantar amma ya gaza cewa komai. Na Faruqee ba,tunda ya shiga class din baiyi manana da kowa
ba,don bayajin koda ya bude bakinsa akwai wasu kalmomi da zasu iya fita daga cikinsa. Dole Faruqee ya
haqura ya kuma tayashi zaman shurun,don dukkansu dama babu me 'yanci ko damar yin break,to inama
kudin?,dukka dana transport din da komai ta hada ta kalmashe.
Sai a hanyar komawa yaji komai daga bakin saddiq. Qwafa yaja yana girgiza kai
"Duk yadda kake tunanin matar nan ta wuce nan,duk kuwa yadda zan fasalta maka,ta samu sassauci ne
daga garemu shi yasa take abinda taga dama,ace mutum ya shiga shekara ta sha biyar,kana girma amma
baka da 'yanci?" Shikam baima iya cewa komai ba har zuwa sanda qafafunsu suka maidasu gida.
Sai da suka gilma ta gaban gidansu kafin su cimma gidan RIQOnsu a yanzu,idanunsa zube bisa fuskar
gidan dake garqame da kwado. Take yaji wata matsananciyar kewar gidan da kewar Abbie da jadda suka
saukar masa. Duk da suna rayuwa ne cikin matsakaicin matsayi na rayuwa,amma rayuwarsu rayuwa ce
me 'yanci da kuma dadi. Duk da suna rayuwa da maama cikin wani baqon hali da murdaddiyar
dabi'a.......hakan yafi musu sauqi a kan rayuwarsu ta yanzun cikin gidan RUQO.
Ya janye idanunsa sanda ya dubu daidai wajen da mahaifinsa ya dogaro da qyar ya biyo bayan maaman
yana cike da fatan zata dakata daga aiwatar da qudurinta nayin nesa da rayuwarsu,wani zafin akan na
dazu ya sake yunqurowa ya mamaye zuciyarsa.
Daga saman balcony din da zata sadaka da ainihin falon suka sameta a zaune ta hakimce. Faruqee ne a
gaba,musaddiq yana biye dashi,sai me babban suna da ko qaunar hada idanu da ita bayayi. Zuciyarsa
yadda take a zafafen nan tana ayyana masa abubuwa masu dama a kanta.
"Idan ka kuskura ka qaraso na saina sanya an maka dukan tsiya......baka isa ka shigamin gida ba tunda kai
din tantiri ne mara kunya.....nan gaba kadan shaye shaye zaka farayi da daba,kaga kenan ka samu hanyar
da zaka hallakani a banza" Ta fada tana miqewa tsaye.
Dukka su hudun sukayi carko carko suna dubanta da jin kuma wani sabon bala'in daya tunkarosu kuma
bayan na dazu da safe.
"Kai har ka isa na fadi magana ka sabamin bare ka maidamin?,don an zagi uwarka da ubanka,su su waye
da ba za'a zagesu ba?,wato gaka kai me zuciya ko,to an zagesu din na kuma zagi banza da wofi".
Da qarfi ya damqi hannun saddiq ya kuma soma ja da baya yana janye jikinsa daga wajen
" Yauwa gwara daka fahimta,don wallahi kabar gidan nan kenan,tun yanzu kana tsayarmin ina ga nan
gaba idan ka gama zama balagagge?".
Da sassarfa Faruqee da har ya isa bakin qofar falon ya soma saukowa yana takowa zuwa garesa ganin
suna nufar gate din fita daga gidan yana qwala masa kira da niyyar tsaidashi
"Aisai ka bishi kaima don ubanku,na fiku iskanci qananun balagaggu" Ta furta tana komawa saman
kujerar ta zauna
"Bar nan gurin" Ta kwatsawa musaddiq daya mace a wajen saboda tsoro da mamaki tsawa,baiyi wata
wata ba ya juya shima yabi bayan 'yan uwansa.
Bai iya tsaidashi ba har sai da suka isa qofar gidansu dake garqame. Sai sukayi carko carko suna kallon
kallon shi dashi. A yadda ya hangi kwantaccen fushi da bacin rai akan fuskar me babban suna sai ya rasa
da wadanne kalmomi zai iya shawo kan me babban suna?,wacce kalma ce zatayi masa aiki?.
"Kayi haquri kazo mu koma,tunda gidan abba ne ba nata ba bata isa ta hanaka zama ba,yau ko kasheni
zatayi saidai ta kasheni" Wani irin kallo ya yiwa Faruqee,ga mamakinsa murmushi ya gani ya subuce
masa.
Da wani irin zafi ya waiwaya ya dauko dutsen dake yashe gefan malalen simintin dake gaban gidan
nasu,har tsoro ya kama Faruqee yaja da gefe,sai yaga ya doshi qofar gidan,ya kama kwadon dake jiki ya
fara bugeshi baji ba gani.
Tsakiyar azahar ne,wannan ya sanya ba yawaitar jama'a a layin bare a samu me dakatar dashi. A yanayin
da yakejin zuciyarsa da kansa a ciki,bayajin akwai ma wanda ya isa ya dakatar dashi din sai MUTUM
DAYA TAK A DUNIYA.....ALHAJI HAMZA KIBIYA.
Zare kwadon yayi ya watsar gefe,kansa tsaye kuma ya soma cusa kai cikin gidan ba tare daya damu da
yana datti ko qurar data lullube qofar ba.
Wannan shine mafarin komowarsa gidansu......tushensa......asalinsa da yaji yafi masa kwanciyar hankali
sau dubu akwan kwanansa cikin babban bedroom din gidan alhj hamza dake dauke da wuta 24/7 da
kayan alatu na rayuwa.
Tun a asalin halittarsa shi jajirtacce ne tsayayye da bai yarda da faduwa ba......sanda komai ya dinga
faruwa kuma daki daki,sai zuciyarsa ta qara qeqashewa ta kuma tsaya kyam......ya karantawa kansa da
kansa cewar shine uwa kuma uban kansa da dan uwansa sadiq.......shine gatan kawunansu,ya fidda
kowa daga cikin zuciya rayuwarsa dama hasashensa. Wannan ya sanya tun rana ta farko da suka dawo
gidan bai kuma karbar koda ruwa daga gidan alhj hamza ba. Duk da yadda ran Faruqee ke baci da yadda
yake wofantar da komai da ya kawo musu din kuwa koda ruwan sha ne. Da kansa ya tsaya,sadiq na debo
ruwa shi kuma yana wanke komai da yayi saura na gidan wanda zasu iya amfani dashi. Cikin kwanaki uku
kacal ya fara Qwadago.
Duk wani aiki da zai samar masa kudi......komai wuyarsa kuwa muddin halas ne yana karba yayishi hannu
bibbiyu. Da wannan din ya dogara.....da dan abinda yake samu din ya dauke musu abinci dama abin
sha......idan faraga ta samu harda kudin transport na makaranta koda na zuwa kadai ne banda na
dawowa.
Sauyawar yanayi da kuma tsarin rayuwarsa ya sake canxashi gaba daya. Yana tsananin son karatu
kowanne iri ne,na addini dana boko gaba daya
*_TURQASHI_*
*_TURAREN WUTAR DA ZAKI SANYAWA DAKI AMMA HATTA DA LABULAYE KAYAN SAWAN DAKE SAQALE
A DAKIN SU KAMA DA QAMSHI?_*
Khumra
Turaren wuta
Kulaccam
Lablab
Oil perfumes
Multipurpose spray
*karki kuskura kada kiyi ganganci ayi babu ke,kai tsaye tuntubeta ta wannan number*
08032119803
Ko ki lalubeta ta nan👇🏾👇🏾👇🏾
*Twitter_kabo daughter*
________________________________
_K'ALBIM Mamuhghee_
_DUNIYATA Huguma_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
*09033181070*
89825722
1000cf
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
*Arewabooks*
https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997
PAGE 10
Baya wasa da islamiyya,amma wahala da nauyin kansa dana saddiq ya sanya ya sallamawa zuwa
islamiyya. Duk da haka bai sare ba,ya lalubi makarantar magariba ta manya ya soma zuwa don karantar
litattafan addini,duk kuwa da nisan zangon tafiya dake a tsakaninsu.
Su kansu ba 'yantattun 'ya'ya bane cikin gidan mahaifinsu......amma duk da wannan ya gaza
barin me babban suna yakuma qyaleshi kamar yadda ya fuskanci yana da muradin hakan. Duk da basu
da 'yanci ko fada aji a gidan......amma hakan baya hanashi dauko abinci daga cikin nasa kwanon data
qayyade musu cikin gidan ya kawo don suyi tarayya suci tare,amma koda wasa me babban sunan bai
taba dangwala yatsarshi a ciki ba.
Abun yana ma Faruqee zafi da ciwo matuqa,har daga qarshe hakan ya sanya suka samu sabani
"Don mama tayi maka laifi ai ba abincinta bane,abincin abba ne wanda har yanzu a nasa zaton kuna cikin
gidansa ne cikin aminci bisa kulawarta,iyakarta da abincin nan tazo ta diba itama taci,don ko dafawa ba
ita ke dafawa,larai ce......kuma ita ke qaramin yawan abincin a boye ba tare da saninta ba,to indai bawai
nima gaba da fushi kakeyi dani ba banga abinda zai hanaka ci ba.....idanma kai ba zakaci ba....kada ka
sake hana saddiqu yaci,kai ka zauna haka can ta matse maka". Busashen murmushi ya saki yana jin
yadda cikinsa ke qugin yunwa,don yau ba wani abun kirki ya samo a aikin ba,wannan ya sanya basu wani
qoshi ba wunin ranar sur.....ga kuma tafiya makaranta a gabansu gobe juma'a.
Yadda Faruqee yayi fushi ya kuma dauki zafi da abun ya sanya yake barin saddiq din suna
hadaka dashi. Shikam yasan bazai taba iya sanya abincin cikin bakinsa ba. A duk sanda yayi yuqurin
hakan sai maganganunta su dawo musu kar kar cikin qwaqwalwa
"Tunda uwarka ta zube ku ta tafi ta barku,banga uban da zai iya zama daku ba......uwarku ma ta barku
ballanta wani?" Aduk lokacin da zai tuna da irin wannan maganar a take yakanji komai ya fita a kansa
ne,tsananin baqinciki ya mamaye walwalarsa,wata irin wuta me zafi na taso daga qasan zuciyarsa da
ruhinsa dangane da imaninsa. Ta wani fuskar da mama da sauran 'yan unguwa dake jifansu da muggan
kalamai sai yaji sam baya jin zafinsu ko kadan,da uwa da uba da kuma dangi ake ado,su kuma basu da ko
guda daya!. Ya tabbata lallai su din cikakkun marasa gata da galihu ne,kuma kowanne suna aka kirayesu
dashi sun cancanta.
Yayi imani inda har jadda tana raye.....koda sunfi kowa talauci da matsin rayuwa......to babu
shakka zasu zamo na sahun gaba gaba wajen zama yaran da sukafi kowa samun gata na kulawa da
soyayyar kaka. Saidai Allah baya barin wani don wani yaji dadi,ya tabbatar haka ubangiji ya tsara musu
tasu DUNIYAr,haka kuma yaso ganinsu a cikinta.
A wannna tafiyar abba yayi nisan kiwon da ya jima baiyi irinsa ba. Yana rayuwa bisa yaqinin lallai
gidansa da marayun Allahn daya dauka riqo suna lafiya,tunda duk sanda zaya kirata hakan take gaya
masa,sannan lokaci bayan lokaci tana hadashi da musaddiq,shima kuma
"Lafiya qalau muke abba" Shine amsar da yake bashi bisa jagorancin mummunan gargadi da idanuwa da
maman take aike masa duk sanda suke wayar. Faruqee ne bata taba yarda ta bawa wayar ba,sai a wani
yammaci da abban yace ya jiyo muryarsa ta hadasu.
"Lafiya amma ba qalau ba amma.....muna buqatar ka dawo a kusa abba" Bata iya barinsa ba ta fusge
wayar daga hannunsa cikin hanzari ganin yana niyyar sauka daga layi.
Maganar ta tsayewa abban a rai,ta kuma sanyashi yaji dukkan hankalinsa yana tarkatowa yana
yowa gida. Duk kuwa da akwai sauran abu daya tsara zaiyi a can din,amman sai yaji komai ya fita a kansa
tahowarsa gida ce abu na farko da yake kwana yana tashi dashi.
*******Kusan dukkansu jan qafafunsu sukeyi,zafin rana yunwa ga gajiya dake tattare dasu. Akwai nisan
tazara me dan dama tsakaninsu da makarantar wanda suke shanyeta a qasa daga tafiya zuwa dawowa.
Babu ranar hutu a garesu idan ba asabar ko lahadi ba. Ga me babban suna kuwa,baya gane asabar ko
lahadin cikin rayuwarsa da DUNIYARSA. Rayuwar tasa gaba daya a birkice take,bashi da wata dogon hutu
daya wuce makaranta zuwa neman kudin abinci.
Yayi wani irin duhu,dukkan hasken fatar nan da suka gado babu shi,ya rame daga ainihin
halittarsa zuwa wata halitta ta daban.
Tun daga nesa ya soma hangen wani abu da yayi matuqar girgiza hankali da kuma tunaninsa,ya
sanya dukkan wani tunani nashi ya fara sauka daga kan layi,ya kuma daina gane me Faruqee daketa
faman bashi labari yake fadi.
Wata qurace take tashi daga wani sashe na gidansu gami da qarar zubewar bulalluka. Gefe guda
akwai tsaiwar tsirarun mutane da kuma yara wadanda basa raina abun kallo,hakanan basa bari abun
kallon ya wucesu kamar qanqantarsa.
Zame hannunsa yayi daga jikin na Faruqee,a gaggauce da kuma hanzari ya soma tattaki har zuwa
inda aikin ke gudana.
"Gidanmu ne fa.....me yayi ake rusheshi?" Ya furta bayan ya tabbata ya tsaya gaban mutanen dake
gabatar da aikin futu futu cikin qasa da qura.
Dukkansu suka waiwayo suna dubanshi,kafin daga bisani wani dan tsamurmurin mutum dake
sanye da milk riga da wando na shadda,da kuma babbar riga ta koriyar shadda gami da baqaf hula daya
karkatata gefe ya qaraso gabansa yana dubansa. Bakinsa cike da gashin baki,kai kace daya daga cikin
qabilun da suka shude ne shekaru aru aru.
"Yaro me kake cewa?" Ya fadi yana saba babbar rigar da a zahiri an tafka babbar asara wajen ware
shaddar aka masa rigar da ita gaba daya,don kuwa yadin ya masa yawa,alamu ma suna nuna kamar
rinjayarsa takeyi
"Gidanmu ne nace,me yasa kuke rushe mana gida?" Ya sake jefa tambayar ga mutumin yana tsareshi da
ido da zummar jin ba'asin maganar.
Qaramar dariya yadan saki yana sosa gashin bakinsa da alama qaiqayi yake masa.
"Yaro man kaza......kai!bakasan tsohuwarka ko ince uwarka ta karbi rabin kudin gidan daga hannun
matata ba sanda zata bar garin?". Fuska da idanu gaba daya me babban suna ya yamutse yana duban
mutumin cike da zallar mamakin da kwanyarsa ta gaza dauka.
" Ko da yake ma.ba fahimta ai zakayi ba,wannan zancan na babanka ne inda yana raye,ba abinda zaka
gne yaro" Yana kaiwa nan sai ya juya yana dubañ mgainan
"Kuyi ku raba ku zagaye mana haqqinmu" Da hanzari yasha gaban mutumin jin kalaman da yake sake
maimaitawa
"Kada su sake taba mana gida,don nan vidan ba gudan mamata bane da zata saidashi,gidan mahaidinmu
ne daya ginashi da guminsa,ta nemeta ta biyata kudinta amma mu ba ruwanmu" Tsaiwa yayi yana
qanqance idanu hadi da duban me babban suna
"Kai wannan yaron da alama zakayi tsaurin idanu,da alama dai abinda ake fadi a kanka gaskiya ne......to
ai ko kai yanzu ba zakace ga inda uwar data haifeka take ba,tunda ta bazama yawon duniya ta watsar
daku.....". Kalmar ta sokeshi qwarai kamar kowanne lokaci. Duk a iya adadin fadar da akeyi bai taba
yunqurin kare musu jifan da ake musu da kalmar ba,amma a yau din sai yaji koda sau daya yana da
sha'awar huce musu wannan takaicin shi da saddiq.......yana da marmarin maida martani koda sau daya
ne tak......amma baya sha'awar bata kariya ko wanketa daga muggan kalaman mutane a kanta,don bashi
da abun cewa a kanta,kwata kwata dukkan wata soyayya qauna ko tausayi na fil'azal a tsakaninsu
yanxun baya jin akwai burbushinsa,abinda ya sani kawai ya kare kansa ya kare saddiq dinsa
"Ba abunda ya shafemu da inda taje ko inda take.......kaman yadda ba ruwanmu da karbar kudinku da
tayi don nan gidan mallakin mahaifinmu ne mallakinmu......abinda muka sani kawai shine mu din
halastattun 'ya'yane da aurar ya samar......"
Daya daga cikin ma'aikatan wanda kuma gidan su yake ta qarshen layinsu wanda ke tsaye
gaban tsani ne ya bushe da dariya
"Dame kwado yafi gaya ku da shegun?,dame kuka fisu?" Yana kaiwa nan ya dauki qatuwar gudumar da
suke dukan saman ginin da ita ya soma taka matattakalar tsanin yana hayewa da zummar ci gaba da
aikinsa na ragargazar ginin da mahaifinsu ya kwashe lokaci yana zuba kudadensa wajen qawata musu
shi. Ya sadaukar da kudi da qarfinsa wajen samar dashi,ya sanya burinsa akai na ganin sun rayu a cikinsa
cikin aminci da kwanciyar hankali.
Kwata kwata kasa jurewa yaji yayi da mummunar kalmar da yaji ya jefesu da ita. Sanda ya daga
gudumar zai doka......daidai lokacin ba tare daya ankara ba ya sanya hannu ya fusgoshi sai gashi qasa
warwas!. Abinda ya sanya dukka jama'ar dake tsaitsaye a gefe tun dazun basuyi magana ba
yunqurowa,masu salati sunayi masu yunqurin tayar da babba magini sunayi.
Wani irin mamakin sauyar rayuwa da mutanen dake rayuwa a cikinta ya kamashi. Da idanu yake
binsu
*_TURQASHI_*
Khumra
Turaren wuta
Kulaccam
Lablab
Oil perfumes
Multipurpose spray
*karki kuskura kada kiyi ganganci ayi babu ke,kai tsaye tuntubeta ta wannan number*
08032119803
Ko ki lalubeta ta nan👇🏾👇🏾👇🏾
*Facebook_kabo daughter*
*Twitter_kabo daughter*
*D U N I Y A TA*
*_H U G U M A_*
PAGE 11
_____________________________
*_YA SUBHANALLAHI_*
*_QAMSHI NA TASHIN KAN ME GIDA_*
*_IDAN KINA DA MATSALA KINA NEMAN TURARE ME KAMA WAJE,KINASON SAKEWA OGA SABON
QAMSHIN DAKI DA PARLOR,KE KANKI KINASO KI SHIGA WAJE A DINGA TAMBAYAR WACE TA ISO NE?_*
*MAZA MAZA JEKI KI GWADA WANNAN_*
___________________________
Daga sanda ya jawoshi ya maidoshi qasa......daga sannan yaga iya yawan adadin mutanen dame
wajen wanda sam baiyi zaton sunkai haka ba,bai dauka suna da yawa haka ba.....amma duk da wannan
yawan nasu babu wanda yayi yunqurin yin wani anu guda daya sanoda ceton rayuwarsu da cetin ginin
gidan dashi kadai suma!mallaka a rayuwarsu wanda zasu nuna suce ya fito daga jini da gumin
mahaifinsu?. Me yasa al'umma ta sauya?,ya dinga duban fuskokin masu luguiguita zancan da kambama
abinda ya aikata din,dukkansu suna tsaye sanda ake himmar rugurguza mafaka guda daya tasu da tayi
saurs,ba wanda ya tallafa,ba wanda ya dakatar. Kusan dukkansu fuskokinsu bayyanannu ne a
idanunsa,fuskokin daya saba gani sunzo neman taimako wajen mahaifinsu,wanda bai taba gazawa ba da
taimaka musu da abinda Allah ya hore masa,amma yau tsantsar butulci irin na dan adam sune suka juye
suna masu tsaiwa suna kallon wasy na shirin zaluntarsu.
A sanda yayi nisa da wannan tunanin a lokacin babba yayi amfani da wannan dama yakai masa
duka,dukan da yazo masa a bazata banda jin hucin wucewarsa da yayi da hucin hannun Faruqee daya
tare masa dukan. Yaja baya yana maida hankalinsa jikinsa,sai ya taka dutse ya kuma yi taga taga ya fadi
da baya,wannan ya sanya babba ya sake yunquro masa da nufin turmesheshi cikin baraguzan ginin gidan
da suka fara saukewa,sai Faruqee shima ya taso ya rufa masa baya da zummar baiwa me babban suna
din dauki.
Cikin zafin nama fushi da kuma taurin kai gami da kafiya da taurin zuciya Shima ya yunqura ya
miqe yana jiran qarasowar babba. Idanunsa a lullube suke da bacin rai,baya hangen nisan tazarar
shekaru da kuma girman jiki dake tsakaninsa dashi.
"Kai.....kai......dakata.....meye hakan?" Muryar nan me cike da kamala tausayi da dattako ta ratso gurin.
Kowa ya tsaya ya waiwaya yana duban saukowarsa daga motar zuwa takowarsa cikin fusassun duwatsun
gurin. Alhaji hamza kibiya ne idanunsa na kai kawo tsakanin Faruqee me babban suna da kuma ginin
gidan nasu.
Mutum ne me cikar kamala da dattako,wanda ya riqe mutuncinsa da kyau. Yana daya daga cikin
dattijan unguwa dake bada Umarni ko shawara abi,musamman da yake yana da abun hannunsa wato
kudi abokan tafiya.
Kunya tadan kama manyan dake wajen da basu hana ba sai tsaiwa kallo da sukayi,wanda sun
tabbatar idanuwansa sun gansu gaba daya.
Bai tsaya sauraren barka da zuwan da suke masa ba,sai qoqarin qarasawa gabansu kawai da
yakeyi bayan yace da saddiq da musaddiq su tsaya daga baya,wanda dukansu suka tsorata tun farkon
rigimar,to amma basu dame kawo musu dauki bare suyi hanzarin garzayawa su kirashi ko zai cecesu.
Ta gefan babba dake tsaye yana kade jikinsa cikin jin nauyi yana kuma huci qasa qasa ya wuce,ya
qarasa inda me babban suna ke zaune warwas ya miqa masa hannu ya tasheshi tsaye.
Yana tsaye a gabansa ya bashi handkerchief yana karkade jikinsa. Idanun alhaji hamza a tsaye
sosai jikin uniform din nasa da suka fara alamta masa wani abu.
"Me yake faruwa a nan ne?" Ya watsa tambayar ga tsamurmurin mutumin daya lura kusan shine
baquwar fuska a wajen.
Baiyi qasa a gwiwa ba ya kwararowa alhaji hamza bayani kaman yadda ya yiwa me babban
suna,bayanin da maimaicinsu yake sanyashi jin kamar ya rufe idanunsa ya budesu ya ganshi ba'a wajen
ba,kamar ya rufe idanu ya kuma budesu ya tsinci kansa haihuwar wata uwar daban ba maama
ba......kaman ya tsugunna qasa ta hadiyeshi ya huta.
Sai daya kammala bayaninsa gaba daya sannan alhaji hamza ya gyada kai
"Nine a matsayin wakilin yaran nan,kuma bana nan,yanzu haka shigowata garin kenan,inaso a dakatar
da aikin nan,ka kuma sameni gobe mu zauna muyi magana akan batun da kazo dashi,ina da buqatar
qwaqwarar shaida da hujja ka taho da ita,idan ya tabbata da gaskiyarka,zaku fadi iya kudin data karba
zan biya na fansarwa yaran gidan da suka gada,idan kuma aka rasa daya daga ciki kasan qarshen case din
basai na qarasa ba" Abba yayi magana yana janye hannun me babban suna sunayin gaba. Ko daya bai
amsa maganar mutanen ba,wanda ba abinda ransa keyi game dasu sai baci da soyuwa. Rayuwa ta
lalace,DUNIYA ta zama wani abu na daban?,babu me kawar da barna?,babu me rungumar dan
wani?,kowa nasa ya sani.
A baya suka bishi yana riqe da hannun me babban suna ba tare da yace komai ba.
Motarsa ya qaraso da ita bakin gate din gidan nasa sannan ya kulleta,ya soma takawa zuwa ciki
yana kiran Faruqee. Cak ya tsaya daga gate din gidan shida saddiq suna kallon abba Faruqee da
musaddiq suna wucewa zuwa ciki.
"Me babban suna" Abba ya ambata sanda ya sanya qafarsa ta farko cikin gidan
"Abba baya shigowa gidan mu yanzu" Musaddiq ya fadiwa babban qasa qasa yana tsoron kada mama
dake can ciki ta jiyoshi. A mamakance ya kalli musaddiq sannan ya waiwaya ya kalli me babban suna
dake tsaye daga baya kansa a qasa.
Yana jin nauyin abba qwarai,yana kuma jin nauyin saba umarninsa,amma bayajin qafafunsa
zasu sake taka wannan gidan har abada kamar yadda yaci alwashi.
"Faruqee meye haka?" Abba ya tambayi farouq cikin rashin fahimtar abinda ke faruwa
"Abba ya koma gidan su,mama ta koreshi". Wani abu yaji ya sauka tsakiyar kansa har kaman qafafunsa
suna neman yin rawa.
" Ya salam ya Allah" Ya fada a fili,tun yaushe ta aikatawa.marayun Allah haka?,ashe shi yasa hankalinsa
yayi qololuwar tashi sanda ake taba ginin gidan nasu tunda yana kallonsa a mafaka guda daya duk
duniya data rage musu?,ashe shi yasa yaji ya kasa samun nutsuwa kwata kwata a kwanakin?.
"Muhammadu" Abba yakirayeshi kai tsaye da cikakken sunansa da ba kasafai yake kiransa dashi ba.
Umarninsa dai dai yake da umarnin mahaifinsa da yayi silar kawoshi duniya,tabbas idan zaiyi
musu da gardama wa mahaifinsa to la shakka zai yi wannan wa abban. Amma fa tabbas inda ya san
abban zai ankara d wuri akan baya biye dashi,allai da yayi nisa da gurin tunda wuri,tun gabanin yayi
masa umarnin shiga gidan irin haka.
A gaba ya jeresu yana biye da bayansu har zuwa sanda suka isa ainihin falon gidan. Daidai
sanda take fitowa daga kitchen hannun ta dauke da jug data tanadarwa abban lemo,haka kuma tasha
ado da lace bakinta ya cika taf da lipstick ja shar dashi.
Har cikin zuciyarta takejin bala'i da masifa suna tsarga mata. Yau kam dukkan juriyarta da karar
da take masa ta qare muddin dai yace dawowa yayi da yaran nan masu zubin mayu. Iya zamanta da
yaranshi ma ya isheta jarrabawar rayuwa bare ya qaro mata yaran da batasan matsayinsu a gidan
ba,suba agololi ba,su kuma ba yaran masu gida ba.
"Ya isa da Allah asama'u" Abba ya fada da hanzari yana daga mata hannu,don wasu maganganun bai
dace ace an yisu gaban yaran ba,koda saddiq da musaddiq basu da shekaru sosai,ai Faruqee da me
babban suna zuwa yanzun sun fara kammala hankalinsu tunda sun shiga shekara ta goma sha biyar.
"Ba inda zasu a gidannan dai wallahi,basu da daki kuma basu da matsugunni tunda dai bakai ka haifesu
ba.....danginsu ma sai watsar dasu wai ballantana kai abba?" Ta fada tana sake matsowa hanyar da zasu
wuce zuwa dakin
"Abba babu kayansu ko daya a gidan nan fa.....baka dade da tafiya ba ta koresu,tunda.ka tafi suma suka
koma kwana a gidansu" Faruqee ya fada gaba gadi,yana jin cewa shima yau yakai bango,komai ta
fanjama fanjam.
"To baqin munafuki,na koresu din,kuma wallahi wallahi koni ko su a gidan nan" Maganar faruqee ta
dagawa abba hankali. A cikin gidan da bashi da maraba da kango suke kwana?,gidan dake cike da
memories na iyayensu da suka gushe?,ta yaya suke iya bacci su biyu rakkin wanda har zuwa yanzu ba
wanda yakai shekara sha bakwai ma bare sha takwas a tsakaninsu?.
"Abba abinci ma aiki me babban suna yakeyi a tasha kullum yana kawo musi gari ko dan wanke"
Musaddiq ya fada a dan tsorace yana satar kallom fuskar mama bayan ya riqe hannun mahaifinsa da
kyau yana boyewa a jikinsa.
Sosai maganar ta dakeshi,zaka fahimci hakan ta yadda kalolin idanunshi suka sauya duk kuwa da
tarin haqurinsa. Farat daya yaji asama'u ta fita a kanshi gaba daya. Duk matar da zata iya yiwa maraya
haka tabbas ya sani nashi yaran ba zasu tsira ba wadanda suke da uwa da uba,Allah ne kawai mafi sanin
haqiqanin abinda su kansu su musaddiq din suke kwankwada daga hannunta idan baya nan.
Bai taba barin garin ya tafi gurin neman kudinsa hankalinsa a kwance ba tun daga ranar daya saki
mariya. Tun daga ranar daya rabu da mariya bai sake samun nutsuwa cikin gidansa ko aminci akan
'ya'yansa ba.
"Ni babu abinda Allah zaiyimin,don su din ba dole na bane,wadanda ma suka zame musu dole sun
yakicesu sun zubda bare ni da aka tsinceni da haqorana talatin da uku.....don haka wallahi bazanyi
riqonsu ba,yaranka dai ba yadda na iya dasu saboda ubansu nake aure"
*ZAFAFA BIYAR*❤🔥
_FITATTUN GWARAZAN MARUBUTAN LITATTAFAN NAN NE MASU DAUKE DA SALON LABARAI IRIN
DABAN DABAN BISA TSARIN TAFIYA DAYA SUKA SAKE YUNQUROWA ☺️😇_
_WADANDA SUKA SABA GABATAR MUKU DA QUNSHIN ZAFAFAN LITATTAFAI DA LABARAI MASU TAFIYA
DA HANKALI DA TUNANI_
*_IRINSU_*
BURI DAYA
INAYA
AMEENATU
DALAAL
BAQON MUNAFUKI
KAIMIN HALACCI
TSUTSAR NAMA
WUTSIYAR RAQUMI
BAQAR INUWA
TABARMAR QASHI
KUFAN WUTA
*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*
*ZAFAFA BIYAR*
*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA
ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*
_K'ALBIM Mamuhghee_
_DUNIYATA Huguma_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
*09033181070*
89825722
1000cf
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
*Arewabooks:Huguma*
https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997
___________________________
PAGE 12
"Qarya kike,wallahi tallahi yarana dinma ba riqonsu kikeyi ba,koda basu taba gaya min ba amma na
tabbatar ba irin riqon uwa da 'ya'yanta kike musu ba.....irin riqon da mukayi alqawarin zakiyi musu"
Qaramar shewa tadan saki tana tafa hannuwanta hadi da qare masa kallo tsaf ido cikin ido
"Dama waye yace maka uwar wani zata iya riqon dan wani tamkar nata?,au ashe bakaji abinda bahaushe
ya fadi ba kenan,riqon uwar wani da dan wani ai sai Allah" Mamakinta ne ya qarasa kasheshi,ransa yakai
qololuwar bacin da har ya mance da yara ma a wajen
"Haka kika ce?,to bari kiji na gaya miki......muddin ba zaki riqe wadannan marayun ba saidai kisan inda
dare yayi miki" Idanu ta fidda tana kallonsa cikin maqurar mamaki,wato ya fifita matsayin yaran a kanta
kenan?,ta yaya zata ma zauna ta karbi wannan fifikon?,ya za'ayi ma tayi sake har yaga warginta haka?,a
gaban yaran ya kafa mata irin wanna sharadin?,ai duk yadda taso ga son zama dashi ba zata karba irin
wannan mulkin qarfa qarfan ba.
Hannayenta ta sake hadawa ta tafa ta kuma riqe qugunta da kyau tana dubansa
"Wallahi kaji na rantse bazan riqe su ba,har nakanma na gaji ai bamuyi abinda zanzo nayi kenan cikin
gidan nan ba"
"Tunda kuwa kikace haka saidai ki qara gaba" Gabanta yadan fadi,amma batajin zata bari ya gano
lagonta
"Hakan shi yafi sauqi,amma bazanje nayita zama da dakon aurenka ba,ka gayan meye matsayin tafiyar
tawa idan na yita?" Ta kuma tambaya tana watsa hannuwa
"Innalillahi wa 'inna ilaihi raji'un" Me baban suna ya furta yana saka hannuwansa dukka biyu ya toshe
kunnuwansa,sannan ya koma ya sulale yana zama tsakanin kujerun falon.
"Tafi nono fari,sai me?,dadin abun ai ba kai kadai bane namiji" Ta qarasa fada tana ture kujerun dining
din ta sauka a gaggauce zuwa dakinta gabanta yana wani irin bugawa da sauri da sauri.
Daga su har abban ba wanda ya iya cewa komai,falon ya dauki shuru kawai sai motsinta daga
can uwar daki tana hada kaya gami da sakin maganganu wanda basa iya jin ainihin me take fadi.
Mintuna goma kacal ta fito janye da akwatunta da qaramin mayafi yafe a kafadarta. Daga inda
yake ya daga rinannun idanunsa yana kallonta. Abba ya saketa ne saboda su,me yasa abban zai saketa
saboda dalilinsu?. Fitowarta sai tayi masa kama da fitowar mahaifiyarsu sanda take shirin barin gidan
mahaifinsu.
Me yasa ake tafiya ne ana barinsu?,farinjini ne basu dashi ko kuwa?,ko wani maqalalle kuma
boyayyen abune dasu?,me yasa iyaye mata basa tausayinsu saidai maza?.
Baisan yaushe ya yanke wannan hukuncin ba,shidai ya tsinci kansa a gaban mama ne,cikin
matuqar tashin hankali da karyar da muryar yake fadin
"Don Allah mama kiyi haquri,kada ki tafi saboda mu......"
"Na rantse da Allah zan zabga maka mari idan baka bani hanya ba,munafukan banza da wofi wadanda
babu alkhairi sam a jikinsu sai masifa da balai nau'i nau'i,ai daya sakenin sai ku ya aureku,gaku nan
gashi,kara da kiyashi daukan mara sani" Sai ta wuce abinta ta barshi da zafafan maganganun daya gaza
mancewa dasu.
"Dawo ka zaun me babban suna,waye yace maka ka bata haquri?,waye yace maka zan iya zama da ita
bayan bata sonku?,ba zata iya zama daku ba?,ba zata iya haquri daku ba?......in sha Allah na muku
alqawarin dawowa da mamanku nan da sati guda kacal" Maganar data Haifar da wani irin farinciki mara
misali a zuciyar faruqee musaddiq harma da sadeeq din da baima mamansu musaddiq din farin sani ba.
Yayin da me babban suna yake binsu kawai da idanuwa,don kunnuwansa da zuciyarsa harma da
qwaqwalwarsa sunyi nisa qwarai da abinda ke wakana a falon.
Jarin maganganun mutane masu tsananin dafi daya soma girma da jinsu yaketa aunawa. Kullum
kwanan duniya wayewar gari zuwa faduwar rana sai yaci karo da wata mummunar kalma da zata
zamewa zuciyarsa tabo wadda ta shafesu da mutuncinsu,duk kuma MAAMA itace sila,dama uwa tana
iya zama silar bacin suna da rayuwar 'ya'yanta?. Tambayar da amsarta ta kasa samuwa a gareshi
kenan,musamman lokacin da MARIYA mahaifiya ga faruqee da musaddiq ta dawo ainihin dakin aurenta
da zummar riqe yaranta harma da marayun Allah MUHAMMAD DA ABUBAKAR SADDIQ
***************
Faffadan tsakar gida ne ma'abocin yalwa da kuma tarin dakuna da zasu nuna maka yawan adadin
mazauna gidan dake cikinsa.
Tun daga qofar gida,zauruka guda biyu masu girma har zuwa farfajiyar gidan da wani filin tsakar
gida da gidan ya mallaka zakasan cewa asalin ginin gidan anyi gine na masu wadata a wani qarni can
baya daya shude.
Duk kuwa canzawar siffar ginin zuwa zubin ginin daya dauki shekaru,amma yanayin yadda akayi
zuba ginin da kyakkyawan tubali hakan ya hanashi muguwar lalacewa ko muzanta daga suffar kyau zuwa
ta tsufa.
Dakuna guda hudu manya manya gidan ya mallaka lailaye da siminti da tsakar gidan ya wadatu
dashi da fulasta wadda ke nuna yau ta jima da samuwa a jikin ginin gidan. Kafin idanunka yakai ga
duqurqusar matakalar bene dake qarshen qofar daki na hudu a jerin dakunan gidan. Rijiya ce da aka dan
dagata kuma aka rufeta da murfi na langa langa. Idan ka sake kai dubanka kuma can zuwa sashen
hannun hagu na gidan,bayan ka wuce bishiyar mangwaro data samu muhalli na dindin da Tsakiyar
gidan,kai tsaye kana iya hangen qofar da tafi kama data makewaye,da kuma qofar babban kitchen na
gidan daya hada kowa da kowa.
Akwai gurabe daga jikin bangon gidan da zai sanyaka ka fahimci a baya akwai wasu shuke shuke
da sukayi zamani daga bangwayen gidan,saidai yanzun babu ko wanne tsiro idan ka cire bishiyar dake a
Tsakiyar wadda gushewarta ita din ba abu bane me sauqi.
A tsaftace gidan yake ba laifi,wanda kusan gado ne da kuma asali da tsafta daya samo cikin
gidan koda kuwa bayan gushewar me gidan da rasuwar mace daya cikin matan aure uku da ma gidan ya
mallaka a lokacin rayuwarsa.
Safiya ce sosai,kusan qarfe bakwai da rabi na safe agogo ya nuna a daidai lokacin. Kowacce qofa
ta gidan a sakaye take,sai wata qofa guda daya qyaure ta ya banbanta da sauran qyamaren gidan
kafataninsu.
Ba zaka gama fahimtar yadda banbancin yake bai tsaya daga qyauren kawai ba.....aah,har sai ka
samu nasarar kutsa kanka cikin ainihin falon dake hade da uwar daki kaman kowanne daki na gidan.
Kyawawan labulaye ne da aka yiwa dakin qawanya dasu ruwan toka wadanda sukayi daidai da
sofas guda biyu dukkansu 3sitter da aka gewaye falon dasu hakanan suka dace da lallausan daddumar da
aka shimfida a tsakaninsu qirar qasar turkiya.
Akwai lausasan pillow guda hudu manya dake zube a qasa dukkaninsu kala daya da labule zuwa
kujerun. Daga bangon dakin ta fuskar hagu kuwa,bango ne da yasha wallpaper me kyau aka kuma yiwa
TV plasma me matsakaicin girma da reciever dinta mazauni na daban. Gaba kadan dasu 'yar
madaidaiciyar AC ce ta tsaye wadda ke amfani da hasken rana da aka yiwa kafatanin dakin wayarin
dinsa. Wannan ya sanya koda babu wuta ko ina cikin gidan,koda babu wuta ko ina a unguwar wannan
dakin baya rabo da ita. Akwai freezer madaidaiciya itama data dace da tsarin dakin,sai manyan frames
masu daukan hankali biyu masu sunayen Allah da ayoyin tsari,biyu kuma masu dauke da zanen nature
me kyau. Sassanyan qamshin turaren icce dake zama a daki ya kama labulaye da kujeru da kyau falon
yake fiddawa ya zarce kuma har uwar dakin,wanda ya cakuda da qamshin turaren daya zamewa
mazauniyar dakin lazim amfani dasu.
Labulen bedroom din aka daga,sannan kuma a hankali ta bayyana hannunta riqe da hijabin
yarinyar dake tsaye cikin uniform.
Matashiya ce wadda duka duka a qiyasce shekarunta ba zasu haura ashirin da biyu ke takowa a
kasalance.
*_TURQASHI_*
Khumra
Turaren wuta
Kulaccam
Lablab
Oil perfumes
Multipurpose spray
*karki kuskura kada kiyi ganganci ayi babu ke,kai tsaye tuntubeta ta wannan number*
08032119803
Ko ki lalubeta ta nan👇🏾👇🏾👇🏾
*Facebook_kabo daughter*
*Twitter_kabo daughter*
__________________________
*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*
*ZAFAFA BIYAR*
*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA
ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*
_K'ALBIM Mamuhghee_
_DUNIYATA Huguma_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
*09033181070*
89825722
1000cf
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 13
___________________________
*_YA SUBHANALLAHI_*
*_IDAN KINA DA MATSALA KINA NEMAN TURARE ME KAMA WAJE,KINASON SAKEWA OGA SABON
QAMSHIN DAKI DA PARLOR,KE KANKI KINASO KI SHIGA WAJE A DINGA TAMBAYAR WACE TA ISO NE?_*
________________________
Sanye take cikin lallausar doguwar rigar bacci me kauri me gajeran hannu off white wanda ta
tsaya daidai idon sawunta.
Zaka iya kiranta doguwa saidai ba cancan ba,irin tsahon da yayi daidai da tsahon da za'a iya kiran
diya mace doguwa,wanda siririn jikinta ya sake taimakawa wajen bayyanar tsahonta,muddin kuma ta
samu damar mujewar jiki ko ta dan qara qiba to tsaf tsahon zai shanye da ba lallai a iya ganinsa ba.
Tana da wani irin launin fata,fari me cakude da sirki sirkin ja,fara ce tas irin hasken fatar da kana
kalla zakasan ba zallar hausa fulani bace,lallai ita din ruwa biyu ne halittarta ya hada nasaba da wani
yaren(half cast).
Ma'abociyar yalwataccen gashi me santsi da tsahon da kana iya hangensa ta cikin hular bacci
dake kanta,a cukurkude kuma a daure cikin siririn band. Yanayin zubin idanunta shike fusgar hankalin
maza da dama,bama maza kawai ba,harda mata 'yanuwanta suke kallonta a matsayin me tsananin
kyau,duk kuwa da cewa ita din kanta ta sani,ba wata me mugun kyau bace na azo a gani,amma batasan
meye yake janye hankalin mutane haka a kanta ba?. Tun tana mitsitsiyarta wannan abun yake tare da
ita,FARINJINI
....wanda a sanda take da gatan uwa mahaifiyarta ke yawaita tofeta da addu'a ko yaya ne idan zasu fita.
Mata ukune cikin falon,matashiya ta biyu wadda shekarunta zasu iya kaiwa sha shida na zaune
dirshan saman lallausan carfet din nasu daya wadatu da tsafta,hannunta riqe da cup na tea,daga gefanta
kuma bowl ne dake cike da chips. Sanye take da uniform irin na sauran 'yan uwanta dake alamta maka ta
kammala nata shirin zaman tsimayinsu take bayaga breakfast data kasa kammalawa har yanzu. Yanayin
yadda take cin abincin kawai zai gaya maka bawai dadin abincin takeji ba,idanma ba haka bane to lallai
akwai abinda yake damunta.
Ta biyun na gefan kujera tana qoqarin saka fara qal din sucks dinta. A qiyasce nata shekarun na
haihuwa zai wahala ya wuce sha uku. Sannan qaramar data isa gareta tana gyara hijabin hannunta tana
qoqarin sanya mata fuskarta shimfide da wani sassanyan murmushi nata shekarun tsakanin tara zuwa
goma suke.
Idanunta akanta da wani irin kallo na tausayi da rahama,zuciyarta na sake narkewa cikin
tausayinsu gami da jin qwarin gwiwar basu kariya da samar musu da komai na buqatar rayuwa duk
rintsi,komai wuya komai dadi. Wanzuwarsu a yanayi na farinciki yafi komai dad'ad'a mata rai da sanyata
cikin nutsuwa da kwanciyar hankali duk kuwa da irin birkitacciyar rayuwar da take fuskanta,wadda bata
da dadi sam sam ballantana ban qaye.
"A'ah.......kaga haneefata anyi kyau" Ta fadi da sassanyan muryarta me wani irin amo me dadi da daukan
hankali idanunta saman fuskar yarinyar data kira da haneefa......yarinyar da ake cewa duk cikin qannenta
ba wanda ke kama da ita irinta,duk da ansha cewa haneefan ta fita kyau,hasken fata kawai zata darata
dashi.
Dariya haneefan ta saki ta daga hannunta zuwa ga 'yar uwartata alamun su tafa,sai ta daga nata
dogayen yatsun ta bata suka tafa din.
Batasan wanne irin son karatu Allah ya dorawa qannen nata ba,wadda karatun bai fiya damunta
ba huda ce,saidai a sannu da tayi tsaiwar daka a kanta yanzun abun ya shiga jikinta itama. Hudan ma
bawai karatun bane bataso,a'ah,kawai hankalinta yafi karkata zuwa ga wasu bangarori. Kaman koyon
abubuwa na qirqire(creatives),irinsu zane zane,dinki,decorations da sauransu. Bata jin akwai wanda zata
matsawa kan abinda yakeso yayi muddin bai kaucewa hanya ba.....to amma kafin sannan tana da
buqatar suyi karatu.......tana da buqatar su karantu da kyau ta yadda koda bayan ranta sun zarcewa raini
da wulaqanci......tana da buqatar suyi karatun da duniya gaba daya zata tabbatar sun gagari rainin me
raini ta fannin ilimi.....tanaso suyi irin nau'in karatun da hattana da maqiyi babu yadda zaiyi zai sallama
cewa eh lallai......jinin hindu sun zama wasu taurari na daban a cikin familynsu gidansu dama unguwarsu
gaba daya......zata nunawa wadanda suke ganin ba zasu iya ba.....ba zasu kai ba......zasu tozarta
cewa......zasu iya iya.....za kuma sukai labarin da su basu kai ba.
A nutse ta waiwaya ta kalleta. Tadan zuba mata idanu na second tana nazarinta. Tun tuntuni ta
fahimci akwai kwantacciyar damuwa a qasan ranta,kasancewarta mutum me wani irin kakkaifan hange
da saurin gano abu. Kaifin fikirarta ya fita daban dana dukkan wani yaro dake cikin gidan,don haka take
saurin fahimtar kowanne motsi taku da kuma sauyawar yanayin qannenta.
"Huda......wai baki duban lokaci?" Batace komai ba huda din,saita zare cup din bakinta ta direshi tana
niyyar miqewa,abinda ya sakata maida idanunta ga cup din kenan. Ko rabin tea din bata sha ba,ta sake
maida kallonta a kanta
"Banajin yunwa dama kwata kwata" Kyawawan idanun nata masu wani irin shape ta lumshe,can qasan
zuciyarta tana furta
"Alhamdulillah,astgafirullah" A duniya daya daga cikin sauti da take matuqar son ta yita ji kenan daga
harsunan qannenta
"BANA JIN YUNWA" Sauti mafi dadi kenan daga bakinsu zuwa kunnuwanta.
Waiwayawa tayi gefanta ta kalleta sanda ta kammala saka takalmi da socks dinta
"Nadra......shiga daki gefan katifata ki daukomin jakata na sallameku......yau din kamar babu me laka a
jikinku"
"Tom" Ta amsa tana saukowa daga saman kujerar da saurinta ta wuce dakin. Sanda take maido dubanta
cikin falon sai suka hada idanu da hudan. Huda ta janye daga kallonta,sai ita din taci gaba da kafeta da
kallo tana dubanta
"Huda"
"Wai meke damunki?" Ta jefeta da tambayar tana kebe baki......harta bude baki zatayi magana ta
dakatar da ita a tsaurare
"Gida......"
"Ba damuwar mutanen gidan nan ba?" Ta jefa mata tambayar tana duban idanunta,a yanzu akwai sirkin
bacin rai kadan a maganarta da idanun nata
"Yaushe kika fara saka maganarsu cikin ranki?" Ta kuma tambayar tata tana kallonta
"Ashe har yanzu baki saba da halayyarsu ba?,bakisan yadda zaki zauna dasu ba?,huda ina duk qoqarin da
nake a kanki ke da kike babba ki fahimci yadda zaki zauna da kowa a cikinsu?"
"Anty bakisan me suka ce ba a kanki.....bakisan me suke fada ba kullum" Ta qarashe maganar muryarta
tana raurawa sosai da alamun zuciya da ruhinta gaba daya sun sare.
"Kome zasu fada huda su fadi,indai a kaina ne karki azawa kanki damuwa.......kome ma zakiji sun fada,ba
wani baquwar kalma da zakiji daga bakinsu ko sabon abu.....me yasa sai yanzu zaki fara sawa kanki kina
damuwa?" Ta qarashe da sigar tambaya. Qasa tayi da kanta ba tare data amsa mata ba,ita kanta batasan
me yasa sai yanzun abun ke damunta ba duk da sun share shekaru dasu a haka.
Daidai sanda nadra ta qaraso ta miqa mata kyakkyawar hand bag din nata fara tas me adon
brown duka jikinta dake dauke da tambarin kamfanin Gucci.
Idanunta masu sheqi ta juya zuwa ga nadra,ta saka hannu ta karbi jakar tana qoqarin zugeta.
"Anata kiran wayarki tunda na shiga" Nadra dake goya jakarta ta fada.
"Okay,barta" Ta amsa mata a taqaice,don ta tabbatar a cikin mutum biyu daya ne yake kiranta,tafi kuma
gasgata zatonta akan dayan.
Zip din da take ajiye canji ta zuge,ta fidda kudin ta lissafa daidai yadda tasan zai ishesu break da
kudin mota,saboda yau din basuyi abinci yadda suka saba ba kasancewar kayan abincinsu ya qare.
Daga bakin qofar falon nasu tayi tsaye hannayenta goye a qrijinta tana dubansu har suka
kammala ficewa daga gidannasu,sai taja Qaqqarfar ajiyar zuciya tana sauke hannayen nata ta juya a
hankali don komawa falon don kwata kwata bata samu isashen bacci ba a jiya,tanaso ta runtsa sosai
sannan ta shiga kasuwa tayi musu saye saye
*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*
*ZAFAFA BIYAR*
*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA
ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*
_DUNIYATA Huguma_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
*09033181070*
89825722
1000cf
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 14
________________________
*_IDAN KINA DA MATSALA KINA NEMAN TURARE ME KAMA WAJE,KINASON SAKEWA OGA SABON
QAMSHIN DAKI DA PARLOR,KE KANKI KINASO KI SHIGA WAJE A DINGA TAMBAYAR WACE TA ISO NE?_*
*MAZA MAZA JEKI KI GWADA WANNAN_*
_________________________
Saidai dai dai sanda ta saki labulayen da zummar shiga ciki din taji sallamarsa ta karade tsakar
gidan. Qaramin tsaki taja,tabbas tunda aka jishi da sassafen nan kamar haka to ba a shakka wata tijarar
yazo yi,ko kuma akwai abinda ya hadoshi da wani. Idan da sabo zata iya cewa sun saba da
halayyarsa,macce daya ce cikin gidan suke dasawa har baka iya jin kansu. Har gwara ita tasan
maganinsa,ta kuma san ta yadda take bulloma tsiyarsa,duk da bata taba tsaiwa ta kulashi ba anji
muryarta a matsayinsa na qanin mahaifi a gareta.
Sakaya qofar kawai tayi ta sake zuge labulen sosai sannan ta wuce uwar dakin ta yadda ba zata
tsaya bata lokacin jin meke faruwa a tsakiyar gidan nasu ba,domin ita din tana cikin jerin sahun irin
mutanen nan ne dai basa shiga abinda bai shafesu ba,wanda ya shafesun ma sai tura takai bango,bata
da magana sam sam bare hayaniya. Wannan hali nata da siffarta ta sanyi da sauqin hali da kuma
yauqinta ya sanya da yawa suke mamakin WANNAN DABI'A TATA......Dabi'ar da har yanzu su kansu basu
da cikakken yaqinin a kanta,duk da cewa suna kallon gamsassun hujjoji ai sun gama bayyana a fili a game
da ita.
Babban bedroom ne qwarai wanda iya dauke gado da wardrobe guda bibbiyu,sai dressing
mirror guda daya. Duk da cewa wai daga bacci aka tashi amma dakin neat yake,komansa akan tsari,ga
kuma wani sassanyan qamshi da yake fita kaman dai yadda falon yake.
Daya gadon da yake shine qarami ta nufa,wanda ke lullube da lallausar shimfida da tattausan
blanket peach color. Tun batakai ga zama ba rurin da wayarta keyi ya cika mata kunnuwa,sai ta haye
saman gadon ta lalubo wayar ta cirota daga gefan pillow dinta.
Iphone 15 ce dake dauke da wata irin cover me kyau data dace da wayar da kuma me wayar
gaba daya,ta zubawa sunan dake yawo saman screen din idanu
*_ibraheem_* ya nuna mata. Wani gajeran murmushin gefan baki ta saki dake cakude da wani emotion.
Siririn tsaki taja saman harshenta,ta fara qoqarin rejecting kiran
"Done and dusted.......an gama da shafinka tun a jiya" Ta fada qasan ranta tana tuna yadda al'amura
suka tafi mata successful kaman yadda aka saba.
Sai data tabbatar tayo blocking ta kuma shafe duk wani abu daya shafeshi cikin wayar,bata bar
hujja ko qarama ba da zata nuna tsohuwa ko sabuwar alaqa ko kuma mu'amala tsakaninta dashi ba. Ta
sake bin wayar ta tabbatar komai ya koma kaman da,sannan ta duba wata ma'ajiya ta daban ta lalubi
wata number ta kira ta kara wayar a kunnenta.
"Ya riskeni qwarai kuwa tun a daren jiya.......ina godiya......na gode sosai,ina me baki haquri kuma akan
sabanin Fahintar da nayi miki a farko.....gashi kuma ko sunanki ma ban sani ba"
"Ba buqatar hakan......infact ma daga yau ba zaki sake samu na ko jin muryata ba......abinda na baki kiyi
qoqarin tattalashi,ki kuma boyeshi daga sanin mijinki.......abu na qarshe saiki tayashi jiyya.....kinsan
yadda zaki sanya masa tawakkali cikin zuciyarsa,don nayi imani ya zuwa yanzu zaiyi wahala bai zauce
ba,na barki lafiya" Ta yanke kiran ba tare data barta tace komai ba,duk da tarin abubuwan fada masu
yawa da take dasu take kuma son gaya matan.
Itama goge number dinta tayi ta kuma sakata a sahun sauran tarin lambobin dake akwatin
katangewa dake cikin wayarta. Layinta layi ne dake da wani irin tsaro na musamman,wanda ba kowacce
number da bata yarjewa bace take iya samunta. Tana da ire irensa sunfi guda ashirin,duk kuma sanda
take da muradi ra'ayi ko kuma buqatar hakan ya taso tana iya sauke wanda taga dama ta dora wani.
Tana shirin shigewa duvet ta kwanta wani kiran ya sake shigo mata. Batason takura sam,sai taja
tsaki tana kallon fuskar wayar.
Shine din dai,batasan me yasa ya matsa da yawa ba,bataso a yanzun akwak enough kudi a
hannunta,tanaso taje hutu koda na taqaitaccen lokaci ne kafin ta fada zuwa wani agenda din.
"Tsautsayi da alama keta kiranka" Ta furta qasa qasa ta jawo wayar tana rejecting kiran shima sannan ta
kashe kiran gaba daya ta jefar da wayar. Kanta ta mayar ta qudundune sosai cikin blanket din,saidai ko
minti biyar bata yi ba cikakke ta miqe zumbur kamar wadda aka tsikara,ta sauko daga saman gadon tana
qoqarin daure gashinta me santsi dake rufe gefan fuskarta.
Kyakkyawar drawer dinta ta bude banqaran hijabs,ta fidda wani qaramin farin hijab cikin jerin
hijban da take amfani dasu a lokaci irin haka idan zata shiga wanka. Sama kanta ta zurashi,wanda
wannan ya fidda kyakkyawar fuskarta tsakanin hijab din,ya kuma fidda wata sihirtacciyar kama akan
fuskar tata. Towels dinta ta nufa ta zari guda daya,sannan ta matsa gefan daya drawer dinta ta jawo ta
can qarshe ta fidda set na kayan wankanta dake cikin wani dan kyakkyawan kwando kaman kwandon
kaba,ta rataye toweldon saman kafadarta ta fara takawa a hankali tana fita a dakin tare da sake gauke
fuskarta da kyau wanda kusan haka dabi'arta take duk sanda zata fita zuwa ainihin tsakar gidan nasu,duk
da dama ita din ba matum bace data cika fara'a.
Duka duka mutanen dake sabgarsu a safiyar ranar cikin sararin tsakar gidan ba zasu wuce mutum
biyar ba. Dukkaninsu kuma mata ne da a shekaru suke qasa da nata shekarun idan ka dauke mutum
daya dake ta bakin kitchen dinsu,zaune saman kujera 'yar tsuguno tana ta kokawa da wutar ice da take
qoqarin kunnawa hayaqinta yana dawo mata cikin idanu yana sake tunzurata da hasalata.
Duk wanda suka hada ido dashi sai ya janye dubanshi daga kanta kamar yadda itama kusan haka
take musu,duk kuwa da cewa wasunsu suna son tankawa a gareta kaman yadda a wasu lokutan yake
kasancewa,saidai wanzuwar ta bakin kitchen din ya sanya ba wanda yayi gigin aikata hakan a cikinsu.
Bata dakata ba har ta isa bakin makewayensu da ko yaushe yake cike da tsafta da kulawa,ta xare
towel din wuyanta ta azashi saman qofar bandakin idanunta nakan shaheed,yaron da aka kawoshi yaye
daga gidan mahaifansa zuwa gidan kakanninsa. Yaron yayarta ne,yayarta ta kusan biyar,d'iya a wajen
gwaggo mace ta biyu a wajen mahaifinsu.
Ido suka hada da yaron,sai ya sakar mata murmushi,a hankali itama ta motsa bakinta tana
maida masa martani. Tana da wani boyayyen soyayya ta yara a zuciyarta,saidai zuwan yaron sai ya zame
mata kamar wani mabudi ko kuma wanzuwar sabon abu da bata saba gani ba cikin gidan wato
murmushi kowacce safiya a tsakar gidan mahaifinta wanda ya jima da shudewa tun bayan gushewar
mahaifiyarta.
Tanason yiwa yaron magana,amma tayi imani rayuka zasu iya baci daga qarshe,dole ta kauda
kai,ta sirka ruwan zafin data fito dashi ta fada wankan.
Kafin ta kammala taji masu buqatar shiga bandakin da yawa,masu qananun mitoci da qorafi
duka sunayi,wasu su juya wasu su zauna suna dakonta gami da ci gaba da yasar da maganganun da tayi
imanin da biyu suke yinsu kamar yadda suka saba.
Zuwa yanzu ta fara tunanin yadda zata maida qaramin dakin dake kusa da dakinsu toilet. Daya
daga cikin dabi'a daya ta gidansu data tsana kenan,sharing toilet.
Gini ne irin na da wanda duk yawan jama'ar gida suna hadaka ne a bandaki qwaya daya tal!.
Zata iya cewa da sauqi nasu tunda akwai wadatar tsafta.
Ko data fito babu wanda tabi takai,sai data kammala uzurinta na daura alwala a nan bakin famfo
sannan ta tattaro kayanta tana barin wajen. Sai a sannan ta kallo mata biyun dake zaune daga bakin
bishiyar.
Daya ta girmi daya a shekaru,saidai dayar ta dara dayan jiki. Sun kalleta sun kuma dauke idanu
kamar basu ganta din ba. Ba abinda ya dameta da hakan
"Ina kwananku?" Ta furta da muryarta me laushin nan tana yin gaba ba tare da tayi koda yunqurin
tsaiwa ba da salon gaisuwar da duk safiyar duniya bata daukewa kowacce cikin su ukun ba muddin zasu
hadu a farfajiyar gidan.
Amsa mata sukayi kaman yadda suka saba din,can qasa suna kuma binta da wannan kallon
dake dauke da tarin ma'anoni can qasan ransu,wasu.
sun furta su sun kuma bayyana,wasunsu kuwa an barwa zuciya AKWATIN SIRRI.
*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*
*ZAFAFA BIYAR*
*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA
ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*
_K'ALBIM Mamuhghee_
_DUNIYATA Huguma_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
*09033181070*
89825722
1000cf
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
*Arewabooks:Huguma*
PAGE 15
A nutse take ratsa falon harta cimma uwar dakin nasu. Duk takunta guda daya sauke qafarta da
dauketa zuciyarta cike take da kewa. Wata qatuwar kewa data zamewa kowanne motsi na rayuwarta
lazim. Kewa ce da zaiyi wuya ita iya barin gangar jiki. Kewar mahadin rayuwa jigon rayuwa mahadin
numfashi wato MAHAIFIYA.
Duk yadda lokaci yakai ga wulwula gudu,duk yadda zamani yakai ga fara yin tsaho da nesanta
bawa daga dukkan tunani radadi da damuwoyin abubuwan da suka shude amma ya gaza yin nasara a
kanta ta wannan fannin. Mahaifiya daban take cikin rayuwar 'ya'yanta,babu ma ya mahaifiya irin
tata......jajirtacciyar uwa data zamewa maraicinsu sutura,ta zame musu bango abun dafawa,ta hana
musu kuka akan rashin mahaifinsu.....sai gashi a yanzun suna kuka.....irin kukan da kunnuwa ba zasu iya
ji ba,idanuwa ba zasu iya gani ba.......ta saka dukkan wani qarfi da iyawarta ta tare wannan shingen
maraicin......tozarta da wulaqantar rayuwa dake shirin danne musu numfashi har ya zuwa lahirar
duniyarsu.......tallafewar data sabbaba mata tarin ciwuka.......nauyi me yawa a qirjinta da
rayuwarta......ya kuma bude mata qofofi masu fadin gaske cikin rayuwarta......ya maida JARUMA a mafi
yawan lokuta.....wani lokacin kuma MAFARAUCIYA dake bude dukkan qarfin qwanji dana zuciyarta don
cimma burikanta.
Ya dasa mata abubuwa masu yawa cikin ZUCIYARTA ya kuma sanya dolen dolen ta sauya akalar
rayuwarta ta fanni da dama. Ta koma tamkar tarwada me wahalar kamawa cikin ruwan da take ninqaya.
Ta kuma koma tamkar hawainiya dake canza kala a duk sanda taso hakan,ta bace ta kuma saje da duk
yanayi ko launin da takeso ko kuma taga dama.
Tana da tarin sunaye masu yawa da a duniya a yanzun bayan ainihin sunanta na yanka SABREEN.
Sunayen da ba'a yiwa yanka ba don tabbatuwar samuwarsu a kanta.
Akwai idanuwa bakuna da hankula masu zafi da batasan adadinsu ba a kanta. Kowanne kuma da
irin nashi kallon.....hasashen da furucinsa dangane da ita.
Karon farko ta sakarwa fuskar nan tata murmurshi data fito tawai bisa fuskar madubin dame
gabanta duk kuwa sa siririyar qwallar dake kwance cikin qwayoyin idanunta masu sheqi kaman an diga
ruwan zaiba. Karaya da kuma qwarin gwiwa na karakaina tsakanin qirjin nata,saidai ko sau daya bata
aminta ta dauki FADUWA TSORO ko kuma ja da baya ba.
K'aramin towel da yafi kama da handkerchief ta sanya ta tsane qwalla don kada ta bata daman
fitowa,ta miqa hannu ta jawo stool ta zauna a kai tana saka hannunta tana kokawar daure sassalkan
gashinta dake qoqarin kwancewa daga daurin farko datayi masa.
A nutse ta jawo set na kayan shafarta da take amfani dasu. Skin care product ne da suke mahadi
da shower gel cream da sauran tarkace,wanda kudinsu duka zai tasamma dubu arba'in.
Kudi ne me nauyi da ciwo a wajen me qaramin qarfi,to saidai ta wajenta amfani dasu sun zame
mata jiki kaman yadda suka zame mata wajibi. Tana son ado,tana qaunar tsafta da qamshi,wanda da a
baya bata basu muhimmanci ba,saidai daga bisani ta gama karantunta tsaf......ta fahimci kowanne taku a
rayuwa akwai abokin yinsa.....akwai sauyawar yanayi da ta zamewa jiki da rayuwa dole......dole sai an
aiwatar da wasu abubuwa ake samun wasu abubuwan,dole sai an gusa koda da taki daya ne sannan ake
samun wasu sabbin damarmakin suke shigowa rayuwar dan adam.
Gayunta na daya daga cikin abinda ya sake sama mata MUMMUNAR SHAIDA da kuma
mummunan zato daga bakunan mutane da dama. Zaton daya kamata ya qona mata rai.....ya sanyata
fidda qwalla masu zafi.....a maimakon hakan saidai kawai ta murmusa,ta kuma motsa ta barka a wajen
da salon abun nan dake nuni da BANI DA LOKACINKI/KA.
Tsaf ta duk wani shafe shafe nata,ta kuma gyars gashinnan me tsanani yauqi sheqi da tsaho,ta
dameshi cikin ribbon me dan girma,abinda ya sake bawa ainihin kamanninta fita ras kenan.
Koda ta bude ma'ajiyar kayanta tsaiwa tayi tana tunanin suturar da zata dace da jikinta a
wannan lokaci. Shaqe take tafff da tarin suturu na alfarma,masu tsadar da koda ba'a gaya maka ba kai
kanka ka sani. Suturun da a tashin farko xakasan sunfi qarfin wanzuwa cikin wannan wardrobe
din.....kaman sunfi qarfin ma ace akwai wani cikin gidan daya mallaki masu darajarsu.
Juya zagayyayun idanunta tayi tana dan lumshesu kadan zuwa bangaren abaya. Sai data gama
nazarinta sannan ta jawo daya daga ciki. Egyptian abaya ce me asalin daraja da kuma kyau wadda
kudinta ya tasamman dubu arba'in da 'ya'ya. Sam sutura me tsada ba damuwarta bace,tana iya
mallakarta a duk sanda tayi marmari ko kuma muradin hakan.
Da sanyinta dinnan da yake cikin halittarta take daura belt din da abayan yazo dashi bayan ta
saka ta farko ta kuma dora alkyabbar da abayar tazo da ita. Siririn mayafi ta zaba daya dace da rigar tayi
rolling me kyau da ma'ana,take zagayyar fuskarta ta fito cif tsakiyar veil din,sai ta kuma duba handbags
dinta dake rataye sama da goma sha biyar kowacce da takalminta mahadi a qasanta.
'Yar qarama ta dauko qirar kamfanin D&G da takalminsa,ta natsa gaban madubi ta dauki
turarenta ta bintike kan ta feshe jikinta dashi,sannan ta zari wayarta ta jefa a jaka tana duba agogon
dake daure a tsintsar hannunta ta doso falon.
Jakar ta ajjiye tana jawo tea flask dinsu tana qoqarin budewa. Bata fiya son cin abinci da wurwuri
da safe ba,to amma kuma tana tunanin zaiyi wahala idan ta fita din ta iya tsaiwa taci komai tasan halin
kanta da kanta sarai.
A tsaitsaye take kurba kyawawan idanunta zube fes saman qaramar waya me keypad data dora
saman cinyarta tanata qoqarin kiran wata number.
Bugu biyu aka dauka,muryarsa ta bayyana cikin wayar da wani irin shauqi da doki
"Da wacce irin saa yay na wayi gari ne?,ya Allah" Ya fadi yana zama gefan gadon bedroom dinsa.
Taqaitaccen murmushi me qaramin sauti ta sake tana kai cup din bakinta,can qasan ranta wani
abu yana yawo gami da kai kawo a ciki. Gaba daya ta manta da rayuwarsa,taso kuma ta gogeshi a babin
rayuwar tata gaba daya,to amma data tuna wani abu,sai take ganin ya kamata ko yaya shima a bashi
darasi.
"Dukka wadannan tambayoyin basu kamaceka ba,tunda dai gani din na kuma kira ai sai ka ajjiyesu ko?"
"Haka ne ranki ya dade" Ya amsata da sauri ba tare daya damu da yadda matarshi ke tsaye saman kanshi
tana dubansa cike da qunar zuciya da kuma takaici ba.
"Zaka iya samuna nan da mintuna goma a gaban flavours na gadon qaya?" Ta jefa masa tambayar tana
ajiye cup din hannunta,daidai sanda yaron ya daga labulen falon bayan ya turo.qofar ya shigo. Washe
mata baki yaron yayi,abinda ya sanyata murmusawa tana miqa masa hannunta dake daure da agogon
fatan daya kwanta a jikinta sosai,gefe guda kuma tana sauraron amsarsa
"Yayi,saika qaraso" Ta amsa masa tana dan kauda wayar ba tare data kashe kiran ba.
"Wace tayi kiranka?,ina zaka je?,wallahi baka isa ka fita a gidan nan ba" Sautin muryar matar ya ratso ta
cikin wayar. Lafiyayyen zagin da taji ya fita a bakinsa ya sanyata datse kiran ba tare data shiryawa hakan
ba,ta lumshe ido tana jin yadda qirjinta yake quntata
"Har yanzu yana nan a yadda yake......har yanzu babu wani abu daya sauyashi" Kalaman dake karakaina
a kwanyarta kenan
"Am sorry.....am sorry" Ta fada murya can qasa tana motsa labbanta.
Sanyin hannun yaron daya taba nata hannun ya sakata bude idanunta. Har ya qaraso inda take
ba tare data ankara ba
"Kaci abincin safe?" Ta tambayeshi tana dubansa. Girgiza kai yayi da sauri,sauta juya gefanta tana masa
nuni da doguwar yatsarta
"Dauko wancan plate din ka cinye duk abinda yake ciki na barmaka" Da zumudinsa ya juya din yana
nufar wajen. Zama yayi sosai bayan ya bude yaga abinda ke cikin,soyayyen chips da ragowar soyayyen
qwai,ya fara kaiwa bakinsa yana murmurshin jin dadin garabasar daya samu.
Qananun surutai da muryarsu tun kafin sukai ga isowa falon shine yaja hankalinta. Ta kafe qofar
falon da kallo har zuwa sanda suka yaye labulen suka bayyana,yana gaba tana binsa a baya......
*_TURQASHI_*
*_TURAREN WUTAR DA ZAKI SANYAWA DAKI AMMA HATTA DA LABULAYE KAYAN SAWAN DAKE SAQALE
A DAKIN SU KAMA DA QAMSHI?_*
Khumra
Turaren wuta
Kulaccam
Lablab
Oil perfumes
*karki kuskura kada kiyi ganganci ayi babu ke,kai tsaye tuntubeta ta wannan number*
08032119803
Ko ki lalubeta ta nan👇🏾👇🏾👇🏾
*Facebook_kabo daughter*
*Twitter_kabo daughter*
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
*Arewabooks:Huguma*
PAGE 16
___________________________
*_YA SUBHANALLAHI_*
_________________________
Idanunshi a kanta sanda yake shigowa zuwa cikin ainihin falon da yake da banbamci da sauran
faluka dake gidan. Itama shi take kalla,kaman yadda suma bambanta a kamanni da mahaifinta haka suka
bambanta a halaye da kuma dabi'u.
"Kai....kai,ubanka.....cireshi daga bakinka......tashi!" Matar dake biye dashi a baya ta furta a zabure bayan
shigowarta dakin,idanunta kuma suka fada akansa sanda yake cin Chip's din hankalinsa kwance. Debe
idanunta tayi daga kansu ta maida kan yaron da ya tsorata sosai saboda yasan halinta,ba shiri ya miqe
tsaye har farantin chips din dake saman cinyarsa ya fadi,tsirarun dankalin ciki da yayi saura ya tarwatse a
wajen.
Gewayesu yayi da gudu gudu zai fice yana matsawa daga wajenta amma duk da haka bai tsira
ba,bayan uwar harara da take narka masa sai data bishi da ranqwashi tana cewa
"Bansan inda ka dauko kwadayi ba don ubanka,saidai daga can bangaren uban naka,don mu nan ba
makwadaita bane,masu kwadayin ma addu'ar shiriya muke musu.....ba zaka jazamin masifa ba......cin
abincin da aka da kudin haram?,ina zamana lafiya?,to muddin zaka ci gaba da shigowa dakin nan kuwa
sawuna a likkafa zan maidaka gidan naka uban" Tayi maganar tana daga tsaye tana kallon qofar da tuni
ya riga ya fice daga ita.
Dauke dubanta tayi daga kanta,don gugar zana irin wannan tash ba kasafai ta fiya damunta ba.
Idan d sabo ta jima da sabawa da ita din,ta kuma zame mata jinin jiki.
"Ni zan fara gaidaki ko kece zaki fara gaidani?" Muryarsa ta dawo da hankalinta daga duniyar tunanin
data fara nausawa. Fararen idanunta ta aza a kansa,mutumin dake a mazaunin mahaifi a
gareta.....wanda ya kamata a ce a yanxun basu da tamkarshi,koda baiyi ya mahaifin nasu ba.....amma ya
zamana ya toshe wani babban kaso cikin gibi da rayuwarsu zata samu.
Qaramin bakinta ta motsa wanda sauri yakan kira da shegen bakin rashin d'a da rashin
mutunci,da wannan muryartata da sautinta ke cike da sanyi da nutsuwa tace
"Lafiya qalau na kwana,sai uban baqinciki da takaicinki dake shirin hallakarmin da rayuwa" Ya furta cikin
hargagi tamkar dama yana jiran ta gaidashinne.
Har yantsu dogon yatsanta yana saman labbanta,yayin data kafe mutumin data kira a dazu da
kawun nata da idanunta,tana dan motsa yatsan nata saman lebenta tana kuma nazarin fuskarsa
furucinsa dama motsinsa.
Ko sau daya bata taba ganin mutunci kima da martabarsa ba......daidai da misqala zarratin bata
taba daukarshi da wani babban matsayi ba......abu daya ta sani,komai lalacewar fura tafi kashin
shanu......komai kashinsa da zabgewa gami da lalacewar martabarsa a idanunta sunanshi kawunta kuma
qani ga mahaifinta.
Maida idanunta tayi ta lumshe kawai kaman yadda ta saba masa a yawancin lokuta......tasan me
ya sanyashi wannan zuwan,wani boyayyen buqatarsa ne dake a qasan rai da bai samu biyanta ba. Ta
tuna haduwarsu ta qarshe dashi a wancan satin daya wuce. Dama ta sani ba zai haqura ba.....shine zai
fake da wasu abubuwa wanda shi kansa ba kubuta yayi daga su ba.....yazo ya samu wannan matar da
qiyayyarsu ta jima da yin tsiro da jijiyoyi a cikin jikinta. Takai qarshen maganar sanda take bude idanunta
saman fuskar bibo.
Haduwa idanunsu sukayi waje daya da nata,ta juya qwayar idanunta tana watsa mata wani kallo
"Ki dain kallona da wadannan tsayyayun idanun naki na rashin kunya masu kama da idanun mage.......kai
ya kamata ka tsaya a kanta saboda tana jawowa bawan Allah zagi,wanda ya jima da mantawa ya zauna a
duniyar.....amma ina kyautata zaton kullum ta Allah sai mala'iku sun tadashi zaune sun nuna masa
qazantar da d'iyar cikinsa ke aikatawa. Ya rasu yabar yara sama da goma sha takwas amma ba wadda ke
hana masa kwanciya lafiya a kabarinsa sai ke?,ai wallahi Allah wadai da haihuwar d'iyoyi irinki.....indai
haka haihuwar take gwara mutum ya zauna a haka" Tana maganar tana jujjuya hannunta guda daya
gami da yarfeshi,idanunta a kafe saman fuskarta,kaman yadda itama tunda ta fara maganar ko sau daya
bata dauke dubanta daga kan bibo ba.
Maganganun nata sunkai mata iyaka,tana jin ta gama daukar iya abinda zata dauka a iya wunin
yau,saboda haka a nutse ta sauke qafafunta qasa ta miqa hannunta ta dauki handbag dinta ta miqe
tsaye tana gyara rolling din mayafinta
"Fita zanyi,kuma ina da buqatar na kulle mana dakin kafin na fitan,idan ba damuwa ko zamu koma
tsakar gida mu qarasa maganar a can?"
"Kaji ko?......dama ai na sani,babu wani sauran wanda take gani da kima a duniya.......yau koda fadima
zata dawo duniya bata isa ta juyata ba bare alhaji" Tayi saurin cafe zancan.
Wani irin juyowa tayi gareta ta zube mata manyan fararen idanunta
"Kaman bakiji me nace ba ko?,nace muje tsakar gida mu qarasa......bankai ga furta cewa banda lokacin
sauraro ba" Ta mata maganar dalla dalla tana kallonta.
Sosai bibo ta kafeta da kallo,har yanzu babu abinda zai sauyata......wannan rashin shakkar da
rashin tsoron suna nan rubuce baro baro cikin ayyukanta da dukka motsinta,dakiyarta da shariyarta da
daukan abu me zafi ta wulwulashi ta sauya masa mizani idan taso.
"Idan ta fito kawu qofar kawai zakaja jam lock din zai shige,ka sameni a qofar gida muddin baka wuce
minti biyar ba" Tayi furucin sanda take takawa zata fice a falon tana riqe da vail din abayarta daya zame
tana qoqarin mayar da rolling dinta yadda yake.
"Tashi muje na sameta a waje din inji da wacce hujjar zata kare kanta kuma" Ya furta dukka jikinsa na
nuna zumudi da qaguwar yaga ya bita.
Da kallo bibo ta bishi tana daga zaune a kujerar ba tare data motsa ba baqinciki yana kasheta. A
yau tana jin kaman ta tashi ta rufe rufa'i da duka. Yau ya tabbata mara amfani kwata kwata a garesu
gaba daya.
"Ko nayi gaba kya rufe musu dakin?" A zafafe ta miqe tana gyara daurin dankwalinta
"In zauna inyi me a nan?,Allah ya sawwaqe,ai ni tawa son zuciyar bai fara sauka har takan kayan
haramun ba" Ya jita sarai,ya kuma san da biyu take maganar,saidai a yanzu baya jin yana da
lokacinta,dukka tunaninsa yana ta'allaqe akan sabreen. Yasan halinta sarai,muddin ya haura mintunan
data dibar masa,yayi imanin da gaske zai iya zuwa ya tarar ta wuce din abinta.
Tana rungume da hannayenta sanda take tsaye a qofar gidan nasu ta bashi baya. Fuskar nan dake
shimfide da wani irin kwarjini yau din cakude take da ninkin rashin fara'a da walwala na tun asali da aka
santa dashi. Har tsakiyar zuciyarta takejin wani abu yana tsikarinta duk da yadda iskar dake yawo sararin
subhana ke kada doguwar riga da dan mayafin saman kanta tana watsa daddadan qamshin turaren dake
tashi a jikinta. Turaren da ita kanta yake sanya mata nutsuwa da kwanciyar hankali,dadinsa ya sanya ta
zabeshi a matsayin turarenta na dindindin,duk da batayi tunani matsayinta zaikai a nan kusa ta
mallakeshi ba.
Ta kalli agogon hannunta,yaci mintuna hudu cikin minti biyar din data bashi,don haka ta fara
takawa sannu a hankali tana matsawa daga gaban gidan nasu.
Tun batayi nisa ba ta jiyo taku da kuma muryar kawun nata,bata da buqatar kallon fuskarsa ko
doguwar magana ta hadasu,buqata gareshi zata sallameshi.....kamar yadda tun tale tale.....kaman yadda
tun can baya bashi da amfani a garesu a yanzun ma bata tunani akwai wani sauran amfani da yake dashi
a rayuwarsu,don haka ta sabule jakarta,ta zuge ta zaro wani abu daga cikin kudin da yayi saura a ciki ta
dunqule a hannunta tana jiran isowarsa
"Ke sabreena......sabreen" Ya hada da qwala mata kira tamkar ya bata bashin kudi tana kuma shirin
gudar masa dashi. Ranta ya sake baci,ta tsani kwakwazo,a banza ma idanun 'yan unguwar da dukka
kunnuwansu harma da hankulansu suna kanta,kowanne motsi ko taku nata a biye suke dashi,sauraro
suke.....jira sukeyi na samuwar dukkan wata dama da zasu samu abun magana a kanta. Wannan ya
sanya tadan saurara daga tafiyar da takeyi tana dakon isowarsa. Ko a sannan tana iya ganin idanun
tsirarun mutanen unguwar da suka samu sararin fitowa da safen kamar ita yana karakaina a kanta.
Irin wannan kallon nasu gareta ya zama tamkar jarrabi ko masifa cikin rayuwarsu. Akwai abubuwa
da yawa tasan da akeson gaya mata amma babu wannan fuskar. Bataga dalilin zallar rashin adalci irin
nasu da suke gwada mata ba suke kuma gwadawa rayuwarta ba. Sun sany hannu dukka da qafafunsu
sun tankwabeta sun kuma tankwabe rayuwarta a sanda take da tsananin buqatarsu......a yanzu kuma
data yankema kanta bata da buqarsu.....a sannan su kuma suke qoqarin dawo da ita su dankwafar da
ita.....suka kuma fidda makamansu da harsunansu wajen illata mata gangar jiki da zuciya.
"Me na samu?" Ya iso gareta yana tambaya sanda motar da take da tabbacin waye a ciki ke dab da isowa
inda take. Kowanne mutun da zatayi mu'amala dashi ko kuma tayi mu'amala dashi din......sau daya tak
take masa wani karatu a taqaitaccen lokaci.......fahimtar waye kai?......meye qudurinka.......meye
motsinka?.....mene manufarka......da sauran dukkan wani abu daya shafi rayuwarka yana zama
RUBUTACCE cikin shafin qwaqwalwarta. Bata fiya manta abu ba,haka bata missing target saidai idan
bata nufaci abu ba.
Ta baya ta miqa masa kudin sannan ta fara takawa zuwa ga motar da tuni ta iso inda suke
harma ta samu wajen tsaiwa.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 17
daga inda yake a zaune din yakejin kamar gilashin window din motar ya masa shamaki daga
kallonta duk da yadda yake tarwai yake kuma iya baka daman gano komai dake ta wajen motar......duk
da haka yana jin kamar ya rage ma idanunsa armashin kallonta,don haka ya kasa haqurin isowartata,ya
sanya hannu ya sauke dukka gilashin nasa qasa.
sau daya tak ta taba ganinsa ido da ido,amma ta haddaceshi tsaf,tun daga abun hawansa har
zuwa halayya da kamanninsa.......
Kakkaura kuma faffada da zaka iya kiransa me jiki saidai bai cancan ba. Maabocin iya ado sosai
da murza hula ta zauna a kansa kamar shi yake saqa ma kansa ita. Yadda turarensa da shigarsa keda
kyau da tsari haka ma kalaman bakinsa,saidai kash!.....daidai da wucewar daqiqa guda bata taba jin wani
abu me kama da SO K'AUNA KO BEGE nashi ya tsartu a ranta ba.
Waishin mcikina meye SOYAYYA ne?. Ita kanta jerin kalmar SOYAYYA da yadda mutanen duniya
suka daukaketa na daya daga cikin abinda ke sanyata dariya koda bata shiryawa hakan ba. SHIRME shine
cikakkiyar ma'anar da take ganin yafi dacewa da a kirata ko kuma CUTA,idan akwai sunan da yafi haka
lalacewa ma a nata ganin daidai ne a kirata da wannan sunan.
Yadda yake tsareta da kallo ya sanya qirjinta ya dinga suya duk kuwa da cewa ta saba da irin
wannan shegen kallon. Kwarjininta na daya daga cikin abinda ya sanya take tsira daga guba da dafin
MAZA duk kuwa da cewa ita da kanta take tsalle ta afka tsakiyar tarkon bisa tsananin lissafinta,ta kuma
samu sa'a da nasarar zame kanta cikin SALO da kuma qwarewar iya wasa.
Da hanzarinsa ya fito ya zagaya don bude mata qofar motar,hakan ya bawa kawu dake lafe yana
kallon komai qare masa kallo.
"Iya shaddar jikin yaronnan kawai ta isheni jari wallahi,wannan tsinanniyar yarina,yanzu meye aibun
wannan da ba za'a aureshi ba?" Ya tambayi kansa da kansa yana naniqe da kudin hannunsa.
Idanunsa ya aza a kanta bayan ya bude mata motar,sai ya sakar mata murmushi,tadan lumshe ido
tana qaqalo nata murmushin cikin dauriya da son maida masa. Gefe guda zuciyarta na cike fal da qarin
wani mamakin akan D'A NAMIJI. ta tuna kalamansa akan matarsa dazun dazun nan,amma a yanzun
gashi a gabanta ita kamar zai narke. Ta yaya zata yadda tayi aure a duniya?,ta yaya zata bari zuciyarta ta
kamu da soyayyar wani namiji?,yaya za'ayi ta banzatar da lafiyar zuciyarta cikin soyayyar wani?,soyayyar
halittar da babu tausayi ko jin qai a tare dasu?,halitta mafi son kai cikin halittun duniya gaba
daya?,halitta me tsananin mugunta da son cutar da halittar mace 'yaruwarta?.
Ba zata iya sadaukar masa da murmushinta na dogon lokaci ba,duk kuwa da cewa fake smile
ne,don haka ta zame jiki ta shige cikin motar ya mayar ya kulle yana sauke ajiyar zuciya. Yana jin duk
duniya ba wanda ya kaishi sa'a a yau din. Yana jin kamar duka ranar tashi ce.
A kujeran driver ya zauna yana qoqarin tayar da motar amma duka ido da hankalinsa yana kanta
"Ko ina ya baro matarsa ta sunna da har ita ya danqara mata wannan sunan?" Wannan ba baqon abu
bane a wajenta,saidai har yanzun mamaki da lamarin maza bai gama sakinta ba.
"SAMHG store" Ta amsa masa a nutse tana gyara agogon hannunta daya goce
"An gama ranki ya dade" Ya fadi cikin zumudi yana tayar da motar.
Sun jima akan hanya yana tauna abinda zaice da ita,don a taqaitaccen saninsa da ita.....mutum
ce me matuqar tsari,nutsuwa da aje komai a bisa gurbi da muhallinsa. Bayaso ya kwafsa kaman waccan
karon,bayaso damarsa ta sake kubce masa,duk da cewa har kawo yanzun baisan me ya aikata daya rasa
wancan damar a wancan karon ba.
Yaji babu dadi ainun saboda ya qwallafa rai sosai a kanta. Ta yiwa zuciyarsa wani mahaukaci
kamu a ganin farko. Yayi tsammanin kudinsa da ajin mataki na rayuwa zai saya masa ita cikin qanqanin
lokaci,sanin da ya yiwa 'yammata kenan a yanzun,ballantana ita dake da kyau da aji irin wannan.
Sanda yake wannan tunanin nata nazarin da karatunsa duka a kansa yake. Yadda yaketa
rejecting kiran dake fama shigowa wayarsa a jejjere. Duk kiran da zai shigo sai ya katseshi. Tuni hankali
da kuma jikinta ya bata wanda ke kira.
"Zan iya cewa wani abu?" Ya tambaya a ladabce yana murza steering motar cikin qwarewa
"Kafin sannan ya kamata ka daga wannan kiran ko?" Ta fada idonta akan fuskarsa.
Motsawa kadan yayi yana duban wayar ta qasa idanu,bai zaci ma ta lura da hakan ba. Haushi ya
soma kamashi akan kiran da take masan babu qaqqautawa. Yasan zancan gizo baya wuce na qoqi,tunda
bai jima da fita a gidan ba,yasan kuma abinda ya fito ya baro a gidan
"Tarin damuwa ce da matsaloli kawai take dauke dashi" Ya furta yana jan siririn tsaki.
Har tsakiyar ranta taji saukar maganar,ta lumshe ido kadan tana budesu. Yana nan din a
haka,yana nan yadda ta karanta. Tayi qoqarin tureshi daga shiga layikanta,tayi qoqarin hanashi shiga
cikin tarkonta don baya cikin irin mazan data zana bisa layi da gurbin rayuwarta,taso ta barshi ya samu
me hukuntashi a gaba.....amma tunda har ya sake dawowa cikin rayuwartata cike da karsashi da
zumudi,to tayi imani hukuntashi yana cikin qaddararta ne. Ba kuma zata qyaleshi ba,a wannan karon
saita hukuntashin yadda ta saba hukunta maza irinsa. Maza irinsa basa tsira daga tarkonta......basa tsira
daga kamunta,hakanan basa tsira daga hukuncinta.
Cikin salo na dabarar da yake gani kaman ba zata gane ba ya latse wayar,ya kuma jefo mata
maganar da tafi damunsa
"Nima bazan bari ka tafi ba" Ta furta,a bakinta bisa mizanin ma'ana qwaya daya tak da hankali zai iya
fahimta,amma kuma an aje ajjiyayyar ma'anar da ake nufi da maganar can qasan zukata.
Wani irin dadin daya sabbaba masa lafiyayyen murmushi ya ziyarceshi. Bai taba kawowa ko kusa a
ransa samun wannan gwaggwabar nasarar a kurkusa haka ba,amma kuma,sai wani sashe na zuciyarsa ke
gaya masa
"Duk kyau ko matsayinta zata sauko......a yanzun fa mata ke neman mazan aure idanu rufe" Hudubar
data shiga kunnensa kenan,kuma ya yarda da hakan dari bisa dari.
"Amma hanan banga alama ba......bansa inane mazaunin da kike rayuwa ba,gida unguwa da sauransu"
"Gaggawar me kakeyi?,kada ka samu damuwa" Ta amsa masa tana jin ya ginsheta gaba daya,tana jin ta
damu qarshen zamansu yazo,ta qagu su isa SAMHG store ya ajeta ya bata sarari.
A hankali ya kutsa motar babbar harabar kantin saida dukkanin kayan buqatar rayuwa,wanda
zaifi kyau ka kirashi da kasuwa a sauqaqe amma kuma a zamanance. Ba abinda basu hada ba na kayan
buqatu,tun daga tufafi zuwa kayan masarufi. Wajen nada matuqar girman da idan ka kirashi da duniyar
siye da siyarwa. Girmansa ya sanya yake da mashigu daban daban da kuma guraren fita mabanbanta.
Cikin tafkekiyar harabar wajen ya aje motarsa,ya kasheta cikin mutuwar jiki da kasala yana
waiwayowa inda take zaune tana qoqarin rataya jakarta gami da daukar wayarta ta riqe wadda ke aje
saman cinyarta.
"Idan ban damuwa zan dan tayaki tattaki zuwa ciki......don naga wajen kamar cike yake da maza da
yawa......ni kuma ina kishin na barki ki fita ke daya a kallemin ke" Ya furta cikin kulawa da wani irin
narkakken so dake ragargazar zuciyarsa.
Da wani sassanyan kallo ta jefeshi,qawataccen murmushin nan dake qawata fuskarta da kuma
labbanta ta sakar masa. Ta rausayar da kanta gefe tana juya idanunta. So take ta sallameshi a iya
haka,bata buqatar doguwar damuwa. A lokaci irin wannan da takai qarshen mission dinta,ko fita unguwa
ba kasafai take damunta ba sai idan buqatar haka ta taso. To amma hakanan taji akwai buqatar ta fita
din,akwai kuma buqatar ta fita tayi musu siyayya.
"Baka da damuwa akan duka wannan......wannan hanan din ba komai idanunta ke kalla ba ballantana su
burgeta" Ta bashi amsa a nutse.
Murmushi ya saki yana qara narkewa a sonta,yana ji cewa zai iya yin komai don ya mallaketa,yana
jin cewa muddin ya sake barinta ta subuce masa a wannan karon ya tafka babbar asarar da bazai iya
maida madadinta ba,baya jin ma zai bari hakan ya faru dashi sam sam.....kai koda tuna hakan na iya
faruwar bayason yayi.
"Na ga zahiri......na kuma tabbatar wannan halittar ta daban ce......gamu cikin neman sa'ar kasancewa da
ita" Ya fada yana lumshe idanu. Kai ta kawar amma tana murmushin yaqe. Ya numfasa bayan ya gama
qare mata kallo cikin shauqi ya dauki wayarsa dake aje tun sanda ya maidata silent ya bude.
Tarin miscall a qalla guda goma kyawawa daga gareta. Ya jawo maballin sama ya sharesu yana
sakin tsaki can qasan ranshi tare da wucewa mobile app na banking da yake ajiyar kudadensa.
Sosai ta jingina da makarin motar idanunta a lumshe sosai,sai kayi tsammanin bacci ko kuma
gajiya ne sukayi mata yawa,saidai a cikin biyun duka babu ko daya a ciki.
"A taimaka a karantomin account number na dan bada wani tukuici" Idanunta ta janye daga saman
wayar nasa,saita tashi ta zauna sosai tana dan sakin murmushi
"Please.......ba wani abu bane me yawa.....just tukucin bani damar ganinki da kikayi a yau ne" Bata sake
ce masa komai ba,sai ta zura hannunta cikin jakarta,wani dan siririn card me ruwan zaibar gold ta ciro ta
aje a gefansa. Ta dauke kai tana qoqarin bude murfin motar wanda ita kanta tasan ba zata budu ta sauqi
ko dadin rai ba......ta kwana da sanin meta aiwatar mata.
Cikin qasa da minti daya taji ya furzar da iska daga bakinsa gami da cewa
"Why not?,godiya me kima......godiya nake qwarai......but motarka tana nema ta riqeni fa"
"Da zatayi hakan data taimakeni ai" Ya amsata yana sake lafewa jikin kujerar. Kyawawan sexy eyes dinta
ta waro waje kadan,sai kuma ta daga hannunta tana duban agogo
"Akwai alqawari da nayi,bana so kuma na saba......idan ka sani na saba kuma......next time kafin na baka
daman sake haduwa dani....." Katseta yayi yana dariya ta hanyar hada hannayensa biyu waje daya
sannan ya saukesu ya juya yana buda side dinsa
Da lumsassun idanunta ta bishi da kallo har zuwa sanda yake zagayawa gaban motar zuwa daya
side din da take zaune. Yayi dukan dabarunsa amma hakan baiba,don haka ya zagayo yana fadin
" Bansan me yake faruwa,lafiya lau qofar yake,bari nasa a duban.....am really sorry" Ya sake apologizing
yana hade hannuwansa.
taka Kai kawai ta daga masa tana irgen lokutan cikar target dinta. Cikin saa kuwa ya juya ya fara
takawa yana barin wajen,wanda hakan ya bata damar janye kallonta sannu a hankali daga kansa,ta
kuma maida saman wayarsa dake ajiye a wajen tana bada haske,tabbacin yunqurin hanata komawa key
yayi daidai kenan,saita katse kiran da takeyi daga tata wayar zuwa tasa don sanya wayar awake.
Tarin miscall dinne kuwa ta samu kamar yadda tayi zato,dukka kuma daga number dake ajiye
cikin wayar da sunan MOM SUHAIL.
"SUHAIL" Ta ambata a fili,idan har bawai ta manta ba suhail din shine sunan first born dinsa kamar
yadda T.j ya tabbatar mata.
Wani irin tausayin matar da batasan ko wacece ba ya fara ratsa ta. Tana shirin karkata akalar
binciken nata zuwa wani sashe na daban saqon SMS ya shigo wayar.
MOM SUHAIL kamar yadda yake a rubuce ta bangaren kira. Bata tsaya dogon jinkiri ba ta
bude,gajeran saqo ne kamar haka.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 18
_Nayita kiranka baka dauka ba,kome meye mukayi da kai kafin ka baro gida ai ya kamata ka tsaya
kaji dalilin kiran da nake maka babu qaqqautawa,bayan ka fito ciwon suhail ya tashi,a yanxu haka muna
asibiti,amma babu ko sisi a hannuna,baka barmin komai ba,already kuma account dina yana buqatar
naje banki na gyara bare nayi hidimata da kudina yadda na saba_.
Wani abu me tauri taji ya tsaye mata a wuya,ta zura hannu a jakarta ta ciro wayarta,tanason
taga nawa ita ya kashe mata?,nawa ya saka mata alhali ko sisi matarsa bata amfana dashi ba?.
Naira dubu dari ta tarar. Wani matsiyacin tsaki ta saki,cikin dukkan arziqinsa ya rasa da meye
zaiyi mata kyauta sai naira dubu dari?. Bata tsaya batawa kanta lokaci ba ta sauka ta koma mobile app
dinsa da bai jima da fita a kai ba.
Daga password har username dinsa fes cikin kanta,tamkar hadaka ko gamayya sukayi dashi wajen
creating dinsu a sanda zai bude manhajar. Cikin qasa da second goma komai ya bude,tarin miliyoyin
kudaden dake kwance cikin account din nasa suka bayyanarwa idanunta,sai ta koms ta jingina da kujerar
motar tana kallonsu,kamar ma bata tsoro ko shakkar dawowarsa.
Numfashi take fitarwa d'ai d'ai qirijinta na sake quntata. Tarin zallar rashin imanin maza yana
sake tabbatar da kansa a zuciyarta.
"Yana da wannan kudin ya fita yabar matarsa babu ko sisi?,yana da irin wadannan kudaden yabar
yaronsa cikin halin ciwo?,yana da wannan kudin ya gaza siya masa abun hawan da idan lalura irin
wannan ta taso baya kusa zata kaisu zuwa ga asibiti cikin gaggawa?.
Tsanar MAZA tsanar SOYAYYA da kuma tsanar AURE suka sake linkuwa cikin ranta. Irin wannan
shaidojin na gani da ido ta din saidai ta bada labarinsu. Shi din ma ba komai bane a cikin maza......bata
kuma san namiji na nawa bane shi din da a yau xai shiga makarantarta.......a yau zata sanyashi ya koyi
darasi kaman sauran,saidai nasa darasin yazo ne a gaggauce saboda gamawa da babinsa da tayi,da kuma
dadewa da tayi da sanin shi din wayeshi?.
Beneficiaries dinsa ta duba,cikin sa'a tun batayi nisa ba taci karo da sunan da yayi daidai da
sunan matar
*ameena mu'azzam*.
Kai tsaye ta saka amount din da yayi mata ta kuma karkatasu zuwa ga account din.
Daidai lokacin data hangi tahowarsa,ta daga hannunta ta zare wania abu daga jikin qofar,sannan
ta maida hankalinta kan wayar kamar ba me wayar ne yake dosota ba.
Hankali kwance ta koma ta goge alert massage din da kamfanin sadarwa suka aiko,ta kuma koma
zuwa ga email a gaggauce ta goge nashi tayi minimize ta maida wayar mazauninta tana karanta sunan
banking da yake amfani dashi,sannan ta zaro tata wayar tana duba ma'ajiyar lambobi dake cikin wayar.
Sunayen dake ajjiye cikin wayar ta fara bi,cak ta tsaya saman wani suna da yayi daidai da sunan
banking nasa,ta danna malatsi na tura saqonni,ta kuma aika da saqon a gajarce
"Done" Ta jefa wayar a jaka daidai sanda ya iso bakin window din suna sake yunqurin buda motar.
Ja daya bakaniken ya yiwa murfin ya bude,sai ya waiwaya yana dubansa cikin mamaki,wanda
shima cikin manakin ya iso
"Kai amma nayi mamakin faruwar hakan" Ya matsa yana kama hannun motar ya matsashi har sau uku.
Mamaki yadan sake kamashi,amma kuma kiransa da tayi d nuryarta me laushi ya dauke hankalinsa daga
nan.
"Okay na gode to" Ya fadiwa bakaniken yana cirar wani abu a aljihunsa adan gaggauce saboda kiran
nata.
Bude mata qofar yayi,ta sako qafafunta ta fito tana gyara zaman abayar jikinta. Cikin nuna kulawa
yake fadin
"Da alama motar bata gaji dake ba,kamar yadda me motar shima bai gaji da kallin wannan kyakkyawar
surar ba......don Allah ayimin lamuni a bani exact gurin da zan sameki.......da gaske nake,banzo da wasa
ba,ni din ba irin sauran samarin yanxu bane......da niyyar aure nazo" Ya qarasa maganar yana lanqwashe
murya.
A nutse ta watsa masa idanunta da suke sake narkar dashi. Batajin daga rana irin ta yau ma zai
sake samun damar tsaiwa da ita a muhalli daya irin yanzun. Wannan itace dama ta qarshe kuma lokaci
na qarshe a wajensa tsakaninsa da ita.
"Are you sure?" Ya tambayeta yana kallonta cikin kokwanto. Saboda shi kansa yasan samunta din abune
me wahala.....ta subuce masa wancan karon.....hakanan haka ya qaraci karakainarsa da nemanta amma
ko me kama da ita babu ballantana ita karan kanta din. Kai kawai ta gyada masa sannan ta juya ta soma
takawa tana barin wajen gami da cewa
"Nike da godiya kyakkyawa" Ya fada murya a lanqwashe yana binta da kallo da zazzafan so,yana jin
kamar ya saceta ya gudu da ita ya mallakawa kansa ita.
A nutse take taka kowanne step da zai sadata da ainihin makeken store din. Murmushi ne
kwance saman fuskarta ita daya,duk da bata juya ba amma ta tabbatar yana tsaye ne yana kallonta,tana
hasaso yadda fuskarsa zata koma a sanda ya laluba asusun bankinsa ya taras da barnar datayi masa,tana
hasaso yadda wannan tattausan kallon zai koma zazzafan kallo da kuma zurfin tunanin TA YAYA AKAYI
HAKA YA FARU?.
Yadda take daukan hankula da idanuwan wasu daga cikin jama'an dake sabgoginsu a waje da
cikin shagon bai dameta ba,don ba wani baqon abu bane a wajen ta. Itadai ta sani,akwai dubbai zuwa
miliyoyin mata da suka zartata a kyau.....don bata tana daukan kanta ta sanya a sahu ko jerin kyawawan
mata ba,amma batasan mene a tattare da ita me matuqar jan hankali irin haka ba.
K'annenta sune gaba da komai da kuma kowa. Buqatunsu kuma sune gaba da nata buqatun.
Don haka duk list na abinda suke buqata ta fara dubawa. Tana tsinta tana jefawa a cart.
Ta kwashi a qalla minti ashirin tana nasu siyayyan sannan ta fara nata. Siyayyarta bame sauqi
bane,tana da tsari tana zabi,ba komai yake burgeta ba kaman yadda a rayuwarta na zahiri ba kowa ke
burgeta ba,komai nata yana da tsari,don haka ta bata lokaci sosai akan nata kayan,ta saki jiki kuma
kamar ba zata bar shagon ba.
Sai data gama tsaf sannan ta gangara bangaren kayan maqulashe. A duk sanda ta samu kudi irin
haka bata rabo da siya musu kayan taba ka lashe,harda ajiye wasu ma cikin daki. A duniya idan akwai
abinda taqi jini shine taji sunce BABU ko BANI DASHI ADDA....kalma ce da bata yarda a yanzun ta shiga
tsari da babin rayuwarsu sam sam.
Sashe ne dake danqare da chocolate kala kala da kuma biscuits. Masu tsananin tsada da kuma
masu matsakaicin kudi. Da ido ta dinga bisu daya bayan daya,wani lokaci can baya daya shude bata isa ta
sanyasu cikin idanunta ba,wani lokaci can baya daya shude sunfi qarfin tabawar hannuwanta ballantana
akai ga batun sanyasu a bakinta.....wani lokaci can baya daya shude saidai ta hangesu......hangema daga
nesa.....wannan ya sanya tayi alqawari......ta kuma ci alwashin muddin tana raye ba zasufi qarfin rayuwar
'yan uwanta ba.
Tana cikin dubawar ta hangi favourite chocolate dinta,ta kasa jurewa sai data daukota ta bareta ta
jefata a baki,daidai sanda taji anyi kiranta da daya daga cikin sunayenta data mallakawa wani.....sunayen
da suke zama tamkar tag ne ga kowanne namiji daya taba shiga rayuwarta.
"Basma" Iya sunan daya kira tun kafin ta waiwaya ya gaya mata waye. Duk wanda ta bawa sunanta
wannan sunan nashi ne shi daya,wannan sunan shita mallakawa shi kadai.....wannan kuma ya zame
mata stamp kuma alama ta kowanne mutum daya taba shiga DUNIYArta.
Murmushi ta saki tun kafin ta juya tayi tozali da wanda yayi kiran.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 19
________________________
*_Katafaren sansanin UMMUMAHNOOR LUXURY,TA SHIRYA TSAF DON SAMA MUKU TSALA TSALAN
KAYAN ADO DA SUTURA NA KECE RAINI IRIN NA 'YA'YA MATA,IRINSU_*
Atamfofi
Laces
Shadda
Materials
Takalma
Jakunkuna
Mayafai
Trolley
Oil perfumes
Numbers
08034469681
08135142610
Handles
Instagram @ummu_mahnoor_luxuries
Facebook ummu_mahnoor_luxuries
___________________________
Iya sunan daya kirata dashi ya bayyana mata kanshi tun kafin takai ga waiwayowa.
Sanda ta juyo din yana tsaye daga bayanta,ya kafeta da wadannan jarababbun idanun nasa data
sanshi dasu tun a lokacin,idanuwan data tsana fiye da kowanne ido a duniya,idanuwan da kuma tafi
tsana bayan baqin mugun halayen dake rataye da jiki da zuciyarsa.
"Malam nasiru....kana lafiya?" Ta fada calmly tana dauko wani box na chocolate din ta jefa cikin kwando.
Takowa ya soma yi yana sake kusantota,har yanzun dai bai dauke idanunsa a kanta ba.
"Kana mamaki ne?.....kayi tunanin bazan iya shaida ka ba ko?" Ta tambayeshi da murmushi a saman
wannan miskilar fuskar da zaiyi wahala kaga fitar murmushin daga samanta.
"Wannan basman bata manta fuskar mutanen da suka taba shigowa cikin rayuwarta.......hakanan
wannan basman bata manta fuskar mutane irinku......hope kana lafiya ko?" Ta sake tambayarsa tana
tafiya a nutse,tana kuma ci gaba da zaban abinda yayi mata tana jefawa a kwandon.
Tarin mamaki ne ya lullube masa zuciya ainun......tsahon lokutan yayi tunanin duk ranar da
sukayi haduwa ta farko da ita zata razana......zata kuma tsorata,idan da yiwuwar ma ta nemi guduwa
duka zatayin duba da girman laifin data aikata masa.
"Tana da wayo......tana kuma da hadari......da alama akwai abinda ta taka" Maganar abokinsa kenan ta
dawo cikin kansa bayan wani zama da sukayi dashi,wannan ya sanyashi Maida hankalinsa jikinsa sosai,ya
kuma tattaro bacin rannan da ta dasawa zuciyarsa wanda har yanxu a cikin bala'i da masifar data sakashi
yake
"Idan kika mantani ai baki cika 'yar halali ba......ai dama idan kere na yawo zabo na yawo dole wataran
zasu hadu" Ya farta cikin fushi.
"Yar halak?" Ta furta a sarari,sai ta dakata da abinda takeyi ta waiwayo ta zuba masa idanu
"Akwai bashi ne tsakaninmu da kake nema na har kalmar kere da zabo zata gitta tsakaninmu?" Kansa ya
daure tamau,zallar raina masa hankali da tayi yaga ta fito muraran. Ji yayi bashi da sauran abinda ya rage
illa ya fiddo mata makamansa.
"Kina iya cewa komai,amma kafin sannan shawara daya zan baki.......ki maido min dukka kudade na da
kika samfe daga account dina sawunki a likkafa.....ko kuma hukuma ta matsaki ki fito dasu" Idanunta ta
watsa masa tana sakin murmushi
"Kasan a inda kudadenka suke?,za kuma ka iya zuwa karba din idan na gaya maka?" A tunzure cikin fushi
da yadda takeson maida maganar wata mara alfanu ko muhimmanci ya kalleta
"Duk duniya akwai wanda ya isa ya hanani karbar haqqina?,akwai wanda ya isa ya cimin haqqina ban
karba ba?"
"Kwantar da hankalinka mana...." Tace dashi still tana murmushi,saita dafe kwandonta ta soma takawa
tana nufar ficewa daga gidan kuma tana fadin
"Gidan marayun nan......a wannan ranar kowanne yaro ya rabauta da duk wani abu na buqata da bashi
dashi,suttura kayan ado na 'yanmatan da kuke sakawa ana musu dauki d'ai d'ai cikin dare ana kai muku
su gidajen shaqatawarku da hotels kamar yadda ka gayyaceni nima zuwa naka dakin hotel din......kana
iya zuwa ka karbi komai dake hannunsu ka sanyashi a kasuwa ka maido kudinka......muddin kuma ba
zaka iya hakan ba,to ina baka shawarar ka fita daga rayuwar SABREEN......ka kuma daina
bibiyarta......idan bakaji ba kuma......zan sake sakaka fidda wasu kudaden masu ciwo da baka shirya
fitarsu ba kamar dai wancan lokacin" Ta qare maganar tana kaiwa qarshen wajen ta karya kwana tana
niyyar bacewa ganinsa.
Daya biyu uku yahada dukka yaga basuyi masa daidai ba. Wani sashe na zuciyarsa ya soma
zugashi da
"Ta yaya kana tsaye qaramar yarinya me qarancin shekaru zata nemi raina maka hankali?".
Ya samu kansa da kansa da tuhumar kansa tare da ganin tsananin baike da wallensa. Wannan
tunanin kadai ya qara masa qaimi,ya taka qafafunsa cikin azama da qwarin gwiwa ya soma rufa mata
baya lokacin da takeji a ranta ta kammala siyan duk wani abu da suke da buqata ita da 'yan
uwanta,wanann ya sanya ta nufi gurin biyan kudin kai tsaye
"Saboda ke kike nema na bani ke nemanki ba?,saboda nine mai laifi bake bace?" Hankali kwance ta
maqale kafada tana sakin siririn murmushi
"A'aha.....ba don dukka wadannan dalilan bane suka sanya ni na baka wannan shawarar ba......na baka
ita ne don gudun kada ALLURA TA TONO GARMA"
Hakanan yaci gaba da rufa mata baya tamkar me tsaron lafiyarta ko wanda aka bashi aikin kula da
ita. Har cikin zuciyarsa yakejin yau zai nuna mata shi waye,zai kuma tabbatar mata tayi mahaukacin
gangancin kuskure data shiga hanyarsa.
Mutum biyu suka samu ana lissafa kayansu jikin qaramar na'urar dake da alhakin qididdige fitar
kaya cikin katafaren shagon.
A hankali ta tsaya daga bayan matar wadda bata iya ganin ainihin fuskarta,saidai shigar atamfar
chiganvy gold mix match da wani irin danyen lafiyayyen lace da aka yiwa qawataccen dinkin buba da zani
ya fito da kamalarta da kuma cikar siffarta. Tsaye yake daga gefanta,matashin da duka duka shekarunsa
ba zasu haura ashirin da takwas ba. Ya bata dukka hankalinsa yana sauraren maganar da takeyi dashi
cikin muryarta dake bayyanar da tsantsar kamalarta da cikakkiyar nutsuwar ruhi data halitta. Yanayin
yadda ya rusuna ya bata hankalinsa yana saurarenta kadai zai bayyana maka zallar ladabi da kuma ganin
girmanta da yakeyi,akwai kuma tag idan ka lura sosai daga gaban aljihunsa dake bayyanar da cewa shi
din ma'aikaci ne a wani guri na daban.
Mai matsakaicin tsaho ce,hakanan me jiki ce saidai ba qiba me yawa cancan ba,ta lullube saman
kanta da 4D Vail me asalin kyau da aka zubawa duwatsu masu daraja akayi adon jiki dasu.
Sassanyan qamshinta ya dinga tasowa a hankali daga jikinta zuwa hancin sabreen dake tsaye
daga bayanta tana kallon tulin kayan siyayyar da aketa jera mata cikin ledar dake dauke da tambarin
store din.
Hannunta dake dauke da wasu kyawawan banguls masu sheqi ta miqawa ma'aikacin gurin tana
cewa
"Bansan me yasa suke son mu'amala da wannan katin bankin ba,duk sun lalace da lamarin cashless"
Murmushi ma'aikacin ya saki cikin tsananin girmamawa
"To ai hajiya yafi sauqin sha'ani ne" Kai ta gyada a hankali tana furta
"To Allah ya kyauta". A nutse ta maida dubanta ga saurayin,tun kafin tace wani abu ya sake matsowa a
ladabce yana bata hankalinsa
"Ka kiramin wancan yawalen da kuma wancan acicin suzo mu wuce kafin rana ta sake dagawa"
"Okay to in sha Allah" Ya amsa mata yana zaro wayarsa daga gaban rigarsa,yayin da ta fara takawa cikin
nutsuwa tana ficewa daga gurin hadi da gyara yafen mayafinta dake qoqarin zamewa.
Wucewar tata ya bawa sabreen damar matsowa gaba don a lissafa mata nata kayan
"Ji mana.......zaki dawomin da duk abinda kika san kin sace ko kuma saimun dangana da hukuma?"
Hannayenta ta goye a qirjinta tana kallon qofa yadda mutane ki shige da ficensu hankali kwance. Yana
da ban mamaki......saidai ita din ta fishi abun mamaki. Inda yasan meta taka a kansa......inda tasan cewa
kafataninsa.....zahirinsa da badininsa a tafin hannunta yake da baiyi gigin matsawa rayuwarta ba har ya
matso gareta har haka ba.
A nutse ta waiwayo ta zube masa farare tas din idanunta masu matuqar jan hankali da fusgar
tunanin me tunani
"Kana sha'awar yin gaba da gaba da hukumar ne?" Ta masa tambayar idanunta a tsaye car tsakiyar
nashi. Idan ya kira kansa gogaggen cikin duniya baiyi qarya ba.....muddin kuwa ya kasance hakan yana
ganin mugun ganganci ne zaiyi ya gaza samun fikirar karantar mutum daga yanayin kallo zuwa lafuzan
bakinsa ba.......
"Kina tunanin abune me wahala a gareni?" Ya amsa mata yana mamakin yadda wannan mugun
kwarjinin nata yake taka masa burki,kaifin idanunta ke hanashi daukan mataki tare da aiwatar da abinda
yayi niyya.......abinda zuciyarsa ke shawartarsa.
"Ko daya....daidai ne kuma" Ta amsa masa tana dauke duba da hankalinta daga kanshi tana maidawa ga
ma'aikacin wanda ya kammala lissafin yana gaya mata adadin abinda zata biya.
"Okay" Ta furta hankali kwance tana maida dubanta ga daya daga cikin ma'aikatan dake taimakawa da
wadanda sukayi siyayya me yawa kamarta
"Okay hajiya" Ya fada yana ajjiye qaramar calculator dake hannunsa yana qarasowa gurin tare da jira a
gama sanya dukka kayan cikin leda.
Sake Waiwayowa tayi gareshi karo na biyu. Kallon da tayi masa ta fahimci yakai matakin qarshe a iya
haqurinsa
"Malam naseer......ka shirya biyan duka bill na siyayyar sabreen ko kuwa tunda kai ka kawo qafafunka
duk da gargadinka da tayi?"
"Sabreen?" Ya maimaita sunan yana kallon idanunta. Kiran sunan sabreen da tayi a maimakon basma shi
ya batar masa da tunani cikin taqi qanqani.
"Naga uban wanda zai sakani biyan kudin nan......na fahimci na sakar miki fa da yawa" Ya furta da zafi
sannan a zafafe ya biyo bayanta. Ya tsammaci zata nemi guduwa ko ta gudu dinma,amma ga tarin
mamakinsa tun bai qarasa isowa gareta ba taja cak ta tsaya tana sauraron isowarsa.
"Ka samu aminci game da haramtattun kayanka da aka aiko maka dasu ta cikin jirgin ruwan dake
tsakanin River Benue da riba niger?.......ko kuma ka shirya aci kasuwar wannan sirrin da jami'an tsaron
dake neman kayan tamkar yadda mutuwa ke neman ruhi?".
Kamar wanda aka sanyawa sasari akan tsaida haka yaja wani wawan burki. Kallonta yakeyi da
madaukakin mamaki. Wanne irin hadari ne da ita har haka?. Wanne nisan ji da gani ne da ita?,nisan
binciken da ya bata damar gano birnannen sirrinsa da ko matarsa da suke kwana daki daya su tashi daki
daya bata sani ba?.
"Ka biyasu kudin siyayyarsu duk yadda suka buqata,na barka lafiya Alhaji Naseer" Ta qarashe maganar
tana takawa hankali kwance tana fita kwata kwata daga wajen.
"Malam qaraso ka bada kudin......ta atm ne ko cash zaka bada?" Muryar ma'aikacin ta katseshi daga bin
burbushin hanyar data wuce da kallo ya juyo zuwa wajen biyan kudin yana sauke wani irin gauron
numfashi me nauyi da zafi cikin tsananin mamaki da tsoro.
*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*
*ZAFAFA BIYAR*
*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA
ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*
_K'ALBIM Mamuhghee_
_DUNIYATA Huguma_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
_YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_
*09033181070*
89825722
1000cf
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
*Arewabooks@:Huguma*
https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997
PAGE 20
________________________
*_ALBISHIR A GAREKU!!_*
*_SHIN KUNSAN UMMUMAHNOOR LUXURIES TA TANADAR MUKU INGANTATTUN KAYAN ADO NA FITA
KUNYA KUWA?_*
*_KAMAR SU_*
Atamfofi
Laces
Shadda
Materials
Takalma
Jakunkuna
Mayafai
Trolley
Oil perfumes
08034469681
08135142610
Handles
Instagram @ummu_mahnoor_luxuries
Facebook ummu_mahnoor_luxuries
__________________________
Iya sunan daya kirata dashi ya bayyana mata kanshi tun kafin takai ga waiwayowa.
Sanda ta juyo din yana tsaye daga bayanta,ya kafeta da wadannan jarababbun idanun nasa data
sanshi dasu tun a lokacin,idanuwan data tsana fiye da kowanne ido a duniya,idanuwan da kuma tafi
tsana bayan baqin mugun halayen dake rataye da jiki da zuciyarsa.
"Malam nasiru....kana lafiya?" Ta fada calmly tana dauko wani box na chocolate din ta jefa cikin kwando.
Takowa ya soma yi yana sake kusantota,har yanzun dai bai dauke idanunsa a kanta ba.
"Kana mamaki ne?.....kayi tunanin bazan iya shaida ka ba ko?" Ta tambayeshi da murmushi a saman
wannan miskilar fuskar da zaiyi wahala kaga fitar murmushin daga samanta.
"Wannan basman bata manta fuskar mutanen da suka taba shigowa cikin rayuwarta.......hakanan
wannan basman bata manta fuskar mutane irinku......hope kana lafiya ko?" Ta sake tambayarsa tana
tafiya a nutse,tana kuma ci gaba da zaban abinda yayi mata tana jefawa a kwandon.
Tarin mamaki ne ya lullube masa zuciya ainun......tsahon lokutan yayi tunanin duk ranar da
sukayi haduwa ta farko da ita zata razana......zata kuma tsorata,idan da yiwuwar ma ta nemi guduwa
duka zatayin duba da girman laifin data aikata masa.
"Tana da wayo......tana kuma da hadari......da alama akwai abinda ta taka" Maganar abokinsa kenan ta
dawo cikin kansa bayan wani zama da sukayi dashi,wannan ya sanyashi Maida hankalinsa jikinsa sosai,ya
kuma tattaro bacin rannan da ta dasawa zuciyarsa wanda har yanxu a cikin bala'i da masifar data sakashi
yake
"Idan kika mantani ai baki cika 'yar halali ba......ai dama idan kere na yawo zabo na yawo dole wataran
zasu hadu" Ya farta cikin fushi.
"Yar halak?" Ta furta a sarari,sai ta dakata da abinda takeyi ta waiwayo ta zuba masa idanu
"Akwai bashi ne tsakaninmu da kake nema na har kalmar kere da zabo zata gitta tsakaninmu?" Kansa ya
daure tamau,zallar raina masa hankali da tayi yaga ta fito muraran. Ji yayi bashi da sauran abinda ya rage
illa ya fiddo mata makamansa.
"Kina iya cewa komai,amma kafin sannan shawara daya zan baki.......ki maido min dukka kudade na da
kika samfe daga account dina sawunki a likkafa.....ko kuma hukuma ta matsaki ki fito dasu" Idanunta ta
watsa masa tana sakin murmushi
"Kasan a inda kudadenka suke?,za kuma ka iya zuwa karba din idan na gaya maka?" A tunzure cikin fushi
da yadda takeson maida maganar wata mara alfanu ko muhimmanci ya kalleta
"Duk duniya akwai wanda ya isa ya hanani karbar haqqina?,akwai wanda ya isa ya cimin haqqina ban
karba ba?"
"Kwantar da hankalinka mana...." Tace dashi still tana murmushi,saita dafe kwandonta ta soma takawa
tana nufar ficewa daga gidan kuma tana fadin
"Gidan marayun nan......a wannan ranar kowanne yaro ya rabauta da duk wani abu na buqata da bashi
dashi,suttura kayan ado na 'yanmatan da kuke sakawa ana musu dauki d'ai d'ai cikin dare ana kai muku
su gidajen shaqatawarku da hotels kamar yadda ka gayyaceni nima zuwa naka dakin hotel din......kana
iya zuwa ka karbi komai dake hannunsu ka sanyashi a kasuwa ka maido kudinka......muddin kuma ba
zaka iya hakan ba,to ina baka shawarar ka fita daga rayuwar SABREEN......ka kuma daina
bibiyarta......idan bakaji ba kuma......zan sake sakaka fidda wasu kudaden masu ciwo da baka shirya
fitarsu ba kamar dai wancan lokacin" Ta qare maganar tana kaiwa qarshen wajen ta karya kwana tana
niyyar bacewa ganinsa.
Daya biyu uku yahada dukka yaga basuyi masa daidai ba. Wani sashe na zuciyarsa ya soma
zugashi da
"Ta yaya kana tsaye qaramar yarinya me qarancin shekaru zata nemi raina maka hankali?".
Ya samu kansa da kansa da tuhumar kansa tare da ganin tsananin baike da wallensa. Wannan
tunanin kadai ya qara masa qaimi,ya taka qafafunsa cikin azama da qwarin gwiwa ya soma rufa mata
baya lokacin da takeji a ranta ta kammala siyan duk wani abu da suke da buqata ita da 'yan
uwanta,wanann ya sanya ta nufi gurin biyan kudin kai tsaye
"Saboda ke kike nema na bani ke nemanki ba?,saboda nine mai laifi bake bace?" Hankali kwance ta
maqale kafada tana sakin siririn murmushi
"A'aha.....ba don dukka wadannan dalilan bane suka sanya ni na baka wannan shawarar ba......na baka
ita ne don gudun kada ALLURA TA TONO GARMA"
"Ni dake zanga wanda allurarsa zata tono garma......"
"Ba laifilaifi malam naseer....." Abinda tace dashi kenan tana ci gaba da tattaki a bayanta. Yau yanason
ganin qarshen gudun ruwanta......yanason yasan ita din wace?......da waye take tare?,su waye suka dauki
nauyinta?.
Hakanan yaci gaba da rufa mata baya tamkar me tsaron lafiyarta ko wanda aka bashi aikin kula da
ita. Har cikin zuciyarsa yakejin yau zai nuna mata shi waye,zai kuma tabbatar mata tayi mahaukacin
gangancin kuskure data shiga hanyarsa.
Mutum biyu suka samu ana lissafa kayansu jikin qaramar na'urar dake da alhakin qididdige fitar
kaya cikin katafaren shagon.
A hankali ta tsaya daga bayan matar wadda bata iya ganin ainihin fuskarta,saidai shigar atamfar
chiganvy gold mix match da wani irin danyen lafiyayyen lace da aka yiwa qawataccen dinkin buba da zani
ya fito da kamalarta da kuma cikar siffarta. Tsaye yake daga gefanta,matashin da duka duka shekarunsa
ba zasu haura ashirin da takwas ba. Ya bata dukka hankalinsa yana sauraren maganar da takeyi dashi
cikin muryarta dake bayyanar da tsantsar kamalarta da cikakkiyar nutsuwar ruhi data halitta. Yanayin
yadda ya rusuna ya bata hankalinsa yana saurarenta kadai zai bayyana maka zallar ladabi da kuma ganin
girmanta da yakeyi,akwai kuma tag idan ka lura sosai daga gaban aljihunsa dake bayyanar da cewa shi
din ma'aikaci ne a wani guri na daban.
Mai matsakaicin tsaho ce,hakanan me jiki ce saidai ba qiba me yawa cancan ba,ta lullube saman
kanta da 4D Vail me asalin kyau da aka zubawa duwatsu masu daraja akayi adon jiki dasu.
Sassanyan qamshinta ya dinga tasowa a hankali daga jikinta zuwa hancin sabreen dake tsaye
daga bayanta tana kallon tulin kayan siyayyar da aketa jera mata cikin ledar dake dauke da tambarin
store din.
Hannunta dake dauke da wasu kyawawan banguls masu sheqi ta miqawa ma'aikacin gurin tana
cewa
"Bansan me yasa suke son mu'amala da wannan katin bankin ba,duk sun lalace da lamarin cashless"
Murmushi ma'aikacin ya saki cikin tsananin girmamawa
"To ai hajiya yafi sauqin sha'ani ne" Kai ta gyada a hankali tana furta
"To Allah ya kyauta". A nutse ta maida dubanta ga saurayin,tun kafin tace wani abu ya sake matsowa a
ladabce yana bata hankalinsa
"Ka kiramin wancan yawalen da kuma wancan acicin suzo mu wuce kafin rana ta sake dagawa"
"Okay to in sha Allah" Ya amsa mata yana zaro wayarsa daga gaban rigarsa,yayin da ta fara takawa cikin
nutsuwa tana ficewa daga gurin hadi da gyara yafen mayafinta dake qoqarin zamewa.
Wucewar tata ya bawa sabreen damar matsowa gaba don a lissafa mata nata kayan
"Ji mana.......zaki dawomin da duk abinda kika san kin sace ko kuma saimun dangana da hukuma?"
Hannayenta ta goye a qirjinta tana kallon qofa yadda mutane ki shige da ficensu hankali kwance. Yana
da ban mamaki......saidai ita din ta fishi abun mamaki. Inda yasan meta taka a kansa......inda tasan cewa
kafataninsa.....zahirinsa da badininsa a tafin hannunta yake da baiyi gigin matsawa rayuwarta ba har ya
matso gareta har haka ba.
A nutse ta waiwayo ta zube masa farare tas din idanunta masu matuqar jan hankali da fusgar
tunanin me tunani
"Kana sha'awar yin gaba da gaba da hukumar ne?" Ta masa tambayar idanunta a tsaye car tsakiyar
nashi. Idan ya kira kansa gogaggen cikin duniya baiyi qarya ba.....muddin kuwa ya kasance hakan yana
ganin mugun ganganci ne zaiyi ya gaza samun fikirar karantar mutum daga yanayin kallo zuwa lafuzan
bakinsa ba.......
"Kina tunanin abune me wahala a gareni?" Ya amsa mata yana mamakin yadda wannan mugun
kwarjinin nata yake taka masa burki,kaifin idanunta ke hanashi daukan mataki tare da aiwatar da abinda
yayi niyya.......abinda zuciyarsa ke shawartarsa.
"Ko daya....daidai ne kuma" Ta amsa masa tana dauke duba da hankalinta daga kanshi tana maidawa ga
ma'aikacin wanda ya kammala lissafin yana gaya mata adadin abinda zata biya.
"Okay" Ta furta hankali kwance tana maida dubanta ga daya daga cikin ma'aikatan dake taimakawa da
wadanda sukayi siyayya me yawa kamarta
"Okay hajiya" Ya fada yana ajjiye qaramar calculator dake hannunsa yana qarasowa gurin tare da jira a
gama sanya dukka kayan cikin leda.
Sake Waiwayowa tayi gareshi karo na biyu. Kallon da tayi masa ta fahimci yakai matakin qarshe a iya
haqurinsa
"Malam naseer......ka shirya biyan duka bill na siyayyar sabreen ko kuwa tunda kai ka kawo qafafunka
duk da gargadinka da tayi?"
"Sabreen?" Ya maimaita sunan yana kallon idanunta. Kiran sunan sabreen da tayi a maimakon basma shi
ya batar masa da tunani cikin taqi qanqani.
"Ka samu aminci game da haramtattun kayanka da aka aiko maka dasu ta cikin jirgin ruwan dake
tsakanin River Benue da riba niger?.......ko kuma ka shirya aci kasuwar wannan sirrin da jami'an tsaron
dake neman kayan tamkar yadda mutuwa ke neman ruhi?".
Kamar wanda aka sanyawa sasari akan tsaida haka yaja wani wawan burki. Kallonta yakeyi da
madaukakin mamaki. Wanne irin hadari ne da ita har haka?. Wanne nisan ji da gani ne da ita?,nisan
binciken da ya bata damar gano birnannen sirrinsa da ko matarsa da suke kwana daki daya su tashi daki
daya bata sani ba?.
"Ka biyasu kudin siyayyarsu duk yadda suka buqata,na barka lafiya Alhaji Naseer" Ta qarashe maganar
tana takawa hankali kwance tana fita kwata kwata daga wajen.
"Malam qaraso ka bada kudin......ta atm ne ko cash zaka bada?" Muryar ma'aikacin ta katseshi daga bin
burbushin hanyar data wuce da kallo ya juyo zuwa wajen biyan kudin yana sauke wani irin gauron
numfashi me nauyi da zafi cikin tsananin mamaki da tsoro.
*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*
*ZAFAFA BIYAR*
*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA
ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*
_K'ALBIM Mamuhghee_
_DUNIYATA Huguma_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
*09033181070*
89825722
1000cf
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
*Arewabooks@:Huguma*
PAGE 21
https://chat.whatsapp.com/DT97XBDyEfyEwniN0a09Cz
__________________________
*_ALBISHIR A GAREKU!!_*
*_SHIN KUNSAN UMMUMAHNOOR LUXURIES TA TANADAR MUKU INGANTATTUN KAYAN ADO NA FITA
KUNYA KUWA?_*
*_KAMAR SU_*
Atamfofi
Laces
Shadda
Materials
Takalma
Jakunkuna
Mayafai
Trolley
Oil perfumes
*_karki tsaya sanya har ayi babu ke,maza garzaya ta nan_*
Numbers
08034469681
08135142610
Handles
Instagram @ummu_mahnoor_luxuries
Facebook ummu_mahnoor_luxuries
____________________________
Sanda take sallamewa saita samu kanta da zama sosai a inda ta idar da sallar tana irga tasbihi da
yatsun hannunta,yayin da kunnuwanta kadan kadan ke jiye mata tasbihin matar dake yinsa can qasa
qasa,saidai lokaci lokaci yana qwacewa ya fito,har zuwa sannan bata waiwaya ko sau daya ta kalli
fuskarta ba,amma daddadan turarenta bai fasa silalowa zuwa cikin hancinta ba.
Wayarta ta matsa haske ya bayyana ta duba lokaci. Tasan ko busari bai iso ba to dab yake da
isowar,ta maida wayar ta ajiye tana kallon sararin cikin masallacin da babu kowa saisu uku. Daidai sanda
zata dauke idanunta dai dai sannan taji matar dake gefan nata taja wani irin qaqqarfan salati
numfashinta yana yayyankewa.
Da hanzari ta miqe,hanzarin daya sanyata cilli da wayarta dake saman cinyarta. Jikinta dukka
yana rawa a gaggauce ta matsa jikin matar
"Lafiya?,me yake faruwa?" Ta furta cikin matuqar tsoro da kuma rudanin ganin yadda take kaman shirin
rasa numfashinta.
Bata iya amsa mata ba,wannan ya sanya sabreen zama sosai ta tallafeta da kyau zuwa jikinta
tana sake maimaita tambayarta a rude
"Ina ganin kaman asthma attack ne" Mace guda dayan data rage a cikin masallacin ta furta bayan ta iso
wajen itama tana dubanta
"Asthma?" Sabreen ta furta a gigice tana jin wani abu yana dukan zuciyarta. Shine ciwo guda daya da
kullum taji sunansa sai zuciyarta ya tsinke,ciwo qwaya dayan da kullum takewa mummunan kallo,ciwo
guda dayan da yayi silar wasu jigo na rayuwarta,har ila yau ciwo qwaya daya da yake wujijjiga
rayuwarsu.
Da sauri ta finciko jakarta bayan da tunaninta ya dawo,ta zugeta da hannu daya daya hannun
yana tallafe da ita,ta daga jakar ta zazzage duka tarkacen dake ciki,cikin matuqar sa'a ta hangi inhaler
dihta.
A gaggauce ta dauka ta kara mata,hannuwan matar dukka rawa suke sanda ta dora nata hannun
saman na sabreen kamar tana son tayata matsa inhaler din,kamar tanason nuna mata tsananin
buqatarta da takeyi.
Cikin mintuna qalilan ta fara samuwa,saidai har yanxun bata daidaita yadda ya kamata ace ta
daidaita din ba. Oily eyes dinta sun cika taf da qwalla
"Kamar asibiti tafi buqatar a kaita" Ta kasa haquri har sai da bakinta ya furta hakan
"Zaifi kyau dai gaskiya don da alama tana buqatar iska sosai".
Dai dai sannan wayarta data watsar ta dauki ringing. Matar ce ta matsa ta miqo mata,ta sanya
hannu ta karba tana fadin
"Ka karba kayana wajen me gadi,gani nan fitowa asibiti zamu wuce" Bata tsaya sauraren abinda zai fada
ba ta katse kiran.
Idanunta ta mayar saman fuskar matar. Wani abu taji ya taba zuciyarta,sai takejin kamar
umminta ce ta dawo,sai takejin tamkar lokacin data rasa umminta. A duk sanda take mutum me dauke
da irin ciwon tsananin tausayinsa yake kamata,duk da itama abar tausayin ce. Duk sanda taga babbar
kaman haka yana fafutuka da wannan ciwon sai ta dinga tuna umminta.
Su biyun suka tallafeta don taji qwarin jikinta,suna takowa a hankali da ita har suka fito zuwa
inda Kekenapep din yake
"Eh hajiya" Ya amsa mata da sauri yana bude aljihun motar ya fidda shi sabo fil ya bata.
A kusa da ita ta zauna tana riqe da face mask din,saita sauke idanunta qasa tana jujjuyashi.
"Zan saka miki wannan saboda iskan mota,motan bana gida bane". Idanunta saman fuskar yarinyar,har
zuciyarta tana jin qauna da jinjina taimakonta a kanta,ta lura tana d'anjin wani nauyi da kuma rashin
sakewa. Qaramar yarinya haka me zuciyar taimako?,sai abun ya qayatar da ita.
Mintuna ashirin daidai suka qarasa private hospital din,wanda a nan file nata dana qannenta
dukka yake. Tuntuntuni ta sallama asibitin gwamnati,yana daya daga cikin muhallan da suka samarwa
rayuwarta gibi,yana daya daga cikin guraren da suka dasa qaton tarihi a rayuwarta,suka kuma ajiye mata
wani tabo na har abada,shi ya sanya daga sanda ta samu dama ta nisanta kanta da dukkaninsu daga
asibitin gwamnati.
Private hospital ne daya amsa sunanshi,babu nau'in wata kulawa da mara lafiya baya
samunta,saidai kuma kudi ne zasu fita sosai daga aljihun majinyaci ko ahalinsa.
Private room suka bata,cikin mintuna goma sha biyar kacal suka bata dukkan taimakon daya
dace,bata samu nutsuwa ba sai da suka shafe awa guda taga bacci sosai ya dauketa tana sauke
numfashin a hankali ta cikin oxygen din da suka maqala mata saboda yadda taso galabaita sosai.
Zama tayi kawai gabanta bayan taja kujera,ta maqale hannunta a qirji bayan ta zube idanunta a
kanta tana dawo da bayanan da likita yayi mata a kanta.
"Ta samu mummunan attack ne,tana samun kulawa sosai to amma kuma kaman yanayi ya nuna ba'a
kiyaye wasu dokoki na masu ciwon,sannan kuskure ne ta dinga fita hakanan ba tare da inhaler ko wani a
kusa da ita ba".
Idanunta ta qanqance sosai tana ci gaba da nazarin maganganunsa. Hakanan sai taji ranta yayi
matuqar baci,indai har mace me irin wannan shekarun bata samu kulawa ba sai yaushe?,indai har ba
za'a kula da dokokin da aka bata ba meye amfanin makusantanta?. Dukkan alamu sun nuna,tun daga
suturar jikinta da komai nata ma cikin wadata da sukunin rayuwa take ainun,to meye zai hana su su bata
kulawa su ahalin nata?.
Idan zata iya tunawa mutum daya ne ta gansu a tare a tsaye cikin store din,har tana bada
umarnin a kira mata wani data kira a cici da kuma yawale. Yawonsu kenan yafi musu kasancewa da
ita?,yanzu haka fa mahaifiyarsu ce amma sun gwammaci tafiya yawo akan su bata kulawa?.
Iska me zafi ta sake fesarwa ranta yana sake tunzura musamman bayan data duba agogon
hannunta. Aqalla awa daya harda rabi da barowarsu store din amma har yanxun basu biyo address na
asibitin data barwa wancan matar sun biyo bayan baiwar Allahn ba?. Sake juya wayarta tayi su huda
suna fado mata a rai. Ta tabbatar zuwa yanzun sun dawo gida,suna can kuma zaune su daya a daki.
Karon farko da taji kaman ya kamata ta siya waya ko qwaya daya ce ta ajiye cikin dakin saboda lalura irin
haka,ko ba komai ba zata barsu cikin zulumi ba,zata kira taji lafiyarsu suma suji lafiyarta,duk kuwa da
cewa komai runtsi a gida takeyin magrib.
Daidai sanda tunaninta yakai nan taji an murda handle na qofar. Kyakkyawan matashin ne ya fara
bayyana. Dogo me matsakaicin haske. Kai tsaye idan kace masa kyakkyawa bakayi kuskure ba,yana da
cikakkiyar suma me santsi tun daga kansa zuwa habarsa.
Yana sanye da dakakkiyar shaddar getzner Neautaral color daketa yauqi da sheqi. Yanayin dinkin
da aka yiwa shaddar yayi masifar dacewa da structure na jikinsa. Dinkin zamani dake nuna zallar gogewa
da wadatar arziqi na wanda suturar ke kwance a jikinsa. Yadda shaddar ke walqiya hakanan hular
kansa,wadda koda ba'a gaya maka kudinta ba zakasan cewa bada qaramin zare aka saqata ba. Qafafun
sanye cikin takalmin Batozzi,hakanan cikin qasa da second biyar dakin ya gauraye da sassanyan qamshin
turarensa.
"Hamma mun sameta,gata tana bacci" Ya furta da kwantacciyar muryarsa da alama kuma yana magana
ne da wani a wayar dake manne a kunnensa,dukka hankalinsa da idanuwansa suna kan matar dake
kwance cikin mazari yana d'okin isa gareta.
"Okay hamma......in sha Allah" Ya sake fadi da sauri sannan ya jefa wayar a aljihunsa yana isa inda take
kwancen ba tare daya damu ya kashe wayar ba.
Rusunawa yayi sosai a gabanta yana riqe da hannunta da dukka hannayensa biyun. Yayi wani irin
laushi,don idan ka kalli hannunsa da kyau kana iya ganin yadda suke danyin rawa.
Dauke dubanta tayi daga kansa haushinsa yana saukar mata,saita maida kallonta akan wanda
suka shigo din tare. Shine dai wanda ta gansu cikin store din tare wanda ta bari ya biya kudin siyayyar da
tayi.
"Kamar kece kika kawota ko?" Ya fadi saboda hada idanu da sukayi. Maganar tashi taja hankalinsa,yadan
sassauta riqon da ya yiwa mara lafiyan ya kuma waiwayo da dukka nasa idanun yana dubansu,don shi
sam sam bai ma lura da kowa ba a wajen.
Kamar yayi mata susa ne a inda yake mata qaiqayi,sai ta miqe a nutse tana saqala Jakarta a
kafadarta,haushinsu yana sake turniqeta
"Eh nice bayan kun yasar da ita kun kama gabanku ba?,waishin kunsan muhimmancinta kuwa?,kunsan
yadda ciwonta ke buqatar a dinga yawan kulawa da ita musamman ita da shekarunta suka fara yawa?.
Ji yayi maganganunta sunyi girma ainun,tasan wace ita din a wajensu har da zataga gazawa da
kasawarsu?. Saidai bai datseta ba saboda yadda yaga hawaye suna cika idanunta
"Mutane da yawa basusan muhimmancin iyaye ba sai sanda suka rasasu......amma ku sani
cewa......yadda suka baku kulawa a sanda bakusan muhimmancin rayuwa ba.....ba komai bane don kun
basu kulawa a sanda sukasan muhimmancin nasu rayuwar......ba kowa a kusa da ita.....ba
inhaler.....yanzu inda numfashinta ya katse fa?" Ta qarashe fada adan tsawace hawayen na fara
gangarowa ta idonta qwaya daya,sai tayi hanzarin kauda kanta gefe ta dauke hawayen da yatsanta. Su
kadai sukasan yanayin da suke shiga idan ciwon ya tasar musu shi yasa babu me fahimtar abun sai
wanda ke cikin yanayin
"Kuji tsoron Allah ku kula da ita yadda ya dace,don yadda muke amana a hannun iyaye haka suma
amana ne a hannunmu,kuma Allah zai tambayemu game da yadda muka kula da tsufansu" Tana kaiwa
nan ta soma takawa tana ficewa daga dakin.
Gaba daya mamakinta ya cikashi,yadda take haqiqancewa ba tare da tasan komai a kansu ba.
Mahaifiyarsa itace rauninsa har abada.....wani abu guda daya me matuqar tsada da muhimmancin da ba
madadinta. Har ta fice ya kasa tsaidata kaman yadda yaso har sai data bacewa ganinsu.
"Bita ka tsaidata......a qalla ko godiya ya kamata muyi mata,sannan kuma muji yadda za'a maida mata
kudaden data kashe tunda na samu an biya bill na komai"
Kamar wayar dake aljihunsa yaji yana motsi,ya dafe wayar sai kuma ya sanya hannu ya fiddota da
sauri. Mamaki ya kamashi,ya akayi bai kashe wayar ba. Hamman ne har yanzu akan layi,duka mintunan
da sukayin wayar na a kunne,sai ya maida wayar kunnensa
"No hamma...." Ya fadi da sauri. Numfashi yaja yana ware idanunsa sosai
"Stop......banason a sake mata hayaniya a wajen nan....if not ran kowa zai baci"
Koda cewa tayi fada cikin yanke hukunci akan abinda bata sani ba.....bata da yaqini amma shi
baiga laifinta ba,ya mata uzuri......hasalima ta burgeshi qwarai,dukkan alamu yana nuna tasan darajar
dan adam ne,sai ya maida hankalinsa akanta yana duba shiga da fitar numfashinta.
*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*
*ZAFAFA BIYAR*
*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA
ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*
_TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_
_K'ALBIM Mamuhghee_
_DUNIYATA Huguma_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
89825722
1000cf
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
*Arewabooks@:Huguma*
https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997
PAGE 22
__________________________
*_ALBISHIR A GAREKU!!_*
*_SHIN KUNSAN UMMUMAHNOOR LUXURIES TA TANADAR MUKU INGANTATTUN KAYAN ADO NA FITA
KUNYA KUWA?_*
*_KAMAR SU_*
Atamfofi
Laces
Shadda
Materials
Takalma
Jakunkuna
Mayafai
Trolley
Oil perfumes
Numbers
08034469681
08135142610
Handles
Instagram @ummu_mahnoor_luxuries
Facebook ummu_mahnoor_luxuries
____________________________
Batasan me yasa ba,batasan dalilin da ya sanyata takejin bacin rai sosai akan abun ba. Ta dinga
fidda numfashi me dumi a hankali daga baki zuwa hancinta. Cikin nutsatsen takun nan nata take nufar
inda tabar busari yana jiranta. Takun da yayi matuqar tafiya da hankali da tunaninsa baya ga zubin
mamallakin takun.
"Wai har yanzu akwai irin mata masu wannan ajin?" Ya furta qasa qasa ba tare da yasan a waje yayi
maganar ba,tana ta'allaqa dubansa a kanta,yana jin tana tafiya da gaba daya kuzari tunaninsa dama
hankalinsa gaba daya.
Tamkar an zungureshi ko kuma anyi masa qaimi,sai ya saka hannu da wani irin hanzari yana bude
murfin motar. Sam gaba daya ya manta da dalilin daya kawosu asibitin,ya kuma manta ma da waye yake
tare,burinsa guda daya tal! A yanzu,ya samu isa gareta,yakuma samu daman yin magana da ita.
Sallamar tashi ta ratsa kunnenta a sanda take dab da isa wajen da Kekenapep din yake. Ta
lumshe idanunta a nutse tana riqe masaqalin jakarta da kyau. Dama tasan hakan zata iya faruwa
duba,zaiyi wahala a kallon farko da tayi masa ya iya tsallake halaye da kuma dabi'uj data hanga kai tsaye
daga gareshi.
"Assalamu alaikum.....don Allah....." Ya katse maganar tashi da kan kanshi lokacin da yasha gabanta
idanunsu suka gauraya waje daya.
Wani kwarjini na musamman,wani yanayi ya tsarga masa irin wanda bai taba jin irinsa ba. Nashi
idanun ya janye a hankali yana qoqarin daidaita kansa tare da zallar mamaki yana kuma tambayar kansa
"Meye haka?,ita din wace?". Baisan iya adadin kalar matan daya gani ba tun da ya fara zama cikakken
namiji zuwa yau. Baisan adadin matan da yayi mu'amala dasu ba daga jinsin yare daban daban,amma
yau daya wata mace da baya tunanin ta rufa shekara ashirin da biyar a duniya na neman yi masa
kwarjini?.
"Lafiya?" Ta jefa masa tambayar tana tsuke fuskarta tare da sake bada tazara tsakaninsu. Qoqarin
daidaita nutsuwarsa yayi,sai ya sake mata murmushi hadi da gyara tsaiwarsa sosai a gabanta,yana jin ba
wata mace da zata iya kaucewa tarkonsa muddin ya d'ana shi.
"Ba lafiya ba......maganar gaskiya kenan.......akwai gagarumin tashin hankali" A mamakance take duba
fuskarsa tana yamutse tata tare da qoqarin sakeyi masa sabon karatun da baisan tana yi ba
Numfashi taja sosai har cikin huhunta sannan ta fesar tana kauda kanta gefe hadi da juya
qwayoyin idanunta. Ba shine mutum na farko data taba gamuwa dashi me irin wannan salon ba,don
haka tafiyar dashi bazai bata wahala ba.
Dukkan wani d'a namiji da zai ratso rayuwarta tayi imanin QADDARARSA ce a nan.......da kuma
zallar tsautsayi. Mafi rinjaye daga cikinsu kuma SON RAI da SON ZUKATA.
Ba kasafai ta fiya bada kai ta farat daya ba,koda ta tsara amsarka,don tuni ta fahimci duk wani
abu da akeson yayi daraja.....kar a bari samuwarsa ta zama ta sauqi. Don haka ta soma tattaki da
zummar kubcewa daga gabansa.
Juyowa ta sakeyi a karo na uku tana kallonsa. Ya fiya zaqin baki da yawa,maza irinsa suna da wani
hali da dabia da tuni ta gama karatunsa. Tabbas akwai wani abu tattare dashi da wata qila take
nema......tana hasashen yiwuwar samun wata qaruwa me girman gaske. Taga irinsa ba daya ba.....ba
biyu ba....ba uku ba,har ba zata iya tantance adadi ba.
Duk da wannan hasashen amma bata yarda ta nuna masa komai ba. Sai ta sake kau da kanta
tana yamutsa fuska
"Matsawarka daga hanyata kamar zaifi zame maka alkhairi akan ci gaba da tsaiwar......ina da tarin
abubuwa a gabana....."
"Bansan ko me ke jiranki ba......amma na tabbatar koda baikai wannan tsaiwar tamu alkhairi ba bazai
wuceta ba" Ya fadi a zaqe da fatan samun nasara
"Na roqeki kada ki watsan qasa a idanu,ki wofantar da wannan kyakkyawar damar a garemu gaba daya"
Ya fadi yana marairaicewa tare da miqa mata wayar hannunsa yana kasheta da idanu gami da karyar da
wuya da raunanar da idanun nasa.
A nutse ta sauke kallonta akan wayar ta kalla. Tsaleliyar iPhone 16 wadda kana dubanta zakasan
bata wani jima da baro dumin kwalin da aka qerata ba. A yangance ta dauke kanta daga kai ta sake
maidawa gefanta bayan.
Wani numfashi ya fusga da qyar bayan ya gama sauraren jerin lambar wayarta data karanto
masa. Sautin muryar nata yana masa wani irin amsa kuwwa a kunnensa. Karon farko daya yadda cewa
muryoyin wasu matan kadai suna iya haddasa fitina a zukata da gangar jikkunan maza. Sai yakejin yana
sake zurfi ason ya kasance a tare da ita
"Sai nakega kaman girma da martabarki ya dara kihau napep.....da zai yiwu da kin sadaukarmin da
wannan tsadajjen lokacin na saukeki a gida....." Yana ajewa tana daga masa hannunta,sannan ta fara
takawa tana wucewa cikin abun hawan da busari ke jiranta.
Har ya bawa napep din wuta suka fice daga harabar asibitin yana tsaye a gurin. Sai daya tabbatar
sun qwacewa ganinsa sannan ya buga qafarshi yana yarfar da hannunsa,wani shu'umin murmushi yana
kubce masa. Ba shakka ita din ME ZAFI ce,ta kuma cancanci dukkan wannan dagawar da kuma jan ajin.
Yana da makamai a hannunsa masu tarin yawan da zai iya yaqar zuciyarta yakuma yi nasara ba shakka ko
kokwanto. Makami guda daya da dukkan namijin daya mallakeshi yake iya sanya kaza ta kwanta ta yanka
masa kanta ta gasa ta kuma kawo kanta da kanta har inda yake don biyan buqatar ranshi.
Iya wassafa samuwar nasara kadai a gareshi ya sanya murmushi ya subuce masa. Ya sake buga
qafa yana wassafa irin yadda zai tsikari rayuwarsa da tsinke yadda ya kamata
"Dole na qarawa kaina kusanci da dukkan qofofin da zasu budemin manya manyan qofofin taskokin da
zan miki hidima dasu don mallakar muradina" Ya furta a sarari yana qanqance idanu,muradinsa yana
sake ninkuwa,burikansa suna sake fadada.
Daidai qofar gidan nasu busari ya ajiiyeta bayan ya fiddo mata dukan kayan daga cikin motar. Cikin
farfajiyar gidan ya ajiiyeta mata kayan sannan ya juya yana komawa ciki.
Tsaye tayi a farfajiyar gidan da iskar la'asar ke kai kawo. Ba wadatar yara sam,wanda koda ace
akwai wadatar nasu tasan cewa ba kowa ne a cikinsu ke aikuwa ba. Kayan sun mata nauyin da ba zata
iya dauka ba,tana tsaka da wanna tunanin ta hangi fitowarfitowar nadra,haneefa na biye da ita.
*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*
*ZAFAFA BIYAR*
*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA
ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*
_K'ALBIM Mamuhghee_
_DUNIYATA Huguma_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
*09033181070*
89825722
1000cf
*_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_*
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
*Arewabooks@:Huguma*
https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997
PAGE 23
___________________________
*_ALBISHIR A GAREKU!!_*
*_SHIN KUNSAN UMMUMAHNOOR LUXURIES TA TANADAR MUKU INGANTATTUN KAYAN ADO NA FITA
KUNYA KUWA?_*
*_KAMAR SU_*
Atamfofi
Laces
Shadda
Materials
Takalma
Jakunkuna
Mayafai
Trolley
Oil perfumes
Numbers
08034469681
08135142610
Handles
Instagram @ummu_mahnoor_luxuries
Facebook ummu_mahnoor_luxuries
__________________________
Dukansu suka watsar da abinda ke hannunsu sannan suka nufota. Fuskokin dauke da
madaukakiyar fara'a wadda har tsakiyar zukatansu ta ratsa. Ita daya ce HASKE GIDANSU.....ita daya ce
FARINCIKINSU hakanan ita kadai ce BAQINCIKINSU. Rashinta a kusa dasu yakan debe dukkan wata
walwala da sakewa tasu,duk da tarin jamaar dake rayuwa a gidan amma duk sanda bata nan din suna jin
gidan kamar babu kowa a ciki saisu.
Cikin jikinta ta rungumesu kaman yadda ta saba,sannan nadra din ta soma jan daya daga cikin
ledojin. Duqawa haneefa tayi itama zata dauki guda daya nadra din ta tsaidata
"Bafa zaki iya dauka ba" Cak ta tsaya tana turo baki
"Anty wai da gaske bazan iya ba?" Murmushi ya qwace mata saboda hangen farincikin da tayi daga
idanuwansu.
"Zaki iya auta" Ta furta tana bude ledar,jakankunan maggi da suka qarawa ledar nauyi ta ajjiye a gefe
sannan ta daure mata ledar tana cewa
"Bismillah auta aiba raguwa bace" Hakan ya faranta mata rai,ta sukunya ta dauki ledar tana cewa
"Ita yaaya nadra kullun komai sai tace bazan iya ba,batasan na fita qarfi ba" Daga sabreen din har nadra
data riga tayi gaba suka saki dariya.
Idonta a kansu har suka mata nisa sannan ta tsugunna a nutse ta kwashe maginta,ta fara
takawa tana binsu zuwa Qofar da zata sadasu da babban tsakar gidan nasu. Zuciyarta a karye tana
hangen haneefa daga nesa. Ta sake sakin boyayyen murmushi,akwai jarumta me yawa dangane da
yarinyar,da alama zuciyarta dakakkiya ce kuma a tsaye take.
Dab da zata shiga din su kuma suna yunqurin fitowa su biyu. A hankali taja da baya tana basu
hanya bayan ta sauke idanunta qasa,saidai duk da hakan da tayi bai sanya ta tsira daga garesu ba.
Qasan ranta akwai haushi takaici da kuma fushin rashin samun nasarar da batayi ba a safiyar
dazu.
"Ke ya kamata mu bawa hanya ta wuce ai......gagara" Ta furta tana qanqance idanu idanun nata fes akan
Fuskarta da kuma abinda ta riqo a hannayenta.
A hankali daada dake tsaye daga bayan bibo din ta gewayo ta gefanta tana cewa
"K'nnnn,gaskiya dai,fitar dare ai 'yan kwalta" Ta fada tana zakudawa tare da bin bayan daada bayan ta
waiwayo ta ajewa sabreen wani kallo.
Da kallon itama ta bisu,sam ko kadan daada bata nuna ta santa ko tasan da zamanta......nata da
sauqi don kome za'ayi a kansu baka taba jin ta tofa nata........batasan wanne matsayi zata aje daada ba a
kanta cikin gidan,ta bibo kuwa fitacciya ce ainun,muddin magana ce a kansu,Ala cuta ala magani har
abada bare ya fiye mata su,koda kuwa wanne irin nau'in alkhairi zasuyi mata ko zasu kowa cikin gidan.
Ajiyar zuciya ta saki tana ci gaba da kutsa kanta cikin gidan tana ta qoqarin kauda abinda takeji
a yau yana taso mata qasan zuciyarta. Abune da take ganin bai kamata ta damu ba......ita din dai tasan
kanta,ta yarda da kanta,sannan tasan wacece ita?,to me ya rage?,me take nema da shaidar mutumin
yau?,mutanen dake rayuwar a DUNIYARta sam basu cancanci ta basu damuwarta ko tayi yunqurin
gamsar dasu game da WACECE ITA?.
Sanda take zubewa saman kujera daidai lokacin haneefa ke isowa gabanta da school bag dinta
da wani.littafinta a hannu
"Anty munyi C.A,a cikin talatin na samu ashirin da takwas......sannan an bamu assig....."
"Kai haneefa haba" Nadra ta fasa tana hade fuska. Murmushi ta saki,saita dagawa nadra hannu
"Qyaleta,zo.nan auta" Ta kirata sanda huda ke qarasowa ta aje mata ruwan pure water me sanyi guda
biyu
"Ki aje komai sai zuwa anjima zan duba,duka yau tare zamuyi assignment din kinji?" Kai ta daga tana
murna ta cilla da gudu ta koma bedroom dinsu da jakar.
"Me yasa baku wuce islamiyya ba?" Gyara zamanta kadan tayi sannan tace
"Jiran dawowarki mukeyi" Rabi tasha ruwan ta ajjiye tana sake karantar wani yanayi na daban daga huda
din
"Sai na dawo sannan zakuje Islamiyya huda?,yaushe aka fara wannan tsarin a dakin nan?" Tadan furta a
zafafe tana dubanta. Qasa da kant huda din tayi,ba kasafai take ganin fushi ko fada dava Fuskarta ba,to
amma duk sanda tayi din ya tabbata laifi sukayi mata babba.
"Kiyi haquri.na tsaya dora abinci ne" Sassautowa tayi kadan tana sauke boyayyen numfashi. Bata qaunar
abinda zai zaunar dasu cikin gidan ko kadan ballantana idanuwa ko kunnuwansu suji ko suga abinda
rayuka zasu baci. Hakanan koda wasa bata qaunar suyi wasa da makaranta. Tana jin ciwo idan ta tuna
iya inda matakin karatunta ya tsaya a shekaru ashirin da daya hudu da take dashi a duniya,wanda a
yanzun kimanin shekaru hudu kenan rabonta da wata bawa wai makaranta.
"Ku shirya ku wuce,duk da lokaci ya fita amma baiyi nisa ba ai" Ta fadi tana duba agogon hannunta
sannan ta fara zareshi daga hannunta.
Tana zaune dukansu suka gama shiryawa cikin fari qal din uniform da baqar doguwar riga daga
sama. Hankalinta bai dawo daidai ba sai data tabbatar sun fita a gidan.
Kai tsaye ta rage kayan jikinta ta zura sassauqar riga sannan ta wuce kitchen din dake falon tana
duba girkin da huda ta fara yi.
Komai yayi daidai,dole ta sanya huda ta koyi girki tun batakai minzali ba. Tana fita ta bar mata
nadra da haneefa,tun bata san ya zata kula dasu ba har ta koya. Ko a yanzun idan huda tayi girki,itama
tayi sai na huda ya dara nata.
Sai data kammale komai sannan ta daura alwalar sallar la'asar,sanda ta idar idanuwanta sun fara
nauyi,tana zaune daga saman abun sallar tana dan murxa idanunta. Ba baccin take buqatar yi ba a
yanzu,tana son magana da jib ne. A yawancin lokuta a irin wannan lokacinne take samun tattauna
maganganu ire iren wadannan,sam bata yarda tayi komai bisa idanunsu,bata taba bari ta rab'a lamarin
rayuwarsu da nata rayuwar,komai tana tsaidashi ne iya muhallinsa.
Hakanan tana hamma ta miqe ta koma daki. Locker gefan gadonta ta jawo,ta fidda
madaidaiciyar baqar jaka dake dauke da mini laptop dinta,sannan ta zaro wayarta dake cikin jaka ta sake
dawowa cikin falon.
Kalmomin sirri ta sanya ta bude laptop din,sanna ta maida hankalinta akan wayarta tana barin
laptop din ta daidaita. Maadanar lambobi ta shiga bincikawa har ta kawo kan sunanshi,ta danna masa
kira tana aza idanunta akan screen na laptop din tana duban hoton daya mamaye fuskarta. Hoto ne da
bata gajiya da kallonsa,duk sanda ta dubi hoton sai taji kamar tana tare da ita,kamar zata kirayeta ta
amsa,kamar zata iya jin kadan daga radadin da take fuskanta,kamar zata damqi hannunta su fuskanci
wannan JUYAYAYAR DUNIYAR su kuma kutsa cikin birkitacciyar rayuwarta su kawo daidaito.
Daga wayar da akayi shi ya katse mata tunaninta,ta daidaita idanunta da suka fara zugi kadan
kadan da alamun son tara ruwan hawaye
"Adda ya zama tsohon tarihi......bashi ba......ko bankinsa basu isa susan ya akayi kudin sukayi fiffike ba
bare inda suka sauka"
Sake duba bagaren kira tayi a nutse har ta iso number wayarsa. Ta tsaya kadan tana kallon
numbers din. Daga yanayinsa da yanayin shigarsa ta tabbatar ba qaramin mutum bane. Amma ko daya
batajishi koda a gefan zuciyarta bama bare a shiga wani batu na daban. Hasalima yadda yaso bata mata
lokaci ne yafi bata haushi,kalaman bakinsa kuwa aqalla taji masu kamanceceniya dasu a bakin gomman
maza......maza iri daban daban,masu mabanbantan halaye da dabi'u.
Tana jan system din kira yana sake shigowa. Ta dora zagayayyun idanunta ga fuskar wayar tare da
zubawa numbers din idanu kamar me nazari. Batasan wadanne irin zukata suke dasu ba.......a sanda
sukaso abu suna zamewa tamkar wadanda ba zukata a qirjinsu,tamkar wadanda hankulansu ke zamewa
daga gangar jikinsu,idanuwansu da dukka kunnuwansu suna rufewa ruf izuwa ga cikar muradinsu.
Dukka layukan da tasan zasu zame mata damuwa ta ciresu kwanaki biyu kenan,ta kuma tabbatar
akwai masu nemanta da yawa.
Qaramin tsaki taja ta saka hannu ta jawo wayar,ta daga tana karawa a kunnenta
*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*
*ZAFAFA BIYAR*
*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA
ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*
_K'ALBIM Mamuhghee_
_DUNIYATA Huguma_
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
*09033181070*
89825722
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
*Arewabooks@:Huguma*
https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997
PAGE 24
____________________________
*_ALBISHIR A GAREKU!!_*
*_SHIN KUNSAN UMMUMAHNOOR LUXURIES TA TANADAR MUKU INGANTATTUN KAYAN ADO NA FITA
KUNYA KUWA?_*
*_KAMAR SU_*
Atamfofi
Laces
Shadda
Materials
Takalma
Jakunkuna
Mayafai
Trolley
Oil perfumes
Numbers
08034469681
08135142610
Handles
Instagram @ummu_mahnoor_luxuries
Facebook ummu_mahnoor_luxuries
____________________________
"Ayimin afuwa nasan wataqila nazo da takura......ba wani abu nake bida ba illa a bani dama zan turo dan
saqo da aike"
"Ka wuni lafiya?" Ta katseshi ya hanyar tambayar lafiyarsa. Wani boyayyen numfashi ya aje,daya daga
cikin dabi'unta da suka banbanta dana sauran matan da ya sani wadanda suke rayuwa shigen
tata......dabi'arta guda daya dake tsundumashi a kokwanto da tunanin WACECE ITA?,YADDA ZAHIRINTA
YAKR HAKA BADININTA YAKE?.
Yana da tarin buqatu da yakeson gabatar mata dasu,saidai kwarjininta da wani irin shakkarta
yakan daki zuciyarsa a duk sanda yayi yunqurin hakan. Ta sha bashi damar haduwa sama da damarmakin
da take bawa kowa......hakan kuwa baya rasa nasaba da yadda yake kame kansa a gabanta
"Lafiya qalau.....saidai tsananin kewarki......na iso qasar nan da burin ki zama mutum ta farko da zan fara
tozali da ita....... Amma inajin nauyin tambayar hakan don kada na aza miki abinda ranki baiso"
"Banayin abinda baniso......hakanan bana yin abinda zan takura" Ta fadi mishi kai tsaye kaman yadda
halayyarta take.
"Na sani nadeeya" Ya amsa mata da karsashinsa,har sai da boyayyen murmushi ya kubce mata.
NADEEYA shine stamp din ya'aqoub,kaman yadda muhseena yake stamp din MASHKUR,mashkur din da
tayi imanin zuwa yanzun qila ya kusa zaucewa da rashin samunta a waya da bayayi. Shi kansa ya'aqoub
din wata irin saa ya taka a sanda yayi katarin samun number wayarsa. Dashi da mashkur dukkansu ta
hadu dasu ne a rana daya,saidai kuma a mabanbantan gurare da lokuta.
"Zaa yimin wannan alfarmar?" Ya tambayeta yana langabar da kansa tare da sassauta muryarsa da kyau
"Zan duba"
"Zuwa yaushe please......zuciyata a jigace take nadeeya.....i beg you karki sakamin lokaci da nisa....."
"Sharada yahaya gusau road,najbil road" Ta fadi a nutse tana yanke kiran.
Wayar ya cire a kunnensa yana binta da kallo. Ya zaci inda yayi mata aike wancan karon wannan
karon ma can za'a kai mata?. Iska ya furzar daga bakinsa,bata da wuyar canzawa tamkar waya
hawainiya. Har yanzu bashi da wani yaqini ko tabbaci a kanta. Baisan komai a kanta ba banda suna da
kamanninta. Yana da buqatar abubuwa masu yawa game da ita amma bata bashi dama ko qanqani a
kanta ba.
"Allah yakai damo ga harawa" Ya fadi yana furzar da iska daga bakinsa. Ya miqe a hankali yana ture
kyakkyawan mulmulallen table na glass dake gabansa cikin qawataccen falon nasa da ya tanada domin
hutawarsa yana laluben number wayar babban yaronshi. Yanason saqon ya isa gareta da wuri,don
yanason ya sanya qaimi ya matsa da kyau don samun kyakkyawan kusanci tare da ita.
A yadda ya ganta baiyi tsammanin za'a dauki wani dogon lokaci ba tare da ya samu abinda
yakeso ba. Saidai duk sanda ya tuna yanayin jin kanta,miskilancinta da shariyarta,sai yaga eh.....ba abun
mamaki bane,mata irinta daban Allah yake halittarsu.
Baki ta tabe tana ajjiye wayarta a gefe,sai kuma taja dan siririn tsaki tana sake bada duka
hankalinta akan system din.
Folder da takanyi rubuce rubuce ta adana a duk sanda zuciyarta ta buqaci abokin hira ta
shiga,ta budeta,sannan ta fara rubutun daga dukkan abinda taji tana da buqatar amayarwa.
Wata irin rayuwace da babu qawa ko aminiya......babu aboki ko amini......qawayenta sune
qannenta da suka fito daga tsatso guda......saidai har kwanan gobe bata bari sun zame mata aminai
ba.......saboda batason tunaninsu da hankulansu su gurbata ya zuwa wani tunani na daban. Tana jin itace
dole.....kuma tilashin daukan alhakin komai yana a wuyanta.
Awa guda harda qarin wasu mintuna ta dauka kafin ringing na wayarta ya janye hankalinta. Ta
dauke idanunta da suka dan sauya launi tana mayarwa kan wayartata,daidai sanda take iya jiyo hayaniya
da ifce ifcen wasu daga cikin jikoki da yaran gidan. Bame son hayaniya bace sam,zata iya rayuwa cikin
muhallin da babu motsin kowacce halitta sai ita......tana da wannan damar ta samarwa kanta irin
wannan muhallin da kuma wannan rayuwar......amma qaqqarfan dalili guda daya tal zaya hanata kaiwa
zuwa ga wannan burin nata,tna buqatar tsira da sauran burbushin MUTUNCINTA tana son ta sake
tabbatarwa da kowanne me zargi abinda yake zargi a ransa yaji haka ne?,ko kuma ya sauya bigiren
ra'ayinsa a kanta.
A nutse ta karanta sunan dake saman screen din,sai ta tattara dukka hankalinta akan kiran ta
ture system din tana jingina sosai da makarin kujerar tata.
"Wa'alaikumussalam" Aka amsa daga daya bangaren cikin matuqar nauyin jiki dana murya.
"Lafiya kike titi?" Sabreen din ta tambaya murya a sanyaye itama. Tana jin dukka wata gaba ta jikinta
tana yin sanyi
"Alhamdulillah sabreen.....,saidai......"
"Aisha ko?,ayshatu?" Kai titi take jinjinawa tana qoqarin hadiye abinda yake taso mata. Saita kass cewa
da sabreen din komai,bataso ta bijiro mata da abinda take da tabbacin itama yafi qarfinta......bataso ta
bijiro mata da abinda zai hautsina nutsuwarta,duk kuwa da tarin qoqarinta.....sadaukarwa da tsaiwar
dakanta akan yarinyar
"Titi ki fadamin me ya faru?" Ta sake jefa mata tambayar tana jin kamar ta tashi a daren ta iskesu a inda
suke
"Ki nutsu sabreen.....Allah yana sane da halin da take ciki......kinyi iya yinki......kinyi kuma iya abinda zaki
iya,mu barwa Allah komai"
"Sabreen.....naira million takwas suke da buqata wajen aikinta" Wani qaramin jiri taji tana niyyar kayar
da ita tana daga zaunen. Tayi luuu da idanunta tana son furta addu'a ko qwaya daya ce amma bakinta ya
kasa lalubota.
"Tabbas titi akwai abinda kika boyemin......baya rabuwarmu wani abu ya biyo baya amma titi baki
gayamin ba......tabbas" Ta fadi muryarta tana rawa. Tana ji har tsakiyar zuciyarta da ruhinta tausayin
aisha kamar zai kasheta.
"Wannan wacce irin DUNIYA ce dake cike da al'umma masu tsananin son kansu?,duniyar da kowa kansa
ya sani?" Ta fadi a sarari tana iya jiyo kukan titi wanda takeson boyewa.
Kasa riqe kanta itama tayi,sai kawai ta tsinke wayar,ta dora Fuskarta saman hannun kujerar da
take kai. Ba zata iya riqe quncin da takeji saman qirjinta ba,ciwo nauyi da kuma radadin ya mata yawa.
Abinda ta saba kamar kullum shi tafi buqatar yi a yanzu wato KUKA. KUKA abu guda daya daya zame
mata solution na dukka matsalolinta,duk da ta dade da sanin kukan baya maganin komai.
A hankali take rera sirin kuka wanda take kokawa rayuwar su da rayuwar aisha. Tsananin
talauci da rashin galihu ya sanya ta tsinci kanta a halin da take ciki yanzu. SON ZUCIYA da rufewar
idanuwa da tsananin zallar rashin imani ya sanya yayi mata silar zamowa daya daga cikin mutanen dake
ziyartar asibiti domin ganin LIKITAN ZUCIYA.....ciwon da yakai minzalin da take buqatar TIYATA don ceto
rayuwarta
*SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI*
*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*
*ZAFAFA BIYAR*
*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA
ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*
_K'ALBIM Mamuhghee_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
*09033181070*
89825722
1000cf
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
*Arewabooks:@Huguma*
https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997
PAGE 25
__________________________
*_ALBISHIR A GAREKU!!_*
*_SHIN KUNSAN UMMUMAHNOOR LUXURIES TA TANADAR MUKU INGANTATTUN KAYAN ADO NA FITA
KUNYA KUWA?_*
*_KAMAR SU_*
Atamfofi
Laces
Shadda
Materials
Takalma
Jakunkuna
Mayafai
Trolley
Oil perfumes
Numbers
08034469681
08135142610
Handles
Instagram @ummu_mahnoor_luxuries
Facebook ummu_mahnoor_luxuries
____________________________
Ita kanta batasan yawan lokacin data dauka a wajen ba,batasan kuma ta jima a wajen ba sai data
fara jiyo muryoyin yaran gidan cikin wadanda ke zuwa islamiyya sannan ta tuna da HUDA NADRA DA
HANEEFA.
Ta tabbatar muddin suka shigo suka sameta a irin wannan yanayin sai hankulansu ya tashi. Wani
irin soyayya da kulawa suke mata,wadda sam sam basa qaunar abinda zai tabata komai qanqantarsa.
Da azama ta miqe tana leqa fuskarta tsakanin labulen falon zuwa filin tsakar gidan. Tanaso ta fita
ta wanke fuskarta ta kuma daura alwala,amma bataso taci karo da kowa ballantana su tunzura hali da
yanayin da take ciki.
Idanunta ta maida ta lumshe muryar titi tana mata amsa kuwwa a kunneta. Cikin duhuwar
idanuwanta tana hangen aisha da wannan innocent face din nata. Har yanzu bata huce ba daga abinda
azzalumin ya aikatawa aishan ba.....duk da burinta ya cika na danganashi da gidan kaso da tayi. Har
yanzu tana jin kamar hukuncinsa yafi qarfin wannan hukuncin da akayi masa a yanzun.
"Million takwas" Sautin adadin kudin ya ratsa kwanyarta. Ta ina zata soma nema?,ta ina kuma zata
samu?.
"Mashkur" Zuciyarta tayi mata hasashenshi farat daya. Tsam tayi da ranta tana juya sunan cikin
zuciyarta. A hankali sai kuma ta dinga gyada kanta,tana bawa kanta da kanta tabbacin yes......a jikin
mashkur yafi cancanta a hada wadannan kudaden,iya wannan tunanin ya sanyata juyawa zuwa dakin
nasu da gaggawa tare da mantawa da niyyar fita zuwa tsakar gida da takeson yi.
Zama tayi sosai saman gadon daga gefe. Locker gadon dake hannun damanta wadda ba kasafai
ta fiya budeta ba ta bude. Tarin tarkace ne a idanun mai kallo,amma a wajen sabreen wasu ajiyayyun
abubuwa ne dake da tarin muhimmanci da amfani a wajenta a mabanbantan lokuta. Har ma idan ka
tambayeta a wani lokacin tana iya ce maka SUNE SABREEN.
mitsitsiyar akwati ce wadda bata fi girman akwatin sanya zobe,ta saka hannu ta daukota sannan
ta bude. Wani qaramin layi ta ciro ta rufe akwatin ta maidata,sannan ta dauki wata farar qaramar
Samsung's ta bude gefanta ta zura layin ta maida wajen ta rufe sannan ta danne madannin dake gefen
damanta. Take ta kawo haske,bayan bayyanar tambari da sunan kamfanin komai ya dawo daidai yadda
ya dace.
Batakai ga danna komai ba saqonni suka fara turmutsutsun shigowa. Tsai tayi da idanunta tana
kallon notifications din har suka gama jerin gwanon shigowarsu suka qare. Kaman ta sharesu ta isa kai
tsaye ga abinda zai sadata da mashkur sai kuma ta sauya tunani.
Ma'ajiyar saqonnin ta shiga,ta fara bin sunayen mutanen da suka aje mata saqon daya bayan
daya don bata jin tana da isashen lokacin da zata tsaya budewa da karantawa.
Kamar yadda ta zata,ta samu saqonnin mashkur da yawa fiye dana kowa,saita wuce kowanne
saqo ta tafi saqon daya tura mata na qarshe kwanaki biyu da suka wuce.
Sallamarsa kadai ta amsa,ta tura masa ta maida wayar ta aje saman locker tana bin fuskar wayar
da kallo,zuciyarta na shirya mata yadda komai zai tafi.
Ta jima da ajjiye mashkur saboda yadda zalamarsa ta fito a fili. Ta jima da ganin ta barshi a gefe
saboda yadda halinsa yasha banban dana kowa cikin mutanen da ta taba tarayya dasu cikin rayuwarta.
To amma yanzu silar matsalar aisha tana ganin wannan shine right time da zata koya masa darasi shima
yabi sahun sauran mazan da suka shude cikin rayuwarta.
Agogon dake manne saman kanta ta kalla tana qoqarin dawo da nutsuwarta waje guda. Zuciyarta
ke wani irin rawa tamkar dai ta soma gajiya da al'amuran da suke tunkarota cikin rayuwa. Wasu su
shude,wasu kuma suna ci gaba da fuskantarta da babbar BARAZANA.
kamar mintuna goma sha biyar sun qaru akan lokacin dawowarsu daga islamiyya na ainihi. Aje
dubanta tayi saman hijabinta na sallah,saita miqa hannu ta dauka tana miqewa da zummar duba inda
suka maqale. Bata wasa da duk wani abu da ya shafesu musamman fita da dawowarsu gida. Duk da su
din kwata kwata basu san ko ina ba idan ka dauke hayoyi da layukan dakan sadasu da makarantarsu.
Kaman jira akeyi tayi taku uku daidai wayar ta dauki ringing. Duk da ta jima bataji ringing din
wayar ba amma babu abinda ta manta daga sautinta.
Taku ukun ta sakeyi ta dawo tana duban wayar bayan zuciyarta ta gama ayyana mata waye din
me kira
"Mashkur" Kaman yadda ta aje number dinsa. Siririn murmushin da bata shirya ba ya subucewa
labbanta. Tana tsaye tana ci gaba da duban wayar har ta qaraci burarinta ta yanke. Bata da niyyar daga
kiran kwata kwata a yanzun,don ba tsarinta bane samun komai daga wajenta cikin sauqi ba. Ta yardarma
kanta tana da tsada,tsadar data sanya kowanne namiji da zai ratsa ta cikin DUNIYARTA yarda da
hakan,ya kuma bita da tsarinta a yadda ya sameta.
Kaman yadda ta zata bazai kira sau daya ya bari ba haka taji wayar ta sakeyin qara,salin alin ta
koma ta maidata silent,sannan ta jawo Locker ta wurgata ta rufe ta kuma soma takawa hanyar falonsu
tana zura hijabin saman wuyanta. Shimfidadden kwarjinin dake boye bayan fuskarta ya sake bayyana
sosai tamkar ta sanya hijabin ne don ado ba domin biyan buqatarta ba.
Slippers dinta masu taushi ruwan hoda dake daga bakin qofar da zura ma fararen qafafunta,ta
murda handle din qofar ta bude ta tura ta fito.
Fayau tsakar gidan nasu yake da wadataccen filin nan da baya rabo da tsafta duk da iyalin da
gidan ke qunshe dashi. Kamar kowanne lokaci kamar kuma yadda suka maidata ABUN KALLO. Kowanne
motsinta yana saman idanun mafi yawa daga cikinsu,bawai don su bata kulawar data dace ba....bawai
don suyi mata gyara idan tayi kuskure ba......badon kulawa ta qauna ba.......saidai don wani radin kansu
da biyan buqatar qashin kansu.
Tana da wani irin kaifin nazarin fahimtar meke kai kawo a kewayenta. A zaune take ko tafiya
take?. Wani yanayi da a baya baya cikin dabi'unta,kuma bata dashi,amma yanayi da salon rayuwa ya
tilastata kasancewa hakan.
Dab da rijiyar gidan wadda daga ita sai hanyar da zata sadaka da ainihin farfajiyar gidan ta ganta.
Tsaye gaban rijiyar dauke da cup da alama ruwa ta gama sha.
Sanye take da atamfa classic da aka yiwa dinkin zamani riga da skirt daya zauna daidai jikinta.
Kanta ba dankwali wannan zai baka damar hango baqar sumarta me sulbi da suka gada ainihi daga
mahaifinsu.
Idanunsu cikin na juna na wasu sakanni,sai ta fara janye nata duban daga kanta tana ci gaba da
nufar soron.
HADIYYA......Idan har a baya za'a gaya mata rayuwa zata ajeta a bigiren da suke kai a yanzun ita da
ita zata qaryata......idan har a baya za'a gaya mata rayuwarsu zata koma kaman yadda take a yanzun
zatace mummunan mafarki ne mara ma'ana....wanda bashi da tushe ballantana makama.
Hadiyya 'yaruwar haihuwarta,wanda mahaifi yayi silar zamowarsu jini daya......hadiyyan da suka
taso qarqashin rainon mahaifiyarta......cikin daki guda saman shimfida guda,duk da murdadde kuma
zazzafan kishin da mahaifiyarta ke bazawa.......amma hakan bai sauya komai ba na kusancinsu.
Sai gashi a yanzun sunyi irin rabuwar hannayen riga. A yanzun haka tana nata karatun cikin
makarantar koyon aikin jinya bisa daukar nauyi da kulawar yayan mahaifiyarta......yayin da tata rayuwar
tayi matuqar shan banban da ta hadiyyan.......take neman ta nutse cikin neman dauki da tallafin data
gaza me kawo mata,har sai da tayi wani irin wawan tsalle da batasan zata sauka a daidai ko kuma garin
saukar tana iya gamuwa da karaya da tarin raunukan da zasu zamewa rayuwarta tabo?. Takai qarshen
tunanin sanda takai bakin qofar farfajiyar gidan ta farko,saita aza tafin hannunta saman fuskarta tadan
shafi fuskar. Tasan bawai kuka takeyi ba,don a yanzun batajin cikin qwayar idanunta akwai sauran ruwan
hawayen da suka rage da zasu bata hadin kan yin kuka. Kawai huci da dumin da fuskarta ya dauka takeso
taji ya huce,idanunta sake mata dan zugi zugi tanason rage musu adadin iskar dake shiga cikinsu.
Karo sukayi da huda sanda take shirin fita shigowa su suna shirin shigowa. Suka ja baya dukkansu
hudan tana dan riqe goshinta
"Ke kuma ina kuka tsaya haka dukka ku ukun har ana shirin kiran salla?" Ta jefa mata tamabayar tana
tsareta da ido. Kafin huda tace komai haneefa ta tsinke da dariya
"Anty.......yaa nadra muka tsaya jira......bata bada hadda ba sai malam ya tsareta" Idanunta ta mayar kan
nadra wadda fuskarta ke a daure
"Garin yaya?,kin soma wasa da haddar ne?" Kai ta girgiza da sauri,tana shirin magaa hudan ta rigata
"Kallo suka tsaya yi jiya da daren bayan kin kwanta" Fuska a daure ta sake maida kallonta a kansu
"Ashe?,yau zaku jawa kanku,sai na tsinke kowanne cable na kallo dake dakin nan"
"Ah wai.......ni abunnan yana dauremin kai?,wai lalatacce shike tarbiyya" Murya bibo ta ratsa
kunnuwanta sanda take dubansu nadra.
Dukansu ido suka azawa bibo din lokacin da take kutsowa cikin gidan. Kaman yadda suka fita ne
dazu,ita da daada,saidai kaman dazun ma daada ratsewa tayi ta wuce abinta ba tare data tsaya yiwa
bibo tayin su wuce ba kamar dazun.
Motsawa kadan huda tayi wanda motsinta kadai ya sanar da SABREEN abinda take shirin yi.
Yatsarta ta kada mata sautin da ya sanyata tsaiwa can tare da hadiyar wani abu me tauri a wuyanta
*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*
*ZAFAFA BIYAR*
*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA
ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*
_K'ALBIM Mamuhghee_
_DUNIYATA Huguma_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
*09033181070*
89825722
1000cf
*_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_*
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
*Arewabooks:@Huguma*
https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997
PAGE 26
__________________________
*_ALBISHIR A GAREKU!!_*
*_SHIN KUNSAN UMMUMAHNOOR LUXURIES TA TANADAR MUKU INGANTATTUN KAYAN ADO NA FITA
KUNYA KUWA?_*
*_KAMAR SU_*
Atamfofi
Laces
Shadda
Materials
Takalma
Jakunkuna
Mayafai
Trolley
Oil perfumes
Numbers
08034469681
08135142610
Handles
Instagram @ummu_mahnoor_luxuries
Facebook ummu_mahnoor_luxuries
__________________________
"Ku wuce muje" Sabreen tace dasu,suk sai sukayi gaba tana biye dasu a baya. Nadra ta hadawa
kayan duka ta wuce musu dashi daki. Ita tayi tsaye dasu kowacce ta gama buqatarta suka daura alwala
suka wuce daki.
Sallah sukayi bayan sun sauya uniform. Har a sannan tana ankare da yadda huda din keta
hadiyar zuciya. Ta sani muddin tace zata saki huda tayi abinda takeso zaman bazaiwa kowa dadi
ba......tafi huda zuciya nesa ba kusa ba......tafi huda dabi'ar take yanke.....amma me?,daga baya ta
fahimci me irin wannan dabi'ar ba kasafai yake nasara ba.
Sai data kammala sallar magariban sannan tabi takan wayar. Ta samu miscal biyar hade da wasu
saqonnin daga gefe. Tabi number tasa da kallo,sai a yanzu takejin ta shirya saurararsa. Kamar yasan tana
riqe da wuyar saiga wani sabon kiran ya sake shigowa,don haka ta miqe a nutse ta koma daki tana
matsawa daga inda su nadra dake cin abincin dare suke.
"Laifin me nayi dana cancanci wannan uqubar fateema?" Numfashi ta saki wanda sautinsa ya isa har
kunnensa
"Ki gayamin ko meye nayi a shirye nake da na nema afuwa" Shuru ta sakeyi tamkar bata layin,saidai tana
sauraren dukka maganganunsa
"Fateema" Ya sake kiranta da sunan da shine nasa STAMP din,sunansa ne shi daya,duk duniya shi ta
mallakawa wannan sunan
"Kinsan irin rayuwar dana tanadar miki?,kinsan irin gatan da nakeson miki?,kinsan yadda nakeson
maidaki tauraruwa a cikin mata?,kinsan yadda nakeso ki koma tamkar sarauniya?"
"Me kike da buqata fateema......ki gayamin,a shirye nake na mallaka miki su......"
"Ko a ina nake a duniya a yanzun haka kika ce kina buqatar ganina zan wanzu a gabanki" Maida idanunta
tayi ta lumshe sannan ta budesu
"Mu hadu yanzu fateema?,ko dan kadanne inaso naga fuskarki"
"Alright" Ta amsa masa a taqaice,abin da yazo masa a bazata,don haka a rude yace
"Venue?"
"Zan gaya maka,i will call you" Bata sake bashi daman cewa komai ba ta yanke kiran.
Wayar ta riqe a hannunta tana juyata a hankali bayan ta zubawa guri daya idanu. Lissafi ne fal
Qwaqwalwarta,dole kafin ta samu abinda take nema saita yi haquri ta sake masa,dole ta dinga bashi
mabanbantan gurare har zuwa sanda tsarinta zai fada aikinta zai cimma nasara.
A nutse ta miqe tana wassafa yadda zata fita yau din da dare,abinda sam ba dabi'arta bane saiya
zama mugun dole,ba kuma zata iya tuna lokaci na qarshe da hakan ya taba faruwa da ita ba,amma
yanzun dole ta fitan,tanason ta amintar dashi sosai a kanta.
Kai tsaye ta wuce ma'ajiyar kayanta tana duba suturar da zata dace da ra'ayinta a wannan lokacin.
Da idanu ta gama qare musu musu,daga qarshe ta tsaya saman wasu Turkish dress masu strip skirt long
sleeve shirt da doguwan kinomo sai madaidaicin veil da zai lullube saman kanta.
Sam bata da ra'ayin sutura me matse jiki duk kuwa da yadda mutane da yawa suke kallon ita tafi
dacewa da irin wannan shigar.
Tsaf ta shirya cikin kayan kalolin navy blue da gray color. Sanda ta gama nada veil din a kanta sai
data sake duban kanta sosai ta cikin madubin. Tayi wani irin sassanyan kyau me matuqar daukar hankali.
Ta miqa hannu a nutse ta dauki turarenta ta feshe jikinta can qasan ranta tana jin fargaba kadan kadan
kan haduwarta da mashkur,saidai kuma wani sashe na zuciyarta yana qarfafa mata gwiwar ba
komai,wannan ne haduwan farko,nothing will happen.
Asalin wayarta ta jawo tana lalubar number JIB. bugu daya tak ya dauka,tadan motsa bakinta a
nutse
"Ko ba hakan bane ai ya zama dole nayi creating time wa ke.....me kike buqata?"
"Karka damu.....mu sanya wancan a mala.....wannan din shine yafi muhimmanci a yanzu"
"An gama.....bani code......let me write it" Ya fada yana dan riqe wayar kadan kafin yace
"Okay.....karanto" A nutse ta karanta masa wasi gajerun lambobi guda uku sannan ta katse kiran. Ta
jawo locker madubinta ta ciro Bluetooth tayi danne danne saman wayar tata ta bada wasu sakanni
sannan ta maqala a kunnenta. Saita aje wayar,ta dauki wancan Samsung din ta kunnata sannan ta fara
yunqurin kira.
Bugu daya tak tayi aka daga,ta kalli wayar da mamaki sanda yake cewa
"Am ready to go princess......ina zaune a mota nida driver a parking lot na gida"
"Yayi.....but if possible ka taho kai daya mana"
Tana kammala saka takalma huda na shigowa dakin. Kallo daya tak tayi mata taga yanayinta ya
sauya. Hudan tadan ritsata da idanu tana dubanta,saidai tun kafin takai ga tambayarta ta bata amsa
"Zan dan fita kadan amma yanzu zan dawo" Iya abinda ta gaya mata kenan ta fara takawa zata fice.
A jikinta taji yarinyar kallonta take,a jikinta taji tana tsaye ne kawai har yanzu,don haka ta tsaya
cak sannan ta waiwayo. Ido suka hada,sai a sannan hudan ta kauda kanta. Iya hakan ya gayawa Sabreen
maganganune sosai cikin zuciyarta,wataqila girma da kimarta kadai zai hanata ta furta mata su. Taku
hudu tayi ta iso gaban hudan
"Dole ce ta saka zan fita huda......amma bazan wuce awa daya ba,idan na dade biyu"
Yatsanta ta dora saman lips tana duban hudan,sai kuma daga bisani ta dauke yatsan tana aza
dukka hannuwanta saman kafadarta,ta kuma zaunar da ita saman stool na madubin dakin
"Ke daya ce tal cikin mutanen da sukasan wace Sabreen gaba daya baya,kada kiyi tunanin na
canza......ban canza ba huda.....kuma har abada bazan canza ba.....nayi alqawari......mommu da abba
dake qarqashin qasa bazan bari suyi kaico dani ba" Kai ta gyada a hankali tana kallon Sabreen kamar
yadda itama ita din take kallo. To amma a hankali tana rasa wannan yardar wanda tasirin maganganu
daga kowanne saqo da lungu na layinsu dama unguwarsu ke kai kawo a kunnuwanta
"Don't lose hope huda......alqawari na.....bazan karyashi ba,ki kula da nadra da haneefa" Ta fadi mata
daga qarshe ta juya tana fita a dakin. Nata ruhin yana motsuwa.
Har abada ba zata daina zargin maraici ba......har abada ba zata daina kuka dashi ba......a wani
sashen na duniya,a irin wannan lokacin,diya kamarta tana qarqashin kulawar mahaifanta ne guda
biyu.......ko kuma qarqashin kulawar wasu amintattun mutane da zasu zame mata makwafin
iyayen.......sai gashi tata DUNIYAR ba haka bane,dukka kafadunta dauke suke da wani irin nauyi dakeson
fin qarfinta ya kaita qas.
Daga baya baya ta sanya busari ya ajeta kafin akai ga shiga gurin a yanayi salo na kula da takunta
kanta dama dukka wani motsi nata.
Sallamar busari tayi tace zata nemeshi idan hakan ta taso,sannan ta fara takawa a hankali tana
nufar wajen.
A hankali take ratsa wajen cikin nutsuwa data zame mata dabia,tana takawa a hankali qamshinta
da kuma yadda shigar ta amsheta kadai suka soma jan hankulan matasa da yawa wajen. Guri ne da
yakan hada matasa maza da mata,wayayyu da suke da gogewa a fannin rayuwa kudi da kuma ilimi.
Wajene kebantacce da yawansu suka maidashi gurin nishadi da kuma debe kewarsu,wasunsu a duk
daren duniya,wasu kuma jifa jifa.
Yadda take daukan hankulansu haka kwarjininta ke dukansu,wannan ya sanya duk wani dakeson
kawo mata caffa ya gaza yin hakan,saidai tazo ta ratsashi ta wuce shi kuma ya bita da kallo.
Tun daga nesa ta hangeshi,ya fita yayi tsaf cikin wani lafiyayyen jeans da shirt da suka dace da
takalmin qafarsa. Kanshi pcap ce daya sauko da ita tadan rufe masa fuska. Hannunsa dauke da wayarsa
yana latsawa a hankali ba tare daya damu da abinda ke kai kawo a wajen ba.
Ta sani,hankalin gomayyar 'yan mata dake wajen tabbas suna kanshi. Mashkur din ba irin mazan
da mace me muradin jinsin maza irinsu zata kall sau daya bane ta iya kauda kai kota wofantar,kusan zata
iya cewa ya hada dukkan komai,abubuwa da dama da mazan da suka taba ratsa rayuwarta ba wanda ya
gama cikasu irin haka. Yana da kyau daidai gwargwado wanda kudi suka sake qawatashi,yayi karatu har
zuwa matakin degree,hakanan dan wulaqanci ne shi,wulaqancin daya zame masa ado a idanun mata
marasa kamun kai. Idanunsa a bude suke tarwai,yana da wata irin wayewa data zarta shekaru da kuma
iliminsa,wanda hakan baya rasa nasaba da fita qasashen waje da yake yawan yi,musamman qasashen
turawa.
Dab da zata iskeshi ya daga kansa sai suka hada ido. Zumbur ya miqe yana zube mata idonshi,har
cikin zuciyarsa yana jin wani abu daya qarasa mamaye gangar jikinsa.
Karon farko daya soma jin ra'ayinsa akan mace na neman canzawa. A yanzun kallo daya
tak.....cikin qasa da minti daya kacal ya soma ji a ransa kamar ya aureta shine abinda yafi dacewa dashi
da ita gaba daya. Kamar alaqar daya shirya da dangantakar daya shirya ginawa a tsakaninsu ba ita ta
dace ba,duk da har yanzu gaza fuskantar AINIHINTA....a wanne mataki na 'yammatan wannan zamanin
take?. Wasu abubuwan nata na masa kama da dabi'un mace ta musamman.....amma wani motsin nata a
wani lokacin sai ya sanya masa shakku akan haka. Kamar dai yanzun,yadda duk da duhun dare ya lullube
sararin subhanana amma hakan bai dasa mata shakku ko ya zama dalilin qin fitowa su hadu ba.
A maimakon kujerar daya ja mata don ta zauna saita matsa kujera ta gaba,saidai kuma fuskarta a
sake tana maida masa martanin murmushinsa.
*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*
*ZAFAFA BIYAR*
*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA
ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*
_K'ALBIM Mamuhghee_
_DUNIYATA Huguma_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
_YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_
*09033181070*
89825722
1000cf
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
*Arewabooks:@Huguma*
https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997
PAGE 27
_________________________
*_ALBISHIR A GAREKU!!_*
*_SHIN KUNSAN UMMUMAHNOOR LUXURIES TA TANADAR MUKU INGANTATTUN KAYAN ADO NA FITA
KUNYA KUWA?_*
*_KAMAR SU_*
Atamfofi
Laces
Shadda
Materials
Takalma
Jakunkuna
Mayafai
Trolley
Oil perfumes
*_karki tsaya sanya har ayi babu ke,maza garzaya ta nan_*
Numbers
08034469681
08135142610
Handles
Instagram @ummu_mahnoor_luxuries
Facebook ummu_mahnoor_luxuries
_________________________
Idanunsa a kanta kaman bazai iya daina kallonta ba yana nashi seat din ya zauna
"Finally dai after wasu watanni......har na debe tsammani sai gashi......" Ya fada yana dan watsa
hannayensa irin na gogaggun samari
"Me ma bahaushe yake cewa?.....me haquri ko?" Ya aza mata nauyin amsa tambayar ta hanyar kallonta
da idanunsa.
Qaramin murmushi kawai ta saki tana maida bayanta ta jingina sosai da kujerar da take kai
din,yayin data daba hankalinta gida biyu. Wani a gurinsa,wani kuma yana kan yanayin wajen dake cike
da 'ya'ya mata. Tayi imanin dukkaninsu uwaye ne suka haifesu,koda ace akwai na gaba da fatiha to
kadanne. Son rai son zuciya kwadayi su sukayi musu jagora zuwa ga turbar da suke kai a yanzu?. Ko
kuma suma kamar ita dinne?.
Idanu ya kashe mata cikin salon jan hankali me zafi,ya kuma sake matsowa sosai har yana
rungumar table din da suke kai zuwa qirjinsa,sannan ya aje manual din da aka kawo ta hannun waitress.
"Choose babe" Ya fadi yana lanqwashe murya kamar wani mace gami da kanne mata idanu. Manual din
da ya tura mata ta sauke idanu a kai. Tarin abinciccika ne iri daban daban,wanda ko kaffara ba zatayi ba
idan ta qiyasta maqudan kudaden da za'a lasa ta sanadiyyar cinsu. Sai data qare musu kallo gaba da
baya,yayin da shi da waitress din ke jiransa ba tare da sun qosa ba,saita maida ta ajiye saman table din.
Ta motsa bakinta zatayi magana kenan sallamar da akayi da wata raunanniyar muryar taja hankalansu.
Dukkansu shi da ita suka maida dubansu ga wajen. Matashiya ce mai matsakaicin haske wadda
idan ka kalleta a qiyasin da zaka fara yi mata duka duka shekarunta ba zasu haura ashirin da bakwai
zuwa da takwas ba da haihuwa. Sanye take fallen zanin atamfa da kai tsaye zaka kirata da atamfa leda ko
roba,duba da yadda ta cukuikuye a jikinta saboda tsufa da rashin quality da kuma yanayi na dan busawar
iska data hadu dashi. Qasan zanin a cinye yake abinda zai wassafa maka kenan shekarun da atamfar ta
dauka a duniya ana amfanarta. Hijabi ne a jikinta daya fara gajiya da rayuwa,tsananin sussuqewarsa ya
sanya ya baiwa me kallo daman hango yaloluwar rigar dake a jikinta.
"Ke kuma fa?,daga ina wa kike nema?" Mashkur dake dubanta sama da qasa da wani irin qasqantaccen
kallo ya jefa mata tambayar.
Rusunawa qasa tayi cikin matuqar taushi da karyar dakai ta hade hannuwanta biyu waje daya
"Taimako nake buqata yallabai......don Allah ka taimaka min da duk abinda Allah......"
"Wait.....wait mana" Ya fada a tsawace har hakan ya sanyata miqewa ta tsaya saman qafafunta.
Waiwayawa yayi zuwa ga waitress din
"Yaushe wajen nan naku ya lalace?,yaushe kuka fara bawa mutane irin wadannan daman shigowa gurin
nan.....wait.....wai bakusan kowa na zuwa irin nan bane don ya huta ya kuma yi uzurin gabanshi ba tare
da kowa da komai yayi disturbing nashi ba?".
Duk joint din da basusan fuskar mashkur ba to tabbas ba cika joint ba......imma darajar wajen
tsada da kuma darajarsa batakai ba......ko kuma dai kawai wajen bai cikin tsari da ra'ayinsa. Wannan
abun ya sanya cikin rudewa ta soma bashi haquri tare da qoqarin nesanta matar daga wajen,duk da
yadda kuwa take roqon su taimaka mata.
A nutse Sabreen ke kallon matashiyar zuwa ma'aikaciyar ma gaba daya. Yar uwarta nace ke
qoqarin rabata da gurin don dai kawai kada ta batawa customer rai ta hanyar da babu girma arziqi ko
darajta dan adam. Yanzun inda ace cikin kyakkyawar shiga take.....inda ace cikin dressing me kyau
take......inda ace jikinta a gyare yake......inda ace zata koma hakan tabbas basai ta tsaya bagging a
taimaketa ba. Ta cikin ruwan sanyi matasa dama manyan ire iren wadanda ke zaune yanzu haka a wajen
zasuyita miqo mata buqatunsu,wanda yadda ta karba da hannu bibbiyu......kwatankwacin hakanne zata
samu nata biyan buqatar.
"Dakata......barta ta dawo" Sabreen din ta samu kanta da furtawa idanunta da suka canza launi suna
saman fuskar waitress din.
"Kamar yaya?,ki barta......" Mashkur ya furta yana maida idonsa ga matashiyar data fara takowa a
hankali zuwa inda suke din
"Nooo" Ta amsa masa da wani sauti da yake tafe da wani irin zafi da ya motsa mata zuciya. Ganin matar
kawai ya tuna mata abubuwa masu yawan gaske,ganinta ya fama mata wani babban ciwo,sai ta sanya
hannunta cikin mitsitsiyar handbag dinta sannan ta zaroshi da dukkan kudin dake cikin jakar ta miqa
mata.
Cike da mamaki take kallon fuskar sabreen din. Saita motsa kanta tana mata nuni da kudin. Wani
irin karyewa zuciyar matar tayi,sannan ta sulale da wani irin qarfi ta tara hannuwanta tana amsar kudin.
Jiki da muryarta dukka rawa suke sanda ta fara jera mata addu'a da godiya
"Ya isa jeki" Mashkur din ya fada yana fatan ta gusa ta basu waje ba tare data bata masa budget ko ta
bata masa lokaci ba.
Cikin jikinta taji cewa ita din mashkur yake kallo. Ta lumshe idanunta tana qoqarin daidaita
mode dinta,sai kuma daga bisani ta sauke mata wannan kallon nata dake saurin waftar hankali
"Are you okay?" Ya jefa mata tambayar cikin matuqar nuna kulawa. Sai da ta danyi gyaran murya sannan
ta gyada kanta
"Am okay....."
"Am sorry ko?,irin wadannan mutanen dear ki daina gaggawar amincewa dasu ko basu taimako.....they
are wicked wallahi at so many times......yanzun kalli yadda ta bata mode dinki gaba daya?" Gyara
zamanta sosai tayi tana maida qafarta daya ta dora saman dayar,sannan ta sarqafe yatsunta saman
qafarta tana sake zuba masa idanu. Rashin tausayi rashin imani da kuma rashin bawa dan adam
darajarsa yana fita fes a tare dashi,wanda hakan ya sanya taji a ranta yayi deserving ayi punishing dinsa
qwarai da gaske fiye da yadda ta shirya yi a baya.
Ya daddage yana sharhi akan baiwar Allahn da baisan wacece ba?,meye matsalarta?,meye
damuwanta cikin sararin subhana?.
"Is okay ya wuce" Ta amsa masa a taqaice tana kallon agogon da yake daure a tsintsiyar hannunta.
Hankalinsa yadan dauko kadan,a duk sanda yaga tayi hakan alama ce dake nuna tana dab da yin
layar zana,layar zanan da idan tayin baka isa bincikota ba sai sanda taga damar bayyanar maka.
"Am......bamu tattauna komai bafa......if possible a qaramin minti goma kacal.....in sha Allah bazan haura
haka ba" Hannuwanta ta aje daga daukan handbag dinta da tayi niyya,ta koma ta sake harde qafafunta
tana kallonsa.
Shima idanun ya zuba mata yana jin yadda kowanne sashe na jikinsa yake da buqatarta
"Wai sai yaushe zaki soni kaman yadda nake sonki fateema?" Ya tambayeta bayan ya sauke wata
wawiyar ajiyar zuciya. Dukka girarta guda biyun ta dage tana sake nazarinsa ta cikin qwayoyin idanunsa
"U mean......kina sona kaman yadda nake sonki?" Sai data lumshe ido kadan as usual sannan ta gyada kai
"Okay,prove it" Ya fada da wani irin zumudi yana gyara zamansa sosai tare da rinjayar da gangar jikinsa
zuwa zuwa mazauninta.
Ido tadan juya,reaction na fuskarta na nuna masa bata fahimta ba,a nutse ta motsa labbanta
"Like?....."
"Dis week nakeson zuwa dubai nayi annual leave dina......zanji farinciki fiye da yadda baki
tsammani.....zanyi alfahari dake zan kuma mallaka miki komai da kike buri cikin rayuwarki......." Sai ya
bude wallet nashi dake aje gefe,ya zaro wani qaramin littafi me abun rubutu a gefansa,ya buda tsakiyar
littafin ya sanya biron,sannan ya aje mata shi a gabanta yana cewa
"Write it down.....,ko meye.....komai girmansa kada ki gaza rubutawa,and zai kasance ne as you wish"
Fararen idanunta ta dora akan littafin kamar me nazarin launin takardar
"Musayar mutunci" Zuciyarta ta raya mata hakan. Wani zafi taji har cikin qwayar idanunta,saita dauke
idanunta dama kanta daga wajen ta maidasu gefe. Cikin qasa da second biyar zuciyarta ta gama tsara
komai,don haka ta waiwayo ta fuskanceshi sosai sanda yake fadin
"What happened fateema?....." Yana leqen fuskarta. Murmushin da ta fuskanceshi dashi ya sanya yaji
relief,fatan samun nasararsa daya soma zagwanyewa duk sai yaji yana dawo masa.
"Nothing......kawai gani nayi kazo da qaramar buqatar da bata buqatar dogon sharhi da roqo har
haka......kaman ma bata buqatar tafiyarmu wata qasa......nan ma zata iya zama dubai dinmu"
"Yes" Ta amsa tana daga masa kai da nata guntin murmushin daya tsaya iya labbanta.
"Thank god.....thank you fateema......ban taba tunanin it gonna be easy kaman haka ba"
"Not now......am tired.....inason na koma gida na kwanta.....see you next time saimu qarasa tattaunawa"
"When?,ina gudun ki kufcemin fa?" Bata amsashi ba sai data gama gyara zaman rolling dinta
"Tom" Ta fada kawai tana shirin daukar jakarta,saidai kuma shi din ya rigata ta hanyar jawo jakar
gabansa.
Duk da bata saka ido da kyau ba,amma idanunta sunga tamkar takardun kudin waje ya saka
mata
Ya sani,daya daga cikin rules nata shine baa yi mata rakiya idan zata tafi,don haka a nan yayi
tsaye goye da hannayensa yana kallom nutsasen takunta har ta fice daga gurin.
Ko daya bata jin me busari yake fadi sanda suke tafiya a hanya. Gaba daya tunaninta yayi nisa
zuwa wata duniyar ta daban.
Lissafe lissafe ne fal kwanyarta,tama rasa da wanne zata fara?,daga ina zata fara?,a ina kuma
zaren lissafin nata zai katse. Zuciyarta da idanunta sunason zuwa ganin aishatu,to amma kuma bata so
taje ta ganta a halin da take ciki alhalin bata tanadar mata da komai da zaya fiddata daga wannan
yanayin ba. Jib ya kirata,ya tabbatar mata aiki duka ya kammalu daga bangare biyu,amma ta gaya masa
ya saurara ta isa gida tukunna.
Goma saura busari ya ajiyeta daga gaban gidan nasu,ta sauke hand bag dinta ta zuge don masa
ihsani kaman yadda ta saba,duk da shi din bai kawo komai cikin balance din da ha kamata ace ya kawo
din ba amma bata damu ba. Sai data zura hannunta a jakar ta tuna bata da komai sai irin kudin da
mashkur ya zuba mata. Tadan jawo kudin gaba kadan tana dubansu,sabbin US dollar ne qar dake qyalli
da qamshin sabunta,saita maida dubanta a kanshi
"Zan saka maka wani abu busari ta account,ka bayarma inna kace tayimin addu'a,saida safe"
"Kinfi gaban haka......Allah ya bamu alkhairi" Ya fada yana dan bin bayanta da kallo. Yana mamakin kirki
irin nata......duk da ita din zuma ce a wani lokuta idan bataso ba,ga zaqi ga kuma harbi. Ya tayar da
napep din yana janyeshi da qofar gidan,qasan ransa kuma yana qididdige adadin alkhairinta a tattare
dasu.
*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*
*ZAFAFA BIYAR*
*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA
ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*
_TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_
_K'ALBIM Mamuhghee_
_DUNIYATA Huguma_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
89825722
1000cf
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 28
Sanda ta isa falon dukkansu ta samesu qudundune saman kujera,kowacce nannade da blanket
dinta. Huda ce kadai zaune saman carpet nannade da hannayenta tana kallo a tashar Arewa24.
Tayi mata sannu da zuwa ta amsata tana wucewa ciki don rage kayan jikinta ta sauyasu zuwa da
na bacci,gashinta ta kama ta daureshi waje daya ba tare da tasa komai ba,don bata fiya son abinda zai
takurata ba duk sanda zata kwanta,ta shafe jikinta da daddadan turarenta me sanyin qamshi data
wareshi ne kawai don kwanciya ta dawo falon.
Tsam huda ta miqe ta gabatarata da abinci,saidai bat jima da fara cin abincin ba wayarta ta dauki
tsuwwa. Jib ne,qaramin tsaki ta saki,a lissafinta ta gama amsa kowanne kira don bacci take da buqatar
tayi,tanaso gobe ta shiga wajen aysha taga yadda jikinnata yake. Abun ya tsaye mata a rai,tana jin cewa
idan tana da dama a rayuwa zata sauya rayuwar Yarinyar ne gaba daya.
"Komai ya kammalu" Ya gaya mata kai tsaye. Dan shuru tayi tana saurarensa,daga yadda yake mata
magana ya tabbatar mata fuskarshi qunshe take da fara'a duk kuwa da bata iya ganinsa.
"Okay.....meye result?"
"Bari na fara da abinda yafi damuna yafi kuma yimin dadi......da farko dai zan iya ce miki
congratulations.......ina kyautata zaton indai zakiyi amfani da damarki sosai yadda ya dace,kin kusa fara
shiga jerin sahun mata masu arziqi......kawai dai" Ya fada yana dan sauke qaramin numfashi
"Wani lokaci duk wani opportunity sai naga kamar kina shuresu ne da gangan......"
"Ina tare da ke,sai na yita tunanin fa me yake damunki?" Yadda yayi maganar a wani sanyaye ya sanyata
murmushin dole. Tasan me yake buqata a nashi son rai ace tana yi
"Ko kadan.....kawai daman da kike samu ya zarta yadda kik amfani da ita......"
"Bani labarin aiki na" Ta zabi shafe wancan maganar gaba daya,don ba me amfani bace a wajenta kamar
yadda nashi hasashen yake bashi.
"Congratulations once again.......daga mashkur har mika'il.....suna daya daga cikin mutanen da suka
mallaki manya manyan dukiya........sunyi tarayya ta wajen hali da dabi'a.........amma ta gurin source of
income nasu sun sha banban"
"Ehnnnn" Ta fadi tana juya abincin gabanta da spoon ba tare da takai ko loma guda bakinta ba tun bayan
kiran nata da yayi
"Mashkur dan kasuwa ne kamar yadda yace.....yana aiki tare da mahaifinsa......mika'il kuma wani babba
ne a wani babban kamfani daya boye sunansa......don kamar yana cikin policy na kamfanin ma'aikata
irinsa su dinga exposing kansu da rank dinsu cikin company din......saidai iya abinda hangena
yakai......company ne babba dake samu da kuma biyan kowanne ma'aikaci albashi me matuqar tsoka"
Yakai qarshe yana sauke numfashi tare da sararawa.
Ajiye spoon din tayi tana gyara zamanta, bayanan sun mata dadi sosai,kuma su suka haska mata
akwai nasara akan mission nata. A hankali tadan aza dubanta akan huda,duk da hankalinta yana ga
kallo,to amma kuma bata bari tayi dukkan wata magana data shafeta a gabansu
Wayar ta sauke tana bin fuskarta da kallo,tunani ne cinkus cikin zuciyarta. Fuskar matar dazu
kawai ke mata yawo a idanu
"Meye amfanin dukiyar da bazaka bayar da ita ba fisabilillahi saidai qarfi ya qwata?" Ta furta a qasan
ranta tana tambayar kanta da kanta. Daga mashkur har mika'il tayi imanin cikin budin da Allah yayi
musun,inda zasi fidda abinda suka mallaka su dinga narkasu cikin nutsuwa a hanyar data
dace......dubban jama'a zasu samu sauqi da radadin da yake damun zukatansu da gangunan jikinsu.
"An kawo miki saqo" Taji muryar huda daga gefanta tana fada. A nutse ta daga kai tana duban hudan
kafin ta maida dubanta ga akwatin data jawo gabanta.
Zuba masa idanu tayi tanason tuna daga ina?. A hankali sai kuma abun ya fado mata,ita sam ta
manta sunyi dashi ma zai bada saqon
"Kaishi daki" Ta fada tana maida kanta ga waya. Wata number ta lalubs a gajarce kuma ta tura mata
gajeran saqon karta kwana
"Received......thanks".
Shi daya ne cikin qawataccen falon da aka qawatashi da dukkan wani nau'in kayan alatu da qawa
na rayuwa. Madaidaicin falone wanda ke da saurin janye idanun me kallo da kuma sauqin shiga rai lokaci
daya ya kuma dace da kowanne mode da mutum yake ciki.
Shi daya ne tal cikin falon,sanye yake da shirt me gajeran hannu sky blue,sai gajeran wandon da
duka duka iyakarsa gwiwarsa.
Yana a tsaye ne yana fuskantar qatuwar t.v plasma dake zaune dirshan saman kyakkyawar tv
stand suna haska wasan qwallon qafa,saidai fiye da rabin hankalinsa baa wajen yake ba.
Bayan gilmawar kowanne minti ko second sai fuskarta ta dawo masa. Ya lumshe idanunsa sanda
aka buga qwallo na qarshe cikin tazarar bada sa'a game rabo wato penalty,ya daga ragowar tsadajjiyar
giyar data rage a qasan glass cup din hannunsa ya qarasa kurbeta,ya dire cup din yana fidda iska daga
bakinsa.
Tsakanin awannin daga dazu zuwa yanzu ya gama tsara yadda zai baibaye rayuwarta da
tsadajjiyar rayuwa......yadda zai narkar mata da zuciya da masu gidan rana......yadda zai maidata tashi shi
kadai......yadda kuma zai siye mata zuciya da kuma rayuwa da kudi wadanda yayi imanin a wannan
lokacin da muke ciki sune maganin kowacce matsala.....suke iya siya maka dukka nau'in macen da
kakeson ka mallaka.....don babu yaren da matan sukafi ganewa irin yaren LUXURY LIFESTYLE.
Kallonsa ya mayar saman system dinsa dake kunne,yana jiran kirane daga wajen CEO na JADDA
DIAMONDCHORE RESOURCES (JDCR).
A duk sanda sunan ya fado masa a rai,ba abinda yake fara zuwa ransa sai GIDAN KUDI. wanna
shine sunan da yafi kiransa dashi......wannan shine full definition nashi da yake ganin ya dace dashi gaba
da baya.
Sake matsawa yayi ya gani koda ya nemeshi?,amma ba wani saqo ko kira kai tsaye ta yanar gizo.
Mamaki yadan kamashi,saboda sanin da yayi masa na zamantowarsa mutum me girmama lokaci tare da
bawa lokaci muhimmanci,yasan tabbas akwai abinda ya riqeshi ne hala.
Baiso yasha komai ba har sai sun kammala duka maganganun da zasuyi through video call. Yasan
halinsa,yana da tsananin zafi yana kuma da masifar kaifin karantar mutum,wanda banda shima ya zama
mutum me tsananin iya takunsa yayi imani da tuni labari ya jima da shan banban.
Yaci wuya ya kuma tsallake turaku gwaji da jarrabawoyinsa sosai kafin yakai matsayin da yake kai
a yanxun. Saidai kuma tsakanin jiya zuwa yau burinsa ya fara fadada. Ya fara jin cewa yana buqatar
budawa a harkokinsa fiye da wannan da yake ciki a yanxu,yana buqatar qarin kusanci da CEO fiye da
wannan kusancin........yana so matakin da suke kai sufi haka shi da shi na qullewa da kusanci tare da
sakar masa ragamar komai na kamfanin fiye da yadda yake kai a yanzu.
Sai ya zagayo saman kujera ya zauna saboda yadda yaji jikinsa ya fara week,alamu dake nuna
abinda yasha din ya fara tasiri a jikinsa,duk da giya ce me tsadar gaske da yake kashe kudade masu kauri
wajen siyota,bata bugar dashi buguwar da zata sanyashi fita daga hayyacinsa gaba daya.
A sannan sai yaji bashi da wani sauran muradi daya wuce yaji muryarta,gaba daya taswirar
qwaqwalwarsa ita take hasko masa cikin shiga da dressing daya dinga ji kamar yayi fiffike ya kamo ta,don
haka ya jawo wayarsa ya fara gwada number dinta. A karo na uku kenan daga dazu zuwa yanzun da ya
fara kiran nata bai samu isa gareta ba,saidai a yanzun cikin sa'a......har ya fidda rai da tsammani......dab
da zata tsinke sai aka daga.
"Kin barni da kewarki ko?" Ya fada murya can qasa. Shuru tayi tana sauraren yadda muryar tashi ke fita
kafin ta motsa bakinta a hankali
Wani siririn murmushi ta saki,irin wanda take saki din a duk sanda wani cikinsu ya kirata da stamp
name dinsa
" Ba yanzu ba" Ta bashi amsa,amsar da a zahiri da gaske take,ta fito ne daga qasan zuciyarta. Ba kasafai
take baka damar ganinta ba a sanda ka damu da ka ganta din,muddin akwai mission a kanka saita kaika
matakin da take da buqatar kaje din.
"Zan katse kiran,bacci ne a kaina,zan sauka saida safe?" Tayi furucin da sigar tambaya,bawai don tana da
buqatar amsa ba.
Bai samu sararin cewa komai ba t gintse kiran tana aje wayar a gefanta tare da bin wayar da kallo
"Zatayi girman kai,zatayi izza tun a ganin farko na sani......amma kuwa zuwanki hannu bazaiyi wahala ba
'yammata" Ya fada a sarari yana lashe baki hadi da sakin wani shu'umin murmushi.
Yana shirin aje wayar wani kiran ya shigo masa. Mato sunan dake rubuce da number dake kiran
nasa.
Wani zunkudawa yayi sanda ya gama hada haruffan me kiran nasa saboda yadda kanshi ya fara
nauyi,ya daga wayar ya sakata a hands free ya ajiyeta,sannan ya koma da baya ya jingina yana
saurarensa
"Sai ogaaaaaa.......sai bosssss"
"Ba kadan ba kuwa.......na samo mana wani sabon zone na caca.......harka ruwa ruwa.......kudi faca
faca.......A wanki gara......abun kuma babu kama" Gyara zamansa yayi sosai yana bashi hankalinsa. Baya
wasa da harkar caca kwata kwata,suna daya daga cikin abinda ke kawo masa maqudan kudade bayan
kamfanin jadda DIAMONDCHORE da ya zame masa lamba daya
"Kaman yaya?,yimin dalla dalla,don wutata ta kusa daukewa" Ya fada muryarsa tana dan rangaji.
Yasan waye ciki da bai dinsa,tunda ya fadi hakan kuma ya gama fahimtar abinda ke faruwa,don
haka ya tattara bayanansa ya gyara zamansa yana cewa
"Wani gurin caca wanda na tabbatar a wajenka me gida local ne......akwai 'yan wasa na haqiqa amma
kuma kai tsaye na fahimci cewa gidadawa ne.......basu da wani wayewa kwata kwata a cikinta.......akwai
kudade amma fa a qasa,na tabbatar a bugu daya zaka tarwatsasu ka kuma yi gaba da duk wani abu da
suka shigo cacar dashi" Wata shu'umar dariya ya saki
"Mato nawa" Ya furta maganar mato din na masa yawo saman kai,saidai gajimaren da yahau ya hanashi
tsaiwa su qarasa maganar,don haka ya sanya hannu ya katse kiran kawai yana furta
*_ALBISHIR A GAREKU!!_*
*_SHIN KUNSAN UMMUMAHNOOR LUXURIES TA TANADAR MUKU INGANTATTUN KAYAN ADO NA FITA
KUNYA KUWA?_*
*_KAMAR SU_*
Atamfofi
Laces
Shadda
Materials
Takalma
Jakunkuna
Mayafai
Trolley
Oil perfumes
Numbers
08034469681
08135142610
Handles
Instagram @ummu_mahnoor_luxuries
Facebook ummu_mahnoor_luxuries
*_inganci da kwalliya shine muradinmu_*
_________________________
*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*
*ZAFAFA BIYAR*
*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA
ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*
_K'ALBIM Mamuhghee_
_AJIYA A DUHU Billynabdul_
_DUNIYATA Huguma_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
*09033181070*
89825722
1000cf
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
*Arewabooks:@Huguma*
https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997
PAGE 29
*SOUTH KOREA*
Yanghwa-ro daya daga cikin lafiyayyun street dake da wani irin daddaden yanayi a kowacce safiya
cikin anguwar hongdae dake tsakiyar south Korea. Yanayi ne me me dadi dake wanzuwa a kowacce
safiya cikin street din dake da wani irin shuru da nutsuwa gami da nisanta da kowacce irin hayaniya daka
iya damun ruhi ko matsantawa nutsuwar dan adam.
Ga duk ma'a bocin fitowa da sassafe tsakanin yanghwa-ro zuwa hongdae geori zai zame masa abu
me wahala baisan baqin fuskar matasan Nigerians din guda biyu ba. Zaratan matasa masu wani irin kyan
zubi na halitta da kuma ajiyayyen kwarjini da kuma haiba. Yaya da qaninsa wanda fitowa jogging kusan
kowaccw safiya ya zame musu kamar al'ada.
Muhammed FU'AD,da kuma musaddiq hamza kibiya wanda yake daga gefan Muhammed FU'AD
din. Idan yayi kamar zasu daidaita wajen sassarfa me kama da gudun da sukeyi sai ya zame har sai FU'AD
din ya wuceshi yana fadin
"Eheennn......don't stop.....don't stop" Da wata iriyar husky voice da Allah ya huwace masa wadda ke
cakude da nishi kadan na gudun da suka dauko.
Yayi kaman zai tsaya din ya kusa sau biyar......hakanan shima yake zaburar tashi har zuwa sanda
suka iso daidai wani guri. Guri ne da kusan kowacce unguwa take da nata wanda aka tanadeshi aka
killaceshi domin hutawar jamaar unguwar cikin wasu kujeru da shimfidaddun tsirrai da suka wadatu da
tsafta suke kuma samun kulawa yadda ya kamata.
Ruku'u musaddiq yayi yana cakewa a wajen,ya kama gwiwoyinsa da hannunsa yana sauke nishin
wahala gumi yana fita daga sumarsa zuwa goshinsa.
"Oh shit" FU'AD ya fada yana jan birki,sannan yayi reverse yayo kwana da hanzari yana dawowa daidai
inda musaddiq ya cake.
Baice masa komai ba ya kama wuyansa ya cafka yana tadashi tsaye sosai saman qafafunsa,abinda
ya sanyashi sakin wata qaramar qara yana matse kafadunsa
"Sorry hamma......am really tired wallahi......i try hamma......kusan minti talatin tunda muka fito muke
wannan gudun.....ko doki hamma sai haka"
"Shut your mouth.......malalaci kawai......da wanna halin da dabi'ar naku meye marabarku da
mata?,inajin mun kusa baku jilban da dankwali kuna daurawa ko?". Sosai dariya taso murqushe
musaddiq,amma yasan bai isa ya yita a gabansa ba. Duk wani training nasa suna shanyewa amma
yanzun don ya gaza cikashe mintunan gudunsa shine ya zama malalaci har zasu fara dauka zani?.
Zanin da ya sake tunawa ya sanya dariyar da yake boyewa ta qwace masa da gaske,don ba wanda
ya hango daure da zani sai saddiq.
Sakin qeyar nashi FU'AD yayi yana watsa masa wani irin kallo da lumsassun idanunsa dake da
wani irin kaifaffen kallo me kashe duk wani zarra ta mutum
"Are you laughing?,da gaske baka gaji ba......zamu qarasa gida a haka,ko sau daya kuma ka sake tsayawa
kasan sauran......salary dinka na wannan watan zan saka abba yayi sadakarshi" Ya fada yana gyara
doguwar socks din qafarshi daya rufe mass har gwiwarsa. Kayan motsa jiki ne a jikinsa,amma yadda
sukyi masa kyau zata tsammaci ya sanyasu ne don ado. Sun fidda duk wata qirar qarfi da Allah ya
bashi,murdaddun muscles dinsa zuwa shaffen cikinsa da qirjin yafi cikin dagowa.
"Hamma......wallahi Allah ba abinda kake tunani bane" Ya fada cikin karya wuya da sanyaya murya
"......Allah hamma kawai musaddiq na hango daure da zani da dankwali......" Sai ya qarasa fadi yana
bushewa da dariyar data sanyashi ya murmusa dole. Dariya yake sosai yana kuma kallon fuskar fu'ad din.
"Iyakarshi kenan" Ya furta a ransa. Murmushi shine maqurar dariya a wajensa ko yaya kuwa abu yakai.
Kai ya girgiza kawai qasan ransa yana tuno wasu abubuwa na sadiq da musaddiq din. Suna da wani irin
wasan da inda ace shima irin farouq ne baya jin yaran zasu shuka abun arziqi idan ba shiririta ba. Har
kullum abba na jin dadin jajircewarsa a kansu,don shima din sun maidashi kakansu qarfi da yaji,yayita
masifa yayita masifa amma a banza,maganae mutum guda ce take ratsasu.....zancan mutum daya ne
yake zama daram saman kansu shine zancan muhammad fu'ad.
Bai sake ce masa komai ba sai ya miqe yana zaro wayarsa dake aljihun wandonsa. Iphone 16
sabuwar qira wanda babban hoton wata kyakkyawar matashiya ya mamaye ilahirin fuskar wayar.
Kyakkyawar bafulatana me wani sassanyan kyau,cikin kamilalliyar shiga data qarawa hoton da Fuskarta
kwarjini. Dududu shekarunta da suka nuna cikin idanunta da kuma fuskarta goma sha takwas ne.....sha
takwas din da aka soma gangarawa cikin sha tara.
Kalmomin sirri ya sanya ya bude wayar,sannan kai tsaye ya tafi zuwa ajiyayyun lambobin da basu
da yawa cikin wayar. Akan wata number dake dauke da sunan ABBA NA ya tsaya,ya danna kira sannan
ya maidata aljihunsa yana gyara zaman Bluetooth guda daya dake manne a kunnensa yana bada hasken
qyallin wuta time to time. Sai kuma ya fara takawa a hankali ba tare daya cewa musaddiq komai
ba,wannan ya bawa musaddiq din daman biyo bayansa a nutse can qasan ransa yana murnar yadda aka
haqura da jogging dinnan haka.
"Shi ya dauka kowa kamarshi ne me jikin qarfe da baya gajiya da motsa jiki......idan na hada qarfi ina zan
kaishi" Yayi gulmarsa a ransa yana biye dashi tare da qare ma bayansa kallo.
Shi kansa yadda yake da ginannun muscles yana burgeshi yana kuma bashi sha'awa,amma bashi
da juriya da qarfin halin da zai building muscles ma jikinsa kamar nashi.
"Abba ka farka?" Ya fada cikin matuqar nuna kulawa bayan yayi masa sallama.
"Okay gamu nan qarasowa" Sai ya katse kiran ta jikin Bluetooth din nasa sannna ya dan soma sassarfa
yana cewa musaddiq
"Oya.... Mu qarasa gida" Kaman zaiyi kuka hakanan ya taka ya soma bin bayansa. Kafin su qarasa gidan
sai da yaji kaman zai zube,cikin ransa yake ganin gaskiyar sadiq ashe da yakanyi ciwo ko ya qirqiro uzurin
qarya duk sanda ya tasheshi ya rakashi jogging. Har gwara ku shiga gym room dashi,wannan idan suka
faki idonshi sai su zabi machine daya su haye su kasheshi ko su rage gudunsa sosai.
A hankali suka qarasa hongdae geori cikij estate din dake unguwar. Gida me lamba ashirin,yayi
tsaye yana danna bell yayin da qirjinsa ke dagawa sama da qasa yana fidda Zazzafan huci daga bakinsa.
Ya jiqe sharkaf da gumi,musaddiq kuwa tuni ya zube saman step biyu dake bakin qofar gidan yana
numfashi da sauri da sauri.
A hankali qofar ta bude,dattijon mutumin nan Alhaji hamza kibiya ya bayyana cikin wata lallausa
kuma kyakkyawar abayar qasar morocco ruwan zuma. Ba abinda ya sauya tattare dashi sai shekaru da
suka fara bayyana kansu a jikinsa.....bayyana ba me muni ba saboda daular rayuwa da kuma jin dadin da
yake ciki daya zarta ya kuma ninka na shekarun baya ta hannun zaratan yaransa guda hudu dukka maza.
"Ina dayan me babban suna?" Alhaji hamza ya tambaya saboda idanunshi basu hango musaddiq ba sam
sam.
Da baki ya yiwa abba cunensa,abban ya dora hannu saman baki yana bushewa da dariya
"Kai......taso dalla.....dama babu me maganinku ai sai me babban suna......tashi nace mace kawai.....koni
nan da shekaru suka fara turamin ina gudun nan,kuma ka gani da idanunka.....ina zakuyi qwarin damu
uwayenku mukayi?,baku da aiki sai hawa mota sai ciye ciye da shaye shayen banza" Abban ya fada yana
wurga hannu. Kai ya daga da qyar yana duban abban
"Abba wallahi.....bazan iya tashi ba da gaske,qafafuna kamar zasu tsinke.....gudun fanfalaqi yau hamma
ya saka mukayi" Yadda yace gudun fanfalaqin ya tilastawa abba sakin dariya,yayin da FU'AD ya girgiza kai
kawai. Suna ganin iskanci a gidan wajen sadiq da musaddiq,kullum kaman basa girma,kullum kallon
kansu sukeyi kaman qananun yara.
"Tunda ba zaka tashi ba ai idan wancan qadangare ya shige maka riga ai ka nema hanyar gida" Wani
mugun tsalle ya doka sai gashi a tsaye kyam
"Yauwa.....dan nema ja'iri,zo ka wuce kaji me babban suna" Abban ya fadi yana komawa ciki fuad yabi
bayansa yana dariya qasan ranshi. Har yanzun musaddiq yana tsoron qadangare kenan tun
yarinta?,abun ya dinga bashi mamaki don shi baiga wani abun tsoro a qadangare ba.
Suna shiga yana biyo bayansu yana dube dube yana fadin
"Wallahi abba ka kusa sakani na saki fitsari a wando......yanzu inda a gaban nasreen......" Tsaf ya kame
bakinsa ba tare daya qarasa ba saboda kallon da FU'AD ya jefeshi dashi,ya sosa kanshi ya sauya akalarsa
zuwa kitchen da kake iya hangensa tarwai ta falon.
Saman kujera ya zauna a nutse yana warware takalman qafarsa,abban ma ya koma inda ya tashi
ya zauna yana daukar mug tare da ci gaba da kurbar zazzafan tea din dake ciki.
"Sannu da gida abba" Ya sake fada yana dan jingina bayansa da kujera
"Sannu fuad shugaban 'yan motsa jiki" Abban ya amsa masa da murmushi tare da maida dubansa ga
takalmansa daya cire. Duk abinda ya cire ko yayi amfani ddashi yasan ya killace shi,zaiyi wuya kaga ya
watsar da kaya ko wani abu makamancin hakan. Ya tabbatar hakan baya rasa nasaba da matsananciyar
tsaftarsa da kuma yadda rayuwarsa ta ginu a shekarun baya,cikin gwagwarmaya da daukar nauyi da
lalurar kanshi. Yana da bala'in tsantsami shi yasa abubuwa da yawa ya gwammaci ya tsaya ya yiwa
kansa. Idan ka ganshi a kitchen yana hada breakfast ko yana dafa tea zaka rantse da Allah ba shine dan
marayan zakin nan ba mamallakin kamfanin JADDA DIAMONDCHORE RESOURCES ba,wanda jaridu zuwa
mujallu kullum kwanan duniya ke zumudi da rububin yin rubutu a kansa ba domin samun daukakarsu da
qaruwarsu. Duk wani rubutu ko labari da wani gidan tv jarida ko radio zasu fitar akan MUHAMMAD
FU'AD tamkar daukaka ce a tare dasu. Matashin mamallakin kamfanin haqar ma'adanai na diamond ne
da makamantansu. Kifi daya a ruwa da manyan masu sarrafa gwalagwalai da diamond na duniya suke
saka fatsarsu domin kamo kaya daga kamfaninsa saboda inganci da kyansu. Diamond guda daya daya
taba tsinta a sanda yake tsakiyar bautar qasa can cikin jahar kogin nigeria.
*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*
*ZAFAFA BIYAR*
*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA
ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*
_K'ALBIM Mamuhghee_
_AJIYA A DUHU Billynabdul_
_DUNIYATA Huguma_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
*09033181070*
89825722
1000cf
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 30
Dan bautar qasar da bai wuce sati biyu a camp ba.....wanda ya fita yawon ganin gari shida
shaqiqin aboki amini kuma dan uwansa farouq hamza kibiya. Haka kawai yayi sha'awar bin daya daga
cikin matasan da farouq ya saba dasu a teburin me shayi wanda duk dare sai yaja fu'ad koda kuwa
bayaso,suje su zauna su sha hira suga yanayin gari da mu'amalar mutanensu. Da fari fu'ad baya so,daga
bisani ne ya sake a hankali bayan da yayi tunanin wannan karin maganar ta bahaushe
"Tafiya mabudin ilimi". Ba yadda zaiyi ya samu ilimin muddin yana nade a camp da kuma dakin. Abinda
yafi damunsa yake hanashi fitar yadda 'yammatan camp din nasu harma da cikin garin suke da son wasa
da wargi gami da son shigewa mutum. Shi kuma abu guda da yafi tsana kenan kaf fadin rayuwarsa.
MACE halitta guda daya da ba kasafai yake mata uzuri ba a rayuwa.....halittar da yayi amanna ya kuma
saddaqarwa kansa su da KUDI tamkar rai ne da bugun numfashi. Halittar da ya gama karatunta cewa tafi
bawa KUDI muhimmanci sama da komai.....kwadayyar halitta me son kanta.....mara tausayi kuma mara
imani koda akan dan cikinta ne kamar dai MAAMANSA.
Farouq yaso hanashi binsu inda suke haqar a sirrance saboda sanin tsananin risk din dake wajen.
Bawai iya barazanar fadowar rami bisa kan me haqa ba.....a'ah.....hatta na a tsakaninsu suna iya farde
wanda ya tsinta din suyi kashe mu raba da abinda ka samu.
"Farouq......ragon namiji shike tsoro.....faduwar gaba asarar namiji......ba'a haliccemu don mu kwanta ko
mu zauna iyayenmu su dinga bamu suna mana wahala ba.....an halicci Muhammad fu'ad don yayi
gwagwarmaya ya kuma fuskanci challenges a rayuwarsa.......na fara gwagwarmaya tun daga sanda na
fara fahimtar Muhammadu sunana ne......na fahimci kuma MAAMA itace ta haifeni......" Ya qarasa
maganar wani abu yana tsirgawa daga tsakiyar muryarsa har cikin qwayoyin idanunsa
"Wai anni bata hanaka zancan maama dinnan ta haka ba?" Farouq yace da fu'ad a sanyaye. Wani
malalacin murmushi ya saki ya sunkuya yana ci gaba da daura boot din qafarsa da kyau. Ta yaya MAAMA
zata bar zuciyarsa wai?,ta yaya?har abada sai randa qasa ta cike idanunsa.
"Na shirya zan wuce sai na dawo" Ya fada yana miqewa tare da zube hannayensa a aljihun wandonsa
yana duban farouq. Harara ya watsa masa sannan ya miqe da hanzari
"Ina zan barka ka tafi kaje ka bace ka jamin jarfa a wajen abba......qafata qafarka.....idan ma zamu bata
mu bata tare" Yayi maganar yana miqewa.
Miskilin murmushinnan nasa ya saki ya juya yana kada kai. Ya sani shine dai kawai a gaba kafin
abba da yake qorafi akai,kawaidai bazai iya barinsa ya tafi bane ya barshi,wanda wannan daya daga cikin
danqon qauna da 'yanuwantaka dake a Tsakaninsu.
Yana shiryawa yana mita har ya kammala suka sulale suka fice daga gidan da aka musu masauki
ba tare da kowa ya sani ba.
"Ni bansan me zakayi da wata mahaqa ba.....dukkanmu abba jira yake mu kammala wannan service din
ya bude mana namu kasuwancin"
"Ta yaya zaka zama cikakken dan kasuwar da yasan daraja da kimar dukiya baka iya gwagwarmaya
ba?.kana daga zaune ba tare da ka tara komai ba?" Fu'ad ya masa tambayar yana kallon hanya kawai ha
tare daya kalli farouq din ba
"Gwagwarmaya cikin wadannan qedarun?,don kawai Samuel ya gaya maka za'a je da kai?,suna da hadari
fa fu'ad?" Murmushi ya kuma saki hankali kwance,har yanzu kuma bai kalli farouq din ba ya sake bashi
amsa
"Muhammad fu'ad dan arewa.....ya fisu hatsari.....zaka gane hakan idan sukayi yunqurin yin wani abu".
Maganarsa ta tabbata kuwa a wajen farouq.
Tun isarsu gurin komai ya fara bayyana. Da wani irin kallo ayarin suka fara binsu saboda ganinsu
baqin fuska kuma 'YAN AREWA dake yara yaran hausa. A haka aka soma tafiyar har zuwa kebantaccen
wajen da suke haqar ba dare ba rana don samo ma'adanai. Samuel shi ya dauki dukkan wani risky ya
shige gaba aka barsu har suka isa gurin cikin wadanda aka aminta da shigarsu wajen.
Duk inda fu'ad zai motsa farouq yana biye dashi,sam wajen shi baiyi masa ba,hakanan a tsorace
yake da wajen,shi sai ya zamana kamar me gadin fu'ad ne a wajen. Duk wani motsi da za'a yi a wajen ko
wani da zai tunkarosu hankalinsa yana wajen.
"Mutanen nan fa hankalinsu a kanmu yake,duk wani motsinmu suna ankare dashi"
"Karka damu" Kawai yace dashi saboda wani abu daya fara hanga wanda ya dauki hankalinsa matuqa.
"Farouq" Fu'ad ya kirayeshi da wani sauti me jan hankali wanda yaja hankalin wanda ke ramin
daura dasu ya kumayi tsai yana jiran jin dalilin kiran.
"Menene"
"Na samo.....na samo" Ya fada da wani irin excitement,yayin da zuciyarsa da kwanyarsa suka cika da
mamakin samun abinda bai taba zaton zai samu ba koda kuwa a mafarki. Har a qasan zuciyarsa ya
gwada zuwa wajen ne kawai don samun experience da karantar yanayin yadda irin rayuwar yake.
"Duba ka gani farouq" Ya fada yana miqo masa. Farouq din da hanzari ya dira ciki yana toshe bakin fu'ad
"Keep quit fu'ad.....ka tono masifa" Ya fadi a tsorace. Da wani kallon mamaki yabi farouq din
"Kaman ya?"
"Kamar yadda ka sani.....kowa dake nan wajen abinda yake zuwa nema kenan kwana da kwanaki.....kana
baqo wanda aka yiwa alfarma.....zuwan farko kayi kacibus da abinda yake dukkansu shine burinsu?.
Akwai shugaba a cikinsu wanda duk wanda ya samo sai yabi qarqashin umarnin shugaba......zai kuma
danqashi a hannunsa....." Tsaki fu'ad yaja saboda dokokin rainin wayo da yaji farouq yana karanto masa
wanda shi baisan dasu bama,don ya fishi zama da hira da Samuel
"Su sukamin wahalar?,ko an gaya maka nazo nan dinne don na yiwa wani qaton zindiqin arne
aiki?.....let's go mu wuce gida" Ya fada yana kama ramin tare da nufar hanyar fitowa.
Sanda yayi tsalle ya qarasa fitowa baima lura da wadanda suka kewaye ramin ba,har sai daya
gama karkade jikinsa yaji sadiq daya fito daga bayansa ya zungureshi.
Lafta laftan yare masu mummunar siffa tun daga halitta zuwa zuciya. Mutumin da alamu suka
nuna shine shugaban yana tsaye a gaba. Ya sake matsowa gaba kadan ya miqawa fu'ad hannu..
Sarai ya fahimci abinda yake nufi,amma yadda yake kallonsu da dukkan wani motsi nasa cikin izza
da nuna isa ya sanyashi jin har cikin ransa bazai taba iya bashi abun ba. Ballantana abinda yake
wahalarsa kuma guminsa ne. Ko daya babu me haqqi a ciki bare yayi tunanin cinyewar zai zama laifi har
a wajen Allah.
"Ka miqo diamond din daka samu aka ce...!" Daya daga cikin wadanda ke daura da ogan ya furta murya a
kausashe yana sake matsowa dab da fuad din saboda nuna masa tsananin buqatar abun da suke da,da
kuma nauyi da girman abinda yake dauke dashin.
Cikin qasa da second biyar ya gama fahimtar motsi da niyyar kowa. Tabbas!.....tabbas babu abinda
yafi dacewa dasu muddin yana da buqatar tsira da wanann abun face tserewa
"Ka shirya farouq.......ka shirya gudun tsira da rai.....ko mu ko su,ka qarfafa zuciyarka da gangar jikinka"
Ya furtawa farouq qasa qasa tare da damqe hannunsa da kyau.
Kaduwa sosai farouq yayi da abinda yaji fu'ad din yana fada.....yasan halinsa muddin ya fadi sai ya
cika.....amma kuma abinda zasu aikata din mugun ganganci ne da zai iya zama ajalinsu.
Bai gama sauke wannan tunanin ba yaji qarar wani abu timmmm sannan yaji an finciki hannunsa.
Sanda zai duba sai ya samu fuad dinne ya kaiwa ogan nasu mummunan naushi har sai da yakai ga
zubewa qasa war was,da wannan ya janye hankalinsu suka tsallakesu,saidai ko taku uku basuyi ba aka
samu wadanda suka rufa musu baya bayan fusatacciyar tsawar da ogan nasu ya buga musu wadda har
yanzu yana zaune a qasa
"Catch them!!" Ya fada qarajin hasaso asarar dake tallafe dashi tare da tsoro da razanin rasa abinda yake
tamkar shine cikamakin burin rayuwarsa.
Wani irin gudu tamkar a indian film fu'ad ya dinga yi,abun har yaso yafi qarfin farouq banda shi
dinma yaci sunan me sunan.
"Wa ya gaya maka ana gudu da waiwaye?......just run!!,run kawai.... Kada ka sake waiwayawa". Ganin
kamar farouq din ya fara karaya ya sanyashi yin wani juyi ya maida farouq din gaba shi yana biye dashi.
Da gaske dai suka fahimci zaratan samarin 'yan arewan guda biyu na niyyar kufce musu,sai kawai
suka fara harbi,harbin da ya gigita farouq qwarai da gaske ya kuma dinga kiran sunan fu'ad akan su
maida musu abinsu.
"Basu isa ba....don ba abinsu bane,arziqi ne na ubangiji daya shimfida a qarqashin qasa saboda
bayinsa,ba don su kadai Allah ya ajjiyeshi ba" Ya fada a zafafe cikin yanayin gudun yana sake fusgar
hannun farouq da kyau. Wani irin samfurin gudu da fu'ad din keyi riqe da hannun farouq sai daya zama
abun kallo a wajen farouq din. Bai taba tsammatar iyawa ko qwarewa haka a tare dashi ba wajen sanin
kurdawa tsakanin manyan dutsuna da qananunsu ba sai a sannan. Bayan shafe dogon lokaci suna
fafatawa Allah ya basu nasarar kufce musu
"Park zamu wuce mu kwana a can daga can muyi gida......ba park na kusa da nan ba,ta gaba da nan"
Fu'ad ya fadi yana kallon farouq
"Ya zamu bar camp kuma bamu dauki komai namu ba......sannan kuma......"
"Kana tunanin sun qyalemu ne?,kana zaton idan muka koma can din zasu barmu mu kwana da ranmu?"
Fu'ad ya tambayi farouq wanda da alama baisan girman ta'addanci irin nasu ba.
*_ALBISHIR A GAREKU!!_*
*_SHIN KUNSAN UMMUMAHNOOR LUXURIES TA TANADAR MUKU INGANTATTUN KAYAN ADO NA FITA
KUNYA KUWA?_*
*_KAMAR SU_*
Atamfofi
Laces
Shadda
Materials
Takalma
Jakunkuna
Mayafai
Trolley
Oil perfumes
Numbers
08034469681
08135142610
Handles
Instagram @ummu_mahnoor_luxuries
Facebook ummu_mahnoor_luxuries
*_inganci da kwalliya shine muradinmu_*
________________________
*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*
*ZAFAFA BIYAR*
*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA
ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*
_DUNIYATA Huguma_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
*09033181070*
89825722
1000cf
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
*Arewabooks:@Huguma*
https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997
PAGE 31
___________________________
Wani murmushi ya saki
"Ai basu ba,ko jamaa da muke tare dasu sukasan abinda muke dauke dashi sunanmu
matattu......maganar diamond da gold akeyi farouq.......kasan nauyi da girman ma'adanin dake
jikinmu?......mutanen nan sun wuce duk sani da tunaninka.....ni kaina da na yarda mubi Samuel da
shirina,na san kuma cikin su waye zan shiga,kaine nake zaton bakasan irin girman wajen da muka shiga
ba.....banda saa tana tare damu bamu isa mu shiga wannan wajen bama bare akai ga samun abinda
muka samu kuma har mu gudo lafiya lau dashi......daga yanzu har zuwa sanda zamu koma qasarmu
rayuwarmu na cikin hadari......take care dude...." Ya fada yana bugun kafadar farouq da ya gama
mutuwar zaune.
Bin fu'ad kawai yakeyi da kallo yana mamaki. Yasan girman hatsarin fiye dashi amma yayi kaman
bai sani ba?,ko a yanzun wannan uban wahalallen gudun ceton ran da sukasha shi kaman ma baiyi ba?.
A yadda ya sanshi da I don't care manner da rashin shiga abubuwan rayuwa sosai bai taba zaton ya iya
daukar risk da tarar aradu da ka ba sai a yanzu.
Tun daga tashar da suka samu mafaka sukasan lallai an baza nemarsu,a daren suka haye motocin
kaya dake lodin arewa suka wuto gida.......wanda sai daga bisani abba yasan komai.
Yayi fada yayi fada kaman zai ari baki......ya kuma yi musu fadan da bai taba musu shi
ba,musamman me babban suna da yake girmama sunansa yake kuma qaunar yaron har cikin ransa.
ANNI ce ta sanya baki aka samu ya lafa sannan aka fara tunanin yadda zaa yi da abinda ya haqo
din,tunda ya riga ya shigo hannu ba batun ace za'a maida musu.
Bisa dukkan dokoki da tsare tsare kan tsaftatacciyar hanya aka tsara komai ya zama dukiyar da a
yanzun suke juyata shida farouq dinsa. Abban kuma ya zame musu jagora madubi.....ma'adanin kuma ya
zama shine kasuwancinsu.....babbar masana'antar karbar haqaqqun ma'adanai su tace su gyarashi su
fiddashi xuwa manyan qasashe,irinsu china,south Korea japan UK da manyan qasashen dake hulda da
cinikayyar ma'adanan qasa masu tsada da daraja.
*_D A W O W A_*
"Kwanaki nawa ya rage mu tafi ne me babban suna?" Zama yayi sosai yana goge gumin fuskarsa da dan
qaramin towel din da magaji(hadiminsa) ya miqo masa.
"Ba zamu wuce sati daya ko kwana biyar ba abba,hankalina yana kan anni......jikintan nan ya fiya
matsawa da yawa" Yayi maganar alamun abun yana tabashi ya bayyana har saman fuskarsa. Idanu
abban yadan zuba masa,har a ransa yana cike da zallar mamaki na yadda me babban suna ke damuwa
da anni da rayuwarta fiye da dukkansu su ukun. Annin da abban yake ganin ba itace halitta ta farko data
cancanci samun wannan qauna da kulawa daga gareshi shi din ba......annin da yake ganin kulawar da
yake bata baifi ya bata kaso hamsin cikin dari ba.......ita kanta wasu lokuta tana sanya damuwa a ranta
game da inda yafi karkatar da kulawar tasa sama da daya bigiren da shine dolensa,.....kuma akafi
buqatar hakan daga gareshi.
"Yanzun haka ma nan da awa daya zan fita,zamu gana da ceo na Labrilliante company,zan miqa musu iya
abinda zasu samu.....don abba wannan karon tunanina ya fara sauyawa" Maganar fu'ad cikin tatacciyar
nutsuwar nan tasa da wani irin jan aji kamar mace ya dawo da Alhaji hamza daga tunaninsa
"Wanne tunani ne fu'ad?" Zamansa ya gyara sosai yana bawa abba dukkan kallo da hankalinsa
"Abba......a yadda mutanen nan daga kowacce qasa suke rububin siyan resources namu da muke
fiddowa daga qarqashin qasar da Allah ya shimfida mana kadai ya isa ka fahimci suna amfani damu ne
suna kuma amfani da damarsu......yanzu haka a daren jiya kafin na kwanta sai dana karba kira daga wani
company dake japan bayan ainihin kamfanin da muke kaiwa kaya......suna taya kayanmu akan farashin
da wancan kamfanin basa bamu......wannan shi yasa nayi wani nazari......abba ya kamata qasarmu ta
amfana da wadannan ma'adanai masu tsada da daraja,wanda mu Allah ya mallakawa su.....abba inda a
qasarsu wadannan ma'adanai suke,babu wani baqar fata daya isa ya sameshi.....it's hardly ka iya isa
wajen......nayi tunanin bude babban company da zai dinga sarrafa wadannan ababen zuwa kayan qyale
qyale na mata.....don dama company daya muke da na alhaji rayyan(dangantakar zuciya),shi kuma
duwatsu masu daraja suke sarrafawa ba gold ko diamond ba".
Shuru abba yayi yana girgiza kai. Tabbas fu'ad din yazo da tunani me kyau daya kamata ace
tuntuni sun yishi
"Na yarda da wannan tunanin naka.....to amma fu'ad qarqashin haka akwai tarin matsaloli da
qalubale......"
"Na sani abba......insecurity na qasarmu ma kawai qalubale ne......amma a hakan.....ya zama dole mu
raya qasarmu da kowanne qaramin chance da muka samu a rayuwarmu......tsoro da tunanin asara ko
faduwa shine abinda zaici gaba da kasheta kowacce rana......bayan tsoron dauko shi akayi aka dasa mana
shi a zukatanmu......kuma ake da buri da fatan ganin ci gaba da wanzuwarsa har zuwa rayuwar na
bayanmu"
"Best son ever" Abban ya furta yana sakin wani irin murmushi tare da jin qarin alfahari da fu'ad din,gefe
guda kuma yana taya ainihin mahaifinsa murnar samun nagartaccen yaro mara tsoro irin muhammad
fu'ad din.
"Allah yaja kwana,ya qara lafiya me amfani" Ya masa addu'ar da yake jinta har cikin zuciyarsa.
"Hakan yayi kyau" Abba ya fada fu'ad din yana sake burgeshi saboda yadda ya dauki alqawari da
matuqar muhimmanci kaman yadda yake girmama lokaci.
A nutse ya tura qofar dakin da sallama a bakinsa,duk kuwa da yasan ba wanda zai taras a ciki.
Dakine da duka duka basufi sati guda a cikinsa ba......amma har ya kama ya kuma rine da sassanyan
qamshin nan nasa dake iya bawa zuciya nutsuwa da kwanciyar hankali koda cikin radadi da qunci take.
Towel din hannunsa ya rataye,ya kuma matsa gaba kadan ya ajjiye takalmin motsa jikinsa wanda
daga ranar da suka tasamma barin Korea sunansa shara. Baya yawo da kaya,kowacce qasa zaije,koda
kwana nawa zaiyi single yake tafiya abinsa,saidai yana sauka a qasar komai da zai buqata na amfani zai
sanya a tanadar masa,yana gama amfani dashi kuma a nan zai barshi ya qara gaba.
Matsawa gaba kadan yayi gaban wata mini dispenser da tafi kama da tulun zamani wadda ke
zaune saman wani kyakkyawan table kusa da mirror,ya dauki disposable cup ya matsi ruwan dake da
madaidaicin yanayi ya fara sha a hankali bayan yayi tsaye gaban madubin idanunshi a kai kamar me
karantar yadda yake zuqar ruwan zuwa cikinsa.
Ya gama ya ajiye saman madubin yana fidda siririyar iska yana ci gaba da kallon fuskarsa a
madubin. Kyakkyawar sumar kansa data wadatu da tsafta ya taba sannan ya gangaro zuwa
madaidaiciyar qasumbarsa data hade da gemunsa wadda ta zamawa fuskarsa wani lafiyayyen ado daya
qara fidda zahirin kyawun fuskarsa,ta kuma qara masa wani mahaukacin kwarjini. Gemun da qasumbar
daya zama topic of discussion a wajen 'yammatan da suka marmace a kansa. Kusan kowacce tana
gayawa kanta namiji babu gashi a fuska ai mace ne,bata taba ganin qasumba da gemu da yakai kyan
nasa ba......tsabar macewa a soyayya ne.....ko kuma zallar tsagwaron gaskiya suka fadi?.
Rigar jikinsa ya yaye zuwa sama sannan ya zareta ya ajjiyeta saman gadon,wannan ya bawa
Ginannun muscles din jikinsa bayyana muraran. Muradden jikin da zai gaya maka adadin lokutan da aka
bata ana bashi kulawa ta fannin lafiya da cin lafiyayyen abinci me gina jiki. Yayi taku daya don dauko
bath set nashi zai wuce toilet sai ya fasa,ya dawo da baya ya dauki wata farar samsung dake ajjiye saman
mirror din.
Yaga miscal amma sai ya fara maida hankalinsa ga dalilin daukar wayar,ya latsa ya fara lalubar
magaji. Umarni ya bashi na abincin da zai hada masa kafin ya fito,saiya maida wayar yana shirin ajeta
kira ya shigo wayar.
Cak ya tsaya yana kallon sunan dake tsalle saman wayar. MOM kaman yadda farouq ya dauka
da hannunsa yayi masa saving. Kafe sunan yayi da idanuwa,wayar tana kadawa hade da zuciyarsa. Sunan
yake tuna ma'anarsa da kyau cikin kwanyarsa.....wadda aka maqalawa sunan ta cancanci wannan sunan
kuwa anya?......ta dace data karbi sunan?,nata ne sunan da gaske?.
Kamar bashi da idea akan yadda ake daga waya,haka yaci gaba da kallon wayar har ta qaraci
ringing ta katse. Ya sake daga qafarsa zai wucs kiran ya sake shigowa. Kamar dai dazu a yanzunma haka
ta gama kadawa ta katse,kira na uku kuma ya sake shigowa immediately,saidai akasin dazu,yanzu sunan
daya fito akai ya banbanta dana dazu.
Lovy dovy shine sunan daya bayyana,sai ya saki qaramin murmushi yana dawowa baya kadan.
Kafin ya daga sai daya kalli lokaci,tabbas ya tsaya saurarenta ya tabbatar saita kwakwashe masa duka
mintunan daya tsara zaiyi a gidan ya fice zuwa Labrilliante amma hakan bai sanya ya fasa dagawa ba,ya
sanya wayar a kunnensa.
Da siririyar baby voice dinnan nata tayi masa sallama. A nutse fuskarsa a sake ya amsa
"Yes habibee.....byeee" Ta fada cikin rashin damuwa da kuma fahimtarsa a duk sanda ya sako mata
uzurinsa. Wayar ya mayar ya ajjiye yana murmushi,daidai sanda a daya BANGAREN.........
*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*
*ZAFAFA BIYAR*
*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA
ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*
_K'ALBIM Mamuhghee_
_AJIYA A DUHU Billynabdul_
_DUNIYATA Huguma_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
*09033181070*
89825722
1000cf
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
*Arewabooks:@Huguma*
https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997
PAGE 32
___________________________
“Waya kuma ake amsawa?” Ta tambaya cikin wata irin isa sa ginshiri tana qanqance
idanunta,qwayar idanun nata suna kan wadda tayi maganar. Kai ta jinjina mata cikin bata tabbaci
“Eh haka ne”. Juyawa tayi ta zauna sosai tana fesar da iska me zafi daga bakinta. Ta qanqance idanu
sosai tare da zubawa guri daya idanu,abinda zai baka tabbacin akwai wani radadi me yawa da take ji
daga cikin zuciyartata
“Alamu kenan suna nuna yaga kiran,nice dai…….nice dai da bazai amsa wayata ba,nice dai da bazai
saurareni ba sai a sanda yaga dama ko kuma aka bashi umarni?” Ta qarashe maganar ta hanyar yiwa
kanta da kanta tambayar. Tambayar da bata haifar mata da komai ba sai qarin qunci da bacin ran da ya
sanyata miqewa tsaye.
Hannunta ta dunqule ciki juna,ta fara kai kawo tana naushin tafin hannunta da daya hannun
data dunqule waje guda. Ba shakka tayi sake ba dan qarami ba,ba shakka kuma hajiya mariya tana son
jefa kanta tsakiyar shingen da ba nata ba. A baya tayi tarin ayyuka game da hakan,amma idan har tace
taga nasara tattare da hakan to tayi qarya me yawa ma,zata iya kiran ayyukanta na baya da JIYA I
YAU,tana tsaye a waje daya babu sauyi ko qanqani,zata zuba idanu ne abubuwa mafiya daraja da kima a
rayuwarta…..kuma mallakinta amma ace suna ci gaba da subuce mata?,suna ci gaba da zama haramiya a
gareta?,shin zata yarda da zamowa ‘YAR RAKIYA ko kuma taci gaba da wanzuwa a mazaunin ‘yar kallo?.
“Ba zata sabu ba!” Ta furta a zabure sannan ta juya da sassarfa tana daukan mayafinta dake yashe
saman kujera
“Tashi samira muje” ta bawa hadimar tata umarni,wadda ke zaune tun dazu guri daya tana duban kai
komo da maganganun da takeyi ita daya
“Ina hajiya?” Ta tambayeta murya a lanqwashe. Tayi imanin tunda har ta buqaci fita irin wannan afujajan
ba shakka ba alkhairi a cikinta sam
“Gidan alhaji hamza!” Ta bata amsa a tsawace da salon abun nan da ake cewa haushin kaza huce kan
dami. Tsam ta miqe tana gyara daurin zaninta sannan ta wuce da sassarfa zuwa shiyyar dakunansu don
dauko hijabi.
Cikin jerin amintattu kuma lafiyayyun dakunan da mansion house din na alhaji hamza kibiya
ya mallaka. Zaune take tsakiyar wani lallausan rug dake a gefe daya na dakin wanda aka masa rukuni da
lausasan sofas qwaya uku da suka zamewa wajen tamkar wani dan qwarya qwaryar falo ne na cikin
bedroom. Wani irin lafiyayyen daki ne da ba zai barka kasan safiya ko dare ba,zafi ko sanyi,damuna
ballanta rani ba muddin ka kasance wanzajje a dakin.
Daga saman rug din take zaune saman abun salla da zai baka tabbacin bata jima da kammala
sallar walaha ba. Salla ceda bata taba wuceta a rayuwa muddin ba wani qaqqarfan dalili ya gifta ba,tun
zamanin quruciyarta har kawo yanzu da girma da shekaru suka hau kanta. Shine kuma ya same mata sila
da tsani na dawowa rayuwa hamza a shekarun baya,a sanda ta yanke zato da tsammani daga sake
rayuwa dashi da kuma yaranta da suka zame mata sanyin idaniyarta.
Akwai haske sosai saman fuskarta,tana saye da atamfar chiganvy gold mekauri kyau da asalin
tsada. Jikinta lullube da mayafi me kauri,yayin da yatsarta ke maqale da qaramin carbi irin na ma tsawa.
Daga gefanta saitin kafadarta shine a kashingide,kana kallonsu zakasan magana sukeyi,magana
kuma irin ta da da uwa,hira cikin nutsuwa qauna da kuma kulawa
“Nikam saddiq……sake kiramin wayata mana,jakata tun ranar da akayi asibiti dani ban sake ganin
gilmawarta ba,akwai muhimman abubuwa a ciki,harda kudaden Amna data bani ajiya” idanu ya zaro
sannan ya miqe yana zama sosai
“What?,anni?,dollars fa?”
“Idan har ba’a gansu haka zata haqura ai,tsautsayi da qaddara tana wuyan kowane bawa”.
Shuru sukayi dukkansu suna saurareb sautin din…..din,sautin dake gaya musu lallai kiran ya
isa ga wayar anni dake tare da documents dinta da kuma sauran kudade masu kauri cikin jakar.
Kamar cikin mafarkinta ta dinga jin wani sauti mara qarfi yana ratsa kunnuwa zuwa kwanyarta.
Shuru tayi ba tare data motsa ba,daddan ring tone din mara hayaniya yana tasowa can qasa
qasa,da alama akwai abinda ya sake rage kaifin sautin.
Sai data fahimci ba cikin bacci bane sannan ta qarasa bude fararen idanunta da suka qara girma
saboda bacci. A hankali ta yamutsa fuskar tata sannan ta sanya hannunta ta maida lallausar sumarta me
tsaho data rufe rabin fuskarta baya,ta juya daga rub da cikin da tayi zuwa rigingine sannan ta miqe ta
zauna sosai tana wuwwurga idanunta zuwa kowanne sashe na dakin don gano ainihin ta inda sautin
yake fita.
Ba kowa a dakin,don tuntuni su huda sun gama shiryawa sunyi abincin safe kaman yadda suka
saba sun wuce makaranta,don ko idanunta bata iya budewa tace dai kawai su buda jakarta su dauki
kudin makaranta su kuma ja mata qofan idan sun fita.
Fes dakin yake kamar kullum kamar kuma ko yaushe,sai ta saka hannunta ta tattare gashinta ta
qulleshi tsakiyar kanta idanunta ta tsaiwa kan medium luggage din dake cike da tsarabar da aka kawo
mata,wadda ko samun damar budeta batayi ba.
Tayi matuqar gajiya a jiyan,tana fita kusan kowacce rana.....amma bata yin awanni masu yawa
kaman haka a wajen. Komai nata yana da lokaci tsari da kuma iyaka. Ta zube fararen qafafunta saman
qaramin carfet data sanya musu daga gaban gadajen nasu saboda sanyin tile,ta jawo dankwali me santsi
ta daura sannan ta miqe tana isa gaban luggage din.
Sai a sannan ta kuma gasgatawa daga cikin qaramar handbag dinta sautin ke fita,jakar ma da
gaba daya ta mance da ita tun ranar data je musu siyayya ta dawo,ko tarkacen ciki bata kwashe ba.
Hannu ta zura tana laluben meye yaketa qara din haka cikin jakar,sai kawai ta wuce gaban gadon ta
zazzage jakar gaba daya saman gadon.
Kyakkyawar purse baquwa ta gani cikin jerin tarkacen dake cikin jakar wanda ta tabbatar duka
nata ne. Onion color me ratsin maroon a jiki. Hannu ta miqa ta jawota,ta dagata a hannunta tana
jujjuyata cikin mamakin a ina ta samo ta?,kuma ta waye?,tun yaushe take cikin kayan nata?. Kamar
anason sanar mata da amsar duka tambayoyinta ne sai wannan siririn sautin da ya tasheta a bacci ya
sake kadawa daga cikin jakar.
Kai tsaye ta zuge jakar,ba wani ba wata ta sani waya ce. Wayace qila da take da alaqa da
mamallaki ko mamallakiyar jakar.
Wata siririyar Samsung ta gani,ta sanya hannu don cirota da gaggawa gudun kada kiran
yanke,take sabbin dollar din dake maqale a zip na daban na jakar suka biyota suka fada saman cinyarta
hade da qananun hotunan passport. Ba wannan bane a gabanta,don haka batabi ta kai ba ta fara duba
sunan dake yawo saman screen din wayar
MUSADDIQU NA....shine full name din dake jikin number. Tadan tsaya tana sake duba sunan da kyau
tare da bitar karantashi,sai kuma tadan tabe baki kadan sannan ta daga kiran ta Kara wayar a kunnenta
Shuru tayi tana sauraren motsin dake fita daga daya bangaren,kafin daga bisani sallamarsa ta
maye gurbin shurun. Muryarsa a nutse dake dauke da kamala yayi cikakkiyar sallama data sanyata motsa
bakinta da tata siriryar muryar tana amsa sallamar.
"Barka da warhaka" Ya fada a nutse.
"Don Allah idan ba zaki damu ba zan iya tambayarki wayar nan ta waye?" Banbarakwai taji tambayar
tazo mata,har sai data sake duba sunan dake jikin wayar,amma yanayin yadda muryarsa ke nuna
kamalarsa da nutsuwarsa ya sanya tayi gyaran murya daban
"Kaman sunan me kiran dana gani akan wayar yana da alaqa me qarfi ko kuma mafi kusanci dame wayar
ko?". Murmushi ya saki,yadda tayi maganar cikin fasahar harshe da tsari sai yaji ya burgeshi,hakanan
kuma a karon farko ya gano muryar,yakuma dago ko wacece
"Hakane ranki ya dade.....idan na canka dai dai.....kamar mutuniyar kirkin nan kuma baiwar Allahn nan
data ceci rayuwar mahaifiyarmu ko?" Dan jim tayi tana son gano ma'anar zancansa,don tuni rayuwarta
taci gaba daga inda ta tsaya,tuni ta shiga wani babin kuma na daban,ta manta abinda ya faru dazu jiya
bare shekaran jiya.
Haka policy na rayuwarta yake. Ba kasafai take bawa komai gurbi cikin rayuwarta ba bare ta
hadu da traffic akan dukka plans nata da kuma tunaninta ba.
"Oops....." Ta furta a hankali,yanayin daya sanya musaddiq sakin murmushi don ya fahimci abun ya
kwanta mata
"Kayi haquri don Allah,ka kuma nawa mama haquri,na hada da purse dinta ne a cikin kayana bisa rashin
sani,bansan ma da ita din ba sai yau da aka kira"
"Ya ka katse wayarwayar inaso mu gaisa nayi mata godiya da ban gajiya"
"Daga canne anni ta yanke......" Ya bawa anni amsa yana duban wayar tare da mamakin yadda take
magana da bada amsa haka cikin taqaice komai
"Babu matsala.....amma zanso sake ganinta ko magana da ita......zanso nayi mata godiya sosai,dukan
wanda yayi saving rayuwarka ai baka da sama dashi.....mutum ne me matuqar kima da martaba cikin
rayuwarka.....har yanzu ina iya jin sanda ta rungumeni sosai a jikinta kamar ta sanni......sai na dinga jin
kamar amna ke riqr dani......ta damu sosai kamar mahaifiyarta ce a cikin halin" Ta qarasa maganar tana
duban fuskar musaddiq,fuskarta kuma na nuna abubuwa da dama da zuciyartata taji. Zamanshi sosai ya
gyara yana murmushi.
*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*
*ZAFAFA BIYAR*
*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA
ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*
_K'ALBIM Mamuhghee_
_DUNIYATA Huguma_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
_YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_
*09033181070*
89825722
1000cf
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
*Arewabooks:@Huguma*
PAGE 33
"Ni kaina anni ina iya hango sanda taketa masifa da fada da gaske wai mun banzatar da
rayuwarki,bamusan illa da kaifin ciwon ba......amma fa anni kaman ina zaton.....anya bata da ciwon
itama ko wani nata?" Yayi tambayar yana duban anni kamar annin tasan zahirin maganar.
Cikin isa izza da jin cewa takai kowanne qololuwar mataki na rayuwa ta ratsa babban falo kuma
na farko na gidan,ta ratse dukkan wasu hadimai da kuma masu aiki na farkon gidan,falon farko har ta
dangane da falo na biyu.
Kowanne taku idan tayi idanunta suna sauke zazzafan kallo ne akan kowanne alatu da kuma
jayan jin dadi na rayuwa dake kowanne muhalli na falon. Kowanne abu da idanunta zaya sauka akai tana
debe kallonta ne daga kanshi cikin jin wani irin zafi da quna gami da radadi idan ta tuna cewa
MUHAMMAD FU'AD ne ya yishi tare da gumin dan uwansa MUSADDIQ.
Da wannan tunanin ta tsaya tsakiyar falo na biyu hannayenta riqe da qugunta tamkar qaramar
yarinyar da take ganiyar fitsara da kuma jin cewa tana daidai da kowa.
Ko ita dinma a yanzun kusan hakan take. Tsaiwarta a falon qiris ya rage dukkan wani ganuwar
haquri nata kawaici da yakana da takeyi su qare,haquri da kawaicin da take ganin tunda tazo duniya bata
taba yiwa wata halitta irinta ba
"Amina nakeson nayi magana da ita" Ta fadi kanta tsaye sanda daya daga cikin hadiman dake da alhakin
kula da wannan sashen ta qaraso.
"Eyeee?" Me aikin ta tambaya cike da mamakin yadda ta kirayi sunan dattijuwar data zame musu baya
goya marayi haka gatsal,babu sayawa ko qanqani,duk kuwa da cewa zasuyi sa'annin juna,amma a garesu
kiran ainihin sunanta wani baqon abune da yake jimawa bai faru ba
"Nace AMINA nake buqatar gani.....uwar farouqu da saddiqu" Ta maimaita a wannan karon da
madaukakiyar muryar data sanya hadimar maida hankalinta ta hanyar dubanta da kyau,sai kuma taja
baya kadan tana cewa
"Kice mata uwar Muhammadu da musaddiqu" Sunayen data furta din ya saka hadimar sake dubanta da
kyau,saidai bata ce komai ba don bata da hurumin cewa komai din,ta taka a hankali ta kama stairs tana
hawa a hankali don isar da saqonta ga anni.
Kafin anni ta furta nata hasashen knocking dinta ya dakatar da firar tasu. Firace da yawancin
lokuta musaddiq din yakan qaraso har quryar bedroom din anni ya tayata don debe mata kewa lokaci
lokaci da hanata zaman kadaici. Duk da cewa gidan cike yake da hadimai wadanda suka aiki qarqashinta
ta kowanne fanni da take da buqata na rayuwa. Hatta hirar akwai masu tayata cikin masu aikin,wadanda
aikinsu kenan,gwanaye ne wajen iya hira da mutum,debe masa kewa da sanyashi nishadi......musamman
FU'AD ya daukesu aiki saboda haka kawai,amma ko kusa ko alama hira dasu bai kama qafan hira da
yaranta ababen soyuwarta ba.
"Badawiyya ce"
"Bismillah qaraso" Anni ta bata umarni tana gyara zamanta saman lallausan abun sallarta.
A nutse kuma cikin girmamawa ta qaraso cikin dakin. Ta tako a hankali zuwa gaban annin ta
tsugunna
"Baquwa kuma?,daga ina?" Tayi tambayar cikin dan mamaki,saboda yau din ba ranar ganin baqi
bane,tana cikin ranakun hutunta,sannan tun bayan dawowarta ma daga asibiti fu'ad ya hana kowa
ganinta,yace saita murmure ta huta tukunna.
"Ban dai kai ga gane fuskarta ba.....tadai ambaci asalin sunanki,tace kuma a gaya miki babar fu'ad da
musaddiq.......kuma...." Tadan fadi tana daga kai kadan ta dubi fuskar musaddiq da ya tattara dukka
hankalinsa akan waya,har sai da yaji sunansa ya fito cikin zancan
".....suna dan yanayi da yallabai musaddiq kadan". Dukkaninsu daga ita har musaddiq din kowannensu
ya fahimci wace......kowannensu ya gane wace take nemanta.
" Banda abun badawiyya,ai ba baquwa bace 'yar gida ce itama.....ki gaya mata ta hauro.....ta qaraso
zuwa falon sama".
"To anni" Ta amsawa anni din a ladabce tana miqewa don isar da umarninta,saidai kuma a can qasan
tata zuciyar mamaki ne kwance. Mamakin yadda annin ta bada umarnin qarasowar matar zuwa falonta
na qarshe wanda daga shi sai dakunan baccinta.....matar da sam bataga ruwa ko alamun kirki a tattare
da ita ba,tun daga yanayin kallonta har zuwa lafuzzan bakinta,to amma menene ALAQARSU DA
YALLABAI FU'AD DA KUMA MUSADDIQU?,tambayar da bata da amsarta kenan daidai sanda ra qaraso
falon.
Tana nan a tsaye inda ta barta,kamar dazun ba abinda ya sauya daga yanayin tsaiwarta a cikin
falon,zuwaira na daga gefanta bayan tayi amfani da sakannin hawan badawiyya sama da saukowarta ta
sake yiwa zuciya da ruhinta wani karatu da sake dorata akan wani bigiren.
"Tace ki qaraso saman" Badawiyya ta furta a ladabce kaman yadda tsarin aikinsu yake cikin gidan
girmamawa ga duk wani baqo da zai sanya qafafunsa cikin gidan alhaji hamza kibiya,walau me dogon
zangon zama,ko kuma me gajeriyar baquntar da bata wuce awanni zuwa mintuna
Kai ta jinjina,eh yana da kyau hakan,ko ba komai a karon farko idanunta zasu ganeta komai da
kyau......idanunta zasu gane mata yadda akayi amfani da kudi da jini da kuma quruciyar d'iyanta don
shimfida kyakkyawan rayuwa ga wasu.
Cikin jin isa taqama gami da izza take taka kowanne step na stairs din,idanunta na sake
qididdige mata adadin dukiyar da aka narkar wajen ginin gidan tare da qawatashi da kayan alatu dana
alfarma na kecewa sa'a. Irin alatun da ita shine nata mafarkin,irin qawar da shine burinta DUNIYARTA.
Yau ga komai a kusa......komai a dab da ita da sunan mallakinta.....amma wani taqi da kuma taku kadan
sun hanata isa ga wannan bigiren. Iya lallausan carpet din da aka mamaye ilahirin stairs din dashi aka
lullube tsadajje marbles din dake shimfide don kada anni taji sanyi cikin jiki da qashinta......duba daya
zakayi masa kasan asalin tsadar da yake dashi. Wani abu ya dinga taruwar mata yana tsaya mata a
wuya,wutar bacin rai taba taso mata kamar ta hallakata.
Sai da badawiyya ta fice daga dakin sannan anni ta janye idanunta ta maida kan musaddiq. Suna
hada idanu sai ya janye dubansa daga kan annin ya mayar ga wayarsa. Ta tabbatar yaji komai kuma
shima ya fahimci wacece tazo din. A karon farko kenan data fara tsomai qafafunta cikin gidan tun bayan
data sake bayyana cikin rayuwarsu karo na biyu.
Yanayin yadda ya share din kamar baisan meke wanzuwa ba yadan sanyata murmusawa. A sannu
a sannu hali da dabi'ar dan uwansa tana masa naso cikin jiki. Saidai bata da tabbas din shima dama yana
da dabi'ar ne ta iya shariya dayin kamar baiga abu ba?,ko kuwa kuma daga bayane zama da madaukin
kanwa ya sanyashi koya?.
"Na'am anni,akwai wani abu da kike buqata ne?" Yayi tambayar badon haka bakinsa yakeso ya fadi ba.
Kai ta girgiza har yanzu tana duban fuskarsa. Cikin ranta tana jin inama wannan dukka tarin
kulawar,.....wannan nuna damuwar da bata muhimmancin zasu rabata ko yaya yake da matar da suke
kira MAAMA?. Saidai ta sani,TUN RAN GINI tun ran zane.....bakin alqalami kuma ya riga ya
bushe......dawo dashi bisa zarafin aiki da damshinsa don gamsar da buqata kuwa aiki ne ba na yanzu
yanzu yau ko gobe ba
"Naji anni.....maama ce" Ya amsa mata kai tsaye. Kai ta sake jinjinawa,ta buda baki zata sake magana
amma ya rigata
"Maama ce.....kuma bani da tabbacin alkhairi ya kawota" Ya sake fadi idanunsa na nuna akwai wani abu
daya taba zuciyarsa. Fuska annin ta sauya tana rage adadin saketa da tayi a baya tadan tsuketa kadan
"Wato kaima kanason bin sahun dan uwanka kenan musaddiq?" Ta Tambayeshi cikin tsuke fuska. Kai ya
jinjina sannan yakai hannunsa ya ture hularsa baya yana shafar sumarshi
"Ba haka bane anni.....akwai wasu abubuwa da wasu lokuta suke iya tasowa dan adam a matsayinsa na
dan adam din,duk kuma yadda mutum yaso ya ture ya goge ko ya shafesu ba zasu taba barin zuciya da
ruhi su huta ba".
" Ya isheni......tashi muje" Ta fada tana yunqurawa sannan ta miqe tsaye tana gyara lullubinta.
Tana sanya qafarta cikin falon qofar bedroom din anni dake falon ya bude. Anni ce a gaba
musaddiq da ya bude mata qofar yana daga bayanta.
Kyakkyawan kallo ta sauke musu a sanda take tsaye tsakiyar falon tana kallon yadda dukiya ke
magana da kanta cikin falon. A iya rayuwar da tayi.....a iye shige shige gami da fadin tashin da tayi cikin
duniya tasan abu me daraja......tasan abu me tsada kamar yadda tasan abu me aji,don haka bata buqatar
batawa kanta lokaci wajen sake nanatawa kanta a nan dukiyar da yaronta ya mallaka take tafiya,da
gaske ne.....ba sharri bane.....hakanan ba cikin labarai na qanzon kurege bane.
Sanda suke takowa zuwa falon yana biye da anni saita gaza dauke idanunta a kansu. A hankali
taji tashin hankalinta yana sake qaruwa. Kana musu duban farko a yadda suka fito shi da anni din baka
isa duk masifarka kace ba diyan cikinka bane. Musaddiq ne.....musaddiq din da tun farar safiyar jiya bata
sake sanyashi a idanunta ba bayan zaman jiransa data dinga yi na yazo suci abincin rana ko dare
tare,abincin da ta yiwa tanadi na musamman,ta barar da kudade sosai a kanshi duka zai gashi ya tashi a
tutar babu,sai gashi a yanzun tare da matar ya zame mata tamkar wani body guard a sanda nata idanun
suke mararin son ganinsa tun jiya.
"Bismillah mana maama ku zauna" Anni ta fadi fuskarta lullube da murmushi sanda musaddiq yake
dauke mata pillows din dake saman kujerar saboda taji dadin zama.
Tana jin kamar ba zata zauna ba,to amma kuma wani sashe na zuciyarta idan bar bata zauna
daidai da nata zaman da tayi saman kujerun da tayi imani da dukiyar d'anta aka siyesu ba....lallai ta sake
zama me daraja a kanta.
A nutse ya qaraso gabanta ya kuma rusuna har qasa a ladabce yana gaidata
"Lafiya qalau......ya mukayi da Kai jiya?" Ta jefa masa tambayar tana son boye fushinta don kada amina
ta fahimci tarin galabarta a kanta ta kuma karanci rauni da ciwon da ta haifarwa zuciyarta.
*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*
*ZAFAFA BIYAR*
*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA
ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*
_K'ALBIM Mamuhghee_
_DUNIYATA Huguma_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
*09033181070*
89825722
1000cf
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
*Arewabooks@:Huguma*
https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997
PAGE 34
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 34
"Kiyi haquri......jiya mun fita da hamma farouq ne,mun samu baqi masu yawa a company,so kuma nike
kula da fitar da kayan da kamfani ya sarrafa dole na tsaya har dare muka kammala muka sallamesu".
Dubansa take sosai,sam harkar kayan gona da kayan abincin da yakeyi batayi mata ba,gani take kamar
akwai wata maqarqashiya da shiri cikin abun. Taso ace shima kamar dan uwansa harkar diamond da gold
yakeyi......ga kayan masarrufi da ma'adanai me zaa tsinta a kayan abinci?.
"Kai wai me ya hanaka bin sawun dan uwanka ne ma?,bayan duk duniya kaine mutum na biyu bayanni
da bashi da kamarka?,don me zaka tsaya kamfani harkar kayan abinci?,kana zaune a Nigeria ya dauki
bare ba dangin iya bana baaba ya tsallaka dashi yana nuna masa manyan harkoki kai kana zaune kana
fama da sabgar shinkafa?". Boom yaji furucin nata ya masa tsawa saman ka,sai yakejin kamar ta samu
ruwan zafi tana kwarara masa tun daga tsakiyar kansa har zuwa tafukan qafafunsa..
A dabarance ya jefa idanunsa sashen da anni take,sai yaga kwata kwata hankalinta da idanunta
baa kansu yake ba,ta aza dukka idanunta ga makekiyar tv plasma din dake aiki suna watso labaran
abinda ke faruwa da mutanen Palestine. Yasan sarai taji,tana da wani irin matsanancin kara,ba sanin jiya
ko yau ya yiwa anni ba......ballantana tana zaune a falon.....da zazzafa kuma kakkaifar muryar da maama
take magana zaiyi wahala ace koda a bedroom dinta take ace bataji komai ba.
"Kalleni nan" Ta fadi cikin nuna zafinta ainun tana karantar yadda yake kaffa kaffa da kunnuwan anni
"Ka tashi ka bani guri,kuma indai ni na dauki cikinka.....nayi naqudarka,na kuma haifeka to tabbas anjima
inason zama dakai.....dole nasan me kuke ciki don ba wani ya haifamin ba"
"Wannan gaskiya ne.....ai ita uwa tafi gaban komai" Zuwaira ta fadi tana satar kallon musaddiq daya
miqe. Kallo daya yayi mata ya wuce yana yin gaba don bashi da lokacinta,hasalima baisan fuskarta ba
baima gane wacece ita ba.....duka bama wannan ke damunsa......zafafan kalaman da ta soma fesarwa
gaban anni su sukafi sanya masa damuwa,tun yanzu kenan?,me zata fada a gaba?,me kuma tazo dashi?.
Wannan tunanin ya tilasta masa jan burki akan rukunin kujerun dake dab da qofar sauka daga
stairs din. Yana jin kamar ya zama dole ya tsaya din,kamar idan ya tsaya din zai iya tsaida wata barnar da
dukka zata fito daga bakinta.
"Musaddiq......sauka zuwa qasa" Anni wadda tana kallonsa cikin qasa da second biyar ta karanci abinda
yake shirin aikatawar. Idanunsa ya zubawa anni,ta karanci yana roqon ta barshi ne amma saita wofantar
da roqon ta sake maimaita masa
"Ka wuce zuwa aikinka.....Allah ya bada sa'a,ka dawo lafiya" Ta furta a nutse kaman yadda ta sabawa
kowannensu addu'a a kowacce rana,a fili ko kuma a boye.
Idanuwan mutum uku ne suka rakashi har sai daya kufcewa ganinsu. Nata idanun ta janye tana
jin suna mata yaji yaji. Wato abun har yakai matakin da ita bata isa ta basu umarni ba subi?,abun yakai
lalacewar da maganar wata itace gaba da tata maganar?.
"Barka da shigowa mariya.....fatan mun tashi lpy". Anni ta furta fuskarta qunshe da murmushi.
"Ba gaisuwa ce ta kawoni ba.....zuwa nayi na tambayeki sai yaushe zaki sakarmin yara na su dawo gareni
kamar kowacce UWA?" Sautin kalmar uwa din yadan bada amsa kuwwa kadan cikin falon yayin daya
dauke kowanne motsi da yake gilma falon na wasu sakanni. Tamkar me nazari haka anni ke kallon
fuskokinsu ita da zuwaira,sai kuma ta gyara zama tana cewa
"Gwara da kika ce UWA baki ce MAHAIFIYA BA......wanne abu aminatu tayi kuma?" Tayi tambayar
hankalinta kwance,tamkar yau ce rana ta farko data fara sanin wata me suna mariya kaf rayuwarta.
Idanu ta zuba mata kamar yadda itama ta zuba mata nata idanun. Babu komai cikin tambayar
annin face zallar rainin wayo da kuma rainin hankali. Tana cewa yanzu yanzu tayi mata tambayar amma
buqatar maimaici takeyi kenan?.
Tattara dukka nutsuwarta tayi da kuma tarin kalaman dake cike fal a bakinta,tanaso a yau ko yaya
ta fanshe haushi da takaicin anni dake kwance a ranta.....haushi baqinciki da kuma Takaicin da suka jima
suna ci mata rai.
"Zuwa yanzu ya kamata ace kinsan cewa da Muhammadu da musaddiq nice na haifi abuna ba kece kika
haifamin su ba......zuwa yanzu ya kamata ace kin warware duk wani qulli da kikayi a kansu....kibarmin
yara na na moresu kamar yadda kowacce uwa ke morar 'ya'yanta......yanzu har takai matsayin da ni zan
daga kira na kira fu'ad yaqi dagamin kira saboda baqin kilbibinki da qullinki ameena?" Qaramin
murmushi anni ta saki tana dan motsa idanunta sannan ta waresu akan maama. Tana mamakin maama
din sosai a yadda take da qarfin halin lissafo abubuwa irin haka. Kamar ma dai ta manta ita din WACECE.
Kamar ta manta su waye yaran da take ikirari gami da!kiransu da sunan 'YA'YANTA.
A dukka zancanta babu wani abu daya dameta ko ya bata mata rai,don bawai yau ko jiya tasan
mariya ba,ba kuma shekaran jiya ko waccan shekaran jiya ta gama fahimtar duk wani karkataccen saqo
shagube da jirwaye da kamar wanka da mariya ke aike mata a fakaice ba. Saidai ko da wasa bata taba
daga mata hankali kota dadata da qasa ba,tunda ta sani cewa tun ran gini tun ran zane......hakanan
mariya din ta riga tabar kari tun ran tubani,duk wani da zatayi a yanzu bazai zame mata damuwa ba,don
akwai idanun data sanya take kallonta dasu.
Abu daya ne da taji bataji dadinsa ba shine abinda fu'ad din yayi. Qin daga kiranta,wanda ita kanta
ba zata daga masa qafa ba akan hakan,kuskure ne babba wanda yana daya daga cikin abubuwan da take
yaqi dasu da son canzasu akai zuwa wani abu na daban,saidai akance mahori ya riga mabada hali.
"Wannan tsohon zance ne da duniya ta riga ta shaidashi......meye abun daga hankali,tada jijiyar wuya ko
wahalar da baki wajen maimaitamin shi mariya?,fu'ad danki ne halak malak da ya fito daga
tsatsonki,haka ma musaddiq.......qaddara ta jefosu hannuwana da taimakon salon taki rawar da kika
taka,shin meye laifin ameenatu a ciki?,rubutacce ne wannan,duk wanda yayi lissafinsa ba daidai ba dole
idan yazo kwashewa ya diba ba daidai ba......ba wanda ya tayaki lissafin bare kiyi tunanin shi ya miki
dungushe" Sosai martanin anni ya tabata. Ta sani magana ce take maida mata a kaikaice wadda bata
buqatar dogon bayani ko kuma fashin baqi.
"Shi lissafi idan akayishi ba daidai ba......akwai hanyoyin gyaransa don a samu a diba yadda ya
kamata,akwai rance akwai ciko akwai kuma bashi.......mariya nake har yau har gobe ameena" Idanunta
anni ta janye daga kanta tana sakin murmushi. Mariya na daya daga cikin halittun dake bata mamaki a
rayuwarta kaf.....saidai ta wani fannin sai taga lamarinta ba abune daya cancanci a tsaya ana masa
mamaki ba. Landline dake kusa da ita ta jawo ta soma latsa wasu lambobi wanda bugu biyu kawai aka
daga.
"Kiyimin kiran amna kice ta kiramin yayansu tace ya kirani yanzu yanzu"
"An gama" Aka bata amsa a gaggauce cikin zaquwa da son isar da buqatarta.
"Kada ki tsananta sanya damuwa a ranki mariya......komai juyin lokaci da zamani fu'ad da farouq ba zasu
taba canzawa daga sunan 'ya'yanki ba......"
".....na jima da sanin hakan" Ta katsi numfashin anni tana miqewa
"Kada ki tsammaci cewa gazawa kasawa ko kuma rashin isa ta sanyani bi ta hannunki don nayi magana
da fu'ad......a'ah.....nayi hakanne don ki sani.......daga rana irin ta yau hakan ba zata sake faruwa
ba.....don zaki rasa dama irin wannan ne har abada.........a sannu zaki manta da cewa kin taba sanin wani
me suna fu'ad ko musaddiq......wannan saqon nakeson isar miki".
Yadda bata motsa ba hakanan bata ce da ita komai ba,har zuwa sanda ta juya tana ficewa zuwaira
tana biye da ita a baya.
Duk da ranta baqiqqirin yake amma ta wani fannin tana jin wani farinciki yana shigarta. Ko
banza,ko kuma yaya ne ta amayar mata da wani sashe na maganganun da suke cizo zuciyarta. Cikin
miliyoyin maganganun da take buri da fatan amayar mata yau din ta fesar mata da kadan daga ciki,saidai
kuma ta kasa samun salama ko qanqani cikin ranta,musamman sanda take ratsa stairs tana saukowa
tana ratsa falon farko na anni din.
Bata da wani buri a rayuwa daya wuce dukka wannan daula dukiya da kuma mulki su dawo
qarqashin kulawarta,su dawo qarqashin mulkinta,su dawo qarqashin umarninta.
Tunda ya sauko ya kasa wucewa yabar gidan kamar yadda anni ta umarceshi,kawai sai ya samu
kansa da samun waje ya zauna saman tsadaddu kuma lafiyayyun sofas din da suka zamo ado wa falon.
Kujeru ne na musamman kaman yadda kowanne falo na gidan ke qawace da nashi kalar kujerun.
Ba komai yakeyi ba,kawai yana zaune ne hakanan,saidai kuma zuciyarsa tayi nisa da gangar
jikinsa. Tun yana da shekaru biyu a duniya yasan wacece ita,yasan abune me matuqar wahala ta iya
zama da anni ta sauko lafiya qalau ba tare data gasa mata maganganu masu ciwo ba. Damuwar anni
damuwarsu ce,sukan gwammace ciwo bacin rai damuwa ko jarrabawa ta samesu amma tabar musu
anninsu ta zauna lafiya.
Motsi da alamun takun mutum da yaji yaja hankalinsa,ya waiwaya da sauri daidai sanda ta
kammala sauka daga stairs din take doso ainihin falon ta yadda zata cimma qofar fita waje.
Da idanu ta kafeshi har zuwa sanda ta cimmasa a inda yake tsaye goye da hannayensa.
"Ka gaza tafiya ko saboda kada kabar wajen na bata ran qanwa ko yayar ubanka!" Ta furta a zafafe.
Kadan zuwaira ta matsa hannuwanta
"Da ruwan sanyi ma saika dafa dutse......kiyi a hankali" Ta furta mata qasa qasa. Kalamanta sun samu
gurbi a zuciyarta saidai basu samu damar sauketa daga fushinta ba gaba daya,don haka taci gaba da
kallonsa a sanda yake tsaye a gabanta ba tare da yace komai ba. Kimanin mintuna biyu kafin ta furxar da
iska daga bakinta sannan ta juya tana barin falon zuwairan na biye da ita.
Sanda suke ratsa farfajiyar farko ta gidan zuwa na biyu.....duk da maganganu da zuwaira keyi
wanda duka akan abinda ya faru cikin gidanne amma hakan bai dauke hankalinta daga tarin zalla zalla
kuma galla gallan motocin dake ajiye qarqashin sashen ajiyar motoci na gidan ba.
*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*
*ZAFAFA BIYAR*
*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA
ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*
_K'ALBIM Mamuhghee_
_DUNIYATA Huguma_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
*09033181070*
89825722
1000cf
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 35
"Na'am?"
"Kinsan adadin lissafi da qiyasin kudaden wadannan motocin kuwa?,kinsan waye da waye matsayi da
matakin rayuwa suke cillashi zuwa ga mallakarsu?,kinsan wanne me tsananin sa'ar ne cikin duniya yake
da rabon samun wadannan motocin?.....zuwaira ace d'ana keda su amma ya rasa a gidan da zaya barni
sai a wannan wulaqantaccen gidan?" Ta fadi da mugun zafi tana nuna gidan da suke tsaye a gabansa da
yatsa.
Kamar yau ne zuwairan ta saba ganin gidan,kamar ba cikinsa take kwana take tashi ba,ta daga
kai tana duban gidan da maama din ke kira da wulaqantacce.
Kyakkyawan gini ne da aka yishi madaidaici me dauke da madaidaiciyar harabar dake dauke da
mota qirar range Rover guda biyu duka don biyan buqatar matar gidan. Wadatacciyar haraba dake
dauke da dogayen katangu da kuma yalwataccen gate dake qarqashin kulawar mutum daya wato malam
saidu. Akwai qaton kitchen da aka zuba masa dukka kayan tasarrufin girki kamar kitchen din 'yar bana
bakwai,kitchen din dake maqale da store dake danqare da kayan abincin da yafi qarfin cikin mutum
ashirin da zasu shekara kullum suna ci kuma ana kyauta dasu.
Babban falo me dauke da dining area......bedrooms guda hudu da kowanne aka qawatashi da
kayan gado 'yan turkey masu asalin kyau da tsada,kaman yadda aka qawata falon da kayan turkey din
hatta da curtains da carpet kuwa. Wuta 24hrs,engine wanki dana guga,Ac hade da fanka,me aiki guda
daya a cikin gida,da kuma me kula da farfajiyar gidan namiji baya ga me gadi malam saidu. Albashin
naira dubu dari duk wata ga mamallakiyar gidan.
Nisan buri......zurfafa da kuma zarmewa a son zuciya.....take laifuka,dannesu da manta abinda
baya ta haifar ya lullube idanunsu su dukka biyun
"Indai zaa yi qiyasi bisa irin nau'in arziqin fu'ad.....idan dai zaa yi duba da gidan daya sanya wadancan
mutanen wanda idan aka sanya gidanki cikin nasu baifi matsayin boys quarters na gidan ba......tabbas ya
wulaqanta haqqin haihuwa......hakanan ire iren wadannan gidajen kinfi qarfin zama a cikinsa saidai kiyi
kyautarsa ga irinmu"
"Na'am"
"Ki rubuta ki ajiye.....muddin ban raba tsakaninsa da aminatu ba tabbas ban haifu 'yar halak ba...."
Maganarta ta qarshe kenan da tayi ta kutsa kanta cikin gidan tana jin gaba daya gidan tafi qarfin
wanzuwa a ciki.
"Subhanallah......innalillahi wa'inna ilaihi rajiun" Malam saidu ya furta yana dire qaramar radio din dake
hannunsa yanata kokawar kunnata.
To amma meye ya kawo wannan cin ALWASHIN?. Me ya kawo wannan CIN BURIN. Saita rabashi
da anni?,rabuwa ta har abada?,sai ta mallakeshi?,MALLAKA kamar wani miji?. Shin me ya kaita alwashi
akan DAN DA BA NATA BA?,wanne rashin imani ne zata tasamma shiga tsakanin UWA da D'A?,shin
mene ne alaqarsu?,wacece ita a tsakaninsu?.
Kasa kunna radio din yayi,yayi shuru tamkar yana nazarin wani abu dake shirin tunkarowa. Ya gaza
fahimtar tsakanin ita da ANNI WACE MAHAIFIYAR?,WACE KUMA UWAR?.
Cikin nutsatstsen takunsa ya miqe daga zaman da yayi saman sofa bed yana sanya rufaffun
takalmansa na fata berluti brand da suka dace da suit da lafiyayyen suit dinsa *hugo Boss* brand da
sukayi fice wajen fidda luxury suit daga zare da yaduka gami da auduga mafi daraja a duniya.
Tsaye yayi gaban mirror yana cirar madaidaicin comb da yake amfani dashi wajen taje
kwantacciyar sumar dake fuskarsa qasan habarsa da kuma kansa. Sumar da ko yaushe cikin sheqi take
da asalin santsinta da wani irin darkness da gashin yake dashi nuturally. Sosai fuskarsa ta sake
fresh,cikakkiyar eyebrows dinsa da eyelashes dinsa masu baqin gashi sun sake fidda ainihin kyawun
fuskarsa,sun kuma sake taimakawa kyakkyawar qasumbarshi wajen sake qawata fuskarsa da wani irin
ajiyayyen kwarjini.
Sai daya feshe jikinsa da sassanyan turarensan nan na din din din sannna ya kalli lafiyayyen
agogon fatar dake kwance luf saman fatarsa. Lokaci ya cika daidai kamar kullum da zaici wani abu,ya
taka a nutse yana isa inda dan kyakkyawan silver tray din ke ajiye wanda komai ke ajiye samanshi bisa
tsarin da akasan wanda zai mu'amala da tray din yake dashi.
Har ya miqa hannu zai dauki glass mug din dake da murfi sai ya dakata saboda qarar wayarshi
dake side pockets na suit nasa.
Hannu ya zura ya zarota yana duba me kiran. Sunan nan dai na dazu ya sake bayyana
"Amna....amna" Ya fadi sau biyu a hankali yana motsa jajayen labbansa da sukayi wani fresh suka sake
fidda red color nasu kamar me amfani da wani kebantaccen abun shafawa labba
Sai daya koma a nutse ya zauna saman sofa sannan ya daga kiran
"Hamma......"
"Hamma......waye yasan tsakaninka da anni kuma?" Wani qaramin qasaitaccen murmushi ne ya subuce
saman labbansa,wanda ya fidda kyawun fuskarsa sosai
"Jealous girl" Ya furta a hankali. Siririyar dariya ta kufcewa amna din,ya latse wayar yana laluban number
annin. Tunda ya tashi da sassafe kafin ya fita yayi kiran layin nata har sau biyu saidai ba'a daga ba,sai ya
bada uzurin banbancin tazarar lokuta dake tsakanin nigeria da South Korea din wala'alla tana nata
baccin ko don yanayin jikin nata ma.
Tana gaban mirror tana fama da tazar doguwar sumarta. Wani abu guda daya da taqi jini shine
duk abinda zai taba mata kai. Tun tana qarama daya daga cikin dabi'unta bata qaunar kitso kwata
kwata,wannan ya sanya har sai da ummunta ta taba aske gashinta,saidai kowanne bawa da irin halittar
gashinsa,don babu jimawa wata sumar ta fara taruwa ta kuma sake cika kan da yalwarta da santsinta har
taso tafi ta baya da aka aske.
Sake runtse idanunta tayi sanda ta sanya comb din a tsakanin gashinta,daidai sanda ta sake jin
daddadan sautin nan irin na dazu. Ta wurga fararen idanunta saman purse din dake ajjiye saman
madubin.
Idanu ta zuba mata,kaman zata dauka sai kuma ta share taci gaba da abinda takeyi,wannan ya
bawa wayar daman ci gaba da kadawa har ta gaji ta tsinke.
Wayar ya sauke daga kunnensa yana duban fuskar wayar. Sai ya sake gwada kira yana mamaki
kadan cikin ransa,don tunda yake da annin bai taba kiran wayarta sau biyu ba ba tare data daga ko ta
biyo kiran ba,sai gashi yau kira na biyar kenan zaiyi mata,duk da annin da kanta tace ya kiratan zasuyi
magana. Kodai akwai laifin da yayi mata?,ya tambayi kansa duk kuwa da yasan ba haka bane. Abune
mawuyaci ka batawa annin rai,musamman su din sanyin idaniyarta guda hudu.
Sake leqa fuskar wayar tayi a karo na uku kenan da ake kiran wayar. Suna daya ne dai
MUHAMMADU. Siririn tsaki taja tana jawo wayar gabanta,cikin tarin abubuwan data tsana harda
maimaita kiranta a waya koda kuwa kiran me muhimmanci ne. Ba wayarta bace amma ranta taji ya baci
data duba taga miscal shida kenan harda na dazu,don haka dab da wayar zata katse ta daga adan zafafe
ta karata a kunne.
Karamar ajiyar zuciya ya saki Lokacin daya fuskanci an daga wayar,a hankali ya maida
hankalinsa ga daukan kiran da akayi,cikin jikinsa sai ya dinga ji kaman ba anni bace. Koda cikin bacci anni
ta daga kiransa zaya fahimta ballantana idanushi biyu.
Kamfanin wayar ya fara irga sakannin da akayi ana riqe da duka layukan biyu,mamaki yaji
yadan fara kamashi,yayin da a nata bangaren kuma ranta ya ninka baci akan na dazu. Ansan ba'a da
abun fada aka addabi mutane da kira ba qaqqautawa?,an daga kuma zaa bar mutane da riqon waya a
hannu?.
"Idan ba wani abun fadin zaa ajjiye wayar" Ta fada tana cije lips dinta na qasa saboda haushin da takeji
cikin ranta.
Daga wayar yayi daga kunnensa yana duba number still duk da yasan number anni ce ba
kuskure a ciki. Amma baquwar muryar me kama da muryar babies itace ta daure masa kai. Sai ya dakata
daga takun da yakeyi don dauko mug dinsa,ya soke hannunsa a aljihun trouser na suit dinsa tamkar me
jin sanyi
"Bansan me wayar ba.....koma wace me wayar wayan baya hannunta......ka jira idan ya koma hannunta
ka sake kira" Ta amsa masa a taqaice tana gintse kiran.
Sautin Din din din na yankewar kiran ya sakashi janye wayar a kunnensa mamaki yana kashesa
"Who's she?" Ya furta a fili yana trying na sake kiran layin,saidai ya taras da na'ura tana gaya masa wayar
a kashe take.
Sosai ransa yayi qololuwar baci,wacce irin yarinya ce haka mara kunya wadda bata iya magana
dana gaba da ita ba?. Maida akalar kiran nasa yayi ga musaddiq zuciyarsa na masa wani irin zafi. Bayan
magana da take fadi kanta tsaye harda katse masa kira?,wayan nata ne?,ko itace tayi kiransa da zata
katse masa waya?.
Daidai sanda yake zaune a falon tun bayan wucewar maama da zuwaira kiran muhammad fu'ad
ya shigo masa. A kasalance ya zaro wayar daga aljihun gaban rigarsa,yana tsammanin driver manu ne ya
gaji da jiran fitowarsa yayi kiransa. Sunan da ya gani a rubuce jikin wayar ya sanyashi sauke ajiyar zuciya
gami da daidaita zamansa. Ya jingina bayansa da kujerar yana kara wayar a kunnensa. A ladabce yayi
masa sallama
"Wa'alaikumussalam.....wace mara kunyar kuka bari wayar anni taje hannunta.....har tana katsema
mutane kira?"
"Turqashi!.....anzo wajen" Musaddiq ya fada qasan zuciyarsa. Ya sani kowanne bayani zaiyi masa ma ba
lallai ya fahimta ba. Ya tsani ya kiraka ka katse masa waya har sai idan shi ya buqaci hakan. Bashi da
abun ce masa don haka muryarsa a raunane wadda tayi laushi saboda tarin tunane tunanen dake kanshi
yace
"Kuskure aka samu hamma......kayi haquri....bari na hadaka da annin" Ya fadi yana miqewa tsaye.
Dogon tsaki yaja kamar zai tsinke harshensa,ya koma saman sofa bed din ya zauna yana jawo
mug din yana duban dafaffiyar tumeric fresh milk din ciki kamar yau ya saba ganinta.
Da sassarfa ya soma kowawa ciki,dab da zai isa stairs din yaja ya tsaya saboda annin dake
saukowa a nutse zuwa qasa
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
*Arewabooks@:Huguma*
Page 36
"Dama baka tafi ba?" Anni ta jefa masa tambayar a nutse tana jifansa da kallon tuhuma. Kalar
tausayi ya koma yana karya wuya
"Saboda kana tsoron kada ta cinye nama na?" Ta sake tambayarshi cikin salo na gatse.
Ya gama fahimtar gatsen take masa amma sai ya basar yana binta da wayar lokacin data wuceshi
tana zarcewa saman kajurun falon ta zabi daya ta zauna
"Kiraminshi......wataqila yayita kiran layina bai sameni ba" Ta fada tana daukan remote hadi da sauya
tashar dake aiki cikin tvn.
Sipping yakeyi na madarar yana irga yadda agogon dake facing dinsa yake bugawa. Ranshi a bace
yake amma yana qoqarin danne hakan. Qarar wayar ya sanyashi waiwayawa inda ya gangarar da wayar
yana kallon kiran musaddiq. Yasan ba kiran qashin kansa bane.....na anni ne,don haka bai barta tana
burari ba ya jawota ya daga yana sakata a kunne.
Da wannan calmness din nashi yayi sallamawa anni. Itama ta amsa masa har cikin zuciyarta tana
jin wani farinciki yana saukar mata da jin tasa muryar dake bayyanar mata lafiya qalau yake.
"Barka da warhaka anni" Ya fada yana dan rusunar da kanshi tamkar yana a gabanta. Yana jin wannan
respect din har cikin zuciyarsa
"Kin tashi lafiya?,ya jikin naki anni?.....ina fatan ba wani matsala ko damuwa?" Ya tambaya cikin kulawa.
Ajiyar zuciya ta sauke hade da furzar da numfashi
"Ba ciwo,sai damuwa da kukeson sakani kai da musaddiq". Maganar ta dukesu duka su biyun,har
musaddiq dake zaune a gefe ta sanyashi daga kai cikin hanzari yana dubanta.
" Subhanallah......subhanallah anni kiyi haquri.....me mukayi?" Ya furta yana jin damuwa sosai cikin
ranshi tare da tuhumar kansa akan sanya damuwa ga ruhin da kullun burinsa ya kyautata musu?.
"Fuad.....yau ka gaida maama daga safen nan zuwa yanzu?" Ta jefa masa tambayar data sanyashi dauke
wuta,sannan a hankali ya hade labbansa guri daya ya kuma amsa mata a hankali da
"A'ah".
"Me yasa?"
"Ba komai" Ya amsa mata kai tsaye,saboda shi din mutum ne da bai iya qarya ba sam komai girman
laifinsa kuwa
"Ba komai".
" Ban tsammaci haka daga gareka ba Muhammadu,kanaso abbanku yaji ba dadi a ransa shima kamar
yadda naji?" Ta fadi cikin tausa murya tamkar tana magana da qaramin yaro.
"Ko kadan anni.....kema da muka sanya kikaji ba dadin yanzu haka kiyi haquri ki yafe mana......za'aci gaba
da kokawa da zuciya,kuma zaa gyara in sha Allah". Murmushi ta saki tausayinsu yana narka mata zuciya.
Lallai duk dan da baiyi sa'a da dacen uwa ba abun tausayi ne shi.
"Bakuyimin laifi ba muhammad.....illa dai lahirarku da kuma fagen rayuwarku da nakeson na sake share
muku ita tas". Idonsa ya lumshe yana jin zuciyarsa ta karaya......inama ana canjen uwa?.......inama ace
anni ita ta haifesu kamar yadda ta haifi Sadiq da farouq?.
"To Allah ya yiwa rayuwarku albarka,ya tsaremin ku daga dukkan sharrin me sharri"
"Kinyi addu'a me kyau anni" Ya furta qasan ransa,don sai yaji kaman ta nemawa kanta tsari ne daga
dukkan wani matakin da maama keson kutsawa dashi cikin rayuwarsu.
Ya jima yana juya wayar a hannunsa,tunani da dama suna kutsawa kwanyarsa. Sai yaji gaba
daya madarar da duka breakfast din da aka kawo din ya fita a ransa,don haka ya maida mug din ya
ajiye,ya miqe ya jawo bedside drawer ya zari dukka abinda yake da buqata ya taka a hankali yana fita a
dakin jiki da zuciyarsa duka babu walwala da karsashi.
Sannu a hankali motar dake dauke dashi zuwa companyn ke tafiya busa qa'idoji da dokokin
qasar,yayin da shi kuma yake kwance jingine sosai da back seat din na motar. Wayarsa ya sake cirowa
cikin rashin walwala ya budeta,bangaren kira ya shiga yana duba adadin miscals na wayar nashi. Miscall
dinta shine na qarshe a jerin kiraye kirayen daya rasa cikin wayarsa. Ya bude numbers din yana kalla
tamkar me qoqarin haddace numbers din. Tsahon wasu sakanni sai ya dauke duban nasa ya mayar ga titi
da yake ita hangowa tarwai ta glass. Haka kawai yake jin bayason kiran,gaba daya bashi da wani hope ko
marmari akan dukka wani abu da ya shafeta,ta kashe komai ta kuma qonashi murqus tun a shekarun
baya da suka shude,ME YAYI SAURA?. Amsar da kullum take biyowa baya shine BABU.
Da wani dan qaramin hanzari ya danne zuciyar tasa ya danna maballin kira,kiran kuwa ya tafi
direct kai tsaye,wanda cikin qasa da sakan goma kiran ya isa ga wayartata.
Duk da jerin dinner abincin daren da me hidima da ita keta faman jere mata a gabanta amma ba
wani abu daya daya burgeta ya ko ya bata sha'awa. Sai yanzu ta fahimci dawowa DUNIYARsu da kuma
shiga DAULARSU ba shine kadai iya abinda take buqata ba. Ba shine kadai iya abinda ruhinta da zuciyarta
suke da muradi ba. Lallai tana buqatar wani abu da yafi wannan muhimmanci a tattare da ita.
Ta juya a hankali tana duban zuwaira data cika plate da pepper chicken tana ci hankali kwance.
Ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tana kallonta
"Zuwaira....."
"Asama'u" Zuwairan ta amsa mata da bakinta daya cika da zallar tsokar kazar gwamnati(broiler).
"Me yake faruwa dani ne?......wa kaman ba nice ma'u ba?,kamar ba nice asama'u ba?,koda karin
maganar nan da hausawa keyi ne yakeson tabbata a kaina?,lokaci shekaru da zamani suna son maidani
wata lusara?......indai hakan ta kasance bazan taba yafewa kaina ba......bana ma fata hakan ta
kasance,dole yarana su dawo qarqashin iko na kamar kowacce uwa.....dole su kasance qarqashin
shimfidaddun dokokina.....suyi abinda nakeso na sakasu....su kuma bar abinda na hanasu......suso wanda
nakeso.....suqi wanda bana so.....su kyautatawa wanda naso su rabu da wanda bana so.........dole na
rabasu da aminatu.......dole Alhaji hamza ya zame musu babban abokin gabar da babu
irinsa......zuwaira.....wannan karon burina da muradina me girma ne.....inaji kuma ina ganin kamar
girman buqatata a wannan karon ya shallakewa aikin MADUGU.....Ina buqatar wanda yafi madugu
zafi.....ina buqatar aiki da zafi zafinsa" Idanun zuwaira suna kanta har ta kammala,sai zuwairan ta nisa ta
ajiye plate din naman hannunta ba don ya isheta ba,sai don gano damarmarki masu girma da yawa a
gabanta.....da wata siririyar qofa da take hangota da fadin gaske daga can ciki.
"Akwai BAHAGO bayan madugu din......bani da kokwanto ko tantama a kansa.....tun ba yau ba......tun
kina kogi na miki sha'awar zuwa wajensa amma kika qi bada hankali.....na tabbatar inda kin aminta da
hakan da yanzu ba wannan matsalar a gabanki.....da tuntuni kin jima da tsallake wannan babin.....saidai
kina da buqatar kudade..... Kudade masu kauri.....kaman yadda aikinsa yake da zafi haka yake da karbar
kudi,saidai ribar da zaki samu yafi abinda duka zai amsa daga gareki".
Zamanta ta gyara sosai tana duban zuwaira. Ta sani ita din gaba take da zuwaira ta fannin
abubuwa masu tarin yawa.....zuwaira bata isa ta hada kanta da ita ba indai ta wannan
bangarenne......amma kuma komai qasqancin bawa akwai ta inda yake iya wuce maka
"Tunanin da ya fara zuwa kaina kenan.....abun nan yana min ciwo.....kamar ni zuwaira?" Ta fadi tana
nuna qirjinta da yatsanta
"D'ana......mamallakin jadda diamondchore resources amma bazan iya kallon mutum nayi masa kyautar
million biyu zuwa sama ba?,zaman me nakeyi a duniya zuwaira?" Ta qarashe fada da wani irin zafi da
take jin ya ishe mata har qasan zuciyarta
"Komai ya qare idan kinbi a sannu.......idanma baki da wannan jumurin zirga zirgar ai kina dani,driver
kawai zaki yiwa umarni......fu'ad kuwa danki ne.....muddin kuma yana neman albarka.....dole ya biki" Ta
fadi tana tallafar farantin namanta da nufin ci gaba da kaiwa cikinta. Daidai Lokacin kiran ya iske wayar
dake yashe a gefe guda.
Tare suka kalli wayar,sai zuwaira da tafi kusa da ita ta miqa hannu ta jawota tana dubawa. Baki
ta tabe sannan ta furta
"Amen......sai yanzu kaga damar kirana bayan da aminatu ta baka umarni ko?" Tayi maganar cikin
tsananin daci da bacin ran dake damfare a zuciyarta.
Idanuwansa ya lumshe kana ya budesu duka Lokaci guda. A duk sanda yaji sautin muryarta
abubuwa da dama take tunasar dashi wadanda suka jima da shudewa. Yana jin kamar tana bankada babi
babi na wata rayuwarsu ta baya da a yanzu yaketa kokawar binneta tana sake boqarewa gami da son
bayyana kanta.
"Ya salam" Ya furta a hankali har kalmar ta shiga kunnuwanta da kyau,abinda yada karya lagonta kenan
tayi shuru bata sake cewa komai ba. Shurun da tayi ya bashi damar sake cewa
"Am really sorry.....naso kiranki to amma kuma ban samu zama ba......" Qaramin tsaki taja me sauti,ita
sam a yanzun ma ba wannan bane a gabanta,kiransa ko akasinsa......hanyoyin biyan buqatarta sune
abinda take da muradin riska
"Ba wani matsala ko?,ba abinda kike da buqata?" Yayi mata tambayar data zama lazeem a kansa a duk
sa'ilin da zaya kirata ta waya ko zaiyi tattaki zuwa inda take
"Akwai matsala......kuma ina da buqatun da zasu zama tamkar abun kunya a tattare da kai ace uwa ta
mutum irinka sunfi qarfinta" Murmushi yaso qwace masa,duk da koda a gabansa kake ba zata fahimci
hakan ba.
Ya riga ya fara harbo layin da ta soma hawa,don haka furucinta bai dagi hankalinsa ba ko kadan.
Ya bata dukkan wani jin dadi ta fannin sutura.....muhalli abun hawa lafiya,abinci da abun shan da kaf
gidan daga ita har masu aiki a qarqashinta babu wanda ke ta'ammali da wani ruwan sha idan ba ruwan
gora ba. Ya bata kulawar da babu yadda za'a girka abinci cikin gidan ba tare da nama ko kifi ba. Ba irin
nau'in nama ko kifin da babu shi cikin gidan muddin musulunci ya halasta cinsa.....hakanan babu nau'in
cima da babu ita a gidan muddin halas ce cikin addininsa.....kamar yadda abun sha ba nau'in da
babu.......ana kuma sake shiga da wani duk qarshen kowanne wata ba tare da damuwa da cewa akwaisu
bila'adadin ba bash kuma qare ba
"Maahma?......wanne abu ne yafi qarfinki?" Ya tambayeta murya a tausashe yana son ya kaita muhallin
da yayi imani can takeson zuwa
"Kudi fu'ad.......a matsayina na mahaifiyarka......bani da wani abu da zai shiga tsakanina da kai sai dubu
dari a wata?" Ta furta tana jin ciwon abun sosai cikin zuciyarta.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 37
Ya riga ya sani tun kafin ta fadi,yasan abinda zata fada din shine burinta na qarshe da zai kaita ga
cikar muradinta. Yana da cikakken sani na haqqin uwa.....yana da cikakken sani na duk wani haqqi da
yake wuyansa daya zamewa rayuwarsa tilas ya saukeshi......a ciki kuma babu wani abu guda data rasa sai
KUDI. Kudin kuma da yakejin ba zaya iya mallaka mata sama da abinda yake bata din ba saboda wani
babban dalili. Inda zai yiwu cikin abinda yake batan ma zayaso ya zama qasa da hakane ke shiga
hannunta. Barin kudi a hannunta GANGANCI NE. Barin kudi a hannunta KUSKURE NE da ya tabbatar
aikatashin zai zamana babu wani abu da zai goge wannan kuskuren.
"Am sorry maahma....." Ya fadi da lallausar muryarsa data karye. Shi daya yasan abinda yakeji a qirjinsa
idan ya daga idanu ya kalli maahma a matsayin mahaifiyarsa.....shi kadai yasan abinda yakeji idan ya
tuna dalilin da yasa take neman kudade haka masu yawa daga hannunsa.
"Idan akwai wani abu ba wannan ba da kike buqata.....ko musaddiq kina iya shaidawa.....am sure zaiyi
handling komai.....na barki lafiya" Ya qarasa maganar yana zame wayar daga kunnensa.
Zazzafar iska ya fitar a bakinsa sanda ya zubawa titi idanu......ya tabbatar duk yadda ubangiji ya
ni'imta rayuwarka.....tabbas akwai jarrabawa da ba'a raba ruhi da rayuwa dasu.
"Sadiq" Ya kira sunansa a hankali,sai sadiq din dake zaune a gaban motar yana fama shirya bayanai kan
yadda ganawar su da kamfanin zata kasance yadan waiwayo
"Na'am"
"Banaso mu wuce awa biyu a kamfanin nan.....inaso kome mukeyi cikin satin nan mubar Korea......gida
nima nakeso mu koma"
"In sha Allah hamma" Ya amsa masa cikin girmamawa sannan ya daidaita zamanshi yana ci gaba da
aikinsa.
Sai data tabbatar ta kammala gyara gashin tsaf,ta saka siririn ribbon ta daureshi. Sosai fuskarta ta
fita tarwai,silky skin din nan nata kaman tana amfani da wani abu daban na gyaran fata.
A nutse ta taka don dauko wayarta dake saman gado,idanunta ya sake sauka kan luggage din da
har yanxu ta kasa budewa,sai ta koma ta zauna sosai saman dan madaidaicin rug na gaban gadonta,ta
jawoshi jikinta ta soma zugewa
Tsala tsalan abayas ne suka fara mata sallama. Abayas masu tsananin kyau da tsadar da suka
amsa kudinsu na qasashen dubai da oman da Morocco. Kowacce abaya da shoe din daya dace da ita
wanda yawanci takalman kamfanin Gucci Hermes kitton da tom Ford ne. Tsala tsala agoguna na kerewa
sa'a data tabbatar kudade ne ba qanana ba aka zuba aka siyesu. Sai wasu siraran abun hannu masu
shining da sukafi mata kama da na gold,daga gefensu kuma turaruka ne turmus masu mabanbantan
qamshi da kuma tsada. Dan aljihun dake jikin luggage din ta zura hannunta,sai ta fiddo kyakkyawan
kwalin,ta juyashi kadan a hannunta,tun bata bude ba ta fahimci kwalin waya ne,saita zazzage ledar
kwalin ya fado. A nutse tayi unboxing wayar data jima da sanin kudinta. Aqalla kudin wayar ya tasamma
miliyan hudu,sabuwar Samsung 3screen da bata gama fita hannun jama'a ba. Ta riqe wayar a hannu
tana juyawa tare da duba qaramin takardar dake nuna a qasar da aka qerata da zafi zafinta acan
Ya'aqoub ya siyeta.
Ajiye wayar tayi a gefe tana bin kayan da idanu,kaya ne masu tsada dukansu,siyayya ta masu aji
masu ji da naira. Babu abinda baiyi kyau ba a ciki amma sam ba abinda ya burgeta. Idanunta ta lumshe
zuciyarta tana motsawa. Ta tuna mata da yawa,a daidai yanzun 'yammata nawa ne kamarta suke can
suna neman yadda xasu tsira da mutuncinsu?,'yammata nawa ne suka rasa darajarsu saboda neman
yadda zasu rufawa kansu asiri?,mata nawa ne suka hadu da abubuwa marasa dadi saboda an rasa me
taimakonsu?,bayan al'ummarmu cike take da mawadata irinsu Ya'aqoub din,wanda kyautar dubban
daruruwa zuwa miliyoyi ba komai bane don su fita da aljifansu?.
Zuciyarta ta tabu sosai,ta shiga tuna wasu shekarun baya da suka shude da rayuwarta,shekarun
da sukaso girgiza duniyarta,sukaso jefata wani baqin duqununun ramin da inda ta afka babu rana ko
wata na fita daga ciki ko tsere masa?.
Sautin qarar daya daga cikin wayoyinta ya katse mata tunaninta,ta bude idonta tana wurgawa inda
wayar take,ta miqa hannu a kasalance ta jawota.
"Mika'il" Ta furta sunan muryarta qasa qasa,yayin da zuciyarta ke wassafa abubuwa da dama a kanshi.
Ci gaba tayi da kallon wayar,batayi yunqurin dagawa ba har zuwa sanda wayar take dab da
tsinkewa.
A kunnenta ta kara wayar,sannan ta maida idanunta ta rufe gami da jan bakinta ta tsuke.
"Hi" Ya furta cikin zamudi tamkar ya mance gurin da yake a zaune. Qaramin tsaki taja qasan zuciyarta,ta
motsa labbanta a hankali
"Assalamu alaikum" Ta fadi a nutse.....sallamar da ta sanyaya masa jiki,ta kuma jefa shakku a cikin
zuciyarsa. Itace macen da yakewa kallon bariki ta farko da take matuqar masa kwarjini. Itace ta farko da
yake hangen wasu kalan dabi'u da suke jefa shakku da kokwanto cikin zuciyarsa. Baisan kala da adadin
matan da yayi mu'amala dasu cikin rayuwarsa ba,amma sai take neman zame masa ta daban.
"Naji dadi dajin hakan.....yaushe za'a bani damar sake ganinki?" Yayi mata tambayar abinda yafi
damunsa kuma cikar burinsa a kanta.
"Sai lokacin yayi......idan yayin da kanshi zai kawoka gareni". Sam ba haka yaso ba,sai kuma yake ganin
kaman daga gareshi ne,ya kamata ya gyara wasanshi.
"Zan iya haqurin jiranki koda na shekara nawa ne......amma inaso kisan akwai zuciyar da tayi matuqar
mutuwa a kanki take kuma da buqatar soyayyarki....."
"Mika'il......" Aka kira sunanshi daga gefe,muryar ta fusgi hakalinsa,yadan waiwaya kadan ya dube
kamilar fuskar nan,daya daga cikin fuskoki biyu dake masa kwarjini cikin kamfanin
"Am sorry......zan yanke kiran,ina fatan samun wayarki a bude zuwa anjima,ba kamar yadda nasha
wahala jiya ba" Boyayyen tsaki ta saki tana yanke kiran hadi da zame wayar daga kunnenta. Ta wurga
fararen idanunta gefe tana sauke qaramar ajiyar zuciya. Wato namiji akan mace tamkar mayen qarfe ne
da qarfen kansa?,musamman idan zaki bashi abinda yakeso?,ko kuma yana hasashen samun wata riba
ko ganima a kanki?.
A nutse ya zuba masa idanunsan nan yana kallonsa lokacin da yake jefa wayarsa a aljihu yakuma
iso bakin zagayayyen table din da yake zaune a kai.
Muhammad fuad jadda CEO abinda ke rubuce kenan jikin wani dan siririn katako dake zaune
sosai saman table din daga gaba gaba. Saidai a maimakon muhammad jaddan,farouq hamza kibiya ne
zaune saman kujerar yana duban mika'il da kyau har ya zauna kujerar dake fuskantarsa.
"Sassaucina fiye da oganku kamar yana son jawo sakaci da aikinku ko?" Ya jefawa mika'il tambayar yana
debe dukkan wani wasa da haba haba da ya saba yi dasu dake saman fuskarsa. Shafar kansa kadan
mika'il yayi cikin rusunawa
"Sorry sir.....urgent call ne shi yasa....but hakan bazai sake maimaituwa ba"
"Mituna nawa nayi ina kallonka ba tare daka sani ba,hankalinka baya jikinka?,ka kuwa san girma da
matsayin position da kamfani ta baka mika'il?" Ya sake masa tambayar yana riqe habarsa da yatsarsa
guda gami da kafeshi da idanunsa sosai. Yanayin ya tabbatarwa mika'il na gaske ne,a irin wannan lokacin
da yake buqatar kusanci na sosai da JADDA DIAMONDCHORE RESOURCES bai kamata ya bari BOSS
muhammad ya dawo ya samu wani shaidan banza a kansa ba
"Sorry sir.....it will never happen again" Kaman bazai daina kallonsa ba sai kuma ya fesar da iska daga
bakinsa,ya tura masa wani folder yana cewa
"Ruwanka ka riqe aikinka da kyau,ruwanka kayi wasa dashi.....daga rana ita yau ba zaka sake ganina a
company dinku ba,wataqila saidai ziyara......ka kuma fini sanin waye boss dinka" Ya qarashe maganar
yana tashi daga saman kujerar.
Yadda hankalinta yayi kan zuwa duba aysha yasa gaba daya ta manta da batun wayar da ta bada
address din aje a karba. Gaba daya ta manta ma da zaman wayar cikin dakinta. Sai data tabbatar su huda
sun dawo daga boko sun wuce islamiyya sannan ta shirya cikin wani dinkin atamfa doguwar riga data
bude sosai daga qasa ta zauna mata daga sama cas jikinta,ta kuma lullube kanta da Chantilly veil,takalmi
da jakan D&G su suka zama cikamakin adon nata.
Kamar ko yaushe tsakar gidan nasu zuwa farfajiyar gidan bata rabo da kai kawon jama'a jifa jifa.
Kamar kullum haka ta ratsasu a nutse ta fice ba tare data damu da idanun dake zube a kanta ba.
Kamar dai kowanne lokaci,abinda ta baro cikin gidan shine a waje. Yawan idanun jama'a dake
kanta ko kadan basu dadata da qasa ba. Tun asali mutum ce me damuwa da lamarin gabanta.
Abubuwa da dama da suke cikin zukatan mutane a kanta bata isa ta gogeshi ba. Abune da tun
yana damunta ya zame mata jiki. Suna mata kallon biri ne tana musu kallon ayaba. Anyi walqiya me
hasken data haska mata abubuwa masu tarin yawan da suke boye cikin hijabin idanuwan jama'a da wani
irin shamaki da tsinkaye da idanuwa basu kaiwa wajen.
Wasu mutanen a riga kawai suke mutane.....wasu dattawan a suna ne kawai kuma a
baki.......wasu jama'ar da ake tunanin suna gyara ko bada gudunmawar gyaruwar al'umma su din GUBA
ne,guba ce wadda bata da magani,guba ce me d'aid'aita komai da wargaza komai.
Daidai sanda takai qarshen tunaninta sai ta fidda eye glasses dinta da ba kasafai ta fiya amfani
dashi ba ta manne qwayar idanunta. Daya daga cikin abinda ya sanya suke mata mummunan kallo da
mafi munin fassara. Eye glasses ne me duhu dake qarawa fuskarta kyau da kuma kwarjini,yake kuma iya
hana mutane ganin ainihin qwayar idanunka.
A nutse takai bakin titi,saidai yanayin kai kawon abun hawa kadai zai gaya maka akwai qarancin
motocin haya
"Ki siya mota kawai ki huta sabreen" Ta tuna kalamin qawarta qwaya daya da take da ita duk duniya
wato haseena. Karon farko tun wayewar garin ranar ta saki murmushin da batayi niyya ba,abinda ya
sanyashi tsaiwa da motarsa cak. Duk da cewa ta daki zuciyarsa tun daga nesa daya hangeta,amma sai
gashi farat daya ta sanyashi tsaiwar da baiyi niyya ba.
Taga gilmawar farar motar amma saita dauke dukka wani hankalinta zuwa wani sashen,qasan
zuciyarta tana fatan bawai ya tsaya bane saboda ita,don a yanzun bata da buqatar qaruwar kowanne
namiji cikin rayuwarta. Tana da tarin matsalolin da takeson ta kammala dasu tukunna,mazajen dake
cikin rayuwarta kuma a yanzun ta sallami kowa da kalar sallamar data dace dashi kafin ta sake sabon
zubi.
A hankali motar ta dawo daidai gabanta ta kuma tsaya cak,sannan aka sauke glass din
motar,abinda ya bawa sassanyan sanyin ac din dake gauraye a motar damar fitowa waje ya kuma daki
fuskarta.
Sallamar da yayi mata ta tilastata waiwayowa ta dubeshi. Nutsatse kuma kamili a ido,wankan
tarwada wanda ko bai miqe tsaye ba ta tabbatar dogo ne. Zagayayyar Fuskarshi da gemu ya yiwa
qawanya,sai idanunsa dake saye a cikin glass.
"Bai dace ace zafin rana yana dukan wannan kyakkyawar fuskar ba.....shigo don Allah na rage miki
hanya". Jin kai da miskilanci cikin jininta yake,duk daga yanayin kamalar data gani a fuskarta ya mata
kwarjini amma saita sake dauke kai ba tare da tace masa kanzil ba.
"Ki shigo domin Allah". Ya furta yana tsareta da idanu har zuciyarsa yana jin tayi masa. Duk da cewa
akwai wani irin kwantaccen kwarjini akan fuskarta wanda bayajin cewa ita kanta tasan tana dashi.
Kaman yadda magiyarsa ta dauki hankalinta haka bullowar kawu ta dauki hankalinta. Duk da
cewa daga nesa yake amma ta zuba masa idanu da kuma wannan komar tata dake saurin karanto lissafin
me lissafi. Cikin qasa da minti daya ta gama karantarsa,zaiyi wuya ace ba ita yaje nema gida ba bai
sameta ba ya fito. Batayi shawara ta biyu ba ta juya a hankali ta kama murfin motar ta bude ta shige ta
maida ta rufe,daidai sanda motar ke tashi ya iso gurin.
"Kaga shegiyar yarinya?,ni zaki gudarwa?,don ubanki ai duk tantirancinki dai idan dare yayi gidan adamu
kike dawowa ki kwana ko?,to mu zuba dani dake.......meye amfaninki muddin ba za'a moreki kudi ba?,ai
amfaninki kiyita kawo mana kudi tunda hanyar da kika zabawa kanki kenan" Ya fada yana yarfe hannuwa
shi daya a gefen titi,kai kace ya samu matsalar kwanya.
Juyawa yayi da zummar barin wajen,saidai taku biyu rak yayi wayarsa keypad dake aljihunsa ta
dauki kururuwa.
"Kai jama'a......Allah yasa ba bala bane.....kash.....shine wallahi" Ya fada yana qoqarin danna madannin
wayar da yayi tsananin tauri saboda ganin rayuwa da yayi.
"Hel.....helo bala.....don Allah kar ka damu.....ai in sha Allahu ina me tabbatar maka damu za'a shiga
wannan cacar.....yo ta ina zamuyi wasa?,bayan kai da kanka ka tabbatar min mutumin nan attajiri
ne......ai ina maka rantsuwa da Allah baka bina bashin rantsuwa wannan karon arziqi ne yake
kiranmu....inata buga buga naga na samu adadin abinda akeso a shiga cacar dasu....kada ka damu,zuwa
nan da dare in sha Allahu zaka jini,yauwa na gode" Ya fada yana sauke wayar,ya soma laluben aljihunsa
don maidata ciki yana sake magana a fili.
"Idan ma Allah ya taimakeni na haye da wadannan kudaden ina zaki sake jina?,ai nima na zama attajirin
kaina don ubanki" Sai yaja qwafa sannan tsaki ya biyo baya,ya juya yana sauya hanya.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 38
Sau biyu yana sake juyawa yana kallonta. Tun bayan sallamar da tayi yayin shigowa motar bata
sake cewa wani abu ba.
A nutse take da dukkan nutsuwarta,nutsuwar data sake janye ra'ayinsa a kanta matuqa.
"Na gode qwarai da baki wofantar da magiyata ba.....hakan ya nunamin kinsan darajar dan adam....."
Maganarsa ta sanyata dawowa tunaninta tare da tunasar da ita a inda take. Batace masa komai ba,tadan
dai motsa kadan alamun tana saurarensa,hakan ya bashi damar ci gaba da magana.
"Da farko dai sunana alhassan.....ko zan iya sanin sunan malamar?" Sunan daya kira kanshi dashi ya
sanyata juyawa kadan ta kalleshi sannan ta maida dubanta ga kwaltar da suke bisa kanta. Kaman ba
zatace komai ba sai kuma ta motsa bakinta
"Sunana....." Sai tayi hanzarin dakatawa. Shima kaman sauran?,yana buqatar a bashi stamp?,yana
buqatar personal suna nashi tamkar dai sauran 'yan uwansa jinsinsa?. Eh yana buqata,saidai shi din bata
jin zatayi wani doguwar mu'amala dashi da har zai buqatu ya zuwa stamp na musamman
"Da alama sunan nan me tsada ne ko?,sai na siyeshi?" Ya fadi yana dan satar kallonta kadan fuskarsa
dauke da murmushi. Kai ta girgiza a hankali
"Sunana sawwama"
"Nice and good name.....me azumi kenan?" Ya fadi yana dubanta kadan. Kafada ta daga,koma meye
ma'anar sunan bai zame mata damuwa ba,kawaidai ta bashi sunan ne don shine sunan da yazo kanta.
"Ma sha Allah......gashi mun iso inda kika cemin,kuma ina da tarin abubuwan fadi don inason alaqar
tamu tayi nisa,tafi haka zurfi,za'a bani wani abu kaman number waya ko adress nazo na sameki?"
"Wayata bata da guarantee adress kuma bani da" Ta bashi amsa ta kai tsaye daidai sanda yake tsaida
motor din a inda ta nuna masa.
"Waya ba guarantee adress aishi zai zama babban guarantee ko?....me yasa kikace baki da adress?"
"Saboda bamu da gida" Ta sake bashi amsa kai tsaye sanda take dubansa da fararen idanunta masu
sheqi da hasken rana ya qara musu qyalli,abinda ya sake daukan hankalinsa kenan. Murmushi ya saki
yana jin tana sake burgeshi
"Alright.....nasan dai ba dan adam din dake rayuwa a titi.....amma bazan takurawa zabinki ba......zaki iya
bani dama ta uku?,damar yin magana dake a nan?" Numfashi ta sauke a hankali tana jin ya takurata da
yawa,ta daga hannunta dake daure da agogo ta kalla sannan ta sauke tana juya idonta daya sashen
alamun qosawa
"Tunda na ganki sawwama naji zuciyata ta kwanta dake.....ta kuma kamu da sonki......naji kuma a raina
na samu matar aure.....ina fatan zaki bani dama....." Statement dinsa na qarshe data samu fahimta
kenan.
Waiwayawa tayi ta dubeshi,shima idanunsa yana kanta,da alama ya gama dukkanin bayanansa
ita yake da buqatar jin ta bakinta. Dauke duban nata tayi,sannan ta saka hannu ta bude murfin motar ta
zura qafafunta ta fito. Da mamaki yake binta da kallo har zuwa sanda ta maida masa murfin motar ta
rufe,tadan rage tsaho kadan tana dubansa da shiny eyes dinta
"Na gode da karamcinka......amma kayi haquri.....babu aure a rubuce cikin rayuwata.....na barka lafiya"
Ta motsa labbanta a hankali sannan ta janye jikinta daga motar.
Soma takawa tayi a hankali tana barin wajen,AURE na daya daga cikin abinda take mantawa dashi
a rayuwarta. Aure yana cikin abinda yake a lissafin qarshe cikin abubuwan da suke ba dole ba a
rayuwarta. Aure yana daya daga cikin abinda take masa wani irin kallon da batasan ajin data zubashi
ba.....babu shi ko kadan a dictionary dinta,idanma anyi zancensa,tana masa kallon wani baqon abu
wanda batasan ranar da zata saba da ji ko ganinsa ba,bare azo da batun wanzuwarsa akan kanta.
Ko kadan bata damu da tsaiwarsa a wajen ba,abu daya ta sani.....kaman sauran mazan,yadda
basu da masaniyar daga inda ta fito......hakanan bata basu qofa ko qanqani game da sanin inda zata ko
inda zata shiga. Don haka bata kutsa kanta cikin gidan ba sai data kadar masa da hankali,ta kuma
tabbatar ya bar layin.
Da sallama a bakinta ta shiga madaidaicin tsakar gidan dake shimfide da sabon simintin da bata
jima da sanyawa ayi musi shi ba saboda jin dadinsu.
Yara ne aqalla kusan guda biyar wadanda shekarunsu bazai haura goma zuwa sha uku ba. Biyu
daga cikinsu wanki sukeyi,daya kuma tana wanke wanke,yayin da guda dayar take jawo ruwa a rijiya
tana zubawa a babban mazubin ruwan da suke amfani dashi a gidan.
Sallamarta ya sanya kowacce ta watsar da abinda takeyi,suka kuma rugo da gudu suna rige rigen
isa inda take. Kyakkyawar fuskarta ta fadada da fara'a itama ta buda hannunta tana tarbarsu,daidai
sanda muryar matar ta iskesu
"Ku da waye haka?" Ta bayyana tare da qarashen tambayarta tana qoqarin daura dankwali saman kanta.
"To ku barta ta qaraso mana" Ta fadi tana juyawa cikin dakin da ta fito,dukansu sai suka bi bayanta
harda sabreen daketa jefawa yaran tambayoyi.
Tare suka zauna da yaran saman shimfidaddiyar dardumar da matar ta shimfida saboda sabreen
din,daya daga cikin yaran ta miqe ta fice sai gata da ruwa adan qaramin jug da cup,yayin da sauran
sukaci gaba da zama a kewayenta.
"Ina Ayshatu?" Tambayar farko da sabreen tayi mata bayan sun gama gaisawa,tambayar data sanya
yaran suka miqe daya bayan daya suna fita a dakin.
Bata ce komai ba matar saita miqe tana dosar wata qofa dake maqale a falon,itama batace komai
din ba ta miqe ta biyo bayanta.
Yalwataccen daki ne dake wadace da tsafts,ba komai a qasan sai wata lamusashiyar katifa guda
daya yashe a qasa. Daga samanta idan ka duba da kyau mutum ce a kwance data lulluba duka jikinta. A
sanyaye sabreen ta qarasa gaban katifar,ta saka hannu ta yaye rufar bakinta yana rawa ta kira sunanta
"Aishatu?" A hankali ta ware idanunta akan sabreen din,sai kuma wani busashen murmushi ya subucewa
kyakkyawar fuskar yarinyar
"Aunty....kece kika zo?" Ta tambayeta da siririyar muryarta. Kasa riqe kanta tayi,sai kawai tayi qasa da
kanta hawaye yana diga daga idanunta. Tana jin tausayin yarinyar kamar zai fasa zuciyarta,tana jin
kamar zata narke a wajen,tana jin inama ace tana da ikon fidda ciwo ta farat daya daga jikin mutum a
yanzu yanzu basai anjima ta cisgeshi daga jikin ayshatu
"Ko baki da ikon cire mata shi yanzu yanzu.....kina iya sama muku dama ke da ita na samo mata lafiya a
duk inda lafiyar take a fadin duniya" Wani sashe na zuciyarta ya bata amsar data motsa mata wani
qwarin gwiwa daga can qasan zuciyarta. Wannan ya sanya ta sake daga idanunta tana kallon aysha. Allah
ne kadai yasan bila'adadin mata da yaran da suka shiga irin yanayin da ayshatu ke ciki duka sanadin
TAIMAKO. Lalacewar al'ummarmu abune me matuqar ban mamaki da daure kai. FYADE ba'a daukeshi da
wani muhimmancin da me aikatashi zai fuskanci hukunci mafi tsananu ba a tsarin doka. Tana iya tuna
yawan kudaden data kashe,shige da ficenta da kai kawo data dinga yi kafin ta samu ayiwa azzalumin
hukuncin da doka ta tanada. A abinda ya yiwa aisha,ba hukuncin daurin shekaru take da buqata
ba......lahira yafi kamata ya baqunta yaje ya hadu da hukuncin mafi iya hukuncin masu hukunci.
Sosai ta bawa zuciya da gangar jikinta qwarin gwiwa,ta zauna sosai ta yiwa yarinyar komai. Ta
bata abinci ta kuma dinga hilatarta,har suka dinga hira tana saurarensu murmushi yana subuce mata.
Hakan ya sanyaya ranta kafin su kebe da ummaa ta sake mata bayanin data yi mata a waya.
"Waje nakeson a fita da ayshatu,inason ta warke sumul taci gaba da rayuwarta,duka duka shekarunta
sha uku,ya kamata ta rayu kamar kowa" Ta fada zuciyarta tana mata zafi. Allah ya dora mata tausayin
yaran da matar kanta da batasan asalinsu ba,amma dukka dawainiyarsu kusan kaso tamanin cikin dari
tana a wuyanta,hatta da hayar gidan da suke zaune a ciki kuwa,banda abinci da ma karantarsu rayuka
shida.
Da idanu ummaa take bin sabreen. Tasan cewa dukkaninsu babu wanda suka hada dangantaka a
tsakaninsu,amma suna jin juna kamar 'yan uwa,suna kuma ci gaba da tsananin shaquwa da juna.....kuma
a yanzun sune 'yan uwan kawunansu.
"Sabreen......kiyi iya abinda zaki iya mu barwa Allah sauran.....samun maganin ayshatu a gida Nigeria ma
miliyan nawa ya kama bare ayi batun fita da ita waje?,kinsan miliyoyin kudin da za'a cajemu?,daga visa
passport masauki abinci da zaman asibiti zuwa kudin magani?" Shuru sabreen tayi tana saurarenta,tana
jin zuciyarta na wani irin ciwo,irin ciwon da mutum kanji a duk sanda yake tsananin son abu amma babu
ikon samuwar wannan abun gareshi. Numfashi taja sosai ta aje tana duban maama
"Allah zaiyi cikin iko da isarsa......na tabbatar Allah bazai taba wofantar da bayin da aka zalunta ba" Kai
ummaa ke jinjinawa tare da yaba tauhidi da yaqinin sabreen.
Ta jima dasu saidai hankalinta yana kan asibiti,don haka lokaci kadan ta qara akai tayi musu
sallama bayan ta aje musu kudi kaman yadda ta saba da basa wuce cefane da zirga zirgar makarantar
yaran.
Tana hanya zuciyarta kamar ta fashe,hakanan ta sake jinta a rikice bayan fitowarta daga asibitin
bayan taji bayani daki daki na yadda zata fita da ayshatu waje ayi mata aiki.
Kudade ne masu kaurin da a yanzun bata dasu bata kuma bawa wani ajiya ba. Batasan tayi
farautar kudi don ta ajiye ta tara abun duniya ba......tana farautarta ne don ta raba a tsakanin mabuqata
marasa galihu irinta,yanzun ka buqata ta taso mata wadda take da girma da muhimmanci a rayuwarta.
Sai taja numfashi mai nauyi,tabbas a yanzun zatayi FARAUTA ta ainihi,tsakanin MIKA'IL YA'AQOUB da
kuma MASHKUR waye zaiyi aman wadannan maqudan?.
_tofa zamuji waye,komarta zatayi kamu ko kuma wannan karon ita zata shiga komar?_
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
*_Arewabooks:@Huguma_*
https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997
__________________________
PAGE 41
Kusan a tare wayoyi uku suka dauki ruri dake nuna alamun ana kiranta.
Mashkur mikail da ya'aqoub,abubuwan farautarta da batasan waye a ciki zai fada komarta ba. Ta
dinga bin sunayen da wayoyin da kallo cikin canki cankin wanda zata fara daga wayarsa a ciki har sai da
suka katse,sai ta barwa ranta wanda ya soma sake kira. Saidai kuma cikin rashin sa'a sai ga mashkur da
mikail suna kiranta lokaci guda. Plate din hannunta ta ajiye,ta sanya hannu tana daukan kiran mikail. A
lissafinta shine mutum na farko da takeson saukewa daga layinta. Dukka wani binciken halayya nasa
suna gwada mata tsantsar dacewar ya karbi sakamako da horo yadda ya dace. Ita kanta batasan adadin
abinda zata diba daga gareshi ba,saidai ko banza ta sanya zata sanyasu a muhalli da guraben da suka
dace.
A jirkice yayi mata sallama da muryar data sanya ta saka masa ayar tambaya. Ta daga wayar
daga kunnuwanta ta duba fuskar wayar tana mamaki
"Bayan neman mata harda caca da harqallolinsa harda shaye shaye?" Ta tambayi kanta cikin mamaki,sai
ta maida wayar kunnenta kawai tana saurarensa.
"Sai yaushe zaki bani dama ne?......ina tsananin kewarki......ina son kasancewa dake" Abinda ya fada
kenan yana jin kamar ana fusgarshi zuwa gareta. Katse wayar tayi tana jan dogon tsaki. Baci kawai takeji
ranta yana yi kota ina tare da azalzala mata akan mikail. Sai ta jawo wata qaramar waya daga gefanta
wadda bata hasken komai ba ta turawa JIB qaramin saqo. Tana jin ya kamata aikinta ya fara ta kansa.
Yadda mashkur yaketa kiranta ba daga qafa ya sanya ta share kiran ya'aqoub ta daga nashi.
Kiran ya'aqoub din ma bata mata rai yakeyi,ta tabbatar dukkan wani magidanci me mata irinsa a yanzun
yana cikin gidansa ne koda a dakinsa ko a sassan yake. Taga maza da yawa da halayensu,daya daga cikin
halayyar tasu kuma da tafi baqanta mata rai take tunzurata shine wannan. Wai ta yaya ma zatayi
Aure?,bayan bataga komai ba a tattare da mazan sai munanan dabi'u dake girgiza zukatan matan su
haifar musu da muguwar illar hawan jini ko ciwon zuciya?,ko mummunan zawarcin da har ki mutu bazai
fita a tarihinki ba?. Har abada tana kallon zaman 'ya mace me cikakken 'yanci a yayin da ya kasance babu
igiyar wani a kanta.
"Saura kadan ki kashemin raina muhseena......hala bakisan girman soyayyar da nake miki ba har
yanzu?......kinsan Allah?,banqi a daren nan ace an daura aurena dake ba?"
"Aure?" Ta furta a hankali tana jin kalmar tayi mata girma da yawa.
"Yes aure muhseena....." Ya maimaita fada yana gyara zamansa cikin tattausar sofa din da yake kai. Yana
fatan samun gamsashen amsa tare da mamakin kansa yadda yarinyar ta sauya masa tsari gaba daya.
Hira ya dinga qoqarin janta dashi,duk da ita din bame doguwar hira bace amma ta dan sake
masa,don itace hanya guda daya da take dashi da zata haska mata hanyar gano gurbin da zata dasa
bomb dinta.
"Kiyimin alfarma daya mana......ki gaya min credit dinki na yimin rakiya dubai for just one week......ni
kuma nayi alqawari zan biya ko nawa ne" Ya fada yana sake jin kowacce gaba tasa tana narkewa da
sha'awarta da sonta. Yanajin koda bata shirya aurensa ba......zai kashe mata ko nawa ne suyi irin
rayuwar da yake muradi......idan da yiwuwar ta zama tashin a gaba sai ta zama.....idan ma hakan bata
samu ba yana ganin duk inda ta kwana sha ne muddin ya tsira da abinda yake qulafucin samu.
"Zan baki dama kiyi tunani......sannan ki yanke ko nawa kikeso muhseena.....ko nawa ne muddin raina
zaikai ga muradinsa".
Maganarsa t qarshe kenan data sake sanyawa sabreen mummunan zato ga maza......maganarsa
ta qarshe data sanyata ta kusa raba dare tana kuka......ta kuma dinga godewa Allah ta wasu fannin.
Mashkur din data tura masa mabanbantan mabuqata da buqatar neman tallafin da duka duka
baikai ko digo cikin abinda ya mallaka ba yasa aka koresu?......yace bashi dashi?.....yace bazaya bada
ba?......wannan mashkur din yau shike bada damar a nemi ko nawa ne zai iya mallaka mata bisa rashin
sanin WACECE ITA?.
Hakan tamkar wata dama ce a gareta kenan da zata samu dukka kudaden da takeso......amma
bisa sharadin sadaukar da abinda yafi komai mutunci a tare da ita?.
Koda ta saba ko tana da damar accepting masa abinda yazo dashi.......tabbas ba zata lamunce
ba......tanaso ta debi kudadensa ta hanyar data saba azabtar da sauran.......tanaso ta debesu ta hanyar
da zaiji ciwon da bazai kankaru ba a zuciyarsa.......tanaso ta debi kudin da zai tsaye masa a rai......yayi
masa ciwo fiye da yadda rayuwa da zukatan matan da ya fadawa mutuncinsu sukayi musu
ciwo......tanason bashi darasi me girma a rayuwa.......tanason shima ya girgiza girgizar da zata tsaida
masa komai na rayuwarsa cakkkkk koda ba tsaiwa bace ta har abada......to amma kuma ta
sani.......babban plan da yake buqatar nutsuwa da tsare tsare masu yawa. Don haka da safiyar washegari
ta tura JIB wani saqon da sunan mutum biyu.
Tana tsaye tana shan ruwan dumin da takesha duk safiya kafin shigarta wanka saqo ya shigo
wayarta. Sanda ta duba sai ta samu alert na kudi daga wajen ya'aqoub. Five hundred thousand ce,sai ta
gyada kai a hankali tana sakin murmushin takaici. Don kyauta yana da kyauta ya'aqoub ba daga baya
ba......abinda bata da yaqini shine haka yake a cikin gidansa?,ko shima fankan fayau ne?.
Saqon godiya ta tura masa a gajarce,ta aje wayar tana shirin wucewa wanka wani saqon ya sake
shigowa
"Patiently waiting for you" Share saqon tayi hade da sauran. Tasan me saqonsa ke nufi a gajarce.
Kowacce safiya izina ce a gareta,kowacce rana kowanne sati da kuma kowanne wata cikin rayuwarta
yana bude mata babi na abubuwa da yawa cikin rayuwarta. Waishin akwai ragowar NAGARTATTUN
MAZA kuwa?,tambayar da kullum idan ta yiwa kanta ita take bawa kanta da kanta amsa da BABU.
Kanta tsaye take takawa cikin tsakar gidan nasu ba tare data daga kai ba bare ta lura da waye a
hagunta ko damanta?. Ba tare data damu da kallon nan nasu data tabbatar a safiyar yau zai ninka ko ma
ya canza salo saboda abinda ya faru a jiya.
Dab da zata sanya qafarta a qofar toilet din nasu dake da sassa biyu bathroom da toilet ta jiyo
muryarsa yana koda sallama. Sallamar da muddin ya yita duk wani dake da hadin kai dashi take masa
dadi......duk wani wanda yake da qulli dashi Kuma yake neman yin ta kansa,mutane kuma kamar ita
sukejin kamar su turashi ya koma muhallin da ya fito.
Koda taso tayi shigewarta toilet din ta tabbatar sai ya ganta don ya iso dab da wajen. Don haka ta
tsaya a nutse tana bude toilet din ta hanyar murza handle,abinda ya bashi damar qarasa shigowa
farfajiyar tsakar gidan.
Da ita ya fara hada idanu kamar yadda nata idanun suka zube a fuskarsa. Kamanni dai da
mahaifinta har kullum sune,bata kuma fasa ganinsu shimfide a fuskarsa,saidai nisan tazarar halayya da
dabi'un sun kai girman tazarar dake tsakanin sama da qasa.
"Yauwa alhamdulillah......ai gwara dana sameki cikin gidan.....zuwan dama naki ne" Kallonsa kawai tayi
ba tare da wani mamaki ba,dama wanne zuwa ne zaiyi gidan ba nata ba?,koda yayi zuwan daba nata ba
to lallai daga qarshe sai ya zama nata ko kuma ya hado da ita a abinda bai zama damuwarta bama bare y
shafeta. Amma tun a jiya tasan tabbas dama zayazo,shi yasa taso su fice kitso da wuri yazo ya taras da
sararinsu kawai.
"Ina kwana kawu?" Ta fada cikin girman nan da bata fasa bashi shi kaman yadda kowa cikin gidan ke
bashi duk kuwa da farin sanin da tayi na waye shi?,sanin da kaf gidan tayi yaqinin ba wanda ya masa
shi......sanin da a qa'ida ya cancanci ta rainashi......amma sai kuma batayi hakan ba.......sanin da ko
yaushe ta tunashi dashi take jin kaico da bacin rai da rashin sanin son ganin gilmawarsa.
"Lafiya qalau......idan kin baro bandakin ki sameni a dakin bibo" Ya fada yana saba babbar rigarsa yana
wucewa ciki tare da jaddada sallamarsa.
Da kallon takaici ta bishi,tasan dama zaa rina,ba wani abu da zai fari cikin gidan ya kwana ya
hhantse baije kunnuwansa ba.......yana kuma zuwa kunnuwan nasa ne ta hanya guda daya rak wato
BIBO. Idanma akwai ta biyunta to bata bayyana ba tukunna. Cikin rashin damuwa da lamuransu gaba
dayansu ta kada kanta ta wuce bandakin.
Babu wani abu da zai sanyata gaggawa a zuwa kiran data tabbatar babu alkhairi sam sam a tare
dashi. Wannan ya sanya ta kammala wankanta a nutse,takuma tsaya gaban madubi ta shirya tsaf kamar
yadda ta saba. Tun bata kammala ba ya aiko kiranta ya kusa sau biyar. Ana shidan ta tsaida nadra da taji
tana gaya musu cewan kaya take sanyawa
"Kace gani nan zuwa" Ta fadima usman daya aiko. Rigar lace tayi niyyar sakawa,don haka ta fara sanya
'yar cikin rigar ta yane kanta da mayafi ta zura slippers dinta tana cewa
"Ku kammala shiryawa ina dawowa zamu wuce" Ta qarasa fada tana sanya qafafunta a waje,huda kuma
ta bita da kallo. Sam bataso ace sabreen din taje da kanta kamar yadda kawu ya buqata ba,ta tabbatar
da cewa ba wai wani abun arziqi zai aiwatar ba face tsantsar son zuciya da son rai kamar yadda suka
saba. Ba wani lokaci da abu irin haka zai taso cikin gidan ya zamana anyi hukunci cikin adalci da sanin ya
kamata.
Hankali kwance ta daga labulen dakin bibo gami da sallama. Su uku ne cikin falon,kawu bibo sai
hadiyya dake zaune saman daya daga cikin kujerun. Qafarta daya saman daya tana kadata a hankali.
Tako ina tana jin kishin wanzuwar komai dake tattare da sabreen din. Kowanne abu tana yinsa ne don
kawai ta samu daqile sabreen din. Ba haka takeso ta bude idanuwa ta ganta ba. Wani qaqqarfan abu ya
dasu a ranta game da sabreen din.
A haka mutane ke raina matakin da take kai.....suke mata kallon wadda ke tafiya bisa baragurbin
bigire......amma ita a nata idanun ta sani cewa sabreen din tayi mata wani irin nisan tazara me tarin
yawa. Bataso ta ganta a haka.....ba'a haka take da muradin ganinta ba,tana son ta sauya daga matsayin
da take kai a yanzun,shine abu daya da zai gamsar da ita.....
*SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI*
*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*
*ZAFAFA BIYAR*
*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA
ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*
_K'ALBIM Mamuhghee_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
*09033181070*
89825722
1000cf
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
*_Arewabooks:@Huguma_*
https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997
________________________
PAGE 42
Janye dubanta tayi daga kan hadiyya,sai ta nemi hannun kujerar dake daga bakin qofa ta zauna
akai,wayarta a hannunta tana qoqarin sakata a silent. Ta manta yaushe ne lokaci na qarshe data shigo
wannan dakin,bama shi ba,dukkan wani daki dake cikin gidan ba muhallin shigarta bane.
"To da kika shigo kikayi mana derere saman kujera ai sai ki sauko ko?" Muryar bibo ta rasa kunnenta.
Dauke dubanta tayi daga saman wayar ta aza a fuskarta. Abubuwanta sun fara mata nauyi akai,tanason
ta fara shige huruminta. Tana ganin kima da martabarta a matsayinta na macen data taba kasancewa
mata a wajen mahaifinta,amma ta lura da sam sam bata kula da wannan.
Dauke idanunta tayi daga kan bibo din,tana ji a ranta lokaci ya kusa da zata sassauta wannan
girma da martabar da take bata,tunda har ita din ta gaza riqo dasu yadda ya kamata
"Gani" Ta fadi kai tsaye tana duban kawun. Zamansa ya gyara yana wani hakimcewa. Jira yake su
kammala da maganar da aka tattagoshi a kanta ya gabatar da nasa batun wanda shine yafi damunsa
"Yanzu ke......wani irin baqin hali gareki ne?.....kin fita ZAKKA ke kadai?,kin addabi kowa kin damu
kowa?,a gidan nan kaf babu wanda yake da matsala sai ke?" Duk da tasan qarshen zancan,ta kuma san
abinda ya sanyashi debo dogon zance har haka amma sai maganganun nasa suka bata mamaki. Banda
tsabar rashin son zaman lafiya na mutanen gidan......a yanayin yadda ta tsara rayuwarta dana 'yan
uwanta,ya kamata ace tana cikin sahun jerin mutanen da za'a mance da wanzuwarsu cikin gidan. Zaka
jima baka ga gilmawarta ba,zaka jima baka ganta zaune a farfajiya ko filin tsakar gidansu ba.....zaka jima
baka ganta a tsaye tana magana da kowa ba,to wai shin me ta tsarewa bibo da ire irenta cikin gidan?.
"Wani abu akace maka ya faru?" Tayi tambayar tana tsareshi da idanu. Fada yakeso rufeta dashi kamar
yadda bibo ke buqata.....amma kuma yana duba da tunanin kada hakan ya sarayar da samuwar tashi
buqatar.
"Yo har sai ance miki ma wani abu ya faru cikin gidan nan banda raini?.....me ya kaiku shiga hurumin
yarinyar nan banda neman tada zaune tsaye?,yarinyar da babu abinda ta sanya a gaba banda
karatunta?,inajin kaf cikin yaran marigayi babu kamarta ko akwai?" Ya qarashe tambayar yana maida
dubansa kan bibo da taketa cika tana batsewa. Dukka salon fadan daya dauko babu wanda yayi mata
"Ina fa?.....mu irin karatu ne,kuma karatu shine a gabanmu" Ta fada tana gyara daurin dankwalinta.
Da idanu kawai take binsu tamkar bata fahimtar koda kalma daya daga cikin maganganunsa,har
zuwa sanda yakai qarshe ya kuma jona da tambayar bayyana fifiko me yawa tsakaninsu da hadiyya.
Tsam ta miqe tana duban kawun
"An gama?,inaso na fita ne" Ta fadi kai tsaye ba tare da tayi duba ga sashen da bibo ke zaune ba.
Dukkaninsu idanu suka zuba mata su ukun,yayin data juya a hankali tana nufar qofa ganin kawun bai iya
cewa komai da ita ba.
Cikin tsananin jin zafi gami da yunqurowar wani boyayyen zazzafan kishinta a kanta ta sauke
qafafunta tana aje wayar hannunta gefe
"Kin gani ko bibo?,ai dama na gaya miki......wallahi bata kunya ko shakkar kowa......ni nasan kawu ba
matakin da zai iya dauka a kai....."
"Ke!.....yimin shuru,rashin kunya zakiyimin?" Ya fada cikin fadan nan nasa yana rarraba idanu. A duniya
idan akwai abinda ya tsana itace kalmar YA KASA KO YA GAZA
"Aah dakata sule......" Bibo ta fada tana daga masa hannunta daidai sanda kunnuwan sabreen sukayi nisa
daga jin cecekucensu.
"rashin kunya har takai wadda waccen figaggiyar gantalalliyar yarinyar tayi maka.....tambadaddiya da ka
kasa saitota cikin yaran dan uwanka......kaf dinsu yara mata goma sha tara amma ita daya ta fita
ZAKKA?,to kada kazo kace zaka zaqemin akan yarinya......me laifi daban wanda za'a huce a kansa
daban?". Ransa ya baci sosai,don shi din irin mutanen nan ne da basa son raini ko wargi ko qanqani.
Banda ma bibo din da taga wallensa......kaf yaran gidan tsoro da shakkarsa suke idan ka cire SABREEN
din
"Ke hajara......dakata,hawainiyarki ta kiyayi ramata......kibar ganin ina daka ta taki.....wallahi ina nan
yadda kika sanni......kawai ina duba wasu abubuwa ne nake rama miki halacci da halacci......amma tunda
iskancin naki a kaina zai sauka a gaban qaramar yarinya irin wannan......to shikenan......ni na zare
hannuna daga sha'aninki cikin gidan nan......" Ya fada yana miqewa cikin hargagi gami da kakkabe babbar
rigarsa.
"Haba sule.....zauna mana kaji......ba haka nake nufi ba.....ni dadina dakai wannan masifar taka da
jarabar". Tsaiwa yayi yana hade rai gami da dubanta
"Ba haka kike nufi ba hajara gayamin abinda kike nufi". Sai kuma ya waiwaya sashen da hadiyya ke zaune
"Tashi ki bawa mutane guri kin zauna kina raba idanu a gabansu" Ya fadi mata cikin tsawa kamar zaibi ta
kanta. Wayarta ta dauka sumi sumi tana yin hanyar shigewa bedroom din bibo din,qasan ranta cunkushe
fal da baqinciki. Baiyi mata yadda takeso ba,ba kuma haka takeso ya yiwa SABREEN ba. Batasan dame
sabreen din ta fisu ba da har tauraruwarta tafi tasu haske cikin gidan,duk da tayi yaqinin ko meye
sabreen din zata juya ta kuma nunawa duniya shi to ba shakka ya samu ne daga dattin ZINA da kuma
dattin BARIKI. Ba abu mafi daure kai irin mazan dake karakaina a kanta tamkar su sadaukar mata da
rayukansu......amma ta gaza cafke koda guda daya ta maisheshi mijin aure?.
"Mazan bariki dama suna auren macen da suka hadu da ita a bariki?,ai saidai su tsotseta tas.....su
musaya wannan zaqin da gardin da suka samu daga gareta da 'yan kudaden da zasuyita mata
barinsa......daga sanda buqata kuma ta biya su tattarata su watsar su qara gaba zu zabi wata". Sai ta tuna
maganar da sukayi taba yi da bibo wadda ke kamaceceniya da kalmomin maleeka roommate dinta. Juyi
tayi kadan saman gadon,tana da burika masu tarin yawa akan karatunta,wannan ya sanya ta sadaukar
da rayuwarka akanshi. Tana so ta ganta tana fantamawa,tanason ta ganta tana haskawa tamkar sabreen
da dukkan wani alatu da jin dadi......tanaso taga maza suna mutuwa a kanta sama da sabreen......amma
dukka ta hanyar karatunta da kyawun sura da Allah ya bata. Tana cikin sahun jerin farko farko da 'ya'ya
masu kyau a gidan......ta tabbata ko wannan ya isheta jari wajen zaben kalar mijin da take buri da muradi
idan aka qara da karatunta da takesa ran kammalashi ta kuma riqi kyakkyawan certificate mafi girman
daraja a idanun mutane.
Ta samesu a zaune sun gama shiryawa sanda ta koma dakin. Kai tsaye ta wuce can ciki ta jawo
rigarta ta sama ta zura,ta hada igiyoyin ta daureta ta zauna dai dai jikinta,abinda ya bawa rigar daman
fidda kyakkyawan shape din nan nata da ba kasafai ya fiya bayyana ba saboda ita din ba ma'abociyar
sanya damammun kaya bace. Sai data sake goge jikinta da sassanyan oil perfume dinta sannan ta fara
rolling dan kwalinta saman kanta idanunta akan fuskarta data bayyana tarwai ta cikin madubin.
Maganganunsu taketa tattaunawa ita da zuciyarta. Dabiar kawun dama bibo gaba daya. Yadda
tsahon lokaci da zamani bai sanya kowannensu ya sauya ba. Ranta da zuciyarta duka ba dadi. Ta iya
rigima tuburan idan taso......ta iya surutu har kayi zaton ma ba ita bace......hakanan ta iya fada musu da
kuma taurin kai......amma daga sanda rayuwa ta soma Karantar da ita wasu darussa sai ta gane basu take
buqata ba,don haka ta tattarasu ta aje a gefe.
Jakar da zata dace da shigar da kuma yanayin ta dauko. Kaman yadda ta saba duba jaka kafin
takai ga fita da ita haka ma wanna,a nan taci karo da kudaden da mashkur ya bata. Maidasu jakar tayi da
zummar damqawa suraj su,daidai lokacin haneefa ta shigo tana kiranta
"Eh" Kamar ba zata mata komai ba,sai ta fesar da iska daga bakinta. Tasan dukkan abinda zai sanyashi
shigowa wajenta baya taba zame mata abun alkhairi face tarin matsaloli fadace fadace da fadin
maganganu barkatai da zasu yamutsa DUNIYARTA tana zaune salin alin
"Kice masa gani nan" Ta bata amsa tana juyawa sashen ajiye takalmanta ta fara dubawa. Takalma ne
kala kala masu mabanbantan shape kudi da kuma kaloli. Wani adadi ne me yawa ma'ajiyar takalman
taci,wanda dukkansu idan ka kalla babu takalmin qasa sa dubu goma.
A duk sanda ta kalli sashen suturar data mallaka a yanzu,a karan kanta mamakinta yana sake
ninkuwa ne. Suturu na alfarmar da yaran masu hannu da shuni ke taqamar mallaka ko jin isar cewa sun
kai. Daya daga ciki ta zaro,ta aje a qasa ta zura a qafafunta sannan ta debi wayoyinta ta jefa a jaka tayi
hanyar fita tana ji a ranta ko sisi a yau din bazai samu daga wajenta ba muddin abinda ya shigo dashi
kenan.
*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*
*ZAFAFA BIYAR*
*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA
ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*
_K'ALBIM Mamuhghee_
_DUNIYATA Huguma_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
*09033181070*
89825722
1000cf
*_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_*
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 43
___________________________
GROUP 1
https://chat.whatsapp.com/DT97XBDyEfyEwniN0a09Cz
*_kina ta ganin kaya kala kala online?,kinason siya amma kina tsoron damfara?,tsada ko rashin ingancin
kaya?_*
*_muna da nau'ikan kaya kala daban daban bisa farashin da ba kowanne dan kasuwa ke iya bada
kayansa akan hakan ba_*
Shadda
Laces
Atamfa
Mayafai
Abayas da jallabiyas
Inner wears
Lafayas
_kai komai daya danganci kayan ado na fita kunya wa dan adam_
*_Me kike jira sallah na gabatowa?,ana can ana ruwan suturu daidai da qarfin kowa?_*
*_ki dinga siya da kadan kadan kina saka kudin kina tara abinki har sukai sanda zaki karba?,ko ki siya
lokaci daya a kai miki_*
*_MASU REPOSTING DA MASU SARI DUKA BA'A BARSU A BAYA BA,KI SIYA KI SAIDA KI SAMU RIBARKI
HANKALI KWANCE,BA TARADDADIN INGANCIN KAYA KO WANDA KIKA BAIWA KUDINKI_*
*_KIYI JOINING KI TURAWA 'YAN UWA DA ABOKAN ARZIQI_*
GROUP 2LINK
https://chat.whatsapp.com/CKY0xZDtpby6MTkGrPkXLr
_________________________
Samunsa tayi zaune dirshan saman carfet yana karakaina da kwanukan da suka gama breakfast.
Ya buda flask din da suka zuba dafaffen naman kai wanda sukaci suka bar sauran sai zuwa dare. Yana
cikin ire iren siyayyar da take musu lokaci bayan lokaci dukka a qoqarinta na ganin basu rasa komai
ba......basu nema komai sun rasa ba......hakanan komai din bai gagaresu ba. Tana da buri me yawa
akansu,tana da mafarki mai fadi......tana kuma fata da sanya ran wataran zata basu rayuwa fiye da
wadda sukeyi a yanzu haka.
Daga kai yayi yana dubanta sanda yake tauna naman,zaqin maggi yana ratsashi.
"To zauna mana banda abinki,kikayi wani dogogo saman hannun kujera?" Ya fadi saboda yadda ta kame
a hannun kujerar rungume da hannayenta. Sam batason ya bata mata lokaci ta kuma fahimci zuwa yayi
yaci mata lokacin
"Kawu ai ina tunanin wancan maganan mun gama da ita ko?,fita nakeso nayi ne ana jira na" Ta fada tana
duba agogon hannunta.
"Kefa kin fiya tsiya da hurwar banza da wofi,ayita tattaroki kina wargajewa?,har sai kin jawo magauta
sun jimu?" Shuruuuu tayi tana me zuba masa idanu tare da mamakin fitar kalamin daga bakinsa. Wai
magauta,ji kuma na nawa?,ko yana tunanin cikin gidan yana da wani magauci a tsakaninsu da ya wuce
shi karan kansa?.
"Tunda sauri kike bari nayi a gaggauce" Ya fada yana sude hannunsa daya nado romon naman kan,ya
gyara zamansa sosai yana kallonta.
"Kinsan hausawa sunce ko kana gudu haifi ka yar.....kuma ita haihuwa rana gareta" Yayi maganar cikin
sigar kwantar da murya da jan hankali. Bata ce masa ta tafasa ya sauke ba,tadai ci gaba da kallonsa yana
bayanansa tare da son jin inda zantukansa zasu tuqe
"Wato wata gwaggwabar mu'amala ce ta taso mana,wadda cikin ikon Allah take buqatar adam zuba
wasu kudade kuma a kwashe da riba me tarin yawa.......to kinsam harka ta samu dai ba'a wasa da ita a
lokaci irin wannan,duba da yadda al'amuran qasa suka yamutse....to na duba na dubo......na laluba na
lalubo kaf 'yan uwa na kusa dana nesa......ba wanda zai rufan sittira ya bani kudin nan aro ko bashi banda
ke diyar albarka" Ya qarasa maganar yana addu'a qasan ransa. Ya santa sarai.....yasan aikinta,yasan
kuma abinda zata aikata da wanda ba zata yi din ba. Ya jima baiga yarinya mai zubin matsorata
ba,wadda kuma a zahiri zuciyarta a tsaye take carrr babu tsoro ba irin sabreen din.
Tsam ta miqe abinta bayan data fahimci cewa yakai aya a maganarsa
"Bani da wasu kudade kawu.....zan fita sai na dawo" Ta fada kanta tsaye tana gyara chain din hand bag
dinta. Daga zaunen ya tada kai yana dubanta
"Wai baki fahimci abinda nake magana bane akai sabreen?" Qaramin murmushi ta saki. Ta sani,idan tayi
rantsuwa ko kaffara ba zatayi ba,zaije yayi caca ne.....abar da ya jima yana tabawa da taimakon
mahaifinta ta soma sakinsa,sai gashi a yanzu gushewar me masa saiti ta sanya ya dawo da dukka wasu
tsaffin dabi'unsa da ake sanya ran yayi adabo dasu. Duk da hanyar da take samar da kudadenta.....amma
tayi imanin ba zata iya diba ta bashi ya buga caca ba. Inda wajen wata lalurar dabanne,ita a karan kanta
lokaci bayan lokaci tana miqa mass,shi kansa yasan tana sahun mutane na farko farko da hannunsa ke
yawan amsa daga garesu koda bataso haka ba.
"Naji kawu...kayi haquri bani dasu" Ta sake fada hankalinta kwance,don sam case dinta bai daga mata
hankali ba,don abu daya data sani shine,ko sama da qasa zasu hadu ba zata iya bada silai tata ya sanya a
caca ba,bayan tarin buqatu da lalurori dake zayyane cikin littafin ayyukanta da takeson wanzarwa. Tana
da babban mafarki akan mutanen da take rayuwa dasu,tana son kowanne ta daukeshi ta dora rayuwarsa
bisa wani gurbi ko matakin da koda bayan ta gushe tasan tayi dashen daya baza rassa sassa da kuma
jijiyoyi masu inganci da qarko.
"Bari dai na miqe don kiga iya adadin tsahona,sannan ki tabbatar da gaske dai nake" Ya fada rai a bace
yana miqewar kamar yadda yace. Kallonsa ta sakeyi sosai,a nutse tsaf ta janye iidonta. Ranta yana baci
mamaki yana sake mamayarta. Bai taba nuna damuwa ko yaya akan yadda suke rayuwarsu
ba,sunci?,basuci ba?,lafiya suke ko akasin haka?,yaya karatunsu lafiyarsu da sauransu,amma a yanzu
qarfi da yaji so yake ya dinga qaqaba mata lalurorinshi wanda koda ya sauke su baya gani baya kuna
darajta hakan bare ya qimanta su.
"Idan ka gama zan rufe dakin kawu,dukkanmu zamu fita ne" Ta fada masa a ladabce tamkar ba ita ta
hana masa abinda ranshi yakeso ba tana qarasa fita a falon,don ta tabbatar idan ba haka sukayi dashi ba
zai yita zama yana jawo zantuka kala kala da daga qarshe zai barta da qunar zuciya da zubar hawaye mai
zafi.
"Indai ni kika tozarta sabreen zaki gani......na tabbatar inda ubanki ne yazo da buqatarsa ba zaki taba
tozartashi ba,ba komai,badai ni kika wulaqanta ba?,to in sha Allah......in sha Allah,sabgar dai da bakiso
za'a yita,kuma sai ta kawo arziqin da baki tunani mara mutunci kawai" Ya fada daidai sanda yake sanya
qafarsa a waje. Baya taja kawai batace masa komai ba,har ya zura takalmansa yayi gaba yana sababi
kamar ya ari baki.
A hankali take takawa huda na gefanta,haneefa na daya gefan tana riqe da hannun haneefan
cikin nata,sai nadra dake a gabansu da yake tana da sauri a tafiya ba laifi.
Dukka su ukun sanye suke da atamfa iri daya kamar yadda mayafansu suke iri daya. Duba daya
zakayi musu kasan suna samun kulawar rayuwa daidai gwargwado. Ba yunwa wahala ko jigata a tattare
dasu,wanda duka hakan ya samu garesu ne ta sanadiyyar YAYA ME KAMA DA MAHAIFIYA da suka samu.
Kaffa kaffa take dasu da rayuwarsu sosai tun daga lokacin da duniya ta gama bude mata dukka
fuka fukai da lokunanta da saqonta.......tun daga sanda duniya ta soma yi mata wani karatu wanda a
sannan ba'a taba yi mata karatun da yakai gefan wannan ba.....tun daga sanda ta fahimci DUNIYA cike
take da ababen tsoro da mutane MAFARAUTA masu banbancin hali da dabi'a cikin abun farautarsu.
A haka suka kai qarshen layinsu suka kuma sada kansu da bakin titin unguwarsu. Tsaiwarsu da
duka mintunan da basu haura uku ba motar ta karyo daga cikin layinsu da yunqurin hawa bisa babbar
kwalta,idanunta suka sauka akan matuqin motar. Za'a iya cewa ido hudu sukayi,shi ya fara gaggawar
janye nasa idanun yana gabansa yana faduwa,sai itama ta janye nata tana jan wani dogon siririn tsaki.
Bata jin har abada......har numfashinta yabar gangar jikinta zata iya manta wannan fuskar tasa.....yana
daya daga cikin mutanen da ba zata taba iya mancesy ba bare akai ga mance fuskarsa......mutumin da
had kullum idan ta tunashi take gayawa kanta shekaru hamsin da takwas dinsa a duniya ya yita ne a
banza da wofi ba tare data qara masa komai ba......hakanan arziqinsa bai qareshi da komai ba sai
dulmiya cikin sabon Allah kaca kaca.
Da wannan tunanin ta sanya hannu ta tsaida musu empty keke napep me tahowa,don zai yi
wahala ta fita ta hada abun hawa da wani ko wata,ta saba da daukan drop duk inda zata muddin ba
busari zai dauketa ba. A mu'amalarta da 'yan uwanta kuwa bata lamunci susan kowa ba ko kuma kowa
ya sansu ba,duk fita indai dasu ne abun hawa na haya take dauka duk da aminta da tayi da busari din
dama JIB,amma ta sanya a ranta kowanne cikin su akwai iyakarss,aikin da yake mata kuma sam bai shafi
'yan uwanta ba,basu da alaqa sam dasu,ko fuskokinsu cikin su ukun babu ta guda daya da zasu iya
shaidawa.
Cikin motar dake girke daga nesa kadan daga shagon. Motar da aqalla ta dauki tsahon kwanaki
tana sintiri a titin,tana kuma daukan dukka sa'o'in a wanni a fake a wajen ba tare da kowa ya damu da su
waye a ciki ba?,meye kuma yake kawosu ba?.
Dai dai sanda suke sauka daga napep din,ta biyashi ta kuma sanyasu a gaba suna nufar babban
shagon wankin kan gyaran fuska da kuma yin kitso na noor's beauty parlor,daidai lokacin ya dauke
idanunsa daga kan wayar hannunsa,idanun kuwa sukayi kyakkyawar sauka a kansu su dukka hudun.
Da wani irin hanzarin samun damar cimma abun FARAUTAR ya tabo dan uwansa dake kashingide
yana lumshe idanu,da alamun gajiya ta fara sanyashi jin baccin dole.
"We found her......" Ya fada da wani irin karsashi da qwarin gwiwa,wanda bai bashi damar jiran abokin
nasa ya kammala zama gaba daya ba yayi swapping da sauri zuwa kakkaifar camera dinsa ya soma
daukan hotonsu bayan zooming camera din da yayi daga bakin window din,ya kuma bada hoto me kyau
duk da 'yar tazarar dake a tsakaninsu. Kafin su shiga ya samu hotuna guda uku kyawawa da suka yalwata
farincikinsa. Yayin da abokinsa dake zaune daga gefe bakinsa ya kasa hutawa daga furta
"Well done" Ba. Harara ya juya ya watsa masa bayan ya tabbatar ya adana hotunan
"Dole kace well done tunda ka kwanta kana shirin yin bacci" Ya fadi masa da gurbatacciyar hausarsa da
zata gaya maka shi din ba ainihin bahaushe bane. Dariya ya saki yana cire hular kansa tare da karkadeta
ya maida saman kansa
"Da gaske na cire tsammani duba da satittikan da muka shafe muna zuwa wajen nan babu wani alamun
nasara ko alamun ganinta.....amma yau dai komai ya fara hawa saiti,meye target na gaba?" Ya tambayi
abokin nasa yana kallonsa.
Haka kawai ta dinga jin wani yanayi yana mamayarta na rashin sukuni da kuma sakewa tun daga
sanda suka sauka daga motar har zuwa sanda take zaune saman kujerun da aka qawata wajen ana kitse
lallausar sumar nadra da haneefa me tsaho da santsi wadda dukka da tsahonta batakai tata yawa ba.
Wayarta ce a hannunta tana duba wasu bayanai da JIB ya tura mata......amma sai takejin kamar akwai
wata mantuwa ko kuskure da tayi.
A karo na kusan shida ta daga kanta tana duban nadra da fuskarta t fito tayi kyau sakamakon
kitson da aka kusa gama mata. Cikin qasa da minti biyu gabanta ya yanke yayi wani mummunan faduwa
"Nayi kuskure.....nayi ganganci" Ta fadawa kanta da kanta can qasan zuciyarta tana jin wata qaramar
fargaba tana mamayeta.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 44
________________________
GROUP 1
https://chat.whatsapp.com/DT97XBDyEfyEwniN0a09Cz
*_kina ta ganin kaya kala kala online?,kinason siya amma kina tsoron damfara?,tsada ko rashin ingancin
kaya?_*
*_muna da nau'ikan kaya kala daban daban bisa farashin da ba kowanne dan kasuwa ke iya bada
kayansa akan hakan ba_*
Shadda
Laces
Atamfa
Qawatattun handbags
Mayafai
Abayas da jallabiyas
Inner wears
_kai komai daya danganci kayan ado na fita kunya wa dan adam_
*_Me kike jira sallah na gabatowa?,ana can ana ruwan suturu daidai da qarfin kowa?_*
*_ki dinga siya da kadan kadan kina saka kudin kina tara abinki har sukai sanda zaki karba?,ko ki siya
lokaci daya a kai miki_*
*_MASU REPOSTING DA MASU SARI DUKA BA'A BARSU A BAYA BA,KI SIYA KI SAIDA KI SAMU RIBARKI
HANKALI KWANCE,BA TARADDADIN INGANCIN KAYA KO WANDA KIKA BAIWA KUDINKI_*
GROUP 2LINK
https://chat.whatsapp.com/CKY0xZDtpby6MTkGrPkXLr
__________________________
Duk wani da zatayi mu'amala dashi......yadda bata yarda yasan daga inda take ko inda
zata......hakanan take nesanta tare da barin duk wani muhalli da suka taba haduwa ko ya taba ganinta a
can din. Cikin tsarinta bata sake mu'amala ko huld da gurin......tana kuma nisantar wajen da duk abinda
zai sanya ta ratsa wajen ko tayi hulda da gurin.
Wannan gurin shine guri na qarshe da suka hadu da alhaj naseer.......shine kuma gurin data
sauya saboda wankin kai wankin qafa da gyaran fuska da takanyi time to time.
Batasan me ya dauke hankalinta ba ta sake dawowa gurin ba,ta karya dokarta da kuma tsarinta da
kanta,ya akayi tayi mantuwa irin wannan?,haka kawai saita kasa samun nutsuwa,ta maida wayarta jaka
ta ajeta gefe,ta hada hannayenta guri daya sannan ta harde qafarta daya saman daya tana sauraren
gilmawar kowanne motsi dake kewayen wajen,tana kuma karantar kai kawo da aikin kowa dake wajen
cikin nutsuwarnan tata da kaifin sansano abu.
Yawan rashin nutsuwarta ya qara yawa,tilas ta miqe a hankali sanda aka kama kan huda wadda
ita daya ta rage sai ita din karan kanta da zaa wankewa kai
"Madam saura ke" Daya daga cikin ma'aikatan ta fada tana kallonta sanda take takawa a hankali tana
nufar bakin qofar wajen
"Okay to" Ta amsa mata tana tattare kayan gyaran gashin data baza.
Cikin tsanaki ta riqe curtain din wajen. Ta sanya idanunta a nutse tana qarewa titin kallon cikin
nazartar kowanne abun hawa dake kai kawo a wajen. A qalla ta kusa kashe mintuna goma a tsaye ta
cikin shagon wanda babu lallai kai da kake waje ka iya ganinta.
Idanunta basu iya gani ko hangen komai da zata iya sanyashi cikin zargi ba,zargin da zai iya
alaqantuwa da wala'alla yanayin da takejin jikinta da zuciyarta a ciki ba.
Ajiyar zuciya ta sauke tana matsawa da baya a hankali cikin ainihin shagon. Ranta yana raya mata
wala'alla don ta fito ne da dukkansu shi yasa ta kasa sakewa,sai taji gaba daya ta qagauta a gamawa
hudan su wuce ba tare data damu da cewar ita din ba'a yi mata komai ba.
"Ta koma?" Ya tambaya daga daya sashen cikin tsananin farinciki,hankalinsa kwance a yau din saboda
samun damar kama bakin zarensa da kyau
"Eh,ta koma" Suka bashi tabbaci daga inda suka janye motartasu suka ajeta. Wani shu'umin murmushi
ya saki,yayi taku biyu yana jan wata dunqulalliyar kujera ya zauna akai
"Na gaya muku....tana da matuqar wayo fiye da zaton me zato.....amma ku sani....muddin aikinku ya tafi
da kyau.....ya kasance kamar yadda na tsara.....ina me muku albishir din qari akan abinda mukayi
yarjejeniya daku"
"Aikinka kamar anyi an gama shi ne" Ya maida masa amsa cikin zallar nishadi
"Take care.....ina sake maimaita muku.....ku kula" Daga haka ya yanke sadarwar dake tsakaninsu,don
baya yarda suyi wayar data wuce minti daya dasu.
*******Sanye take cikin daya daga cikin suturu na alfarmar da suma zame mata abun sawarta. Walau
fita zatayi?,ko kuma tana zaune ne kawai a gida saboda gwada qarfin izzarta tare da son nunawa duniya
matsayinta da kuma kashe qarfin kwadayin izza da kwadayin sauran kayan qyale qyale na rayuwa.
Ni'imtaccen falon nata da takejin qarfin iko da isarta sun zartasa a killace yake tsaf kamar yadda
dabi'arta take na mace da batason qazanta sam sam,yana gyare ne tsaf bisa jagorancin masu aikin da
suke duk wata hidima ta gidan ba tare da tayi cas ba bare as idan ka dauke bada umarni.
Ta kasa hankalinta ne gida uku,daya yana ga bada umarnin yadda takeso a tsara table din don
zuwan musaddiq cin abincin dare gidan,daya yana ga duban cikar lokacin da zai iso din,yayin da dayan
yake kan zuwaira tana sauraren zantukanta da a mafi yawan lokuta sukafi gama da banbadanci.
Sake gyara zamanta tayi tana daidaita zanin embroidery vlisco atamfa din dake jikinta wadda
kudinta ya tasamma dubu sittin. Ta zube idanunta akan zuwairan karo na uku
"Duk yadda zanyi zuwaira.....kome meye ne zai faru dole zan dauki mataki fa.....ba irinmu ake zuwama
da irin wadannan abubuwan su bari ba.....komai tsiya musaddiq da fu'ad 'ya'yana ne halak malak,babu
wanda ya isa duk duniya ya kankare wannan matsayin" Ta fada har cikin zuciyarta tana jin zafi tsana da
qyamar anni......tana jin a duniya ita da alhaji hamza sune manya manyan maqiya kuma abokan gabar da
bata da sama dasu. Sake duba agogo tayi,yadda taga lokaci yana ta ja ya sake sanyawa ranta ya baci
"Zuwaira yanzu haka yana can ta riqeshi har sai sanda tayi masa izini zai taho gurina?" Kyabe baki
zuwairan tayi tana tallafe kanta da hannunta tare da dogarashi jikin kujera,sannan ta karkatar da kanta
tana kallon wani sashen,tabbacin abun yana mata matuqar ciwo kenan
"Kema ai kinsan kwanan zancen.....ai kinyi sake maryam ba dan qarami ba kuwa". Maganganun zuwaira
suka sake zame mata tamkar allura,taja wata doguwar qwafa bacin ranta yana ninkuwa,a take taji duk
wani danshi na maqogaronta ya bushe ruwa take da buqatar sha. Kamar ko yaushe a tsawace tayi kiran
sunan me aikinta,ta nufota a gaggauce,ba tare data bari ta qaraso ba tace da ita
"Koma ki bani ruwa......banason kowanne sai swan.....karki maimaita kuskuren jiya". Jikinta yana ruwa ta
amsa mata
" In sha Allah ba za'a samu matsala ba" Ta juya da hanzari hanyar kitchen.
Su biyu ne kadai zaune saman lafiyayyen dining din na wata iriyar mulmulalliyar kwalba me garai
garai. Komai na gidan an zubashi ne bisa nunawa kudi iyakarsa,komai me kyau ne me kuma asalin
tsada,kamar yadda komai aka zubashi bisa tsari.
Anni ce saman daya daga cikin kujerun,jikinta sanye da wata sassauqar cotton abaya 'yar asalin
moroco wadda ta dace da jikinta da kuma shekarunta. Kanta sassalkan dan kwali ne da yazo da
rigar,tana riqe da waya da alama wani kira take amsawa da ya janye hankalinsu su duka ita da musaddiq
dake zaune saman kujerar dake fuskantar tata. Idanunshi akan annin yana dariya saboda yana iya
sauraren abinda siririyar muryar ke fadi ta wayar. Jikinsa na sanye da yadin senate me asalin tsadar.
Sosai yadin ya kwanta masa a jiki ya kuma dace da kyakyawar hularsa dake aje saman table din daura da
plate din abincin da yaci rabi yana riqe da cokalin yana sauraren wayar anni.
"Don Allah anni kice mata ta zauna kin yafewa nanna ita" Ya fada qasa qasa yana boye dariya da
muryarsa don bayaso ta jiyoshi. Annin ta jishi sarai,murmushi me sauti ya kubuce mata,saita cira wayar
daga kunnenta tana cewa
"Ga qaramin yaaya zai baki saqo" Ta aje masa wayar a gabansa taja nata plate din a hankali taci gaba da
diban abincinta tana ci tana kuma saurarensu.
Idan daru ne tsakanin amna da musaddiq a gidan ba wanda baisan da zamanshi ba. Saidai kuma
akwai shaquwa me tsananin qarfi tsakaninsu da ba wanda ya isa ya taba daya a gaban dayan. Wani sabo
da 'yan uwantaka ce me zurfi a tsakaninsu wadda tadan sha banban da wadda ke tsakaninsu da FU'AD
da kallon UBA kusan sukeyi masa.
Tana jin yadda suke fafatawa da yace mata an barwa nanna ita,ya dinga kwasarta yana dariya
anni na zaune kawai tana murmushi har sai daya tabata sosai sai ya yanke kiran,daidai sanda farouq ke
shigowa falon.
Sassanyan matashi,cikamakin barin zuciya ruhi da rayuwar mamallakin kamfanin jadda diamond
chores resources muhammad fuad jadda. Kaman twin brother dinsa fu'ad yadda ake kallonsu kenan,illa
banbancin career da kowanne yake dashi.....yana da wani ajiyayyen kyau nutsuwa da haiba. Su biyun
kam sun zamewa duniyar 'yammata da yawa jarabawa,ba'a maganar 'yammatan da karansu baikai
tsaiko ba.....yammatan da basu da damar nuna yatsa ko tsaiwa a dandamalin da kowacce diya da take ji
da gata da kudi zata tsaya......yammatan da saidai su gansu jikik TV mujallu da jaridu da kuma sauran
kafafen sadarwa......aah.....wannan fagen na 'YA'YAN GATA ne,yaran da iyayensu da kuma su kansu suka
ci suka kuma tayar da kai,yaran da suke da chance 50 to 60 percent na ganinsu,walau a gidajensu ko a
guraren ayyukansu,ko tafiya ta hadasu a filin tashi da sauka na jirgin sama a kowacce jaha dake
Nigerian,ko kuma su hadun cikin qasashen da aiki ko kuma hutun da sukan tafi dukka family din alhaji
HAMZA KIBIYA zuwa wasu daga cikin kebantattun qasashen da sukanyi quri'ar zuwa.
Wata irin nutsuwa suke da ita,wanda kwata kwata harkar mata bata gabansu. Har gwara gwara
farouq din,akwai wasu banbance banbancen dabi'u da kuma halaye tsakaninsu da fu'ad. Tun asali farouq
mutum ne meson comedy ko yaya ne,abinda zai sakashi dariya da nishadi,yanason yaga ya tsokani
mutum abinda ya sanyashi yasha wahala qwarai a hannun mariya......sabanin sadiq da yake da tsoro da
kuma tsantseni. Saidai dukkansu a yanzun girma ya sauya wasu daga cikin halayensu. Raino na uwa da
Allah yayi musu alfarma suka sake samu,sai dukka wannan tsoron na sadiq ya gushe,ya koma tsaiwa da
jajircewa akan komai,saidai kuma ua biyo halin fu'ad na matsanancin miskilanci shariya da kuma maida
kansa kamar baya fahimtar abinda kake aiwatarwa. Dauke kai da banzatarwa akan abu idan baiso
ba,zaman kadaici da rashin son hayaniya ko doguwar magana. Farouq yana nan da halinsa,saidai ya ragu
sosai,kusan dukka sakewarsa cikin gidan ne,idan ya fits waje ya koma boss saidai cikin abokai kuma. Shi
dinma ya samu abokin tayi wato musaddiq,wanda shine copy dinsa,idan suna a gidan maida anna suke
kamar kakarsu,abu daya ne yake bata salama idan fu'ad yana nan,tofa nan daya,sunsan qaryarsu tasha
qarya,dole su shafa mata lafiya subar bakinta ya samu salama.
A boye musaddiq da sadiq suka fara zuwa zance abinsu. Ba wanda ya sani sai ranar da fu'ad ya
fahimta. Da wannan salon hukuncin nasa ya ritsasu a falo,kowanne ya rasa da bakin da zai masa
bayani,amma koda anni ta iskesu ana shari'ar goya musu baya tayi
"Ba wanda bazai iya riqe mace ba a cikinsu,tunda sama ta kasa,ai bai kamata qasa ta gaza ba" Ta bawa
fu'ad amsa. Ya fahimceta sarai,ya kuma fahimci anni dasu take shida farouq......kai tsaye ma idan an
tashi shi din za'a ce,don dama farouq din dab yake da bayyana nemansa gasu annin,shi dinne bashi ga
tsuntsu bashi ga tarko,bai kuma san ranar da zaiyi tsuntsu ko tarkon ba,don a yanzun baya jin duk
yarinyar da yace zaya aura din zai iyayi mata adalci,don a qasan ransa ko digo baya jin marmarin
aure,baya ma taba hange ko hasashen gashi da macen auren ko gashi a sunan magidanci......duk da cewa
shi kansa shaida ne akan jikinsa yakai geji yakai iyaka ya kuma kai maqurar buqatuwa zuwa ga diya
mace......duk da tarin yanayin da yakan tsinci kansa a ciki.....shi kansa yasan kowacce irin lafiya ake da
buqata yana da ita,don ba'a maganar cikakkiyar lafiya ma ga mutum ma'abocin motsa jiki. To amma
baisan dalili ba.....ko kadan sabgar bata gabanshi,hasalima!,zai.iya cewa bai taba jin soyayyar wata 'ya
mace a zuciyarsa ba......bai taba daga idanu ya kalli wata mace yaji ta burgeshi ba......bai taba zama koda
da minti daya ba....kaf rayuwarsa tunda ya mallaki hankalinsa wai yayi imagining aure cikin rayuwarsa
ba. A yanzu ya sake gina rayuwarsa bayan ginin da yayi mata shi yafi sawa a gaba,aikinsa kasuwancinsa
da sana'arsa sune budurwarsa kuma matarsa,baya da wani buri a yanzun illa ya sake zama gwani ta
fannin ayyukansa gaba daya.
*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*
*ZAFAFA BIYAR*
*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA
ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*
_DUNIYATA Huguma_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
*09033181070*
89825722
1000cf
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 45
________________________
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
*_kina ta ganin kaya kala kala online?,kinason siya amma kina tsoron damfara?,tsada ko rashin ingancin
kaya?_*
*_wannan tsoro da taraddadi ya yanke miki indai da HUGUMA CLOSET_*
*_muna da nau'ikan kaya kala daban daban bisa farashin da ba kowanne dan kasuwa ke iya bada
kayansa akan hakan ba_*
Shadda
Laces
Atamfa
Qawatattun handbags
Mayafai
Abayas da jallabiyas
Inner wears
Lafayas
_kai komai daya danganci kayan ado na fita kunya wa dan adam_
*_Me kike jira sallah na gabatowa?,ana can ana ruwan suturu daidai da qarfin kowa?_*
*_MASU REPOSTING DA MASU SARI DUKA BA'A BARSU A BAYA BA,KI SIYA KI SAIDA KI SAMU RIBARKI
HANKALI KWANCE,BA TARADDADIN INGANCIN KAYA KO WANDA KIKA BAIWA KUDINKI_*
__________________________
Yana da matuqar karsashi da qarfin zuciya......da kuma fuskantar dukkan wani goal nashi har sai ya
cimmasa ya kaishi qasa. Baya taba bari buri tsoro ko fargaba suyi masa iyaka ko shamaki......faduwa
kuma bata sanyashi yayi giving up,wannan shine sirrin nasarar da kullum yake dada samu.
Za'a iya cewa kai tsaye farouq hannun damanshi ne,don haka ba wani motsi ko mission nasu da
dayan bai ganewa koda bai gayawa daya ba,duk da cewa ma babu boye boye gaba daya a tsakaninsu.
Wannan ta sanya farouq ya jima da fuskantar fu'ad,idan magana kake ta aure ko soyayya to kada ma ka
fara kiran sunanshi a ciki,domin baya gane komai ta wannan bangaren. Yakan jima yana dubansa cikin
mamaki,ya bawa kasuwancinsa lokacinsa da rayuwarsa fiye da komai baya ga familynsa,wato shi sadiq
musaddiq anni da abba,kullum lissafinsa da target dinsa moving forward.....moving to the next step. A
hankali ya fara zolayarsa don gane gejin yadda idanunsa basa gane kowacce halitta da ake kira da DIYA
MACE,sai ya sake karatun nasa da kyau yadda ya kamata,har daga qarshe ranar yakai kusan biyu na dare
saman system yana duba wasu sabbin diamond da aka samu nasarar cirowa,yadda zasu sarrafashi da
kuma kamfani mafi dacewa da zasu kai.
Shi kam har yayi bacci ma kai na biyu ne,ya fito main parlor na sassansu ya sameshi zaune
dungurgur saman sofa yana fama da zazzafan coffee don hana idanunsa kamuwa da bacci. Farouq din da
mamaki yake kallonsa,saidai baice masa komai ba har sai da yaje fridge ya ciro ruwa me sanyi ya dawo
gefansa ya zauna
"Sannu bawan kasuwanci" Ya fada cikin gatse,gatsen da bai damu fu'ad ba saima maida idanunsa kan
ruwan hannun farouq din da yayi. Har ya dauke idanunsa kamar bazai magana ba cikin dabi'ar nan tasa
ta shariya da banzatar da abu,sai kuma ya dawo da dubansa kanshi.
"Kana da jarabar son aure.....amma kana kashe kanka da abubuwan banza da wofi.....kana namiji me
yake hadaka da kayan zaqi da sanyi?" Yayi masa tambayar fuskarsa a hade yana duban idanunshi.
Qaramar dariya farouq din ya saki yana qoqarin bude gorar hannunsa
"Kasan me?,nifa bazan iya rayuwar da kakeyi ba,duk wani abu me dadi ka haramtawa kanka ci sai d'ai
d'aiku,ka tattaro abubuwan da sam basu da dadi ko dandano a harshe kullum dasu kake
mu'amala......yanzu kalla don Allah" Ya fada yana nuna tray din gaban fu'ad da awannin baya kadan ya
gama amfani dashi.
"Gasashen zaitun.....hadin salad me man zaitoon,shayin ginseng,wolf Berry smoothie.....meye mai dadi a
ciki?" Ya fada yana yamutsa fuska.
Idanu kawai fu'ad ya zuba masa har yakai qarshen zancan. A nutse ya saki wani qaramin
murmushi da bai bayyana ba yana dauke idonsa daga kan farouq
"Dukka abinda ka lissafa yanxun kaje kayi binciken amfaninsa ga jiki da lafiya" Ya amsa masa yana jawo
wata takarda dake aje a gefansa yana son hadesu waje daya da stapler.
"Tashi don Allah ka tafi mr ciye ciye karka cikamin kai da bayanai.....kaci gaba da ciye ciyenka yadda kake
da hazaqar son kayi aure,auren zai baka amsarka". Dariya ta kubcewa farouq din harda buga qafa
tamkar ba dare ba
" To mijin aljana.....don dai na tabbatar zaiyi wahala kaidai idan aka kira me ruqiyya yayi maka ruqiyya
inajin mata hudu gareka cikin jinsin aljanu".
Duk yadda yakai ga pressure dinsa hade rai ko salon miskilancinsa farouq kadai ke saukeshi. Ya
addabeshi wasu lokutan har yaji kamar ya makeshi amma ba yadda ya iya dashi,don kaf duniya baya
gashi ba wanda yake masa karan tsayen da yake masa irin haka. Ko a yanzun ma sai da yayi silar fitar
murmushi daga kyakyawar fuskarsan nan ma'abociyar tsukewa da ba kasafai ta fiya fidda fara'a
"Kaga bakina alaikum na huta ai.....don wadannan matan na bil'adama......." Sai kuma yayi shuru ba tare
da ya qarasa fade ba. Ba kasafai ya fiya son tona abinda ke danqare a zuciyarsa ba,baisani ba ko Allah ya
nufeshi da rahama daya zare son aure ko son mallakar mace kwata kwata daga zuciyarsa ba?.
Dan kadan farouq ya kalleshi ta gefan idanu ganin ya dauko magana ya kuma katseta,sai shima yayi
shuru kawai bai sake cewa dashi komai ba.
Tun daga wannan lokaci idan yaso masa tsiya da shaqiyanci yakan kirashi da mijin aljana. Anni tayi
tayi ya daina amma ina,lamarin farouq sai a hankali,mugun shakiyyi ne idan yaso,idan kuma ya sakaka a
gaba ka saku kenan......amma kuma tamkar hawainiya yake,idan yaso canzawa zaka rantse da Allah bashi
bane matsokanin nan ba.
"Yana nan sunatayi shi da mutuniyar" Anni ta bashi amsa tana dariya qasa qasa.
Baki ya tabe yana bubbude warmer din dake jere kan dining din
"Wannan autar taki anni taci kai wallahi.....wai ita an gaya mata zama zamuyita yi da ita a gidan
nan?,baka gaya mata gaskiya wallahi" Ya qarasa maganar yana duban fuskar musaddiq cikin salo na
harara.
Dariyar ta kubcewa musaddiq ya kalleshi da kyau yana daidaita zamansa idonsa akan farouq
"Yanzu don Allah BB(big brother suke masa abbreviation),so kake ayita kada mata hanjin ciki?,duka duka
amna nawa take?"
"Allaaaaahu akhbar.....kaga masuyi don Allah,dama kana cikin masu lalatata a gidan nan......don Allah
kayita gaya mata damu zata rayu.....Allah ka sakata ne kawai a keken bera......itafa har yanxu bata da
hankali na lura......na godewa abba ma da yace sai taje ta raka nanna......tafiya duka duka sati biyu kawai
amma ta cika mutane da qorafin yhan yhan yhan......itafa gida zata dawo waye ya mutu waye ya
tashi.....shi kuma wancan mijin aljanar yana can yana sake daure mata qarqashi...."
"Sunan nan bazai fita a bakinka ba ko?" Ta sake jefa masa tambayar tana dubansa.
Gyara zamansa yayi yana wani tsuke gira,shi ala dole yana son zama serous.
"Allah dai ya bada haquri anni......amma shima ai anni ba sunan da yafi dacewa dashi sai
wannan.....banga alamar lafiyarsa qalau ba" Ya qarasa fada qasa yana fara serving kanshi da abincin da
yafi so. Idanu anni kawai ta tsura masa tana kallonsa ba tare da tace komai ba,ita kanta yadda fu'ad keyi
da lamarin yana tabata,ko a fuska ko kuma a aikace bai taba damuwa da ganin dukansu su ukun suna
shirin yin aure ne su barshi ba,yana shiga dashi akayi dukka maganganun da zaayi da iyayen yara,amma
shi yana zaune ba wani damuwa a gabanshi,saima lissafin yadda zaici gaba da juya kwabo ta koma dari.
"Kaga MAN.....ka koma gaya mata gaskiya,aurar da ita zamuyi da wurwuri.....ba zancan yin PHD a gidan
nan.....munason ganin jikokin 'yar uwarmu mace". Daga anni har musaddiq ba wanda farouq din bai
bawa dariya ba ganin yadda yayi maganar da gasken gaske har yana tabo hannun musaddiq din don ya
jishi da kyau,ya kuma basar ya soma cin abincinsa.
Na anni kawai idanu,tana tsarkake girman ubangiji da yadda yake halittar bayinsa da
mabanbantan dabi'u da kuma halaye. Yara hudu,mace cikon ta biyar amma kowanne da nasa halin da
dabi'ar. Ta sauke boyayyar ajiyar zuciya kunnuwanta suna sauraren hirarrakinsu. Bahaushe yayi gaskiya
da yake cewa DA D'A DA DUKIYA BA'A YI MUSU MUGUNTA,DON BA'ASAN ME MORARSU BA SAI ALLAH.
tana tuna wani lokaci can baya.....shekaru da suka shude,sanda ta tsoma qafafunta da sunan kome gidan
tsohon mijinta alhaji hamza. Yadda tasha baqar wuya kafin ta daidaita lamuran gidan ta kuma maida
kowa cikin hayyacinsa. Me babban suna tafi shan wuya akansa akan kowa,tasha gwagwarmaya kafin ta
samu nasarar cire wannan fushin baqin rai da kuma mummunan fenti da ya yiwa kusan kowa da yake
kewaye dashi idan ka dauke 'yan gidan nasu. Rashin yarda da rashin sakewa da jama'a wanda har yanzu
tana fuskantar ragowa da kuma tasirin wannan dabi'ar tattare dashi da bata gama barin jikinss ba. Wani
irin yanayi me ban tausayi da har yaso taba karatunshi.....boyayyen kuka duk dare da rashin bacci. Ta
dauki dogon zango cikin musu addu'a da neman daidaitar rayuwarsu. Tofi rubutu da addu'a dukka kafin
lamuransa su fara daidaita. Sai ta fuskanci kyara tsangwama ga duk macen da zata dososhi koda
qanqanuwar yarinya ce. Bata fuskanci yadda abun yayi musu!mugun tasiri ba sai bayan wasu shakaru
data haifa musu Aminatu amna me sunanta kenan.....haihuwar data tabbatar matsanancin rabo ne,don
ko a wasa bata taba tunanin wai zata sake wata aba wai ita haihuwa ba.
Da fari tsakaninsa da amna idanu ne kawai,baya ma zama.inda take bare daukarta,ta fahimci
kaman wata kakkaifar gaba ce tsakaninsa da jinsin mata,ita kadaice mace cikin miliyoyin mata da take
samun kulawa da qauna daga gareshi wanda ita dinma sai da suka debi shekaru yana dari dari da ita.
Bata tsananta tuhuma ba,tasan incident din daya faru dashi a baya akan mariya da mariya sune suke
hunting dinsa.
Wannan abun bai karye ba tsakaninsa da amna din har sai sanda ta fara laulayin haqori. Kashin
haqori matsananci daya sanya mata amai da zawo da yaso wucewa da rayuwarta. A ranar a kuma daren
har sun fidda rai da ita,tayi wani suma a hannunsa. A ranar taga gigicewa mai tsanani a tattare dashi,shi
daya ne yake da qwarin gwiwar daya dinga mata wasu abubuwa don dawo da mumfashinta,sai gashi
cikin ikon Allah ta dawo.
Tun daga wannan ranar kulawarsa a kanta ya zama na dabanne,sabo ya shiga tsakaninsu,ta tashi
ta ganshi a matsayin yaya kuma uban da bata da kamarshi.
"Kamar akwai inda zakaje ko?" Anni ta tambayi musaddiq da suke hira da farouq
*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*
*ZAFAFA BIYAR*
*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA
ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*
_TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_
_K'ALBIM Mamuhghee_
_DUNIYATA Huguma_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
*09033181070*
89825722
1000cf
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 46
____________________________
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
*_assalamu alaikum warahmatullah_*
*_kina ta ganin kaya kala kala online?,kinason siya amma kina tsoron damfara?,tsada ko rashin ingancin
kaya?_*
*_muna da nau'ikan kaya kala daban daban bisa farashin da ba kowanne dan kasuwa ke iya bada
kayansa akan hakan ba_*
Shadda
Laces
Atamfa
Qawatattun handbags
Mayafai
Abayas da jallabiyas
Inner wears
Lafayas
_kai komai daya danganci kayan ado na fita kunya wa dan adam_
_bisa farashin da zaiyi daidai da buqatarka_
*_Me kike jira sallah na gabatowa?,ana can ana ruwan suturu daidai da qarfin kowa?_*
*_ki dinga siya da kadan kadan kina saka kudin kina tara abinki har sukai sanda zaki karba?,ko ki siya
lokaci daya a kai miki_*
*_MASU REPOSTING DA MASU SARI DUKA BA'A BARSU A BAYA BA,KI SIYA KI SAIDA KI SAMU RIBARKI
HANKALI KWANCE,BA TARADDADIN INGANCIN KAYA KO WANDA KIKA BAIWA KUDINKI_*
_____________________________
Tana tsareshi da ido. Duba daya ya yiwa annin ya fahimci tambayar ta yita ne kawai bawai don tana
son sanin amsa daga bakinsa bane....aah,ta yita ne don tanason tunasar dashi wani abu
"Kamar zan fita din......amma kuma banason fitar" Ya fada yana kallon qatoton agogon dake manne a
bango.
"Amma dai ina fata kana sane da girman umarnin uwa ko?,sannan kana sane da girman
alqawari......haka kuma uwa uba baka manta dashi ba?" Dukka jikinsa ne yayi sanyi,sai yadan sadda
kansa qasa kadan. Lallai ba shakka inda ace dukka iyaye haka suke tamkar anni da zaiyi wuya.....za'a
tirza,hakanan za'a sha fama kafin a samu baragurbin yara cikin al'umma.
Kai ya jinjina,sai ya soma ture plate din gabansa,ya dauki wayarsa ya sanya gaban aljihunsa ya
miqe yana fadin
"Sai na dawo"
"Allah ya kiyaye......" Anni ta bashi amsa tana satar kallonsa. Tako ta ina ba alamun jin dadin zuwan da
zaiyin,ba wani sukuni walawala ko farinciki irin na da a sanda zai hadu da iyayensa.
Da kallon tausayi ta bishi dashi har ya bacewa ganinta. Ta janye idanunta tana sauke zazzafar ajiyar
zuciya,sai suka hada idanu da farouq dake zaune yana cin abinci a hankali.
"Daga musaddiq har muhammad tausayi suke bani har yanzu,har yanzu wannan tabon da aka barwa
rayuwarsu yana tare dasu bai goge ba". Kai farouq ke gyadawa yana duban anni
"Gaskiya kika fada anni......musaddiq nashi me sauqi ne,ba wanda abun ya yiwa illa matuqa yake kuma
taba halayensa da dabi'unshi har yanzu irin fu'ad......akwai fushi saurin daukan zafi da yawa cikin
halayensa......shariya rashin son yin magana ko hira da kowa,wanda yawancin lokuta idan irin hakan ta
faru nasan abinne ya motsa masa,shi yasa sau da dama nake maida kaina wani iri a wajensa saboda na
sama masa farinciki duk qanqantarsa". Kai kawai anni ke jinjinawa,har cikin zuciyarta tana jin ba
dadi,abun kuma yana tabata.
Wani gauron numfashi ta sauke tana ajiye wayarta data dauko wadda ta kasa juriya tana shirin
kiranshi kenan. Kacokam ta aza idanunta ga bakin qofa tana tsumayin qarasa shigowarsa tana jin yadda
yake gaisawa da ma'aikatan gidan faran faran. Irin sakewa da ta tabbata idan ya shigo ciki baya iya irinta
da ita.
Da sallama ta yaye kakkauran curtain din dake bakin qofar ya shigo. Ganinsa kawai da
tayi,zuciyarta kuma na ayyana mata cewa wannan din d'anta ne halak malak sai taji wata izza ta sake
daduwa cikin kanta
"Kina da wannan kadarar.....kina da wannan damar don me yasa zaki bari a qwace miki su cikin sauqi
haka?" Ta yiwa kanta da kanta wannan tambayar.
Gyara zamanta tayi sosai sanda ya iso ciki,ya zauna saman daya daga cikin kujerun yana dan
tsagaita dubansa daga inda take
"Barka da dare" Ya furta a nutse,har yanzun baya jin wani sabo shaquwa ko soyayya nata a tattare
dashi,yana jinta kamar kowacce baquwa......yana kuma jinta kamar kowanne baqon abu na rayuwarsu.
Qoqarin wadata fuskarta da fara'a tayi kaman yadda zuwaira ta shawarceta don samun isa ga
burika da muradanta cikin sauqi
"Ai na cire tsammani da zuwanka musaddiq......wai dama haka duniya take?,......na zaci komai girman
laifin uwa d'a yana iya yafeshi ko?" Ta fada murya a sanyaye. Idanunsa kadan ya daga yana kallonta,ya
kasa gamsuwa da ita har yanzu,yana jin inama ace yadda ta furta wadannan kalaman a bakinta haka
suke har cikin zuciyarta?.
"Kibar wannan maganar maamah,abune daya riga ya shude,kin wuni lafiya?" Ya maida maganar da
tambayar lafiyarta
"Alhamdulillah.....saidai yayanka ya watsar dani musaddiq,ya barni cikin buqatar rayuwa da abubuwan
da a zahiri ya cancanci ace nafi qarfinsu amma suna neman fin qarfina" Ta fada a karye.
Mamaki sosai ya sake lullubeshi har ya gaza jurewa sai daya daga idanunsa ya qarewa suturar
jikinta da kuma falon da take ciki kallo. Tana cikin ni'ima da wadatar da babu abinda ta nema a
rayuwarta ta rasa amma tana kiran abubuwa da dama sunfi qarfinta?. Anya kuwa da kyakkyawa da
kuma tsakakkiyar zuciya ta dawo cikin rayuwarsu?,anya wannan tsohon maqalallen halin baya tare da
ita?. Shine mutum na farkon da yafi kowa sanin cewa hammansa baya wasa da ci sutura sha muhallinta
da lafiyarta,bayan ya dauke duka wannan kuma da wani ajiyayyen salary na dubu dari duk wata,duk da
aqa'ida ba wata qwaqwarar buqata guda daya da ashekarunta ta yima rayuwarta saura. Hatta da man
fetur da ake zubawa motocinta guda biyu bai daukewa kansa ba,to me take nema sama da wannan cikin
dukiyar da aka sameta a sanda ta nisancesu?,cikin dukiyar da aka sameta a sanda ta gujesu?,cikin
dukiyar da aka sameta a sanda take can cikin duniya tana kalar rayuwar data zaba?,kalar rayuwar data
fifita sama da ta rayu dasu?.
"Bana jin akwai sauran abinda hamma ya rageki dashi maamah" Ya gaza jurewa sai daya fadi mata
idanunshi tsar a kanta zuciyarsa kuma cike da mamakin furucinta. Idonta itama takai kansa tana kallonsa
Ci gaba yayi da kallonta yana fahimtar abubuwa da dama tattare da ita,a yau kuma a yanzun sai
yaji shima ya shirya tambayarta
"Idan har ya miki kadan kuma hamma bai kyauta ba......wacce buqata kike da ita da zakiyi da kudi?"
Tambayar sak irin ta dan uwansa kenan......amsar kuma da ba zasu taba samunta a bakinta har abada
"Musaddiq......yanzu bayan ci sha sutura da biyan duka sauran buqatu da zasu taso Shikenan iya abinda
nake da buqata a matsayina na 'yar adam?,bayan ina da d'an da a kullum idan zai bani kyautar million
daya bazaiji komai ba a jikinsa daga abinda ya mallaka?"
"Maamah......kin taba zuwa da wata buqata kinaso ayi miki kaza?,ko a yiwa wane kaza wanda ba zallar
kudi zaki amsa ba da hamma ya taba qinyi miki?" Ya jefa matar tambayar yanason gane ainihin gaskiyar
da takeson lullubewa
"Kai musaddiq.....kalleni nan......dukkanku ke da fu'ad nina haifa abuna......banyi lalacewar da don zaku
yimin wani abu sai na zama tamkar almajira a wajenku ba....."
"Allah ya baki haquri ya huci zuciyarki" Ya fada kawai don kawo qarshen zancan. Can qasan zuciyarsa
babu gasgatawa ko yarda da ita ko kadan. Idan yayi rantsuwa ko kaffara bazaiyi ba,ba haka siddan
hammansa yaqi yarda ya sakewa maamah tsurar kudi ba,ya yadda dashi dari bisa dari,yana komai bisa
bayyananniyar hujja da kuma dalilai. Kawai dai mutum ne shi me tsananin zurfin ciki da
miskilanci,wannan ya sanya idan ya aiwatar da abu babu lallai ka fahimci don me yayin?,kuma bazai taba
zama yayi maka wani bayani ba game da hakan.
Shuru ne ya biyo baya na wasu mintuna,tanata qoqarin controlling kanta don har yanzu bata kai
ga cimma burinta na abinda takeson taji ba. Ta furzar da iska kadan sannan ta fara kiran daya daga cikin
masu aikinta.
"Ki sauke kayan abincin nan a nan....ko dining din zaka hau kaci?" Ta tambayeshi tana dubansa.
A zahirance so yake ya gaya mata ya qoshi,baya buqatar cin komai,amma ya tabbata fadin ba
abinda zai haifar sai wani rigima da tashin hankalin,don haka yadan gyara zamansa
"Kinji ai abinda yace". Suna zaune ta dinga sauke kwanukan abincin. Warms na alfarma masu tsananin
tsadar da ko a gidajen masu sukuni sai wane da wane.
Da kanta maamah din tayi serving nasa don buqatarta shine ya saki jiki yaci sosai ta yadda zata
samu daman yin magana dashi ta kuma samu duka information din da takeso.
"Bismillah sauko" Ta fada da salon bada umarni nakai tsaye. Bai musa mata ba ya zamo ya sauko din,sai
ya fara kai hannunsa ya dauki glass cup na lemo yana juyashi a hannunsa.
"Muci tare ko?" Kai ya gyada kawai yana duban kwanon. Komai yayi masa banbarakwai. Ko a shekarun
baya da suke da qananun shekaru ya iya abinda qwaqwalwarsa zata iya riqewa baya jin sun taba zama
kwano daya,sai yanzun da ya zama cikakken mutum?. Ko a baya sanda bai kammala iya cin abinci ba
idan ta zuba musu ta tura musu ta shiga sabgar gabanta hamma ne ke zama ya bashi komai zafinsa har
sai ya qoshi.
Hira take sako masa a hankali a hankali,tana cin abincin yana juya cokalin kawai a ciki bayan ya
dire cup din lemon.
Sai bayan data soma karantar kamar sakin jiki tattare dashi sannan ta aje nata spoon din tana
dubansa cikin murmushi
"Ya akayi kai da dan uwanka musaddiq wanda duk duniya bashi da kowa bayan kai amma ka nesanta
*ZAFAFA BIYAR*
*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA
ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*
_K'ALBIM Mamuhghee_
_DUNIYATA Huguma_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
*09033181070*
89825722
1000cf
*_H U G U M A_*
PAGE 47
"Ya akayi kai da dan uwanka musaddiq wanda duk duniya bashi da kowa bayan kai amma ka nesanta
kanka da kalar sana'arsa ka maida kanka baya ta hayar sanya jikinka a al'amura ta harkar gona?,bayan
sana'ar ba taka bace,gadon gidan Alhaji hamza kibiya dinne zasu daukeka su cusa ka?,sannan su raba
dansu da fu'ad kai su tsigeka daga gareshi?,wanne irin ragon azanci ne wannan shirme da
shashanci?,sannan wannan kadai ya isa ya nuna akwai mummunar manufa da qulli cikin zuciyar amina
da manufa aka shirya wannan".
Maganganunta sunyi masa girma qwarai,mamaki kuma ya lullubeshi har sai daya tsaya kawai yana
duban yadda maamah din ta haqiqice.
".....bazan yarda ba a rabamin kan yarana,bayan a mahaifa guda suka kwanta......don wannan zalunci ne
kawai,duk yadda zakayi ka nema komawa sashen da dan uwanka yake aiki,shima kuma zan masa
magana kaji?" Sai ta qarashe kuma cikin kwantar da harshe saboda magana ta gaba da takeson yi.
"To" Kawai ya iya cewa da ita,ya sani basai an gaya masa ba,maamah din tayi nisan da batajin
kira,hakanan dukkan wani bayani da zaice zaiyi mata yana zaman bata lokaci ne kawai a wajenta.
"Yanzu bayan kamfanin diamond ai ina sanya ran zuwa yanzu addu'ata ta cicciba Muhammad izuwa
mallakar wasu boyayyun mafanunnukan ko?" Ta fada tana murmushi tare da tsare musaddiq da kallo.
Dubanta yayi sosai,yana ji har cikin zuciyarsa da gangar jikinsa bai gamsu xa yanayin tambayar
tata ba,don haka girgiza mata kai kawai yayi
"Bansan komai a kanshi ba maamah tunda ba sashe daya muke dashi ba" Wani abu ne ya tsaya mata a
wuya,amma sai tayi qarfin halin danneshi ta amsa masa da
"Haka ne......amma dai baka ce bakasan qarfi da nauyin kudaden da suke shigo masa ba ko?" Sake daga
kai yayi yana dubanta zarginsa yana sake tabbata
"Bana ce ba maamah.....abune da ya shafi sirrinsa kuma ba a qarqashinsa nake aiki ba.....ni ina qarqashin
farouq"
"Eh to.....maganar gaskiya sai yanzu na fahimci kimiyyar da ta sanya amina tayi kutin kutin din cusa
danta wa Muhammed kai kuma ta rabaka dashi.....kana jininsa wanda bashi da na biyunsa a duniya
amma bakasan komai nasa ba?.....wanda ni nayi imanin a yanzun inda zan zaunar da shi saddiqun nayi
masa ire iren tambayoyin da nayi maka din yana da amsar kowacce fes?.....wannan itace hanya mafi
sauqi da zata samu salwantar da fu'ad da dukka abinda ma ya mallaka". Idanunsa ya runtse yana jin zafin
mummunan zaton da maamah din ke jifar 'yar tahalikar dashi.....matar data zame musu bango
majingina,matar data zabi farincikinsu akan nata.....matar da silarta ne a yau suka zama dukkan abinda
suka zama din.....suka kawo izuwa matakin da suke kai a yanzu......matar da banda ita da yanzu shi da
muhammad din duka da take taqama dashi ba'asan a wacce shiyya nahiya ko yanayi suke ba.
"Maamah..." Ya fada yana bude idanunsa a kanta ba tare da ya shirya tsaida maganarta ba.
"Duk yadda kike tunanin anni fa ba haka take ba.....idan baki godewa anni ba bai cancanci ki jefeta da
mugayen zato ba......kamfanin nan da rayukanki suke baci akai asalin diamond din da aka samu ba
hamma bane kawai ya sameshi ba.....a lokacin suna tare da BB farouq......"
"Amma shi ya haqo shi kuma ya samu nasarar tsira dashi.......ka dauka bansan dukka wannan ba?" Tayi
maganar tana tsareshi da idanunta da suka cika da bacin rai. Lallai sai sun nuna mata fifikon matar can
akanta?,bayan bata da masaniya akan sanda ta dauki cikinsu bare kuma haihuwarsu?.
"Eh hakane.....amma shi BB farouq baida sha'awar harkar diamond noma yafi so shi yasa......"
".......shi yasa aka fidda haqqinsa aka bashi nasa kason......dukiya ta zama ta muhammad sh
kadai......amma duk da haka basu qyaleshi yana amfana da abarsa shi kadai ba.....saboda nasa kason da
nasa bangaren na haqar ma'adanai yafi noma albarka da kawo samu,shi yasa suka tattare shi suka kuma
dora masa dukan lalurarsu suna zuqeshi sannu a hankali.....suka kuma nesantaka dashi.....suka haramta
maka sanin komai daya shafeshi ta cusa danta" Ta qarashe maganar da wani irin ciwo da emotiona daga
zuciyarta
"Maamah....." Ya kira sunanta yana son dakatar da ita. Baya qaunar ko kadan wadannan kalaman marasa
dadin sauraro suna fita daga bakinta zuwa kawunan mutanen da suka yiwa rayuwarsu tsaiwar da babu
wani mahaluki daya taba yinta
"Ni na zabi fannin noma da kayan abinci......basu suka sani ba....ba wanda ya bani shawara....."
"Musaddiq!.....ina fada kana fada duk akan mutanen can?,to waishin ko zaka koma cikin aminatu ta sake
haifarka a matsayin danta bani mariya ba?". Maganar yaji tayi tsauri da yawa,kuma ya sani uwa uwa ce
komai lalacewarta,hakanan ba'a canzawa tuwo suna,don haka ya miqe tsam,don dama a qagare yake da
wannan zaman da baiga ma'anarsa ko alfanunsa ba. Ya dauka zasuyi hira ne irin ta d'a da uwa?,ya dauke
zata tambayeshi bayan ta barsu yaya suka rayu?,ya dauka zata nuna nadaman barinsu da tayi sun basu
gama zama mutane ba?,sai gashi gaba daya hasashenta da hangenta ba'a nan yake ba?,da gaske ne
abinda zuciyarsa take raya masa ta biyo DAUKAKARSU DA DUKIYARSU NE?.
"Allah ya baki haquri ya huci zuciyarki,sai da safe.....na barki lafiya" Ya fada yana juyawa a hankali yana
fita daga falon zuwa farfajiyar gidan.
Da kallon takaici ta bishi,shi kansa me sukuni da wadata ne wanda zai iya kashe mata ko nawa
take buqata ballanta a gangaro kan muhammad,mahaukatan kudade ke shigo musu daga harkar noma
kayan abinci da sauran kayan masarufi da sukeyi,kuma su rabasu cikin qasashen Africa dama qasashen
qetare. Tana da dukka information daidai gwargwado a kansu.....amma sai gashi wadatar kowannensu
yanason zame mata hoto.
Yadda ranta yake a bace sai zama ya gagareta,takai ta kawo kusan sau uku tana ji har cikin
zuciyarta ya dace ta gaggauta daukan mataki,ya kamata tayi wani abu akai kada komai yaci gaba da
tafiya a haka. Daidai sanda takai dab da qofar taji horn na mota da kuma shigowarta farfajiyar gidan,bata
bi takai ba amma zuciyarta tana mamakin baqon daren da sukayi.
Mintina uku kawai tayi sallama cikin falon. Sallamar data sanya maamah din waiwayowa tana
amsa mata fuskarta babu walwala.
Sanye take cikin wani lafiyayyen lace ruwan zuma. Kallo daya tak zakasan cewa ba na qananun
mata bane,ba kuma qananun kudi aka sanya aka mallakeshi ba haka dinkin boubou din da aka zuba
masan. Zagayayyen dauri ne saman kanta da zai gwada maka adadin wayewarta da kuma zurfinta a
sanin data yiwa duniya. Mayafinta na yafe a kafada daya,daga hannayenta har zuwa wuyanta adon sarqa
zobe da bangles ne da babu ko tantama da shakka na gold dinne. Ita din idan ka kalleta baifi ka bata
shekaru arba'in da biyar ba,saidai kuma ta dara hakan,don a yansu tana dosar cika shekaru sittin ne a
duniya.
Daga bayanta wata macece wadda duka ba zata haura shekara arba'in ba. Riqe da wata
kyakkyawar handbag wadda babu ko tantama jakar matar dake gaba ne saboda dacewa matuqa da tayi
da kayan jikinta.
Maimaita sallamar tayi a karo na biyu tana duban maamah fuskarta a sake. Wannan ya sanya
maamah din tayi qoqarin sakin tata fuskar gami da sakaya damuwarta a gefe,cikin mamaki da tarba me
kyau ta matsa gareta tana tararta
"Tun shekaran jiya fa?,gajiya nayi ma na gudo,amma ason dan ahalan sai farkon sabon wata zamu dawo"
Ta furta tana neman wajen zama.
"Yadda ya kamata kuwa.....wai nikam musaddiq nake gani yana fita sanda nake shigowa da mota?". Dan
tabe baki kadan maamah din tayi sannan ta amsa cikin salon rashin bawa maganar muhimmanci
"Shine mana"
"Ko ya ganekin ma babu lallai ya miki magana ai harira" Ta amsa mata boyayyar damuwar fuskarta tana
bayyanar da kanta.
Kallon tsanaki hajiyar mamallakiyar sunan harira ta yiwa maamah kafin tace
"Ban gane me kike fada ba mariya" Qarasa bawa sauran boyayyar damuwarta qofa tayi ta fallasa
kanta,don tambayar sa harira tayi mata ta zama tamkar susa ce tayi mata akan ciwonta
"Ina da damuwa harira.....ina da damuwar da har kwanan gobe na gaza gano maganinta".
A nutse hajja harira ta waiwaya ta dubi 'yar aikinta,wadda ke tsaye daga gefe,tunda suka shigo
taketa faman gaida maamah din amma bata ma jita ba bare ta amsa
" Ajiyemin jakar ki fita daga waje ki jirani" Ta fadi mata. A ladabce ta ajiye jakar sannan ta juya da hanzari
tana ficewa,abinda ya bawa hajja harira damar maido hankalinta ga maamah
"Nayi tunanin kawo yanzu kinyi nisa daga dukkan wani abu me suna damuwa daga randa dan cikinki ya
zama mamallakin kamfanin diamondchore?"
"Daga sannan sabuwar damuwa ta fara hajja harira" Maamah din ta furta ranta yana matuqar quna
"Idan na kalli yadda kike fantamawa hajja sai na sake tabbatarwa kaina lallai akwai aiki a gabana......aikin
kuwa shine YADDA ZAN MALLAKE 'YA'YANA". Wani irin duba hajja hariran take mata,sai kuma ta kyabe
baki
"Keda wanne baccin kikeyi da baki aikata hakan ba mariya?,wanne gangancin ya kaiki?,bakisan daga
ranar da Allah ya yiwa 'ya'yanki arziqi ba.....akwai tarin mutane da dama da suke marmarin juye
matsayinki su haye kai ba?.......kin ganni nan mariya?,kaf 'ya'yana babu wanda ya isa ya aiwatar da wani
abu komai girmansa kuma komai qanqantarsa ba tare da sanina ko yardara ko sahalewata ba.....ke koda
matansu ko 'ya'yansu zasu yiwa kuwa sai da sanina da yardaya,a cikinsu babu wani gida da bansan me
yake gudana a cikinsa ba 24hrs......yanzu haka katafaren gini na sanya sukeyi na bai daya duka zamu
zamana a muhalli guda....." Kai kawai maamh ke gyadawa,a yau ta yarda ta miqa wuya ta kumayi
surrender kan cewa harira ta fita shu'umanci,iya yadda tae bada.labarin cike da izza da alfahari kawai ya
isa gaya maka gaskiyar haqiqanin zahirin abinda ke faruwa kenan......jikinta ya isa ya sake qarfafa maka
zancanta.....tsanin alfahari da takeyi yayin bada labarin kuma zai gaya maka yadda take jin dadin yadda
take tafi da rayuwarta.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 48
"Inaso na zama uwa mafi gata a duniya harira,inason na zama uwa mafi izza akan yaranta......inason na
zama uwa mafi zama abar alfahari abar nunawa a duniya....inason 'ya'yana su dawo qarqashina.....na
mulkesu kaman yadda ubangida yake mulkar bawansa......su zamana a tafin hannuna kamar yadda jariri
sabuwar haihuwa yake zama a hannun mahaifiyarsa".
"Lallai mariya burinki me girma ne......amma dai kinsan ki baro kari tun ran tubani ko?,ko mu da muka
raini yaran har suka girma muka aurar dasu,bamu gusa ko nan da can ba muna gabansu suna gabanmu
sabunta ayyukanmu mukeyi akai akai.......munayi matansu sunayi,wanda keda nasara shike samun
rinjaye.....ballantana ke,yaranki ina da tabbacin suna buqatar gagarumin aiki kafin samun saituwarsu
akan bigiren da kikeso".
"Abinda ya wuce ya wuce hajja harira.....yanzu meye abinyi?" Gyara zamanta tayi sosai tana bawa
maamah dukkan hankali da nutsuwarta
"Akwai plans guda biyu,plan A da plan B......idan A baiyi aiki ba zamu wuce zuwa na biyu"
"Yauwa......na farko akwai wajen mutumina da zan kaiki wanda shi yakemin aiki akan komai da
kowa......"
"Kai....kai.....amma kin gama min komai" Maamah ta fada tana gyara zamanta da kyau fuskarta na
washewa da madaukakiyar fara'a,saboda ta hangi zuwan nasararta a nan kurkusa......ta hangeta tana
fantamawa fiye da yadda hajja harira ke fantamawa din.
"Ba komai fa.....zaman tare ai ba qarya bane....zaki zayyane masa dukkan abinda kike da buqata wanda
nake da imani a kansa mallaka sai yadda kika juyasu.....akan mansur ya fara yimin aiki,lokacin da yayi
aure sai na fuskanci wani abu,maganata qasa take da maganar matarsa,dukkan umarni da zabi nata ne
sai abinda taga dama sai kuma abinda tace.....a sannan na farga,amma in gaya miki inayi yarinyar nan
tana nata har daga qarshe na hadu da DAN DUMA....tuni na saka ya qara mata wuta a gidan,mansur ya
saketa tayi gaba,tun daga ranar dukkan wanda zaiyi aure a cikinsu nice nake zaba masa yarinyar da
nakeso ya aura din,wadda zan cimma buqatuna ta hanyarta,wadda zan juyata ba musu ba kuma
damuwa......to kema wannan shine plan B dinki idan na farko yaqi aiki"
Shuru maamah tayi tana jinjina kai,lallai duk iya yadda take ganin mulki da isa da kuma izzar
hajja harira ta wuce nan. Wannan shine cikakken ma'anar HAMSHAQIYAR UWA ko kuma CIKAKKIYAR
UWA. Idan so samu ne tana son kamar haka ko sama da haka
"Amma banajin musaddiq zai qara watanni shida ba tare da yayi aure ba"
"Ko yau yau zaa daura auren kina iya ruguzawa,ki maye gurbinta da wadda kikeso" Ta fada kanta tsaye
cikin confidence.
"Waye babbar damuwarki a cikinsu?,muhammadu?" Kai ta jinjina. Tafi damuwa da kamashi a hannu fiye
da musaddiq. Tasan waye fuad din,yana da tsauri da tsananin da ita kanta tayi imanin mafi rinjayen aikin
a kansa zaa gabatar
"Haka ne wannan" Ta fada tana murmushi,tana jin cewa qarshen matsalarta yaxo,tana jin cewa lokaci
yayi da zata cika muradanta
"Yaushe zamu tafi zuwa wajen DAN DUMA?,kinsan ba'a bori da sanyin jiki" Ta karkata tambayarta ga
hajja hariran cikin zumudi da farinciki,tana jin bacin ranta yana zagwanyewa.
Tunda suka fito daga wajen a cikin jikinta kawai takejinta uncomfortable. Haka kawai take jin kamar
akwai wani abu,tayi dukkan research da idanunta hankali da kuma tunani bata ga wulgin kowa
ba,hakanan bataga alamun ana bibiyarsu ko wani abu da yayi kama da hakan ba. Saidai har suka soma
nisa da wajen bata samu nutsuwa ba,abinda muddin ta soma jinsa a jikinta zaiyi wahala idan baby
afkuwar wata matsalar.
"Me napep idan zaiyuwu ka kaini madabo.....zan qara maka wani abun" Tacewa me abun hawan. Malam
ne yaketa fado mata a rai,dattijo kuma kamilallen mutumin,ma'abocin nutsuwa karamci da kuma ilimin
addini.
Asalin haduwarsu ta fara ne a ranar da zasu rabu da ameen,daya daga cikin mazan da suka taba
shiga rayuwarta dama tarihinta. Abun yaso ya kwabe mata har ameen din yaso fahimtar ainihin wace ita
ba tare da takai ga fita daga layin ba. Ya sanya aka biyo sahunta tiqa tiqan qattin dake gadin qofar gidan
nashi harda rakiyar karensu guda daya.
Malam din shi ya musu kaca kaca,ya kuma hada harda ameen din daya tako da kansa,ya nuna
masa daraja da martabar mace,sunaji suna gani yayi saving nata a hannunsu ya wuce da ita sukaci gaba
da takawa a qafa har titi.
Ita dinma a hanya bai qyaleta ba,ya dinga yi mata fada bawai don ya fahimci wacece ita ba?,ko ya
fahimci ainihin abinda ya hadosu. Donme tana diya mace zata bari takai gefin magriba a irin wannan
unguwannin?. Haka kawai taji ranta ya nutsu da dattakonsa da kuma addininsa,rana ta farko da wani ya
taba yi mata fada irin wannan tun bayan shudewar iyayenta. A daren ranar tayi kuka tayi kuka,kukan
kuma kukan dadi ne na yadda yau aka samu mutum qwaya daya daya tsaidata da zuciya daya yana mata
fada kanshi tsaye. Tun daga wannan ranar malam din ya zame mata daya daga cikin mutanen da suke da
martaba a idanunta. A duk lokacin da kudi suka samu takan dauki wani abu tayi tattaki taje ta gaidashi,ta
kuma bayar wa almajiransa tace ayi ma iyayenta da suka rasu sadaka.
Matarsa tana da matuqar kirkin da ta dauketa kamar diya kaman yadda malam ya dauketa diya a
wajensa. Duk sanda zataje gidan bata gaza fahimtar wasu abubuwa daga sabreen. Macace mai matuqar
hikimar da sai da takai daga qarshe ta karanci wace sabreen din,sai ya zamana itama bata fiya boyewa
inna komai ba muddin ta tambayeta din,gidan sai yake zame mata wajen samun nutsuwa a wadansu
lokutan.
Unguwar madabo,daya daga cikin tsaffin unguwanni dake birnin kano,wadda take da dadadden
tarihi. Hakanan ta tara malamai da masana addini masu yawan gaske.
Tsukukun loko ne da ko adaidata sahun a matse yake shiga,wannan ya sanyata ta nemi ya ajiyesu
daga bakin babban lokon da zaka karya ka shiga qaramin. Ta bude jakarta ta sallameshi,sannan suka fara
takawa ita dasu zuwa ciki.
Tun a rumfar dake qofar gidan ta tabbatar malam baya nan,don babu tabarmin karatu,hakanan
daliban nasa sai jifa jifa kowa yana sabgar gabansa,don haka kai tsaye suka wuce zuwa ainihin cikin
gidan.
Da sallama a bakinta suka kutsa kai,gidan yana nan kamar kullum cike da tsafta. Ba kowa a filin
gidan sai hayaqi dake fitowa daga kitchen da alamu ana gab da kammala tuwon dare. Yaransu bakwai da
malam,maza hudu mata uku kuma dukkansu sun aurar dasu,don haka inna ce kadai ke rayuwa cikin
gidan,sai babbar jikarta da aka kawo mata don ta tayata zama.
Sake sallamar tayi,kusan lokaci daya aka amsa mata daga kitchen din da kuma rumfar dakin inna.
Cikin qasa da second daya wadda ke kitchen din ta fito. Matashiya ce da duka duka bata wuce sa'ar huda
ba,murmushi sosai take saki,ta baro cikin kitchen din tana goge hawayen fuskarta da hayaqi ya sanya
mata tana takowa
"Inji maqi baqo ko rumasa'u?" Sai ta saki 'yar dariya tana kamo haneefa
"Muje yau inna taga su auta,tanata zancanku tace kwana biyu shuru,gashi batasan muhallinku ba bare ta
binciki ko lafiya?,layinki Kuma kwata kwata baya shiga" Ta qarasa maganar tana riqe da hannun haneefa
wanda tuni sukayi gaba zuwa dakin innar.
Sai a sannan da rumasa'u tayi zancan layinta baya shiga ma ta tuna yana daya daga cikin
layukanta da suka tafi hutu,sai ta taka a hankali tana bin bayansu zuwa ainihin falon innar.
Dare dare ta samu haneefa gefan cinyar inna. A duniya gidan yana daga cikin gidan dasu haneefa
din keson azo,don sai ya kasance musu kamar wani gida daya qwaya tak na 'yan uwansu da suke iya
ziyarta su kuma sake,sakewar da basa iyayinta cikin ainihin gidan mahaifinsu.
"Wa'alaikumussslam.... .ina nan ina tuhumar amaryata me takeci naga tana ta tsaho?,kunyi nisan zango
wannan karon AMEENATU(real name dinta kenan)". Murmushi ta kuma saki,a duk sanda innan ko
malam sukayi kiranta da sunan ba wanda ke fado mata a rai sai mahaifinta. Shike yawaita kiranta da
sunan,sunan da ya kasance na qanwa ga mahaifinsu guda daya tak da aka haifa a tsakanin su maza su
uku,tazo kuma ta rigasu rasuwa a wajen haihuwa tabar nata yaran mata duka su uku.
"Kuna raina inna....abubuwa ne suka sha kaina" Ta fada tana zama itama.
"Malam yau duka bai zauna ba,ya tafi kasuwar qauye,amma yana hanya nasan in sha Allahu".
Kamar kusan kowanne lokaci idan sunzo gidan,komawa take 'yar kallo,nadra haneefa harma da
hudan suke sabgoginsu.
Lumshe idanunta tayi tana sauke boyayyar ajiyar zuciya. Ta tabbatar yau ta faranta musu ta kuma
rage musu kewa qunci da takurar zama waje daya. Tana so ta dinga kaisu guraren da zasu dan sha
iska,amma tana tsoron koda da kuskure suga wani abu da zai iya affecting tunaninsu.
Suna matuqar son a zo gidan,amma kuma duk dadewar da za'ayi ba'azo din ba ba zasu taba tada
mata zancan ko suyi qorafi koda kuwa sau daya ba,har sai ranar da sukazo din.
A nan sukayi sallar magariba,sukaci kuma tuwon dare. Suna haramar tafiya malam din ya dawo.
Sosai shima yaji dadin ganinsu,ya bude kuma duk abinda yazo dashi din kama daga
rake,gyada,quli kabewa,dinya da sauransu ya diba musu. Walwalarsu ta dadu sosai a sannan,duk sai da
suka fice da zummar zasu tafi ya rage saura Sabreen din,ta xuge jakarta ta fiddo kudi ta aje gaban malam
"Malam ayimin sadaka,sannan ayi mana addu'a". Kudin ya kalla sannan ya kalleta.
"Idan kin fita waje ki raba musu da kanki kamar yadda aka saba" Ya tareta
"Malam don Allah kayimin alfarma ko rumasa'u ta raba musu,tabbas don dare yayi ne da bazan karya
maka tsarinka ba,malam kai kemin fadan kaiwa dare a waje" Ta fada murya a karye. Tanason masa
ihsani,amma mutumin yana da wani irin kamewa da gudun duniyar data tabbatar bazai karbi komai nata
ba
"In sha Allah malam" Ta fada tana yin qasa da kanta kunya da nauyinsa suna kamata. Tana jin kamar
inna ta gaya masa wani abu a kanta ko zata gaya masa,saidai ta sani ko daya innar nada cikakkiyar
kamalar da bazata taba fadin sirrin wani ba
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 49
Tunani ne kala daban daban cikin kanta sanda suke abun hawa har suka isa gida.
Banda hadiyya data samu tana zance a farfajiyar gidan nasu bata hadu da wani babba ba sai yara
dake dan kai kawo a tsakar gidan nasu. Zuciyarta a karye take bude musu qofar dakin. Wannan shine
tabbacin basu da wani sauran gata.....ba wani wanda ke tsaye yana jiran dawowarsu......babu wani da zai
tambayi ina sukaje?,me yasa suka dade wuni sur a waje?,ba wani me musu barka da dawowa,dasu dawo
da kada su dawo duk daya.....ire iren wadannan abubuwa ke qara mata wata qaqqarfar zuciya tare da jin
cewa.....ZATA SADAUKAR DA TATA RAYUWAR don samarwa rayuwar qannenta gobe me kyau.....zata
zame musu makwafin uwa da uba,dukkan wuya da dadi.....zata hanasu dandanar duk wani kalar
baqinciki na rashin gata dama rashin abun kulawa da rayuwarsu.
Dukansu a qoshe suke kuma a gajiye,don haka basu jima ba kowacce ta nema wajen kwanciya,don
dama ita haneefa suna shigowa ta bingire a wajen.
Sau biyu tana yaye labulen tana duban tsakar gidan nasu. Wanka takeso ta fita tayi saboda yadda
gajiya kebin jikinta,uwa uba ma kuma ita din tun asali mutum ce data saba da yin wanka da dare kafin ta
kwanta,saidai kuma daga baya abun ya zame mata qalubale babba,saboda kallon da ake mata da wasu
idanu na daban.
Yadda ta fita dinnan ta wuni a waje ba zata iya kwanciya haka ba,don haka taci gaba da dabuwa.
Akwai daukewar qafafu sosai,wanann ya bata daman cire kayan jikinta ta daura zani ta kuma lullube
sassalkan gashinta da babban towel,ta dauki kayan wankanta.
Tana shirin fita nepa suka kawo wuta,don haka ta tsaya ta kashe solar din dakin ta maida musu
nepa sannan ta fito.
Ta tsaya daga bakin famfonsu tana tarar ruwa. Tsakar gidan tarwai da haske,kuma tsaf tsaf
dashi,dabiar gidan qwaya daya tal dake burgeta,wanda idan ka dauke wannan babu wani abu dake
burgeta cikin gidan dama jama'ar gidan gaba daya.
Allah yasa har ta gama tarar ta wuce wankan ba wanda ya fito. Ta kammala ta nade jikinta da
zanin ta dauro towel din a sama ta fito.
Tana duqe baqin famfon tana daura alwala. Bude toilet din wankan da akayi ya sanyata daga kai.
Sukayi idanu hudu da ita,saita miqe sosai ta tsaya maimakon dazun da take duqe tana daura alwala.
Kallon bibo din takeyi kamar yadda itama ita take kalla,tun daga qafafunta har zuwa kanta da
yake lullube da towel.
"Ha'illallahu.....mahammadurrasulillahi......ke duniya ina zaki damu?,aah?yanzu wankan ma sai kinzo
gida?" Bibo taja qaramin salati sannan ta kama haba tana sake qarewa sabreen kallo.
Wani abune yazo ya yiwa sabreen tsaye a wuya,ta lumshe idanun takaici. Ta gama fahimtar
zahirin abinda bibo ke nufi......ta kuma gama fahimtar abinda inda ta dosa,saidai kafin ma ta sake daga
qafarta ta sake jin muryarta
"Kiji tsoron Allah 'yar nan......ki daina sanyawa mala'iku suna tsaida iyayenki cak cikin kabarinsu......yanzu
wannan wankan....." A fusace da kuma wani irin zafin nama ta waiwaya tana duban bibo,abinda ya sanya
towel din kanta zamewa sumarta ta fito.
Bata qarasa ba itama sai tabi kan nata da kallo. A bushe yake ba kuma alamun damshi ko
lema,hasalima ta nannade doguwar sumar tata da tayi gado ta uwa da uba a tsakiyar kanta ta cusata
guri guda,wannan ya sanya bibo din hadiye abinda taso fada din.
"Ke zaa cewa kiji tsoron Allah,kuma zan maimaita miki kiji tsoron Allahn" Ta fadi da ita a nutse sannan ta
fara takawa tana dosar dakinsu.
Idanma tace zata riqe zafin da qirjinta yakeyi da suya to tabbas ta yiwa kanta qarya,don haka ta
sulale saman kujerar falon ta saki wani marayan kuka.
Bibo na daya daga cikin qalubalen rayuwarta,bibo na daya daga cikin mutane na gaba gaba da
suke mata wata irin adawa mara fasali ba tare da tasan meye ne ta tsare musu ba. Ta jima a wajen tana
kuka har sai da fuskarta tayi wani pink pink,sannan ta samu ta sauya kaya taja jikinta zuwa kan gadonta
ta kwanta tana rufe idanunta tare da sauraron bugawar jini daga kanta wanda keson komawa ciwon kai.
Sassanyan ringing dinnan shine ya sakata bude idanunta. Shaf ta mance da batun wayar sai yanzu
da tayi kuka. Tunawa tayi tayi alqawarin kai wayar a yau,kada ma su tsammaci ko ta gudu da
sune,wannan ya sanya ta miqa hannunta qasan pillow din data ajeta dazu ta dauko da nufin dagawa ta
basu uzurin gobe in sha Allah aje a karba.
Bata wani tsaya bata lokacin duba me kiran ba,tunda tasan koma waye zai kira a irin wannan
lokacin tabbas makusanci ne,don haka ta shafa ta daga ta kuma Kara a kunnenta.
"Assalamu alaikum anni?" Ya furta cikin husky voice dinsa dake cakude da wani irin nannauyan sauti
dake nuna izza da zatin mamallakin muryar. Yayi sallamar a sanda yake tsakiyar system da kuma tarin
tarkacen takardun dake dauke da plan na ginin sabon kamfanin samar da kayan qyale qyale na mata
mafi tsafa da daraja da za'a dinga qawatashi d wani yanki na diamond d gold.
Wani yankewa gabanta yayi ya fadi,zuciyarta kuma ta buga sosai har tana jin sautin bugun cikin
kunnuwanta. Batasan dalili ba batasan kuma me yasa taji hakan ba,sai ta buda bakinta a hankali da
muryarta da tayi nauyi saboda nauyin dake cike a qirjinta
"Ba ita bace". Shuru ne ya biyo bayan fitar sautin nata. Ita tana bawa kanta tabbacin wancan mutumin
ne daya kira duba da shurun da aka sakeyi mata kaman dazu,shi kuma kwanyarsa tana son alaqanta
sautin da muryar mara kunyar yarinyar nan data dag masa waya.
Kusan a tare suka daga wayar daga kunnuwansu. Ta samu tabbacinne ta hanyar karanta sunan
dake yawo saman screen din.
Sauke wayar yayi daga idanunsa,yaja siririn tsaki yana kashe wayar. Sautin tsakin yakai mata har
kunnenta,wani mummunan baci taji ranta yayi. To ita meye nata a ciki da har zai bita da tsaki?,waye
wannan daya cika izza haka?,wanne irin mutum ne me izgili da rashin sanin daraja da martabar dan
adam?,don kawai a bisa kuskure wayarsu ta fado cikin kayanta sai ta zama abar wulaqantawa?. Samun
kanta tayi da latse wayar kawai ta kasheta gaba daya ranta yana suya,cikin ranta kuma tana yiwa kanta
alqawarin a gobe wayar ba zatakai sha biyu na rana ba a hannunta zata kira busari yakai musu duk inda
suke.
"Wanne irin wulaqanci ne da rashin sanin abinda kukeyi da zaku ci gaba da barin wayar anni a wani
wajen?" Fuad din ya furta daidai sanda ya kira musaddiq.
"Kayi haquri hamma,ta fadi inda za'a karba anje ba'a samu ba,anyita kiran wayar kuma ba'a dagawa".
"Koma meye banason na sake kira naji muryarta.....kuyi magana da ita idan wayar takeso ta sauke layin
daga kai,ka sanya ayima annin swapping a dauki wata wayar a hada mata".
" Ka kwantar da hankalinka me babban suna,banjin yarinyar tana da niyya ko nufin riqe wayar nan,akasi
kawai dai aka samu da ajizanci irin na dam adam......tana da kirki qwarai,ita ta kaini asibiti ta kuma zauna
dani har sai da musaddiq ya iso". Wata sassanyar iska ya saki daga bakinsa,sai yanzu ya tuna inda yasan
muryar
"Itace mara kunyar yarinyar nan data tsaya tana yiwa mutane fada akai don ta kaisu asibiti?" Ya jefawa
anni tambayar da nutsatsiyar muryarsan nan.
Murmushi ne ya subucewa annin. Tasan halin fu'ad qwarai da gaske. Yana da tsananin kamewa da
rashin son shiga sabgar kowa
"Ba rashin kunya tayi ba muhammadu......fada ta yiwa musaddiq,kuma ai ta fadi gaskiya ne,ta kuma yi
daidai,sun tafi yawonsu sun barni,a jikina kuma babu inhaler kwata kwata,a nata ganin indai hakan taci
gaba da kasancewa komai ma yana iya faruwa". Shuru ya ratsa tsakanin bayanin anni,yana ji kawai annin
tana son bata kariya ne saboda halinta na bawa kowa uzuri komai girman laifin da ya aikata mata
"Is okay....." Ya fada yana sauke siririyar ajiyar zuciya a qoqarinsa na fesar da bacin da ranshi yayi
"Suna kula dake kuwa?" Ya sake tambayarta da wannan seriousness din nashi. Murmushi ta saki kadan
"Qannenka suna qoqari sosai,ina samun kulawa tamkar kana nan.....saidai kewarku,ina fatan komai yana
tafiya kaman yadda aka zata?,kowa kuma yana lafiya?" Murmushi ya saki,wanda mutum uku keda
wannan baiwar sakashi murmushin koda baiyi niyya ba,anni abba da farouq kada ma farouq din yaji
labari. Abune me wahala ka tsinci murmushi akan fuskarsa,akwai mutane da yawa dake da tambayoyi da
yawa a kansa
Wasu tambayoyin na isa kunnensa ta harshen farouq,wasuma kam baisan ana yinsu ba.
"Ba zamu wuce kwanaki hudu ba anni in sha Allah". Farinciki ya wadaci fuska da zuciyarta
"Hidima ai bata qarewa Muhammadu muddin akwai rai a jikina.....fatan da zakuci gaba da yi mana shine
Allah ya qara mana lafiya....."
"......da nisan kwana me amfani" Ya qarashe fadi. Qaramar dariya ya sanyata a wannan karon
Koda suka gama wayar baiko motsa ba a wajen,yayi zaune da wayar kawai a hannu yana juyata.
Duk yadda zai fasalta anni a rayuwarsa da zuciyarsa bazai kwatantu ba. Ita din uwa ce data amsa sunanta
na uwa. Wadda tayi sadaukarwa da yawa cikin rayuwarsu,sadaukarwar da tayi musu ba qarama
bace,sadaukarwa ce da UWA kadai ke iyayi wa danta.
Asthma dinta bata taba hanata taba ruwa saboda su,asthma dinta bata taba hanata sammakon
tashi koda da sassafe ne a lokacin da hazo da sanyi suka lullube sararin samaniya......a yanayin da kuma
yafi zama barazana ga masu lalurar......asthma dinta bata hanata tsaftace musu muhallin
kwanansu......bata hanata dafa musu abinda zasuci
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 50
koda ita din bataci ba,bata kuma hanata kulawa da lafiyarsu koda ita din bata da cikakkiyar lafiya.
Har tsakiyar zuciyarsa yana jin wata qauna me girma tana tabashi game da anni,tayi musu abinda baki
bazai iya fadi ba,zuciya da ruhi ba zasu iya mancewa ba. Ta musu hidima da jikinta da kudinta da
lokacinta harma da lafiyarta,irin hidimar da ya debe tsammanin zasu sameta,irin hidimar da suka
buqaceta a yunwace daga wajen wadda tayi silar zuwansu duniya amma ta gagaresu.....kulawar da baiyi
tsammanin zasu sameta ba daga gurin kowacce mace a duniya. Baiga abinda zai samu a duniya ba da zai
manta da anni.....baya tunanin akwai abinda anni zata nema daga gareshi ta rasa.
Yana shirin sauke wayar tasa don ya tattara tarkacensa ya wuce daki ya samu bacci koda na awa
biyu ne kafin zuwan lokacin sallar asuba sai kiranta ya shigo.
Kamar ko yaushe ya zubawa kiran idanu,a duk sanda zata kirashin sai ta tuna masa da abubuwa
masu yawa. Aduk sanda kiranta zai shigo wayarsa saita tada masa wani abu daga can qasan zuciyarsa.
Bashi da wani zabi da ya wuce ya daga din,sai ya sake zama sosai ya ya dauki wayar yana karawa
a Kunnensa,
Cikin jin isa da izzar cewa ta haihu.....cikin isa da jin izzar ita din a yanxu wata abace cikin
duniyar.....cikin jin izzar ta isa takai qololuwar gata a cikin jerin iyaye mata ta amsa sallamarsa.
"Barka da dare.....an wuni lafiya?". Maimakon ta amsa masa saita sake daidaita kanta,a dake take masa
magana
"Yanzun ace bankai kima da martabar da a kullum zaka kirani kaji ya na kwana ya na tashi ba?" Ta maida
masa gaisuwar da qorafin abinda me masa suya a qirji.
"Afwan.....kiyi haquri" Ya zabi furtawan. Har cikin zuciyarsa,har kuma tsakaninsa da Allah kirantan kaman
yadda take buqata wani baqon abune cikin rayuwarsa dama lokutansa. Yadda ta zamewa rayuwarsu
baquwa haka dukkan wata mu'amala da zaiyi da ita take zama baquwa a wajensa. Koda yayi niyyan yin
hakan saboda sauke nauyi da haqqin haihuwa dake wuyansa sai ya manta sam sam,tunda abune da aka
fareshi bada dadewa ba,sabo dashi kuwa zai dauki lokaci kafin ya shiga jiki da zuciya,bayan haka
ma......kwata kwata mu'amalar dake a tsakaninsu wata irin tattaurar mu'amala ce da babu taushi a
jikinta bare ta shiga zuciya da kyau ta tsayema tunani.
"Koda baka nemeni ba ni bazan zubewa duniya ku ba.....ku zama inuwar giginya na nesa kasha dadi...."
Ta fadi tana watsa hannuwa ba tare data tuna da kuskuren rayuwarta na farko ba.
Numfashi ya aje,maganartata ta zama tamkar wani tuni ne daya dace ace kanta da kanta ta yiwa
shi
"Ba zata zubewa duniya su ba....." Baisan zubewa ta nawa ya rage tayi musi ba,kalamanta a kullum sake
haska masa ita yake,yayi imani yana kuma sake samun gamsuwa da dalilai masu tarin yawa dake
bayyana masa lallai AKWAI DALILIN dawowarta cikin rayuwarsu......lallai ta dawo ne bawai da sunan
nadama ba ko gyaran kuskure......AKWAI DALILI AKWAI KUMA HUJJA.
Wasu yana kallonsu shimfide a zanen tafin hannun qaddararsa,wasu kuma baisan daga inda zasu
soma bullo musu ba.
"Ba'a canzawa tuwo suna Muhammad,kuma ko ma meye ka zama sai dana haifeka sannan ka zama
din......mahaifiya daya ce kuma ni dince dai". Idanunsa ya lumshe na wasu sakanni kafin ya samu budesu.
Ba abinda maganganunsa ke haddasa masa sai sake jagula duk wata qanqanuwar nutsuwa tasa da yake
qoqarin samarwa kansa.
"Kiyi haquri" Ya sake maimaita mata kalaman da ta dade da haddacesu daga bakinsa.
"Yaushe zaku dawo?,idan ba nan kusa bane dawowar taka ka sanarmin......don nasan sai yadda akayi
dakai,sai kuma abinda aka shimfida maka".
Yaji saukar kalamanta sosai har saman zuciyarsa. BATA SON AHALIN ALHAJI HAMZA KIBIYA ya
dade dayin wannan karatun a qanqanin lokacin data duro cikin rayuwarsu......ya kuma san halinta tun
daga sanda ya fara rarrabe abubuwa har zuwa sanda ta fice daga rayuwarsu. Idan batason abu bata
sonshi kenan......dadi ko wahala basa sauyata akan abun. Idan taqi taqi kenan.....hakanan idan taso taso
kenan......bata ja da baya akan duk abinda ta sanya a gaba......bata rasa ABUN HARINTA komai dadewar
lokaci.
Wadannan abubuwan ya sanya ya sanya dukkan wata nutsuwa da karatu nasa a kanta......ya
sanya duk wani nazari da dogon hange da tsinkayensa a kanta,yasan wacece......sanin da ita kanta
batasan bata kuma yi zaton yakai zurfin haka ba.
"Ba zamu wuce satin nan ba in sha Allah" Ya amsa mata kamar yadda ya amsawa anni a dazun.
"Har sai ankai sati?" Ta masa tambayar a zaqe,har abun yadan so bashi mamaki,don sam salon tambayar
nata baiyi kama da ta zaqu ko tsahon kwanakin sun mata yawa da zasu bayu ga ganinsa ba,tabbas yasan
akwai dalilin tambayar a qasa.
"Kudi nake buqata ka turamin ta account dina akwai amfanin da zanyi dasu......kada suyi qasa da million
daya" Tayi maganar kanta tsaye cike da karsashi da qwarin gwiwa kaman yadda hajja ta kwatanta mata.
Mamaki kadan ya kamashi.....saidai ya ajeshi a gefe
"Akwai abinda baki dashi?,cikin gidan ko sutura ko wani abu makamancin haka?,ko akwai wanda kike da
buqatar ayi masa wani abun?"
"Duka babu ko daya.......shin waima sai ina da wannan buqatun zan buqaci kudi daga wajenka?,yarinya
ce ni qarama ko kuwa?,ko banyi isar da zaa dauki tsabar kudi a bani ba har sai akwai dalili ko hujja?"
"A'ah......"
"To dakata......ba sharhi nakeso ba......kayi abinda nace daga yau zuwa gobe". Sai yaji alamun yanke
kiran,abinda ya tilasta masa sauke wayar daga Kunnensa yana binta da kallo.
Yatsunsa kawai ya dora saman goshinsa yana murzasu a hankali,kadan kadan yake furzar da iska
me zafi daga bakinsa. Tabbas yasan da akwai wani abu......akwai wata a qasa......
Wanzuwar kudi a hannunta kwata kwata ba alkhairi bane,kuma ko yanzun bayajin alkhairi ne ya
sanya ta nema.
Cikin lokaci qanqani yaji jijiyoyin kansa sun qara adadin gudunsu da kuma harbawarsu,abinda ya
haifar masa da fara jin alamun ciwon kai. Bayason hayaniya......bayason matsala kwata kwata,wannan ya
sanya yake nesa da mutane da al'amuransu,banda kasuwanci daya daukoshi tsundum ya jefa cikin
mu'amalantar mutane qarfi da yaji.
Ba wani karsashi ko qwarin gwiwa ya dauki dukan abinda yasan yana da buqata,a maimakon
tattare takardun nasa gaba daya da yayi niyyar yi ya kuma shiryasu kamar yadda ya saba. Yana da wani
irin tsafta da duk abinda yayi amfani dashi zai wahala ka sameshi ba'a killace ba.
Kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki haka ya tura qofar dakinsa idanunsa akan dakunan abba
da saddiq daya tabbatar zuwa lokacin sun jima da yin bacci,wani lokacin sai ya dinga ji kamar su kadai ne
basuyi sa'ar rayuwa ba.....sai ya dinga ganin kamar kowa ya dace da rayuwa me kyau amma banda su.
Duk sanda irin wannan tunanin ya fado masa yakanyi qoqarin korar shaidanne daga ransa.
A gefan gadon ya zauna,ya miqa hannu ya kunna bedside lamp,dan siririn hasken da baida takura
da yawa ya bayyana. Hannunsa ya zura qasan drawer din da fitilan take kai,ya ciro wani mini wallet
dinsa,ya bude ya sake zaro wani qaramin hoton dake ciki.
Duk da hoton baida cikakkiyar kala amma fuskar mutumin ta fita sosai,kamannin nan nasa da
murmushinsan nan da idan ya kalla sai yaji kaman idan ya kirashi zai amsa.
Wani abu ya tsaya masa a wuya,yayin da idanunsa suka sauya launi,gefe daya wani qaqarfan abu
da ya jima yana kokawa dashi akan maamah din ya fara taso masa,sai ya fara hadiyar zuciya kadan kadan
yana qoqarin hadiye bacin ranshi,tamkar me hadiyar lomar abinci,don daga inda inda kake kana iya
hangen Adams Apple dinsa daya zamewa wuyansa dama fuskarsa ado yana kaikawo daga sama zuwa
qasa.
A duk sanda ya kalli fuskarsa cikin hoton sai yaji duk duniya ba wanda ya kaisu maraici......a duk
sa'ilin da zai kalli wannan jarumar fuskar sai yaji zuciyarsa ta cika da qiyayyar kowacce d'iya mace a
duniya idan ka debe anni da manal......wata irin wuta ce take ruruwa a zuciyarsa a kanta......har yakanji
kamar bazai iya sake kusantar muhallin da take bama ballantana yaci gaba da accepting nata ko kyautata
mata a matsayin uwa.
Fuskar abban wata fuska ce da a kullum take tunasar dashi gwagwarmaya da ainihin
ma'anarta.....fuskar tasa fuska ce dake karanta masa tare dayi masa bitar cusgunawa....uzzurawa da
azabtarwa irin ta diya mace. Kowanne hoto nasa da abinda yake karanta masa.....hakanan da abinda
yake tunasar dashi. Ko kusa ko alama....ko sau daya.....hakanan koda wasa bai taba sha'awar aure ba
ballantana wata diya mace. Yana kallonsu a wasu halittu ne na daban da babu imani ko tausayawa cikin
lamuransu.
Sanadin ciwon abban....da silar data sanya ya dinga ci gaba abune da bayason tunawa,abune
dake dake tilasta zuciyarsa juyawa MAAMAH baya da dukkan abinda ya danganceta. Koda ya tuna da
abin a sanda take daura dashi yakanji baya buqatar kallon fuskarta ko kuma sauraren muryarta,yanaji
cewa ba abinda zai bashi sukuni face yayi nesa da ita.
*_AKWAI WANI SIRRI.....AKWAI WANI BOYAYYEN SIRRI CIKIN DUNIYARSA_*
*******Sannu a hankali take tafiya cikin daya daga cikin layukan da suke zame musu turba kuma hanya
ta isarsu gida a duk sanda suka rasa samun abun hawa ko kuma kawai jin rikici irin na dalibin dakan
qirqirarwa kansa tafiyar qafa haka siddan.
Ita daya a hanya amma tanata mamakin yadda yau aka raba musu lokacin tashi daga makarantar
alhalin tunda suka fara tsahon shekarun tare ake tashinsu. Ta cika tayi fam akan yadda nadra din da
haneefa sukayi gaban kansu suka taho gida abinsu ba kamar yadda suka saba ba abinda basu taba yi ba.
Gefe daya kuma na zuciyarta ya cika da saqe saqe tare da tunanin yadda zata qarqare haddace
ayoyin qarshe na shafin da a yau zata bada haddarsa a islamiyya. Kaman daga sama,babu zato kuma ba
tsammani taji an finciki qaramar jakar da take dan cillata a hannunta wadda ke dauke da muhimman
abubuwa da dama. Sanda ta daga kai kuwa a firgice barawon ya soma nisa da ita yana gaya mata
"Idan kina da gata,ko kina da me qwatoshi ki turo shi" Sai ya juya cilla sassarfa ya fada wani lokon dake
daura dasu.
Ko wanne sashe na jikinta rawa yake,tayi wata irin tsorata da bata taba yin irinta ba.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 51
Abune da bai taba faruwa da ita ba koda wasa,ta waiga gabas da yamma kudu da arewa,ba kowa a
layin,babu gicci ko wulqawar kowa,ko cutas da ita zayayi zaiyi ne hankali kwance,abinda ya sake kada
mata hankali kenan,ta soma yunqurin tattara dukkan qoqarinta wajen ganin tabar layin.
Taku uku tayi ya shawo kwana. Hannunsa riqe da jakartata da yanzu yanzu aka wafceta. Birki taja
ta tsaya,gudun zuciyarta yana sake qaruwa kaman zuciyarta zata fito ta bakinta. Ta qura masa idanu
tana kallonsa kaman yadda shima ita yake kallon. Guduwa takeson tayi amma ta kasa kaman an kafeta a
wajen.
Duk taku daya da zaiyi yana sake ganin kamanni na jini da kuma yanayinta da SABREEN din.
Yana mamakin yadda ta iya boye komai nata,yadda ta iya bad da bami,ta iya nutsewa da narkewa cikin
sararin duniya ba tare da ka iya gano daga ina take fitowa ba ina kuma take komawa?.
"Karkiji tsoro......ni ba cutar dake zanyi ba.....jakarki na karbo miki,nazo wucewa naga abinda ya
faru,karbi jakarki" Baya taja kadan,bata jin aminta dashi sam sam a zuciyarta. Wani irin raino da horo
sabreen ta yiwa kowannensu na rashin yarda da baquwar FUSKA muddin sunanka NAMIJI.
"Da gaske nake miki.....ba cutar dake zanyi ba,idan kuma baki yarda ba ga jakarki nan" Ya fada yana
ajiyeta a tsakaninsu sannna ya juya ya fara takawa yana barin wajen fuskarsa shimfide da
murmushi,qasan zuciyarsa kuma fes cike da murnar samun CIKAKKIYAR NASARA da kuma tabbacin
DAUKAN FASA mafi ciwo a gareta.
Sai data tabbatar ya bada tazarar da koda ya juyo zuwa gareta zaiyi wahala ya cimmata sannan
ta taka ta isa ga jakar,ta tsugunna ta dauka,ba tare data damu da datti da qurar data debo daga qasa ba
ta rataya tana maida idanunta kansa.
Tafiyarshi yakeyi baiko waiwayota ba,ta kalli jakar ta kuma kalleshi,sai ta buda bakinta a hankali
tana furta
"Na gode". Cak ya tsaya tamkar dama yana dakon martaninta ne,sai ya waiwayo yana sake fadada
fara'ar fuskarsa
"Nima na gode.....sunana....." Dakatawa yayi kadan saboda tuna wani abu da yayi
_"Tana da wayo,tana da hadari.....da alama kuma akwai abinda ta taka_ kalaman suka dawo masa kai fes
"Sunana BASSAM....kefa?" Ya furta yana murmushi tare da samun gamsuwar lallai sunan zaifi saurin isar
da saqo a maimakon ainihin sunansa na NASEER. Bashi da buri baya kuma fatanbta fahimci komai har sai
zuwa sanda komai din ya kammala......har sai zuwa sanda shi da kansa zai mata bayanin komai. A lokacin
da yake buri da kwadayin jin sheshsheqar kukanta......a yanayin qunci baqinciki da kuma tarin damuwa
da yake fatan ta hallakata......koda bata hallakata ba yana fatan tayi mata mummunar illar da koda gaba
ba zata qara gigi kasada ko gangancin shiga shingen mutane irinsa ba.
"Kefa 'yammata?" Ya tambayeta cikin lanqwasa murya da tausasa harshe gami da sanya wani amo me
sanya nutsuwa ga duk me saurare.
Lokaci daya ta danji ta samu nutsuwa kadan,sai ta sauke boyayyar ajiyar zuciya sannan ta bashi
amsa
"Huda" Ta furta a nutse tana jin wani iri da kiranta da sunan 'YAMMATA da yayi,karo na farko cikin
rayuwarta da wani ya taba kiranta da wannan sunan.
Murmushi ya sakar mata yana gyada kanshi gami da lumshe ido yakuma budesu a lokaci guda
"Nice name.....duk wanda ya baki wannan sunan ya iya zaben suna". Maganar tasa ta sanya fitar
murmushin dole a saman fuskarta. Tadan murmusa kadan,abinda ya sake sanyashi ganin kamanninta
muraran da sabreen. Wutar daukan fansanshi ta sake ruruwa cikin ransa.
Dagowa tayi a karo na biyu ta sake kallonsa,sai taji wani dadi zuciyarta tana saki kadan. Duk
wanda zaya so sabreen a wajensu basu da kamarshi......kaman yadda suke nisantar wanda zai kawo suka
a kanta ko wanene.
"Nadan rakaki kadan ko?,ki fita daga layin nan,don har yanzu ban gamsu da sahihancinsa" Ya fadi yana
duban gefe da gefansa bayan ya zube dukka hannayensa cikin aljihu.
Tayashi duban itama tayi gabanta yana dan faduwa,ta yaya zata iya jerawa dashi wai?. Amma ko
kafin tace komai ya fara takowa zuwa inda take tsayen yana jifanta da murmushi,tadan ja baya kadan
dole ta fara takawa ya rufa mata baya
"Kada ki damu,bawai zamu jera bane,ba wanda zaisan tare muke......kawai dai zanyi gadinki har ki
aminta" Kalmar aminci daga bakinsa ta sanya taji ta sake,sai taci gaba da tafiya,shi kuma yana biye da ita
da 'yar nisan tazara a tsakaninsu.
Duk wani taku nata guda daya yana lasafta yadda komai zai wakana......a yanzu bayan wutar
daukan fansa dake ransa,wata wutar daban ta soma rura kanta da kanta a zuciyarsa.......bayajin koda ba
komai tsakaninsa da sabreen zai iya qyale wannan danyar 'yar shilar ta wuceshi. Duk da bata qarasa 'yar
uwarta ba a komai.......amma zata sama masa nutsuwa yayi yaqinin hakan ko yaya take kaman yadda ya
dade yana tsara zai samu daga yayartata.
Bai tsaya ba har sai da qafafunta suka isa babban qofar gidan nasu,sai ya samu waje nesa kadan
saboda gudun bacin rana da bacin aiki,ya tsaya kawai yana jifanta da wani mayataccen kallo tamkar
mayunwacin zaki.
Har ta sanya qafafunta sai ta dakata ta waiwayo,suka hada idanu abinda ya bashi damat jifanta da
wani shu'umin murmushi. Itama murmushin ne ya subuce daga bakinta tana jin cewa ya kyautata mata
matuqa,abinda ba kasafai suke samunsa daga wajen al'ummar da suke kewaye dasu ba,don haka
wannan din ya qawatar da ita. Bakinta ta bude a hankali ta furta kalmar
"Na gode sosai". Duk da tasan ba lallai ya iyajinta ba,amma zai karanci bakinta. Ya kuma karanta din,sai
ya daga mata kai don haka ta juya tana shigewa cikin gidan.
Haka kawai murmushi ke fita a fuskarta tana tuna yadda komai ya kasance. Badan shi ba Allah
ne kadai yasan abinda zai faru da ita a wannan qonannen layin da babu kowa. Ba yadda kuma zatayi,nan
dinne dai hanyar wucewarsu tilo guda daya,inda da wata hanyar tabbas ba abinda zai sanyata ta sake bi
ta nan wajen.
"Ke dawa kike murmushi ke daya?" Sabreen dake tsaye gaban fridge dinsu tana duba adadin pure water
da lemon daya rage musu a ciki ta fada hannunta dafe da murfin fridge din. Cikin sauri ta gyara yanayin
fuskarta tana qoqarin adana takalmanta data shigo dasu
"Ba kowa adda...." Idanunta ta zube mata sosai tana son karanto wani abu amma bata samu nasarar
gano komai ba,saidai duk da hakan haka kawai takejin bata nutsu da irin amsar huda din ba. Emotions ke
sauya yanayin fuskar mutum,walau na farinciki ko baqinciki,dole idan ya nuna saman fuska to akwai
wani labarin a qasan zuciya.
Sakin fridge din tayi bayan ta rufeshi tana takowa tsakiyar dakin
"Wacce irin tafiya kukayi ne yau ke dasu nadra?,kinsan dai banason kuna raba tafiya ko?" Ta fadi tana
zama idanunta still akan fuskar huda din.
"Wallahi dama nace zamu hadu dasu.....kawai adda ina fitowa na samu wai sun wuce gida?,yau bansan
me yasa aka rarraba mana lokacin tashi ba" Ta qarasa maganar fuskarta a bace da gaske. Idanunta tadan
dauke daga kanta tana sauke numfashi
"Banason irin wannan tafiyar,kome raba lokacin su dinga jiranki" Cikin ranta tana jin abun kwata kwata
baiyi mata ba.
Qaramar dariya ya sakarwa kansa bayan ta shige gidan. Fara takawa yayi hankali kwance yana
barin layin. Tabbas shima zai buga nasa wasan yadda ya dace,zaiyi wasa da rayuwarta da kuma
hankalinta yadda ya kamata......zai gigita mata rayuwa ya dagula dukkan wani lissafi nata......zai guntule
dukkan wani farinciki nata kaman yadda ta gurgunta ta kuma dagula rayuwa da nutsuwarsa. Yanaji a
ransa abun zai bashi nishadi qwarai,zai kuma qarasa goge baqinciki qunci da takaicin data qunsa masa.
********Cikin nutsuwar nan tasa yake saukowa daga matakalar jirgin riqe da kyawawan briefcase guda
biyu. Tasa data Alhaji hamza kibiya.
Biye yake da dattijon,yana aje tasa qafar a duk muhallin da ya cire. Kamilallen dattijon da adadin
furfurar dake baibaye a fuskarsa da kuma gashin kansa suka sake tabbatar da dacewar sunan dashi. Cikin
kamala yake komai nashi,sanye da shadda dinkin babbar riga da maroon hula dara sak ainihin shigar
marigayi malam aminu kano.
Muhammad fu'ad jadda,mamallakin kamfanin jadda diamond chores resources wanda ke biye
dashi a baya. Sanye cikin dinkin kaftan da yayi matuqar qara masa kwarjini da wani irin haiba me cika
idanun me kallonsa. Idan ka kallesu shida Alhaji hamza kibiya din zakayi tsammanin shine ainihin mahaifi
gareshi saboda yadda tsahonsu yake kusan daya da kuma murjewar jikin. Bayansa kuma sadiq ne janye
da luggage dinsu. Shikam t.shirt ne jikinsa da trouser,ya lullube qafafunsa da lafiyayyen boots ba kaman
fu'ad ba dake sanye da wani lafiyayyen halfcover ba dan qasar itali da aka samar dashi da dinkin
hannu(sau da dama mu a nigeri muna raina takalman hannu,amma a qasashen qetare babu takalma
masu daraja da tsada irin handmade shoes,wani ma kana ce masa handmade ne ka bata show din😂,nija
my nation ).
😂
Tare suka jero kafada da kafada shi da Alhaji hamza din zuwa muhallin da farouq yafi tsaiwa a
duk sanda yazo daukosu daga tafiya irin wannan. Ko a yanzun da suke nufar mota don isa gida ma duk
hirar akan kasuwanci ce. Abun yana bawa Alhaji hamza mamaki. Duk qwarewarsa da qaunarsa da
kasuwanci fu'ad din ya shallakeshi. Kowacce rana kowacce safiya,kowanne dare da wuni plan din
rayuwarsa da komai nasa yana kan kasuwanci. Me za'a bunqasa?,me za'a qirqira?,me kuma za'a
gyara?,ina ne nasara take a bunqasata?,ta ina faduwa take ayi hanzarin bawa gurin kulawa da kariya?.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 52
Yana jingine da motar yana kallonsu,idanunsa fes a kansu. Yana masa dadi yana kuma sanyawa ya
manta cewa fu'ad ba dan uwansa bane na jini a duk sanda ya ganshi kamar haka da Alhaji hamza din.
Yana alfahari yana kuma qara ninka alfaharinsa akan muhammad fu'ad din. Shi kansa ya
sallama......jajirtaccen mutum ne da jajircewa take a cikin jinin jikinsa.
Ya maida idanu a hankali akan yanayin takunsa. Tafiya ce me cike da ginshira gami da cikakken
kuzari da karsashin da zai bayyana maka adadin cikakkiyar lafiyar da yake da ita.
Daga abban har fu'ad din hankalinsu baya wajen,yana duba wani qaramin takardu da suke dauke
da bayani da taswirar burinsa na gaba wato ginin katafaren kamfanin samar da kayan ado na sarqoqin
mata da zai dinga amfani da wani sashe na ma'adanan da yake haqowa.
Tun daga fitowarsu gaba daya security guards dinsa da ya bari a gida kowanne ya koma kan
aikinsa. Dukan inda ya ajiye qafarsa nan suke maida tasu.
Murmushi ya subucewa farouq,ya dawo kenan,kuma yanzun za'a fara. Bayaso abba ne ya
tilastashi daukan guardsmen duba da yanayin qarancin tsaron da ake fama dashi. Uwa uba ma zaiyi
wahala a nasibin rayuwa daya samu......da irin mu'amalarsa ace ya zauna haka gayansa yana yawo babu
masu tsaron lafiya tattare dashi.
Wani lokacin idan yaso yana kubce musu ne yayi fitarsa shi kadai a mota yasha iska ya dawo. Ba
kasafai ya fiya son fita qasashen waje sai idan harka haka ta taso takai kayan da sunyi yawan yayi
wakilci......amma yanzun ya koyi fita din lokaci bayan lokaci haka siddan ma don ya samu ya sarara yayi
rayuwarsa shi kadai. Mutum ne da bayason matsi,bayason takura,zai iya rayuwa me dogon zango shi
kadai a wani muhalli na daban,shi yasa ko a yanzun a sassansu gini ne me zaman kansa dake dauke da
bedroom and parlor da toilets kowa shi kadai. Saddiq da musaddiq sun hade dakunansu saboda kowa
nashi apartment din ya masa girma. Amma oga fu'ad shi daya ne a nashi,hakama farouq,sai shi farouq
din da lokaci bayan lokaci yakan dawo sassan fu'ad din yayi kwanaki yana kwana a nan sannan ya koma
wajensa.
Kullum ya hangi fu'ad din daga nesa ba abinda yake tunawa sai wannan matashin dan bautar
qasar,mara tsoro kuma mara shakka,cikakken jarumin daya shiga yankin daba nasa ba,yayi abinda koda
haifaffen yankinne ya aikata bazai sha ba.....ya kubuta da tarin nasara. Farouq yadan sake murmusawa
yana tuna yadda yaci wahala bayan uban gudun da sukayi,ya tuna yadda fu'ad din yayi jinyarsa tamkar
ba dashi akayi gudun ba
"Ba abinda nakeji man.....ni dakai ba daya bane,sau nawa ana gaya maka ka dinga gym saboda yuwuwar
samuwar irin wadannan lokutan na qwatar kai?,sai kuyita zama kaman mata,baku da wani banbanci
dasu?" Ya tambayi farouq din a wancan lokaci yana dage masa dukka girarsa bayan ya bashi maganin
ciwon jiki yasha.
"Yanzu wannan pain killer din da kake fana dashi......da warm water da fenugreek kake sha da yafi maka
amfani". Harara ya balla ma fu'ad din yana dubansa
"Ba zaka qarasa kasheni ba da wadannan home remedies din naka ba" Sai ya juya ma fu'ad din baya
yana sauke numfashin wahala yabar fu'ad din da sakin siririn murmushin nan nasa me tsada. Miqewa
yayi yana dauke cup din
"Idan home remedies bai kasheka ba......son jiki da rashin exercise....aci a kwanta duka ya
kasheka......naga wanda zai aureka da qaton tumbi" Ya qarasa maganar yana jefa kwalin lemo a dutsbin.
Duk da farouq na cikin yanayi a sannan saida murmushi ya qwace masa.....fu'ad mahadin rayuwarsa ne
kuma mahadin zuciyarsa ne kaman yadda ya tabbatar a wajen fu'ad dinma haka yake.
Kafadarsa y
"Ina nan ina kallon gujajjen dan bautar qasar nan da bai kammala service dinsa ba sai a garin kano".
Murmurshin nan da shi daya ke iya fidda masa shi daga kan fuska ya saki kadan yana sake kaiwa
kafadarsa duka. Dariya kadan ya saki shima farouq din
"Ina hasaso yadda zasu cinye namanka danye duk sanda suka fahimci daga ma'adanin qasarsu ne aka
samar da attajirin nan mamallakin jadda diamondchore company........" Murmurshin ya sake sanyashi
saki,sai ya saka tafin hannunsa saman wuyansa yana dan karyar da wuyan kadan
"Naman muhammad jikan jadda yafi qarfin cinsu umaru...." Ya bashi amsa da anihin sunansa,abinda ya
sanya farouq din sakin dariya sosai. Kafadar fu'ad din yadan bubbuga
"Na sani.....nafi kowa sanin wannan dan uwan nawa wanne iri ne......tun daga ranar da mukayi temple
run dinnan na sake yadda da hakan..."
"A nan zaku gama hirar ne?,idan ku baku gaji ba ku tallafa ku kaini naga aminatu na" Muryar abba ta
sauka kunnuwansu.
Fu'ad ne ya waiwaya don farouq yana fuskantar abban ne. Dan murmusawa kadan fu'ad yayi ya
matsa yana yunqurin budewa abban qofa,amma farouq ya rigashi
"Dukkanku kai da abban yau qarqashin hidimata kuke....baqinmu ne ku daga South Korea".
"Sannu sarkin noma.....godiya muke" Shima abban ya fada cikin barkwanci bayan ya shiga motar.
Dashi da farouq din baya suka shiga bayan ya bawa shugaban security dinsa umarnin su bisu a
baya.
Kusan duka a hanya ma dai tattaunawar ta kasuwanci ce. Farouq din yana bawa abban labarin
yadda abubuwa suka kasance bayan tafiyarsu
"Amma tabbas sai ka sake sanya idanu akan mika'il.....ina suspecting wani abu tattare dashi,duk da bana
ce gashi ba,amma nasan kai din zaka fini fahimtar komai" Farouq din ya furta.
Idonsa fu'ad ya dauke daga kan wayar hannunsa,wanda saqon mika'il dinne ya shigo,mutum na
farko daya fara masa saqon barka da dawowa kafin kowa. Bai cewa farouq komai ba,amma kuma
maganar tasa ta samu gurbi sosai a zuciyarsa ta zauna,sai ya gyada kansa a hankali yana sake maida
dubansa ga wayar.
**"Anni an gama komai" Ta furta sanda take saukowa daga saman tsararren dining area din daya dauki
kyakkyawan family dining table na wani mulmulallen tangaran kai kace an samar dashi ne daga
burbushin diamond ko gold da kamfanin jadda ke wankewa su fiddashi. Fara ce tas,mai matsakaicin
tsaho,saidai bata da qiba ko qanqani. Yanayin sumar gaban kanta kawai zai fada maka akwai suma me
yawa a saman kanta wadda bata da duhu ta danyi brown kadan bame yawa ba. Yanayin yadda ta datsi
daurin dankwalinta daga tsakiyar kanta shi zai baka daman ganin hakan sosai. Straight gown ce a jikinta
ta atamfa me igiyoyi hagu da dama wadda ta daureta daga gefen qungunta guda daya.
"Ma sha Allah.....sannunku da qoqari....sun wuce ne?" Anni data daga kanta daga tab din hannunta da
take duba wasu addu'o'i ta fada.
Fuska tadan yamutsa kadan tana zama kujerar gefan annin gami da ajiye qaramin towel din
hannunta a side table sannan ta dauki wayarta dake ajiye akai tana qoqarin budeta
"Kowa ya wuce......yanxun abba da hamma kawai muke jira" Ta qarasa maganar murmurshi yana subuce
mata.
"Umhummm......wato shi saddiq shine marainin wayonki da baki ta tasa ko?" Anni ta fada tana maida
idanunta ga addu'o'inta . Fuska ta yamutsa,duk da bata kalli annin ba amma ta amsa
"Bar wannan anni,wa yake ta tasa,ba abinda ya iya sai takurawa mutum ba dalili......hamma takurawarsa
me dalili ne idan bakayi abinda yace ba ko baka kiyaye dokarsa ba......amma yaa saddiq.....hmmmm....ko
wayar nan yanzun ya shigo yana ina dannawa sai yayi challenging dina" Ta qarasa maganar tana zamewa
ta kashingida saman kujerar tana maida hannunta kan shafinta na X.
Ita da annin kowa ci gaba yayi da uzurin gabansa,wannan ya bawa falon daman daukan shuru na
wani lokaci kafin ta daga kanta. Haka kawai ta qarewa anni kallo sai ta saki dariya
"Anni.....kinsan tsadar kayannan?" Ta fada tana kallon kwantaccen lace din jikin annin dake wani yauqi
da santsi duk kuwa da cotton ne. Peach color da ratsin green,bashi da nauyi ko kadan
"Anni Allah hamma yana shagwabaki......ki zauna da kaya me tsada haka a gida duk dogayen
rigunanki?....amma dai....to,hala abba aka yiwa kwalliya?" Ta fada qasa qasa tana qunshe bakinta da
hannu. Kadan ta dubeta ta harareta
"Akwai kayan da sukayi tsadar da zan kasa yiwa abban kwalliya dasu?" Kai ta girgiza tana qoqarin maida
kanta ga wayarta tana qoqarin boye dariyarta
"Aah anni wallahi" Ta fada da sauri tana duban anni still tana son shanye dariyarta
"Kici gaba.....inajin zan dauki shawarar farouqu ne,zaki komawa nanna ne kiyi zamanki a can". Kyabe
fuska tayi da kyau tana aje wayarta gefe kaman zata saki kuka
"Dama haka yaa farouq din yace?,duk haqurin zama cikin mazan da nakeyi ban da sister?....."
"Oho koma.meye gwara ki koma can,tunda kinga can dinma akwai mata 'yan uwanki sai kinfi jin dadi".
Sosai ta sake kwabe fuska tana duban anni
"Da gaske anni zaki iya bayar dani?" Daga kai tayi ta dubeta
"Ba mace bace ke?,wataran ba aure zakiyi ba?" Ta tambayeta,ai kuwa saira soma matsa hawaye tana
juyawa annin baya
"Ai dama na sani......gidan nan babu wanda yake sona sai hamma da abba na......shi dama yaa farouq
kaman ya bayar dani kyauta yakeji.....ni bazanyi aure ba.....dake zan yita zama". Yadda tayi maganar zata
yita zaman da ita sai ya bawa anni dariya amma ta dake
"Sai kiyi kuma" Tace tana ci gaba da scrolling sama tana duba adduo'inta.
"Kinga.....ki daina biyewa ta BB farouq.......indai ina nan ba wanda zai matsa miki.......i swear"
Muryar musaddiq ta biyo bayan sallamarshi. Tuni ta miqe ta zauna sosai tana qoqarin goge hawayenta.
"Kaima kana biye musu yaa musaddiq wani lokacin.....amma dai ka fisu" Ta fada tana daidaita zamanta
saman kujerar.
Qaramar dariya ta qwacewa anni tana qoqarin ajiye tab dinta a gefe
"Uhumnnn..... Ai dama ba kasafai akewa amna abun arziqi ba.....wanda ke mata abun arziqi kai tsaye a
gidannan Muhammadu ne......har kun dawo?" Ta tambayeshi tana duban musaddiq dake dariya qasa
qasa.
"Sun sauka amma basu qaraso gidan nan ba.....amma na tabbata suna dab da isowa don tun dazu suka
tafi daukosu". Ta amsa masa tana miqa hannu ta karbi purse din nata da yake miqa mata.
Tana yunqurin budewa su kuma suna magana tsakaninsu shi da amna. Ta zuge jakar cikin rashin
tabbas da yaqini,ta bude ne kawai don taga meye yayi saura a cik,me ta samu?,amma ga mamakinta sai
ta samu komai a muhallinsa ba tare da an canzawa komai waje ba bare a cire wani abu,sai wayarta data
nuna low battery da alama ba'abi ta kanta bama bare a sakata a charge.
"Ba abinda aka rasa a ciki musaddiq.....ba abinda ta taba kota dauka" Ta fada da mamaki idanunta cikin
jakar
"Nima dana bude nayi mamaki,amma nace bari na kawo miki ki duba komai bansan ko akwai wani abun
daban ba"
"Aiko yadda na zuba kudin a jere ba'a canza tsarinsu ba" Ta fada tana sake fiddosu
"Amma dai ka yiwa yarinyar godiya ka karbamin number wayarta ko?,ko mamarta na sake yiwa godiya?"
"Ikon Allah......gashi bata bari ko sau daya na mata godiyar alkhairin data yimin ba.....na kasa manta
damuwa da kulawar data nunamin" Annin ta fadi tana juya abun a ranta.
Bai samu ce mata komai ba saboda qarar bude gate da shigowar motocin da suke da tabbacin
baqinsu sun iso
"Alhamdulillah" Anni ta fada tana murmurshi gami da ajiye wayar da jakar a gefe.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 53
Dukkansu da sallaman a bakunnasu suka shigo. Suka amsa musu suna miqewa tsaye tare da dakon
qarasowarsu cikin falon,saidai amna ta kasa jurewa. Da sauri ta taka zuwa bakin qofa ta riqe abbannata
da kyau tana dariya idanunta saman fuskar fu'ad
"Abba sannu da zuwa....hamma....hamma sannu da zuwa" Ta furta matsanancin murmushi yana subuce
mata
"Sannu 'yar abba qanwar hamma.....hamman dai aka matso a tarba aka fake da abba". Abban ya fada
yana lakuce mata kumatu. Dariya suka saki fu'ad yana tayasu da murmushinsa
"Amnee......barkammu" Ya amsa mata cikin kulawa. Sakin abba tayi ta matsa dab da fu'ad din tana
karbar briefcase dinsa
"Su amna an iya munahirci" Muryar sadiq ta shiga kunnenta,sadiq din dake tsaye ta bayansu abban.
Gotasu tayi kadan tana leqensa,sai ta bata fuska
"Duk abinka bazanyi welcoming naka ba.....abba me yasa baku samu wata bolar South Korea kun yar
dashi kun gudo ba?" Ta qarasa tambayar tana kallon abba a shagwabe. Ba wanda maganar bata bawa
dariya ba a cikinsu
"Idan muka yar dashi ke zaki fara qorafin muje mu dauko miki shi ai"
"Dan aljanna" Ta fadi tana juya idanunta abinda zai sake tabbatar maka da sauran quruciya a tare da
ita,hakanan kuma tana fama da sakalcin auta da gasken gaske.
Kasa jiran isowar abban tayi,sai ta taka ta ruskeshi a tsakiyar falon. Ta rusuna tana masa sannu da
zuwa gami da gaidashi duka tare da qoqarin amsar qananun tarkacen dake hannunsa. Cikin nashi
tsananin kulawar da kallon kewa yake amsa mata,fuskarsa ta wadatu sosai da fara'a yana tambayar
lafiyarta dama ta jama'ar gidan gaba daya.
Hankalinsa yana kansu,qauna da kulawar dake tsakanin anni da abba sune abu guda daya tak da
suka rage wadanda suke bashi hope din wataran qila zai iya aure. Soyayyar da sukema juna wani irin
dasashen abu ne da har yanzu yake tasiri a tsakaninsu,babu alamun gushewa sam sam. Yanayin
rayuwarsun yana burgeshi,wata irin mu'amala annin kewa abba,irin mu'amalar da bai taba ganinta ba
tsakanin MAAMAHnsa da ABBEY dinsa ba. Mu'amalar da bai taba zaton akwaita tsakanin miji da mata ba
sai a wajen annin.
Gabanta ya qarasa shima kaman ko yaushe,cike da ban girman nan da yake jinsa har cikin ruhinsa
ya tsugunna yana gaidata. Bata iya tsaiwa saman kanshi ba saboda girman shima da take bashi
sakamakon sunan MUHAMMADU da yake dashi......da wata ajiyayyar kima da martaba da take ganinsa
dashi saboda dattakon halinsa data sani tun bai cika shekara sha takwas bama a duniya.......uwa uba
yadda yake tattalin farincikinta kadai ya sanya kowanne lokaci takejin tamkar jikinta ya tsaga ya fito.
"Lafiya alhamdulillah me babban suna.....jiki na warware tun tuni......dama ta jima bata tashi ba,akasi
kawai aka samu a ranar,nafi tunanin kuma matar da mukayi salla tare ne turarenta yayimin qarfi da
yawa".
Dan qwarya qwaryar zama sukayi cikin falon na duba lafiyar juna,qananun zolaya tsakanin amna
farouq da musaddiq abban yana shiga yana raba gardama kafin daga bisani anni tayi umarni
"Abinci ya zama ready.....zaku shiga ku watsa ruwa tukunna ko?" Ta fada tana duban abba me gayya me
aiki
"Hakan yana da kyau ko me babban suna?" Ya maida tambayar ga fu'ad. Murmushi kadan ya saki,suna
girmama ra'ayinsa qwarai,sunan da yake dauke dashi ya bashi wannan girman a iyalin da suka san girma
da martabar sunan. Wani abu da sam sam bai gani ba ga maamah,tana iya kiransa a lokacin quruciya da
sunan ta kuma zabga masa zagi fada da sauransu
"To abba" Ya amsawa Alhaji hamza yana miqewa. Farouq ne ya miqe ya dauki luggage din fu'ad din yana
nufar qofa
"Muje na taka maka badon halinka ba......don wallahi ka shiga uku duk sanda mukayi aure muka barka
kai kadai a gidan nan". Yayi maganar qasa qasa yadda su abba ba zasuji ba.
"Kayi asara wallahi.....kai ta qara qiba ma kake,kaci gaba da gandamewa a gaban annin?,idan bakayi
wasa ba gaba gaba sadakarka za'a bayar Allah......"
"Munyi asara dai ni dakai mayen aure......idan kun tashi kuyi shelata a masallacin juma'a".
"Basai munkai ga nan ba......owner na diamondchore resources company guda.......ko a sirrance akayi
shelarsa mugun ciniki zamuyi Allah,a zaba maka guda hudu qwarara......matsalar kawai har yanzun ni
kaina bansan color na macen da kakeso ba.....". Shammatar farouq din yayi yakai masa wani wawan
duka sai daya qame,don maganar ta fara isarsa,yasan kuma farouq baisan bari ba,baisan ya isa ba.
"Kaci bashi......sai na dauki fansa.....ka qarasa cikin da kanka na fasa rakiyar" Ya fada yana jingine masa
luggage dinsa daidai qofofin sassansu
"Tafi nono fari" Fu'ad din ya fada yana zura key ma qofan sassansa yana budewa,saidai fuskarsa kwance
take da murmushi yana juya halin farouq din. Shi daya farouq din yakewa haka.....kamar yadda shima
farouq din kawai ke akwai 'yar hakan a tsakaninsu.
"Alhamdulillah" Ya furta a sarari murya can qasan bayan ya isa ainihin bedroom dinsa,yana jin ma'anar
godiyar daga qasan zuciyarsa. Tarin godiya ce fal zuciyarsa game da ubangijinsa,godiyar da har wani
lokacin ya dinga jin baisan ta yadda zaiyiti ba takai gurbin da akeso. Ubagijinsa ya gama masa komai.....ya
kyautata rayuwarsa fiye da yadda yake tsammani.
Komai na sashen nasa a killace a kuma tsaftace akan tsari fiye ma da yadda yakeso. Wani irin
qamshi ke tashi,abinda ya sanyashi sakin wata nannauyar ajiyar zuciya data sanya yaji wani nauyi ya ragu
sosai daga saman zuciyarsa. Yana yiwa qamshi wani jarababben so,a duniya qamshin yana daya daga
cikin jerin abubuwan da yafi qauna. Qamshi yana sanyashi maqalewa waje,kaman yadda akasinsa ke
sanyashi rabuwa da waje.
Yana iya baiwa farouq dinsa komai amma indai ta fannin abinda ya shafi turare ne to zaka iya jin
musunsa dashi. Bai yarda ba a taba masa turaruka,gwara ka zaba ko na nawa ne ya siya ya baka kyauta.
Kayan jikinsa ya dinga zarewa har sai daya rage saura fara qal din vest din jikinsa da gajeran
wandon da bai qarasa gwiwarsa ba. Muradadde kuma ginannen jikinsan nan dake dauke da wasu
lafiyayyun muscles dake alamta ainihin qarfi na siffa ta zahiri da badini ya bayyana,lullube da wadatattun
gargasa ta ko ina. Wankan yakeson yayi amma shigowar kira ya hana masa hakan,tilas ya samu saman
sofa bed ya zauna yana amsa kiran.
Amsa kiraye kirayen ya daukeshi lokuta masu tsahon da har musaddiq ya dinga zuwa dubashi
zasuci abinci. Daga qarshe ya basu excuse akan suci din idan ya kammala zai fito.
Fitowar da bai samu daman yi ba kenan,don sanda ya fito a wankan gaba daya kasala da tsohuwar
gajiya ce ta saukar masa,dole ya haye gadonsa bayan ya maida da dakin dark ta sakin dukka manya
manyan curtains dinsa,ya kuma kashe kowacce fitila da zata iya bashi haske don baya son bacci a duhu
sam sam. Koda baccin yakeyi kana kunnata ka tasheshi. Sunsha fafatawa da farouq akan hakan,don shi
mutum ne da kwana cikin haske bai dameshi ba. Wannan dalilin yasa ko a yanzun yafi sha'awar kowa ya
zauna a sassansa,ba kasafai ya fiya son takurawa mutum da salon tsarin rayuwarsa ba.
*****Su biyun dukansu suna zaune ne saman buzu na fatar dabbar da basusan wacce iri bace. Kaman
yadda dukkaninsu jikinsu ke sanye da sutura ta alfarmar da zaka fahimci rayuwa ta basu sukuni yadda ya
dace,saidai tasu salon miqa godiya wa mahaliccinsu da suka munana hanyarta.
Daga atamfar jikin hajja har lace din da maahma ke sanye dashi wanda ya darawa atamfar hajjan
tsada isashen jari ne ga mutane masu yawan gaske. Kaman yadda jakar maahma din da takalman data
sanyawa qafafunta suke wani jarin me zaman kansa ga wasu mutanen. Takalmin da fu'ad din yayi mata
order dinsa da kanshi tun daga qasar Italy.
Kusan yadda ta bawa mutumin dan duqurqushi me zubin wada hankalinta hajja bata bashi nata
haka ba.
Daya daga cikin qoqunan gabansa da suke kife ya daga,qoqon da babu komai amma saiga haske
ya cikashi. Tafukan hannayensa ya saka yana rufe qwayar da hannunsa nasa. Idanunsa ya runtse,wasu
irin maganganu ya dinga furtawa da ba'a gane abinda yake fadi,tun yana fada a hankali a hankali har ya
fara furtawa da sauri da sauri da kuma qarfi har muryarsa tana amsa kuwwa. A hankali jikinsa ya fara
wani irin kakkarwa tamkar wanda aka jonawa shocking. Da wani irin sauri yan fusge hannayensa daga
saman qwaryar yana yarfar dasu kamar wanda wuta ta taba,sai kuma ya sake maidasun yana canza
salon yaron da yakeji ba irin na dazu ba.
Ya kusa minti biyu a haka,wata irin zufa da basusan daga ina take ba ta gama jiqeshi sharkaf.....a
hankali a hankali ya soma sassauta muryarsa sannan ya fara daidaita yanayinsa kafin ya bude idanunsa
da suka ninka ja akan asalin jan da suke dashi.
"Matso!" Yace da maamah a tsawace. Tsoro ba kalma bace da ta santa ba kaf ray uwarta......qafafunta
sun taka gurare da dama amma a yanzun saita samu kanta cikin shakka da d'ar d'ar har ta matso zuwa
inda yake mata nuni
"Ba shine wannan ba?" Ya fada da qarfi yana nuna mata qoqon.
Fu'ad ne kwance saman gadonshi yana baccinsa hankali kwance kaman yadda ya kwanta a ainihin
dakinsa dake gidan Alhaji hamza kibiya. Mamaki ya qarasa cikata,ba shakka fu'ad ne,kuma dakin ya mata
kama da dakunan gidan Alhaji hamza,sun dawo kenan kaman yadda yake shaida mata dazu da sassafe
kan suna hanya?.
Daga ita har bokan ba wanda ya samu cewa wani abu dif hoton dake cikin qwayar ya bace
kaman an dakeshi harda tartsatsin wata wuta.
"Kin gani ko?,ba mutumin da muka sha wahalar kawoshi zuwa garemu saishi......baya ga haka kinga
yadda surarsa ta dauke da gaggawa......abinda ke bamu tabbacin aikinsa yasha banban da dukka ragowar
aiki da muka taba yi a baya......akwai tashin hankali......akwai wahala.......akwai kuma qalubale!!!" Ya
furta da kakkausar muryarsa mara dadin amo da sauti bare sha'awar saurare.
Dukkan kayan aikin nasa ya tattara ya zuba cikin qwarya daya daga cikin qorai biyu dake
gabansa,take suka bace bat tamkar ba'a taba halittarsu ba a wajen.
Jajayen idanunsa da babu rahama,musulunci ko imani a ciki ya daga ya kalli maamah dake
dubansa babu ko qiftawa.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 54
Idanu yadan zuba mata na wasu mintuna da har sai data dan sha jinin jikinta. Sai kuma ya saki
wani busashen murmushi da yafi kama da kukan jaki yana kallonta
"Ba shakka kin haifi jarumi......kin haifi yaron da taurarinsa suke da tsananin hasken da ba kasafai ake
samun galaba ayi kutse a cikinsu ba ko asha kansu.......yaronki yana tattare da abubuwan al'ajabi da
baiwarwarki masu yawan gaske wadanda ko ke uwar da kika haifesa bakisan yana dasu ba......cikin
mutane dubu guda daya ake iya samu irinsa......". Kai kawai take jinjinawa tana sauraronsa. Tun sanda ta
haifi fu'ad din tasan daban yake da sauran yara,to amma a yanzun kalamansa daga mata hankali
sukeyi,kamar sunason shinshina mata rashin nasararta ne......kamar suna shinshina mata rashin yiwuwar
aikinta?.
"Aiki a kansa ba qaramin abu bane me girma......akwai tsari a jikinsa......yana da addu'a sosai tare da kare
kowanne abu da musulunci yayi umarni akai.....baya shan giya.....baya zina.......baya kallace kallacen
abubuwan haramun......hasalima azumin da addininku yace a dinga yi litinin da alhamis baya
wuceshi.....abinda zai bada mamaki banda wannan uwar goyon nasa da uban goyonsa ba wanda yasan
yanayin wannan azumin koda farouq makusancinsa......."
"Kana nufin yanzu mallakar da nakeso ayi masa.....da shiga tsakaninsa da iyayen goyonsa bazai yiwu ba
kenan?" Ta dawo dashi zuwa ga ainihin amsar da takeso taji.
"Zaki iya samun biyan buqata.....zaki kuma iya samun faduwa......biyan buqatarki ya ta'allaqa da adadin
sadaukarwar da zakiyi da kudaden da zaki ajiyewa shaqiqanmu don suyi miki yadda ya dace......amma
fa....." Ya fada yana daga yatsa
"Tabashi abune da zai iya zuwa da hadari......mafi qarancin sakamako shine a gaza yin nasara a
kansa......muddin rashin nasarar ta zarta haka kuwa.....dani da dukkan wani shaqiqi da mukayi aiki dashi
zamu iya samun nakasa,harda shudewa daga rayuwa ma idan ta dauro,saboda haka......aikinki aikine me
tsadar gaske " Yayi maganar yanayin muryarsa daga qarshe yana canzawa alamu dake nuna saukar
mutanen boyen da yake aiki tare dasu a kansa.
"Kalli nan!" Taji an furta daga bakin mutumin amma da mabanbantan muryoyi marasa dadi da batasan
mutum nawa bane suka hadu suke maganar.
Waiwayawa tayi tana duban inda ya daka,saiga lambobi a jere wanda data dubesu da kyau suka
bayyana kansu a matsayin million goma.
Sosai adadin ya daketa,duk da tasan a qa'ida tana cikin arziqin data bawa wannan adadin baya
amma kuma batakai ga samunsu ba zuwa yanzu. Ta waiwaya ta kalli hajja dake zaune tana kallon
komai,don dokarsa shine me matsala dashi yake magana. Da idani ta mata tuni da tsarinsa,baya yanka
kudi a nemi ragi.....daya daga cikin kusakuren da zaka iyayi wanda zai tunzurashi kenan.
Kamar wadda wuyanta ya qage ta maido dubanta gurin,saidai zuwa sannan lambobin da hasken
da suka nuna mata yawan abinda zata biya din ya shafe daga wajen ba komai. Ta maida kallonta ga
duqurqushin bokan da kamanninsa suka juye,saita gyada kanta
Sau biyu hajja tana juyawa tana kallon maamah wadda ta kafe kwaltar da driver ke zabga gudu
akai. Tunda suka fito daga wajen bata ce komai ba,magana bata hadasu da kowa ba. Tun a dazun ta
fahimci tayi nisa ne qwarai a tunani,kaman ta qyaleta amma sai ta kirayeta don tanaso taji ta bakinta
"Banji kince komai ba tunda muka fito?" Ajiyar zuciya me nauyi ta sauke sannan ta dora idanunta akan
na hajja din
"Daga yanayin ayyukansa,da kuma bayanansa kawai na gamsu cewa aikinsa me zafi ne......abinda kawai
ya tsayemin a rai yanzu shine ta yadda wadannan kudaden zasu samu" Tayi maganar alamunta suna
nuna lallai lallai a matse take da buqatar mafita
"Danki ne,dole ki bashi umarni yabi don babu wata uwa sama dake......idanma hakan bai yiwu ba,cikin
kadarorinki ki saida wani abu.......ko kice masa wasu zaa yiwa wani abu da kudin da zarar yasa anyi abun
ki saida abun kiyi zarafin gabanki". Ajiyar zuciya ta sauke ranta yana mugun baci
"Yanzu har takai idan ina da buqatar abu a wajen dana saidai nayi qarya ko na biyo ta wata hanyar?" Ta
yiwa hajja tambayar.
"Biyan buqata ai yafi dogon buri,kome ya faru.....kuma kome kika saida,wuyarta aiki yayi yadda
akeso......sai kin maida ninkin baninkin da bakisan adadinsa ba......sai kin karba kin gaji......saikin tara fiye
da yadda kike buri......saikin zame musu tamkar abun bautarsu wajen yi miki biyayya.....a yanzun da zan
kira auwal dake wata qasar,nace masa ya dawo nigeria yau yau inason ganinsa.......na rantse miki da
Allah a qasar nan zai kwana,koda babu jirgi bazai kwana a gida ba saidai a airport.......saidai idan nice
nace masa ya koma gida ya kwanta ya taso gobe......koda ya koma bashi da cikakken nutsuwa har sai gari
ya waye ya kawo kansa gareni......bari yau zan nuna miki qarfin ikona ki gani da kanki" Ta fada tana fiddo
wayarta daga jakarta.
Kai ta jinjina kawai tana dubanta,tana jin inama ace itace hajja?.....tana hasashen ranar da wannan
damar zata samu a hannunta?.....tabbas saita sanya aminatu kuka da idanunta........sai ta sanya zuciyar
aminatu da hamza sun buga da qasqancin da zasu gani daga yaran da su suka rainesu har suka zama
abinda suka zama a yanzu
(Tabbas gaskiya ne da akace ka guji sharrin wanda ka kyautatawa.......me makon jin dadi kyakkyawan
fata da kyakkyawan mu'amala ta shiga tsakaninsu da mutanen da suka maida mata 'ya'ya
mutum.....amma ga nata salon sakamakon,Allah kayi mana tsari daga sharrin dukkan wani abu me sharri
mutum ko aljan,me rai ko maras rai ameen ya hayyu ya qayyumu).
Bugu daya tak aka daga kiran da hajjan tayi,muryarsa ta fito tarwai yana gaidata. Cikin kulawa ta
amsa masa sannan tace
"Kaga yahaya.......naje unguwa ne sai na sallami driver da xummar zan tuqo kaina na dawo gida......."
"Me yasa hajja?,ta yaya zakiyi tuqi da kanki?" Ya fada a tsananin firgice kaman wanda akace masa ta
hallaka. Murmushin qasaita ta aje
"To ai yanzu ma gashi na kasa dawowa din da kaina duk kasala ta rufeni...."
"Matarka nakeso ka turomin ita zata maidani......kace ta kirani na bata kwatancen inda nake yanzu haka
ina jiranta......kada kuma ta batamin lokaci" Ta fada tana bata rai
"An gama" Ya fada zuciyarsa na rawa.
"Kinsan matar da nace a kiramin?" Kai maamah ta girgiza tana shakkar yiwuwar wanzuwar umarmin da
hajjan ta bada yanzu yanzu
"Matarsa ce......itace taso dagamin yatsa taso tayi fito na fito dani,a zatonta tana da malaman da xasuyi
mata aiki fiye da nawa......tanaso ta mallaki yahaya ta mallakeni.....har na sanya ya saketa na sakashi ya
dawo da ita don tazo taga iyakarta......taga iya mizanin nawa aikin.....don tazo ta banbance tsakanin aya
da tsakuwa,ta sake kuma fahimtar da gaske fa shi ruwa ba sa'an kwando bane......ita kanta a yanzun sai
yadda nace mata,duk dana fahimci kanta yana fusga wani lokaci kaman wasu abubuwan idan nayi mata
tana jin ciwonsu,shi yasa nakeson na qarasa horata da kyau" Kai kawai maamah take jinjinawa,abun yayi
mata da kyau.....salon kuma ya burgeta yahau mizani da gwargwado na abinda take hasashen
shimfidawa kanta. DA FUAD DA MUSADDIQ DAMA MATAYEN DA ZASU AURA SU ZAMA QARQASHIN
IKONTA. wannan shine cikakken iko da isar UWA. Ta fada a ranta
"Wannan shine cikakken iko da isa.....ki katange komai kaman yadda sanda kk sha wahalar komai din ke
daya kk sha" Hajja ta fada tana jinjina kai
"Indai ni na haifi fuad ya zama tilas ya fidda kudaden nan ya bani.....zan motsa masa qwanjina.....zan
kuma banbance masa uwa da mahaifiya a wannan lokaci karo na farko" Maamah ta sake fada a ranta.
Ya jima riqe da wayar bayan gama waya da mahaifiyar tasa yana juya wayar a hannunsa. Sassa
biyu na zuciyarsa kowanne na qalubalantar dan uwansa.
"Tayi daidai,ko mutuwa hajja tace muyi daidai ne......ai ta isa....girmanta yana da yawa,to laifin me ma
tayi?,koni ta kira zuwa zanyi bare matata,komai tayi a kowanne lokaci ko yanayi daidai yake" Daya
sashen yake fadi,yayin da daya sashen zuciyarsa yake cewa
"Ta yaya tana tsaka da hidimar gida,ya tabbatar yanzu haka tana can tana yiwa hajjan girkin rana daya
zama wajibi aka kowacce matar danta tayi mata shi kulli yaumin rana da dare ba fashi......(tsarin girkin
abincin gidan tsarin girki ne na bai daya,duk da irin girma da wadatar gidan tukunya daya ake dafa
abincin safe rana dana dare,raba girki ne a tsakanin faccaloli tamkar kishiyoyi,kowacce zatayi kwana biyu
'yar uwarta ta karba,hakanan a tattare a babban dining room dake dauke da family dining table akecin
dukka abincin. A nata fadin don a tattala mata dukiyar 'ya'ya,kuma dukkansu zasu samu sauqin kashe
kudi a gidajensu,tunda kome zaa siyo hadin gwiwa zaayi a kawo......amma kuma ta gefe daya.....tsabar
nuna isa izza da mulki ne,da kuma dabarar karantar motsin kowa cikin gidan ba tare data shiga sashen
kowa ba don ta tattaro kowa din waje daya.
A yanzun ya tabbatar tana can tana wannan hada hada.....bama wannan ba......fita haka katsam a
lokaci guda ba shiri?. Wannan sashen dake hango masa rashin dacewar shine sashe mafi rauni a
zuciyarsa,don haka wancan bangaren ya rinjayeshi ya danna mata kira kanshi tsaye.
Sanda maamah ta bude baki da zummar sake magana kira ya shigo wayar hajja. Ta daga wayar
tana kalla,sai ta sake wani murmushi me sauti
"Naja'atu ce" Ta fada cikin nishadi,saita daga wayar tana sanyata a hands free
"Salamu Alaikum hajja......daddynsu arfat yace kina buqatar nazo daukarki......kina daidai ina?" Fuska ta
tsuke tamkar ba itace ta gama dariya yanzu ba
"Ke banason hauka......haka akeyi daga kiran waya ba gaisuwa ba komai?,duk kinzo kin gaidani dazu da
safe amma yanzu mecece?,la'asar fa muke dosa?" Shuru yadan biyo baya kafin muryarta ta sake
bayyana a karye
"Ina 'yan kaba,kizo daidai bakin kasuwar turawa ki jirani" Daga haka ta katse wayar.
Dubanta maamah tayi tana mamaki
"Hajja me kuma zai kaimu 'yan kaba?,ai sam ba hanyarmu bace" Zamanta ta gyara tana sake sakin
shu'umin murmushi
"Eh mana.....ai so nake ta sake gane girman izzar tawa......sai bayan mun isa gidan ki zaki fahimci sauran
aikin". Sosai maamah ke duban hajja din,lallai dole tasha kan kowa da komai,dole ta murxa kambunta
yadda takeso. Sai yanxu take tambayar kanta ya akayi tayi sanyi haka ta sake?,hajjan da a baya a wajenta
take daukan courses na abubuwa amma yanzu nema take ta zama malamarta qarfi da yaji?.
"Ai duk wanda yayi bacci a wannan zamanin zaiga bacci.....ba yara na ba ba surukaina ba.....hatta da
jikokina.....yara da manya dukka sai abinda hajja ta shimfida"........
Ji yayi tamkar an daka masa tsawa tsakiyar baccinsa ana kuma masa umarni da ya farka. A nutse
ya farka saidai kuma yanajin wani irin sauti mara dadi yana amsa kuwwa cikin kunnuwansa tamkar dai a
mafarki akayi masa tsawar. Idanunsa ya lumshe a hankali yana son tuna abinda ya faru din,amma kansa
blank bai iya hasaso komai ba
"Hasbiyallahu la'ilaha illa huwhuw,alaihi tawakkaltu wa huwa rabbul arshil azeem" Ya furta a hankali
bakinsa yana motsawa.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 55
Tsam yayi da ransa yana jin yanayin jikinsa yana sauyawa daga ainihin yadda ya kwanta din a
dazun. Numfashi ya aje a hankali ya yaye blanket din ya miqe,ya zauna sosai saman gadon. Duk da
knocking din da akeyi din hakan bai hanashi hada hannuwansa guri guda yayi addua ba,ya shafa saman
fuskarsa a nutse sannan ya zuro qafafunsa qasa ya miqe.
A nutse yake takowa zuwa ainihin falon nasa dake cike da nutsuwa,shuru tamkar ba cikin gidan
yake ba,komai komai cikin matsananciyar tsafta a killace kamar yadd yakeso koda yaushe ya dinga ganin
komai a hakan.
Yana ci gaba da jin jikinsa da wata 'yar maqalalliyar kasala har ya isa qofar falon,ya murza key ya
bude qofar amma bai murza handle ba,ya barta a haka yana komawa da baya hadi da bada umarnin a
shigo.
Tun bai zauna ba ta sako qafafunta falon,dauke da wani kyakkyawan kwando me qananun
tayoyi,yana da mariqi tamkar na luggage ko trolley da zaka iya rageshi ko ka qarashi sannan ka jashi
yadda kakeso.
"Wa'alaikumussalam" Ya amsa yana zama saman daya daga cikin qawatattun sofas din da suka yiwa
falon qawanya masu tsananin taushi da kyau na gaske,yasa hannunsa yana lalubem remote na A.c din
falon don ya rageta. Shi din ba kasafai ya fiya son ac ba ko ya qureta har haka ba,wannan din sai oga
farouq,a nan ma zaka iya jin kansa dashi.
"Hamma barka da warhaka". Ta fada cikin shagwabarta da marairaitar nan tata data zama a halittarta.
Labbansa ya motsa kadan da wani yanayi da yafi kama da murmushi
"Habibtyn hamma" Ya furta a nutse kaman yadda tsoron qarewar haruffan bakinsa. Sunan daya kiratan
dashi ya sanyata ta sake rakwarkwabewa. Ta tabe fuska tana kallonsa
"....hamma na dauka ka daina yayi na......BB farouq yacemin ka samo wadda ta sace zuciyarka.....tunda
ta sace zuciyarka wai kuma tayi snatching naka a wajen kowa....she owns you ita kadai". Qaramin
murmushi ya sake subuce masa wanda yafi na baya. Rigimar amna yawa ne da ita,har yau bata girma
baisan kuma sanda zata girma din ba,yafi tunanin aure ne kawai zai kawo mata wannan hankalin da
girman. Gefe daya farouq,shikam a duniya yanaso yaga ya tubura amna din,wani lokacin yana yi ne
kaman hankalinsu daya,abinda kuma bazai taba zama hakan ba
"Zo nan" Ya fada yana yafitota da hannu gami da nuna mata gefansa. Sai ta tako din a hankali ita da
kwandon nata har ta iso gabansa ta zame ta zauna sosai
"Baki gaya masa tare zaku zabi mata da hamma ba?,baki gaya masa sai wadda kikace tayi kinaso sannan
hamma ya aura ba?" Yayi mata tambayar yana kallon qwayoyin idanunta abinda ya qara mata karsashi
da qwarin gwiwa. Murmushi ya subuce mata data tuna da wannan
"Na gaya masa hamma sai ya tabe baki,kasan me yace?" Kai ya girgiza yana qara girmama quruciyar
amna din,tabbas auta ba wasa ba,ko yaya sai wannan quruciyar ta tabashi
"Wai ita soyayya ba ruwanta da jiran lokaci ko dacewa,sace zuciya takeyi ko an shirya ko ba'a shirya
ba....." Ta qarasa maganar daidai sanda farouq din yayi knocking hadi da turo qofar yashigo gaba
daya,don yaji muryarta alamun suna zaune daga falonne.
Tsaf kalaman nata da suka fito daga bakin farouq din duka zauna masa akai,sai ya daga kai yana
dubansa sanda yake takowa falon. Ya bude baki zai fara mata tsiyan nashi fu'ad din ya tari numfashinsa
"Kai kakeso ka lalatamin kunnuwan qanwa?.....kai kake karanta mata yadda soyayya take ko?".
Wani dariya ya saki yana saka hannu ya dauki green apple guda daya cikin apple din dake ajiye
cikin wani dan kwando nan saman fridge din dake kusa dashi yana takowa falon
"Har yanzu kallon jaririya kuke mata ba?.....zakusha mamaki sanda ta kawo wani tace itace shi
takeso,aure takeso kuyi mata".
"Hamma....." Ta fada idanunta suna yin rau rau tana duban fu'ad. Hannu ya daga mata alamun tayi shuru
kada tace komai,sai ya maida dubansa ga farouq din
"To sai me?,idan ta fada dinma ai daidai ne". Yana zama a gefansa yace
"Ni zanfi kowa murna da hakan ai......tashi ki bamu waje" Farouq din ya fada yana komawa serious dinsa.
Duk sanda yayi irin hakan ta tabbatar Lokacin wasa ya fita kenan,don haka bata musa ba ta tsugunna
tana rage plates da bowls din da tasan fu'ad ya gama amfani dasu saboda ta sanshi bai fiya son tarkace a
waje ba,yanzun saisu sanyashi fasa cin abincin gaba daya.
Spoon ya dauka kawai ya saka a plate din fu'ad din bayan fitar amna,wannan din ba wata sabuwar
dabi'a bace,kusan sun saba cin abinci kwano daya,tun daga wancan lokacin da suke fafutukar rayuwa da
samarwa kawunansu 'yanci,har zuwa yanzun da suka zama cikakkun mutane kuma 'yantattun 'ya'ya.
A nutse suke cin abincin kuma ci gaba da tattaunawa akan tafiyar tasa. Har suka kammala basu
tashi a gun ba,sai da kiran anni ya shigo masa waya.
"Ka shiga wajen maamah kuwa?" Tambayar data fara yi masa kenan
"In sha Allah anni" Ya fada a nutse,sai ta katse wayar shima ya sanya hannu yana sauka daga bangaren
kiran gami da fidda siririyar iska daga hancinsa.
Miqewa farouq yayi abinda ya sanya fu'ad din daga kai daga zaune ya kalleshi. Kafin yakai ga
tambayar shi ya rigashi magana
"Na jima ban shiga abuja ba,ina jin gobe ko jibi zan shiga din......."
"Safe journey" Fu'ad din ya fada a taqaice yana miqewa shima. Siririyar dariya farouq din ya saki yana
tsare fu'ad din da ido wanda alamu ke nuna yana Neman hanyan wucewa ne daga wajen
"Kar muyi haka dakai.....karka canza kuma daga yadda na sanka......ko da da sau daya baka taba yimin
kara ka rakani wajen fannah ba.....kayimin alqawari next time idan na tashi zuwa tare zamuje......."
"Yanzun daga daukomin dogon sharhin nan farouq.....cewa nayi bazani ba?.....kawai dai kasan ba abu
bane me sauqi gajimare ya gama yawo dani na sake komawa wani tsakanin kwana daya ko biyu
kawai......infact ma kasan yanzun shirye shiryen dake gabanmu ai.......ba cikakken lokacin batawa a irin
wadannan abubuwan.....but duk da haka bazan karya alqawari ba.....if zaka iya jirana na kammala sai
muje din". Dariya ce taso qwacewa farouq din amma ya maze,ya san dama zaa rina,kuma wannan dogon
bayanin da yakeyi duka yana neman hanyar guduwa yaqi zuwa ne.
Bai taba ganin mutumin da soyayya bata taba burgeshi ko d'ad'ashi da qasa ba ko yaya takai ga
bawa jama'a sha'awa ba irin fu'ad din. Bawai ya tsani mata bane......aah......amma yadda yake nesa
qwarai da al'amuransu kai tsaye idan kace bai jituwa da shirginsu bakayi laifi ba.
"Kanka tsaye kacemin yanzun ma ba zakaje ba.....kacemin ka shirya nunawa fannah iyakata....ni din ba
kowan kowa bane a wajenka" Ya fadi yana hade rai sosai idonsa akan fuskarsa. Kallon idanun farouq din
yayi,bai wani damu ba yasan halin kayansa sarai,yasan ya fada ne don ya motsashi,don haka ya daga
kafadunsa
"Ka fada soyayya ne at wrong time......har yanzun kana da sauran lokaci da ya kamata ace kana gina
kanka ne bawai soyayya ba......ita soyayya idan lokacinta yayi zata kawo kanta da kanta"
"Kaiii.....inaaa......a wannan lokacin da mutum ke bacci da qyar?,am against you fa har abada indai ta nan
wajen ne.....kaidai da waccan aljanar tayi maka shigar sauri zamu ci gaba da nema maka magani......" Bai
qarasa ba yaji saukar spoon a kafadarsa,ya goce spoon din ya fadi qasan marbles,sai ya soma sauka daga
dining area din yana dariya abinsa gami da cewa
"Tafiya abuja dole ce......zan siya ticket harda kai......alfarma daya zan maka zan daga zuwa next week
cikin weekends din" Yana kaiwa nan ya fice abinsa daga parlor din.
Kai kawai ya girgiza yana murmushi qasan zuciyarsa. Bazaice ko sau daya ga sanda suka taba
samun sabani da farouq ba ko wani ya bata ran dan uwansa. Wani hadi ne daga buwayi gagara
misali,idan kaga musaddiq da Sadiq zakayi tunanin sune uwayensu daya,kaman yadda da yawa ake
tunanin shi da farouq din twins brothers ne da suke da kamanni daban daban.
Baiyi mamakin jin ba ruwan zafi a toilet kaman yadda ya saba samu koda yaushe ba,don dukka
ma'aikatansa da sauran masu masa hidiman sassansa ya basu hutu na satittikan tafiyarsa south
Korea,don haka ya kunna heater ya dawo cikin bedroom din sannan ya wuce kai tsaye yana fita daga
ciki.
Qofa ce qwaya daya tak wadda batakai duka sauran doors din falon fadi ba,ya budeta ta hanyar
key din dake maqale a jiki ya turata a hankali ya shiga.
Dakin yana da dan duhu don haka ya laluba makunni ya kunna fitila take haske ya gauraye dakin
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 56
A yadda qofar dakin take daga waje,ba zakayi tsammanin taras da yalwataccen daki me wani irin
tsari da kyau ba kaman haka. Ci gaba yayi da kunna kowacce fitila ta cikin dakin,kama daga ta bango
zuwa kyawawan table lamps masu wani irin kyau me daukan hankali. Wani irin guri aka tsaga daga
sashen nasa da yayi Linkin da ainihin farfajiyar gidan bangaren da duk yawan taro ko hayaniyar jama'a da
gidan zaya tara zaiyi wuya ka iya jinta muddin kana wajen. An qawatashi da wasu irin shelves da drawers
masu mugun kyau da daukan hankali da aka tsara takardu documents zuwa litattafai nau'i daban daban
daga yarukan duniya daban daban da yake iya fahimta yake kuma iya magana da wasunsu.
Ragowar bangunan kuma manyan frames ne masu asalin kyau da tsada na qasar turkey da dubai
da aka kashewa kudade masu ciwo aka tsara sunayen Allah da ayoyin qur'ani masu girma da wani irin
ruwan gold daya sake baiwa frame din kima kyau da daraja. Akwai kyakkyawan table din daya zama
cikon ado wa home office din nashi da yake hade da kujerarsa,sai kuma wasu cushions da aka zuba
gajajjeru da ba zasu bata tsarin wajen ba,daura dasu kadan kuma wani board ne dake dauke da rubuce
rubuce barkatai da baya rasa alaqa da tsare tsare na abubuwan da ya sanya a gaba zaiyi.
Komai na room din neutral color ne kaman yadda dayan bedroom dinshi yake,abinda zai
bayyana maka kenan normally bayason kaloli masu hayaniya can can can.
Da gaske a yanzun target dinsa shine bude kamfanin......babban burin da a yanzun bashi da wani
sauran abu daya rage masa kamar shi,saidai abune daya tabbatar yana buqatar qarin jajircewarsa da
kuma aiwatar da komai cikin sirri har sai an kai gabar da ya kamata komai din ya bayyana.
Ba alaman qura ko datti ko qwalli daya,don duk wanda ke aiki dashi yasan tsarinsa da kuma
dokarsa. Waje ne da ba wanda yake bari ya shigar masa sai family dinsa,anni farouq amna saddiq sai
musaddiq......sai kuma amintaccensa mutum guda daya me sunan malam.
Ya bude lockers da yawa,ya kuma jona abubuwa da yawa kafin ya daidaita komai ya juya yana
fita a dakin da zummar zuwa sanda zai dawo komai ya zama normal,don yau din aiki yakeson yi sosai
kafin ranar Monday ya isa kamfani ya duba yadda ya barsu.
Fes ya fito a shirye,sanye da lallausan yadin filtex fari qal mai qarancin nauyin da har kana iya
hangen farar vest din jikinsa data lafe takuma saje da yadin sosai saboda tsananin haskenta. Sassanyan
qamshin nan nasa dake da daukan hankali yake fitarwa sannu a hankali,fuskarsa tayi fresh cikin yanayin
da zai nuna maka cikakkiyar nutsuwar zuciya da ruhi da yake da ita. Sabanin wasu lokutan,yanzun kanshi
saye yake da hular data dace da yadin jikin nasa,sai half covers din daya sakaye doguwan qafansa a ciki.
Komai rashin nisan waje bazai taba iya taka qafarsa ba tare da ya sanar da anni ba,yanzunma
sassanta ya bulla,yana tafe yana amsa waya har ya cimma sassan nata.
Bai iya ci gaba da amsa wayar ba sanda qafafunsa suka shiga ainihin falon,sai ya zare wayar daga
kunnensa sakamakon sautin karatun qur'ani dake fita daga speakers din dake daura da qatuwar plasma
din dake girke saman mulmulallen tv stand din.
Karatu ne cikin muryar babban malaminsa sheik abdurrahman assudais,qira'ar dake balain kashe
masa jiki tare da saukar masa da nutsuwa koda yana cikin bacin rai. Falon anni na dabanne,badai ka
shigo ka samu ana kallace kallace marasa ma'ana ba bare akai ga batun jin kida ko waqa,kusan duka
haka ta azasu akai,suma kuma haka suka taso.
Lokaci irin wannan magariba ke kan hanyar qarasowa,zaka sameta zaune cikin kamala tana wani
abun da zaya amfani lahirarta,imma girkin abba ita da amna,ko ka sameta da carbi,ko tana sauraren
wani karatun addinin.
Yanzunma suna tare da amna din,wanda daga gefan amnan kadan wata baquwar matashiyar ce
da zata girmewa amna din da aqalla shekaru biyu ko uku.
Yana shigowa ta sanya remote tayi qasa da karatun sosai tana murmushi. Ya qaraso a nutse ya
zauna daga gefanta yana tanqwashe qafafunsa tamkar ba wanda yayi shirin fita ba,sai kuwa ta tareshi
"A'ah miqe....ai sai ayi magariba kana zaune a nan.....kaje ka dawo.....don abincin dare ma yau banda kai
a gidan nan" Girarsa duka biyun ya daga alamun mamaki,yanayin daya qarawa fuskarsa wani irin kyau,ya
kuma fusgi hankalin matashiyar qwarai da gaske
"Anni yau din nayi wani laifi ne....?" Ya fada calmly idonsa akan annin. Kai ta girgiza
"Ko kadan......kawai nasan idan kayi dinner a daya gidan naku hakan zai farantawa maamah sosai,zai
kuma sake bada fahimtar juna da shaquwa a tsakaninku". Tayi maganar cikin kwantar dakai itama tare
da fatan kaishi zuwa ga abinda takeso din.
Kansa yadan motsa kadan,har yanxu anni kaman bata fahimci daga ina ainihin tushen matsalarsu
ya fara ba?,har yanzu kuma kamar annin bata fahimci menene yake riqe da matsalar tare da sake wanzar
da ita ba?,wanne fahimtar juna da shaquwa a yanzun ake nema tsakaninsu ne?.
"Saika dawo......kace ina gaidata" Ta fada tana daukan remote zata qara volume,abinda ke alamta masa
ta gama fadin bayaninta kuma batason yayi sharhin komai akai
"Lovy dovy" Ya fada yana xuba hannunsa a aljihun rigarsa yana jin karsashinsa da duk wani walwalarsa
yana ja baya tamkar wanda aka tura gidan kaso.
Murmushi tayi,tsokanarsa takeso tayi amma kwarjinin nan nasa ya taso ya danneta
"Say it amna....." Ya maida mata cikin caring din daya kusa sanya matashiyar narkewa. Bata taba zato
koda a mafarki yana da wannan siffar ta kulawa haka ba......bata taba hasashen akwai dabi'a ta sauqin
kai a tattare dashi har haka ba
"Muhammadu.......yi tafiyarka......ku wuce ciki keda unaisa ku wankemin bottles dinnan,suna kitchen
basu da yawa".
Duk da yaso ya wuce din kamar yadda anni tace amma dole sai daya dan tsaya a farfajiyar gidan
suka gaisa da ma'aikatan gidan,sannan kuma me sunan malam yayi masa tattaki suka fice daga gidan
bayan ya shaidawa security dinsa ba nisa zaiyi ba baya buqatarsu.
Yana takawa a nutse yana sake fuskantar gidan wani yanayi yana riskarsa,abubuwa masu tarin
yawa da suka saba dawo masa a duk lokacin da zai gifta ko ya shiga gidan.....al'amura masu nauyin dake
iya motsa zukata qwarai da gaske. Wannan yana daya daga cikin abubuwan da suka sanya yake janye jiki
da rayuwarsa sosai daga gidan. Duk da komai na fasalin gidan ya canza,ba wani abu da yayi saura
dangane da ainihin ginin gidan na baya,to amma dai wannan filin....wannan gurbin da wannan muhallin
da aka aza tubalin ginin gidan har yanzu dai shine a wajen. Har yau har kwanan gobe idanunsa basa
mantawa da tsarin gininsu na asali,wannan ya sanya idan ya kalli wasu guraren sai ya tuna da JADDA sai
kuma ya tuna da ABBANSA,duk da guraren a yanzun sun sauya sun koma wasu abubuwan na
daban,amma tambarinsu yana nan kafe qasan ransa da zuciyarsa.
Cike da girmamawa,martabawa tare da kallon Cikakkiyar kima da darjtawa malam sa'idu yake
miqewa sanda ya fuskanci dosowarshi gidan.
"Barka da zuwa yallabai.....sannu da zuwa" Malam sa'idu yake fadi cikin mutuntawa.
"Barkanmu da warhaka baba.....mun sameku lafiya?" Fuad din ya furta shima cikin tsananin bada girma.
Malam sa'idu bawai me gadi bane kadai a gareshi,yana da wani role da yake takawa da kuma wani
ajiyayyen matsayi da fuad din ya bashi ba tare da sanin kowa ba.
Malam sa'idun da asalinsa me saida kayan marmari ne a bakin titin tsohon layinsu,wanda a yanzun
layin ya koma tacan katangun gidansu yake,qofofin sun dawo bayan gidansu na asali,inda kusan gaba
daya fuad din ya siye layin sai tsirarun gidajen da suke mazauna ciki suna da buqatar zama a ciki. Tun
asali bayan layin nasu suna kiransa ne dama da layin 'yan gayu,don kusan manyan gidaje ne ata
wajen,kamar yadda kusan mafi rinjayen unguwar tasu layinsu ne kadai keda qananun gidaje jifa jifa. To a
yanzun layin duka ya zama qarqashin kulawar fuad da wani irin kwalta da aka zuba,gate a farkonsa da
qarshensa da manyan fitilu jere reras.....cctv cameras da masu gadin layin saboda tsaron dukiyar
mazauna layin da rayukansu.
Bayajin malam sa'idu zai iya ficewa daga tarihin rayuwarsa ko zuciyarsa. Yadda mahaifinsa baya
iya cin komai haka malam sa'idu zai hada fruit ya bashi daidai qarfinsa lokaci bayan lokaci duk sanda
Allah yakai wucewar fuad ta wajen,ana tsaka da haka malam sa'idu yaje ganin gida,bai kuma dawo ba
har sai bayan wasu shekaru. Bai manta da yadda malam sa'idu ya nuna jin ciwon rasuwar abbansa
ba,wannan ya sanya ko da rayuwa ta kawosu inda suke a yanzun ya nema malam sa'idu. Kyautata
rayuwarsa yayi da gasken gaske ba tare da mutane sunsan da hakan ba......amma sai ya ajeshi a
mazaunin me gadi bisa shawararsu da amintarsu shi da malam sa'idu din,kuma hakan bai hana ya bashi
albashi ba duk wata,saidai ba irin albashin da ake jifan gamagarin masu gadi ba. Malam sa'idu baisan
wace maamah ba bare anni,tun a baya wajen sana'arsa yake lazimtar zama,bai tara jama'a bare gulma
dayi da gidajen alumma ya shigo ciki har yasan abinda gidan wani ke ciki,abu daya ne dai da har yau bai
fahimta ba,jaddada gadin gidan da kula da shige da ficen matar gidan daya kasa tantance matsayinta a
wajensa. Da yake bame damuwa da abinda bai shafeshi bane bai taba tambaya ba,yana dai aikinsa
yadda akace,duk kuma abinda muhammad din yake da buqatar sani yana sanar masa.
"Mu zauna daga nan" Fuad ya fada yana neman wajen zama saman bencin da malam sa'idun kan dan
kashingide akai wani lokaci.
"Aa haba yallabai.......ai sai ka bata kayanka kuma......bari a dauko maka kujera daga cikin gida kafin
mutanen gidan su qaraso"
"Yi zamanka" Ya fada cikin ko in kula. Mamaki ya sake kashe malam sa'idu. Duk uwar dukiyar daya
mallaka,kyau....ilimi duk basu sanyashi jin ya bambamta da sauran jama'a ba.
"A'ah....su biyu ne" Ya amsa masa kai tsaye,don ba tambayar da zaiyi masa da zai boye masa wani abu.
Kai ya daga yana duban malam sa'idu din jin ya ambaci ita da wata.....Allah yasa abinda yaketa qoqarin
kaucewa da fatan kada ya faru ba shine ya soma faruwa ba
"Eh ya kusa awa biyu zuwa uku haka" Ya sake amsa masa. Idanu yadan zubawa malam sa'idu din kamar
yanason fahimtar wani abu daga gareshi,sai kuma ya janye idon yana fesar da iska daga bakinsa,sai ya
samu kanshi da Maida wayar aljihunsa kawai ya miqe daga zaman da yayi niyyar yi da,ya dawo gaban
gidan ya tsaya sosai jikin realer da aka yiwa gaban gidan adon flowers da ita,idanunshi bisa hanya
zuciyarsa na karanta masa abubuwa iri daban daban.
Tun dazun tunani da hankalin maamah yana kan hajja,har zuwa lokacin da mintuna kadan suka
rage musu su isa ga unguwar
"Yarinyar can fa hajja kin kaita wata unguwar tana jira". Murmushi hajja ta saki da qaramin tsaki a hade
A hands free ta saka wayar,bugu daya ta daga. Akwai qaguwa sosai cikin muryartata,amma kuma
bata isa ta nuna hakan ba koda da wasa kuwa
"Hajja na qaraso"
"To yayi.....na bar wajen,zan turo miki address na inda zaki sameni,na gaji gida nakeso na wuce,kada ki
wuce minti biyar baki iso ba"
"To hajja" Ta amsa mata a sanyaye. Katse kiran tayi,murmushi na subuce mata ta kalli maamah
"Yanzu nan zata zo cikin minti biyar?" Maamah ta tambaya cikin mamaki
"Kuma mijinta shi zai maidani gidanma a gabanta ba....da kai da kaya ai duka mallakar wuya ne". A
gajarce ta tura mata adress din,sannan ta fara qoqarin kiran yahaya daidai sanda suke karyo kwanar da
zata sadasu da shimfidadden jadda street din dake rubuce jikin wani qaramin allo dake kafe a farkon
layin.
Tunda ya hangi motar ya ganeta kafin takai ga isowa. Yaci gaba da bin motar da idanu har ta
qaraso qofar gidan,tayi kuma yi tsaiwar bawa malam sa'idu umarnin bude mata hanyar shigewa,sai a
sannan ya sauke hannayensa yana duban tayoyin motar da sukayi bududu abinda zai shaida maka ba
qaramar tafiya akayi da motar ba,tafiya me tsaho kuma cikin guraren da basu da shimfidadden titi ya
saka kai yana wucewa ciki kafin malam sa'idu ya kammala bude musu gate din.
Kansa a qasa yake takawa cikin gidan,haka kawai zuciyarsa yakejin bai gamsu da yanayin fita da
kuma shigowar motansu a yanzu ba. Cikin falon ya yiwa kansa gurin zama. Ba kowa a ciki,don dama
muddin idan bata nan din bata aminta da masu aikin nata su kusanci falon har sai ta dawo.
Tun tsaiwarsu bakin gate din ta ganshi,wannan ya sanya driver yana aje motar qasan rumfar aje
motocin ta bude ta fito
"Ya da sauri haka ko duk gajiyar ce?" Hajja ta tambayeta sanda take tattaro jakarta
"Yaroncan Muhammadu na gani,yana ciki yana jira,bansan tun yaushe ya shigo gidan ba.....banyi zaton
jirgin safe zasu biyo ba" Ta fadi hankalinta yana yin cikin gidan. Da kallo hajja tabi maamah din ganin
yadda duka hankalinta yayi cikin gidan,sai kawai ta jinjina kai ta soma yunqurin fita a motar itama tabi
bayanta.
Qafafunsa na harde cikin juna yayin daya jingina bayansa da makarin kujerar,ya zube idanunsa
duka a bakin qofa yana jiran ganin shigowarta. A wannan yanayin ta murda qofar ta shigo,tanata qoqarin
azawa fuskarta rashin sukuni da gasken gaske. A wannan karon batajin zatayi masa da wasa akan dukka
buqatun da zata bijiro masa dasu.....dole yayi yadda takeso wanda shine zai zama cikamakin burin
MALLAKAR 'YA'YANTA.
Duk yadda taso tayi diban watsin tsiya dashi amma sai kwarjininsa yakeson bugar da ita.
Hausawa sukace kuma wanda yayi me kyau ya sani haka wanda yayi maras kyau. Idanun da yake binta
dashi sai ta dinga jin kamar yanason karantar daga ina take?,me kuma taje yi?.
"Sannu da zuwa" Ya fada a nutse yana zare qafafunsa daga cikin na juna daidai sanda take aje mayafinta
da jakarta
"Ai kaine da sannu" Ta fada a taqaice tana ta tattalin fushinta da bacewar fara'a daga fuskarta,saidai
kuma wani bangaren na zuciyarta yanata saka mata tsarguwa da kuma shakku.
Hada ido sukayi a karo na uku,sai ta kasa jurar kallon da yake binta dashi din
"Kana mamakin na baka umarni baka bi ba kazo na sameni a raye ban mutu ba ko?" Ta fake da
wannan,don batasan da abinda zata iya qalubalantar kallon nasa dake mata wani irin nauyi da kwarjini
ba. Idanun nasa ya sauke a qasa yana girgiza kansa,baikai ga cewa komai ba ta sanyo kai da tata
sallamar.
Ita dinma dashi suka fara hada idanu,saidai nata kallon yafi na maamah tsini a nata idanun da
zuciyar. Kwarjininsa ya cikata fal,hakanan alfaharin ganin farko wa mamallakin jadda diamondchore
resources ya cikata.
Sunansa ya jima da shiga kundin nata lissafin,saidai a dukka hasashenta bata taba tunani ko zaton
samunsa a nan kurkusa ba.....bata taba kawowa cewa yana da wata alaqa ta jini me kusanci irin haka da
tsohuwar qawa kuma aminiyarta mariya ba.....bata taba hasashen mariyan tana da nasibin haifar
babban mutum har kamar Muhammad jadda ba.
"A'ah.....yaron namu ya iso kenan......maraba" Ta fada tana sauya reaction na fuskarta cikin qasa da
second biyar tare da takowa cikin falon a hankali. Akaikaice yake dubanta da wani irin kallo,sam baisan
fuskarsa ba......bai kuma tuna ko yaya a inda ya santa ba,ta yaya ita din akayi tasan wayeshi?,yaya akayi
tasan daga tafiya ya dawo?.
"Bana jin zaka iya shaidani.....shi ya sanya banyi mamakin musaddiq daya kasa ganeni ba.....ga yayansa
ma ya gaza shaidani?" Ta fadi tana sakin fara'ar da bata kai ga qarasawa ainihin zuciyarta ba,yayin da
kwarjininsa ke barazanar hanata samun abun fadi. Still dai baice komai ba yana ci gaba da dubanta. Ko
dis baiji matar tayi masa ba,bai hangi dattako ko kamala da sukayi daidai da shekarunta ba a tattare da
ita,sai kawai ya dauke kallonsa daga kanta don baiga amfanin maida hankali tare da son qoqarij fahimtar
abinda ya tabbatar daga qarshe bame amfani bane,amma ina suka fita har na tsahon awannin ita da
maamah din?. Tambayar data maqale masa kenan,bashi kuma da amsa.
"Lokacin sallah ya kusa,zanyi salla na dawo" Ya fadi yana juyawa a nutse yana fita a falon.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 57
_________________________
https://chat.whatsapp.com/D4mOQ8gmKb7EXZ2sNcmLdy
Assalamualaikum
Yar uwa kinason kiga kitchen dinki a cike da kayan amfani masu kyau da inganci amma Kuma kina
tunanin chake kudi kisaya a dunkule??
Koda yarinyace Dake da takusa aure kinason kifara Tara mata kayan kitchen??
To damuwarki tazo karshe Yar uwa kinzo inda za'a share Miki hawayenki *ALFAT KITCHENUTENSILS*
(Adashen Yar gata), sun shirya tsaf dan ganin sun sama Miki ingantattu Kuma masu kargo Yan zamanin
kayan kitchen.
Zaki dinga tura kudinki idan yakai wani minzali saiki karba duk abunda kikeso daide kudinki.
Dannan link dinnan domin kisamu damar shiga group dinmu don zabar kayanda kikeso da Kuma ganin
yadda abubuwan suke kasancewa. Nagode
https://chat.whatsapp.com/D4mOQ8gmKb7EXZ2sNcmLdy
____________________________
"Yaa huda.....yaa huda?" Muryar haneefa ta ratsa kunnuwanta dai dai sanda take kwance
qudundune cikin bargonta. Kusan idan bawai dare ne yayi ba hakan ba dabi'arta bace,amma a yanzun
yana neman ya zame mata dabi'ar da sabreen ta fara karantar hakan.
Batakai ga ce mata komai ba,don ba abinda ta gani behind kwanciya din da take yawan yi,sai ta
barshi kawai a zuwan yanayi ne da yakan sauyawa kowanne dan adam. A yanzu ma gaba daya hankalinta
yana kan ayshatu.....ciwonta gaba yake qara yi,ga mika'il a gefe,ga mashkur shima daya sanya wuta da
yawa a kanta. Ya'aqoub ne kawai me dan sauqi saboda bai cika zafafawa ba. Dukkansu batason kowa ya
subuce mata a daidai wannan lokacin da shirinta ke qara zurfi a kansu,kuma tafi hangen samun nasara
da wuri akan mika'il da mashkur,don shi ya'aqoub a yanzu tunaninsa yafi karkata kan yadda zai shawo
hankalinta ta aminta ta aureshi,abinda kuma bataga ranar yiwuwarsa ba. Wai mema zata tsinta ne a
auren?,bayan tana ganin yadda su mazan suke?,tana ganin kuma yadda matan ke komawa?,ko hanyan
aure yanzu mutum yayi mata ai bai qaunarta ballantana ace mata tayi. Duka tsari da halayyar mazan
baiyi mata ba ballantana ta cusa kanta a sabgarsu da nufin zama tsakaninta da waninsu zama na din din
din?.
Miqewa tayi a dole tana duban haneefa,sai haneefa din ta miqo mata takarda tana cewa
"Wani ne wai a waje yace a baki...." Da sauri ta fiddo mata idanunta waje sanda muryar sabreen wadda
ke amsa waya take dosowa cikin dakin. Yadda suka daga kai suka kalleta duka su biyun ya sanyata janye
wayar daga kunnenta tana kallonsu
"Lafiya?" Tayi tambayar tana sauya yanayin fuskarta. Wani faduwa gabanta yayi,cikin tsoro tsoro ta
girgiza kanta tana qaqalo murmushi tace
"Ba komai.....ina kwance haneefa ta tsoratani,na dauka wani abune da naji tanata tashina". Idanu ta
sake zuba mata na daqiqu sannan ta amsata tana zama gefan nata gadon
" Ko bata tsorataki ba dama ai yaci ace kin tashi,an kusa kiran sallah.....uniform dinku nadra ta wanke
tunda kin koyi laziness......kije kiyi alwala ki dawo ki kwashe abincin tukunya a flask a wanke sauran
abinda ya rage".
"Tom" Ta fadi tana matse takardar a tsakiyar hannunta tare da tunanin yadda zata miqe da takardar ba
tare data lura da ita ba,to amma kuma ci gaba da zama dinma tunanin mafita tamkar tana bata damar
dora ayar tambaya ne a kanta.
Aljihun skirt dinta ta tuna dashi,cikin dabara ta cusa a ciki,sannan ta zame ta sauko tana gyara
inda ta kwanta din,ta daura dankwali saman doguwar sumarta ta juya tana fita a dakin. Dauke idonta
tayi daga kan tab dinta ta bita da kallo. Haka kawai ta gagara samun nutsuwa kwanaki biyun nan,duk
motsinsu a kan idanunta yake,kuma da gaske tana ganin dan sirkawar wani abu kadan tattare da huda
din.
Bandaki kawai ta wuce kai tsaye tana fata da zumudin budewa taga meye a takardar?.
Sai data samu guri cikin toilet din ta zauna sannan ta ciro takardar ta kuma warwareta.
Kaman yadda ta zata shi dinne,sunansa kawai data gani sai bugun zuciyarta ya qaru da kaso
hamsin cikin dari.
Yau kwanaki uku kenan,ya rakota daga hanyar makaranta har dab da gidansu kamar yadda ya
saba a kowacce rana......tun tana gocewa har ya fara zame mata sabo ba tare da sanin nadra ko haneefa
ba wadda yanxun aka banbanta musu lokutan tashi qarfi da yaji ba tare da kowa yasan dalili ba. Ya zame
mata kamar abokin rakiya a yanzun.....tun tana dari dari da tsoro har hakan ya fara gushewa daga
zuciyarta.
A ranar alhamis tayi matuqar mamaki yadda ya tsaya suna tsaka da tafiya,ya kuma kafeta da
idanu
"Ke kyakkyawa ce" Ya fadi yana jin wutar sha'awarta na ruruwa a ransa tamkar yadda ya dinga jin ta 'yar
uwarta. Yana jin kamar ya dauketa a yanzun ya wuce da ita ya aikata abinda ya tanadi aikatawa,saidai
kuma bazaiyi haka ba,yanason komai ya kasance a daidai sanda zatafi jin ciwo da radadin da zai iya zama
ajalinta,ya kuma tarwatsa farincikin da take musu tattali. Yanason idan ya tashi ya tarwatsata
tarwatsewar da ba zata taba dawowa ta gyaru ba ballantans ta koma yadda take.
Idanu ta waro tana dubansa,yadda yake yawan kambata da kurantata ya sanya kusan kullum sai ta
kalli madubi......kusan kullum sai ta kalli kanta da kanta taga wannan kyan da yake magana a
kai......wannan budurwar da yake yawan kiranta dashi. Tun bata ganin abinda yake fada din har ta fara
ganin,amma tana ganin kaman bata ca canci kowacce rayuwa ba a yanzun......karatu shine yafi da cewa
dasu kamar yadda yaa sabreen ke gaya musu
"Ina sonki huda.......ina tsananin qaunarki tun daga ranar dana fara ganinki.......zuciyata tana miki wani
mahaukacin so da bansan iya adadinsa ba......wallahi inaji a zuciyata tamkar zanyi hauka saboda ke
huda......ki soni don Allah......ko baki sona ni zan koya miki yadda zaki soni din". Kalaman da suka
tsoratata suka kuma razanata kenan. Kalaman kuma da Naseer din ya shiryasu ne kawai don ya soma
wasa da tunaninta da qwaqwalwarta,plan na biyu kenan daga cikin tsarikansa.
Baya taja tana girgiza kai,tana jin tsoro yana shigarta. Wacce irin soyayya a shekarunta?,duka
duka nawa take?,koda yaa sabreen bataga ta kawo kowa tace shi zata aura ba,bataga wani yazo qofar
gidan da sunan zance wajenta ba.....koda abinda ake maganarshi a kanta da nasu idanun basu taba
ganinta cikin motar wani ko tsaye da wani ba har zuwa yanzun da take tsaye a gabansa. Ko rakota da
yakeyi kullum kwanan duniya a tsorace take......wani lokaci zuciyarta tana raya mata idan sukayi kacibus
da yaa sabreen fa?,sai kuma zaqin bakinsa da daddadar hirarsa ta yaudare tunaninta da kunnuwanta.
Tayi mugun tsoratar data dinga ja da baya da baya tana girgiza kai. Yana tsaye ya kafeta da
idanu,abun yana masa sugar sosai. Irin hakan yafi buqata don ta haka ne sabreen din zata fuskanci
girman nasa aikin. Ya samu sabon ruhi sabon gangar jiki da baisan komai ba game da rayuwa......zai
hurewa zuciyar kunne,sannan ya mori gangar jikin yadda yaso ya kuma watsar da ita tamkar wani
yasashen abu maras amfani. Yana tsaye harta gudu a layin ta bacewa ganinsa,sai ya bushe da dariya.
Hakan da tayi ya tabbatar masa qwaila ce,ya kuma bashi tabbacin baa taba gaya mata kalmar so
ba sai a kansa
"Allah sarki......gashi baki fara da jin kalmar ba a sa'a......anyway......ko mene ya faru dake 'yar uwarki ce
taja miki" Ya fada yana juyawa don barin layin ya qarasa inda yaransa ke cikin mota suna jiransa.
Hannunta har rawa yake sanda take warware takardar. Tsakanin alhamis jumaa asabar da kuma
yau lahadi ba wasu mintuna biyar kyawawa da suka wuce ba tare da tunanin abinda ya faru tsakaninsu
ya dawo kanta ba. Duk juyin da zatayi sai kalamansa sun dawo mata,kallonsa murmushinsa da
kambamawarsa. Fuskarta kam ta kalleta yafi sau adadi tana sake duba kyawun surarta da yake yawan
jaddadawa. A yadda take gani ba mace me kyan yaa sabreen dinsu......ashe itama to tana da kyau dinne
da gaske?,ko kuma yana fada ne kawai?.
*_Hello me kyau,fadin azabtuwar da idanuna da zuciyata sukayi saboda rashin tozali dake ba abu bane
me sauqi......ina fata zaki daure a gobe ki barni naga wannan kyawawan idanun da zuciyata ta mutu a
kansu.....idan ba haka ba.....zan iya rasa numfashina_*
Da sauri ta duqunqune takardar ta kuma jefa a toilet ta bita da flushing zuciyarta na bugawa
sosai. Tsoro zumudi fargaba da mamaki dukka suka hade mata har ta rasa wanne tunani ma zatayi.
Bugun qofar bandakin da akayi ana jiranta ya sake rudata,sai kawai taja qofar ta bude ta fito ba
tare da tayi komai ba,taja burki bakin famfo ta daura alwala tayo dakin nasu.
Gaba daya tunaninta ya karkata ga saqon,har ta mance da batun kwashe abinci tayi zaune saman
kujera tana bitar saqon da ya riga ya rubuta kansa da kansa a kwanyarta. Fitowar sabreen din ya sanyata
tunawa,ta miqe da hanzari ta nufi kitchen.
Yanzunma da kallo sabreen ta bita har ta shige kitchen din. To wai me yake samun huda take
wasu wasi haka?. Bata sani ba,sai ta girgiza kai ta taka hannun kujerar tana dauko babbar dardumar da
sukan shimfida suyi magariba da ishai akai suyi bitar karatun makaranta ta taimaka musu da wanda zata
iya.
Da ruwan zafi sosai tayi wanka bayan wucewar hajja saboda ciwo da jikinta yake mata sakamakon
zaman mota data jima batayishi kaman haka ba. Ta shirya kanta cikin fafi indian abaya me laushi,ta yane
kanta da mayafin abayar daya kasance medium cotton kaman yadda jikin dogon rigar yake.
Cikin falon tayi zaune bayan ta kirayi me aikinta ta canza mata channel. Qafafunta a miqe saman
side glass table din,hannunta dauke da glass cup dake cike da lemon raspberry tatacce me asalin tsadar.
Babu wani abu da zata ci ko tayi amfani dashi cikin gidan da yake da qaramin kudi. Komai nata me tsada
take zaba,hatta da ruwan da zata sha kuwa ballantana akai ga sutura ko wayar hannunta.
Ko a yanzun haka ta gaya masa tana buqatar ya sauya mata iPhones din hannunta guda biyu.
Iphone 15 da wata tsaddadiyar waya sabuwar qira da kamfanin Samsung's. Duka duka wayoyin ba
wadda tayi wata uku,to amma garin gane ganenta ta hangi wasu sabbin fitar,su kuma takeso ta riqe.
A komai tafison ta zama cikin sahun mutane na farko da ake ganin komai sabo a wajensu. Inda
tana da iko komai zai zamana ana ganinsa ne ta wajenta,sanda zai soma zagayawa hannun masu kudi
irinta ita ta dade da cin zamaninta. Ta sani,a dukiyar da d'anta yake dashi yana da qarfin kudi da mulkin
da zai iya sanyawa a qera mata duk abinda take buqatar ya kasance nata ita kadai daga kowanne
kamfani a fadin duniya,to amma ta fahimci rayuwarsa baya daidaitata dai dai data sauran masu kudin
irinsa. Ba kuma haka takeso ba.....ba haka take muradi ba......tanaso ta gansu suna rayuwa daidai da
matakin arziqinsa. Ta fahimci yana cikin sawun mutanen da ba kasafai suke bayyana arziqinsu ba,sai
abinda ya riga ya bayyana ba yadda zasuyi dashi.
Aka idar da magariba akayi ishai shuru. Tun tana tattalin maganganun da zatayi dashi har wasu
suka fara bace mata. Ta daga kai ta kalli agogon dake shirye saman tv din falon takwas da rabi na dare,to
shin sai yaushe zai shigo?,sai yaushe wannan abun zaizo qarshe?.
Sannu a sannu sanda taga an doshi tara na dare babu alamunsa,wayoyinsa dukka a kashe shida
musaddiq din da zata sanya ya kira mata shi a duk inda yake.
A ranta ta dinga jin cewa hadin baki ne......a ranta kuma ta dinga ji aminatu ce ta hanasu.....a
yanxun haka qila suna can gabanta......ta zaunar dasu sai abinda tace musu.
Wannan tunanin ya dugunxuma mata zuciya,har taji bata da wani sauran zama cikin gidan.
Dakinta ta wuce kawai bayan ta ajiye kofin lemon,ta shiga zaro takalmi cikin jerin takalman alfarma dake
adane a shoe rack dinta. Cikin zuciyarta takeji yau din Alhaji hamzan zata tunkara......tanaso taji shine
yayi mata cikin yaran ko ubansu?,tana so taji da ita dasu wai waye ahaqqu dasu?.
"Nazo muje ne?" Zuwaira ta tambayeta sanda taga tana dosar qofar fita daga falon
"Zauna basai kinje ba" Ta amsa mata a gaggauce tana fita a gidan.
Mugun bugun da takewa tafekeken gate din gidan ya fusata securities din gidan,saidai kuma
lokacin da suka duba wadda ke bugun ta na'uarar tsaro dole kowannensu fusatarsa tayi nata guri.
Basusan ainihih matsayinta ko ita wacece ba......amma yadda suka fahimci girmamawar da take
samu daga mazauna gidan ya basu alamar cewa tana da nata matsayin na daban.
Ko kallo security din daya bude mata qofar bai isheta ba ballantana tabi takan welcoming nata da
yakeyi tare da bude mata qofa ta biyu da zata sadaka da farfajiyar gidan. Daga nan wasu security din su
sake marabtarka kashi na uku kenan kafin kakai ga ainihin cikin gidan ka zarge qofar da zata sadaka da
babban falon anni na farko.
Bata taba tunanin zata sake takowa cikin gidan ba karo na biyu.......don duk lokacin data tako din
alatun gidan yakan zame ma idanu da zuciyarta barazana. Tana jin kamar kowanne abu idan ta kalla a
gidan yana mata izgili ne tare da gaya mata da dukiyar danki aka samar dani......baki kuma da wata izza
ko power ta mallakata.
Kowanne taku daya idan tayi cikin gidan ranta quna yake......sak fasalin yadda takeso gidan da
zata rayu ya kasance sai gashi kacokam a yau din irin wannan dream house din nata mallakin aminatu
ne.. Wasu mutane da basu da masaniyar sanda ta dauki cikin fuad har ta haifeshi.
Qofa ta qarshe da zata bata daman shiga falon annin nanma sai data jinkirtawa na'ura sannan ta
bata izinin shiga,ta dauke kanta ranta yana suya da wani irin fushi. Tafi qarfin ta tako gidan alhaji hamza
har abada.....inda sun bata girma da martabarta da a yanzun ba shakka ita ake zuwarma haka neman
gindin zama.
Tana sane da yadda mabuqata ke yawan ziyartar gidan karbar taimako a duk sati......taimakon
da ta tabbatar daga fuad ake rabashi.......sai gashi ita duk yadda taso ta dinga cina farfajiyar nata gidan
da mabuqata,tana raba musu kudi a envelope yadda taso abun bai samu yadda takeso ba. Bai hana
taimako,amma saidai ta rubuta list na mabuqatan ya hadasu dana gidan alhaji hamza a raba musu
taimakon tare.
Bata samu yin sallama ba,sai Allah ya sanya tana sanya qafafunta a falon idanun anni dake
kashingide cikin lausasan sofa ya sauka a kanta.
"Ikon Allah" Anni ta furta tana miqewa daga kashingidar da tayin tana sauke qafafunta qasa idanunta
akan maamah
"Da kinyi zamanki ma.....don ni ba wajenki nazo ba kaman yadda na alqawarta zuwa na na qarshe gidan
nan......wajen hamza nazo" Maganar tata tazo qarshe dai dai sanda amna ke fitowa daga kitchen ta zuba
abincin dare,don tace yau zaman cin abincin abban yayi dare da yawa,ba zata iya jiransa ba da wuri
takeso ta kwanta.
Kallon kallo sukayi tsakanin maamah din da amna. A kallon farko ta fahimci wacece duk da
wannan shine karon farko da ta fara ganin yarinyar ido da ido. Autar alhaji hamza kenan,yarinyar da ake
gaya mata irin sabon dake tsakaninta da fuad......yadda take ji dashi da yadda shima yake ji da ita
"Idan har kikayi da wasa kina zaune zakiji ance 'yar gida akayi.....wannan matar zata aura masa
autarta..... Kinga shikenan komai ya qarasa watsewa" Muryar hajja ta dawo mata akai cikin tattaunawar
da sukayi da hajjan a dazu dazu kan hanyarsu ta dawowa gida.
"Ke amna......dubamin abbanku idan ya kammala,kice maza maza yayi baquwa"
"To" Ta fada tana ajiye plate din sannan ta miqe tana nufar qofar da zata sadata da sassan abban nasu
ba tare da tabi ta ainihin farfajiyar gidan ba. Tana tafe tana waiwayen maamah,itama ta lura da
hakan,sai taja wani tsaki me matuqar qarfi abinda ya sanya amna din maida kanta tana yin gaba.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 58
___________________________
https://chat.whatsapp.com/D4mOQ8gmKb7EXZ2sNcmLdy
Assalamualaikum
Yar uwa kinason kiga kitchen dinki a cike da kayan amfani masu kyau da inganci amma Kuma kina
tunanin chake kudi kisaya a dunkule??
Koda yarinyace Dake da takusa aure kinason kifara Tara mata kayan kitchen??
To damuwarki tazo karshe Yar uwa kinzo inda za'a share Miki hawayenki *ALFAT KITCHENUTENSILS*
(Adashen Yar gata), sun shirya tsaf dan ganin sun sama Miki ingantattu Kuma masu kargo Yan zamanin
kayan kitchen.
Zaki dinga tura kudinki idan yakai wani minzali saiki karba duk abunda kikeso daide kudinki.
Dannan link dinnan domin kisamu damar shiga group dinmu don zabar kayanda kikeso da Kuma ganin
yadda abubuwan suke kasancewa. Nagode
https://chat.whatsapp.com/D4mOQ8gmKb7EXZ2sNcmLdy
_________________________
Farfajiyar gidan ba kowa sai qofar dakin malam saidu da yake iya hangowa wanda yake a bude.
Juyawa yayi zuwa sassan da spare din famfo dake bawa shukokin gidan ruwa yake,ya xame
takalminsa,ya kuma xare agogon hannunsa ya jefa aljihu sannan ya matsa ya kunnashi. Dukkan
hannayensa ya tara yana kallon saukar ruwan,sai yaji wasu kalamai suna dawo masa a ka
_"ka mutu mana......ai ba a kanka aka fara mutuwa ba,kuma ba'a kanka zaa daina ba......talauci da fatara
tafi mutuwarka yimin barazana......ta kuma fi mutuwarka dagamin hankali"_
Wani abu yaji ya tsaye masa a tsakanin numfashinsa daya sanya ya cire hannayensa daga
famfon. Wasu daga kalaman maamah kenan a can shekarun baya a bakin famfo tamkar irin haka,daidai
sanda abban nasu yake daura alwalar sallar magariba. Takalmansa kawai ya mayar yana jin bazai iya ci
gaba da xama a cikin gidan ba. Ire ire wadannan abubuwan da ba wanda ya sansu saishi,.....koda
musaddiq kuwa......suna sanyashi yana jin kamar numfashinsa zai fita a wasu lokutan.
"Ko buta zaa baka ranka ya dade" Muryar malam saidu ta ratsa kunnensa sanda yake dab da qofa. Kansa
kawai ya gyada masa yaja ya koma ya zauna,ba jimawa ya dawo da butar,ya karba ya fara dora alwalar a
gaggauce,ya gama ya bashi ya karba ya maidata wajenta
"Zo muje malam said" Fu'ad ya fada yana ware hannun rigar sa.
Tare suka jera shida malam saidu din,duk da yadda yaso ya zuqe saboda girmamawa,me sunan
malam kuma yana daga bayansu kadan ta yadda bazaiji wani abu da suke tattaunawa ba
"To ba laifi ai" Ya amsa masa,don ya saba lokaci lokaci dama yakan masa tambayoyi game da gidan ya
kuma buqaci amsarsu.
"Waccan matar da suka shigo da hajiya meye sunanta?,wace ita a wajenta?,yaushe ka fara ganinta a
gidan?,sannan kamar sau nawa ta taba zuwa ko take zuwa?,ita kadai ce koda wasu?,tana dadewa cikin
gidan?,suna yawan fita tare ko aah" Yakai qarshen dukkanin tambayoyin nasa sanda suka kai bakin
masallacin,don haka yayi shuru yana adduar shiga masallaci a madadin tarin tambayoyin.
"Lallai na sake yarda da maganar bokan can.....lallai akwai aiki qwarai akan yaronkin nan" Hajja ta fada
duk da nata yaron da matarsa data shanya a waje kowanne cikin motarshi yana jiran fitowarta.
Labba maamah ta cije kadan sannan ta saki sanda take maida riga maras nauyi a jikinta
"Ni kuma cewa nayi miki zan qyale wannan aikin ya cimmani?,na zuba idanu naga iya gudun ruwansa na
yau kawai......amma duk abinda yakai gobe zakiji kirana......a gobe nakeso mu koma a fara aikinnan"
"Ai da zafi zafi akan bugi qarfe....." Hajjan ta fadi zuciyarta na saqa mata abubuwa masu yawa.
Har bakin gate din farko ta tako tana yiwa qawartata godiya da ban gajiya. A nan suka gaisa da
yahaya da matarsa. Yadda ta samesu a jere kowanne da mota yana jiran dakon fitowar hajjan ba tare
daya isa yabar wajen ba ba bisa umarninta ba ya sake ninka kwadayinta itama na kaiwa wannan
bigiren,sai taji kamar ta jawo wadannan kwanakin da tayi imanin suna dab da zuwa......ranar ea zata
nunawa aminatu da hamza cewa ruwa ba sa'an kwando bane.....hakanan koda giwa ta fadi tafi qarfin
wawa.
Haka siddan?,daga maqotaka?,ba sidi ba sadada a kama mata yara a musu muguwar
mallaka?,bayan ko sanda ta tafinma suna da wayon da zasu iya kula da kansu?. Da wannan qananun
mitocin ta isa cikin gida.
Ya kusa minti ashirin yana fuskantar gate din gidan,harde da hannayensa kawai yana duban
qofar kwanyarsa tana digesting maganganun da sukayi da malam saidu daga hanyar masallaci zuwa
dawowarsu. Baisan a wanne matsayi zai ajjiye maamah din ba.....karo na uku da wani abu ya sanya yake
tunanin ANYA ITA DINCE TA HAIFESU?,anya ita din UWACE?,akwai zuciya irin ta uwaye a qirjinta kuwa?.
Me yasa kullum DUNIYA itace a gabanta sama da komai?,yayi tunanin shi da kowa ma zata canza ko
kuma ta canza din.....amma sai kuma akasin tunaninsu ya biyo baya.....akasin tunanin da shi kadai gani
na zuciya da lura da bin takunta sannu a hankali suke karanta masa komai a kanta....karatun da idanuwa
kadai sunyi kadan su iya fahimta ko ganeshi.
Hannayensa ya sauke jikinsa a mugun mace,baya jin zai iya komawa cikin gidan nan,idanma yace
zai koma din abinda zai wanzu tsakaninshi da ita bame dadi bane. Ko haduwarsu na 'yan mintuna kadai
ya sake wani karatun. Ya dawo lafiya?,wacce nasara ko qalubale ya riska?,duka ba damuwarta
bane......damuwarta shine KUDI.....me yasa bai turo ba?. Abu guda daya da bai taba faruwa tsakaninshi
da anni ko abba ba......basu taba neman anini taro ko sisi daga hannunshi ba.....a hakan take neman
kudin da zata rabashi da Alhaji hamza da aminatu?,mutanen da su suka bashi RUHI na rayuwa da yake
yawo a jikinsa a yanzu?.
Kansa ne yaji ya sara,sai ya sake qara azamar barin qofar gidan ya juya zuwa nasu gidan. Gidan
da a baya shine gidan maqota a wajensu amma a yanzun basu da gidan daya kaishi.
Tun a gate ya sallami kowa,ya gaya musu da wuri zai kwanta don gobe zasu fita da wuri,duk da
baida yaqinin goben a yadda zai tashi saboda wani nannauyan ciwon kai daya saukar masa yanzu yanzu.
Tun bai qarasa sassansa ba ya kashe duka wayoyinsa,yabi ta qofar baya don bayason kowa
yasan ya shigo din ya wuce sassansa.
Bai kunna kowanne fitila na sassansa da zai bada alamar yana ciki ba,sai ya wuce a hankali kamar
kazar da qwai ya fashewa a ciki zuwa study room dinsa,ya tura qofar ya shiga ya maida ya rufe.
Zaune kawai yayi saman sofa idanunshi a kulle,yayi nisan nazarin da shi kansa baisan wane zare a
tunanikansa zai kama ba. Abu daya ne da yafi daure masa kai da dagula masa lissafi,qoqarin da takeyi da
gaske na sai ta raba tsakaninsu,indai haka ne wannan fitar tasu tana da alaqa da qudurinta.....indai haka
ne kudin da take nema lallai yana da alaqa da qudurinta......indai kuma haka ne tabbas wannan
BAQUWAR FUSKAR akwai tata rawar cikin mission din......duk da yasan wannan din tsohon quduri ne
dake ranta.....amma dukkan alamu sun nuna ta samu MAKAMASHI.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 59
Shuru ne ya biyo baya tsakaninsu,babu wanda yace da dan uwansa komai tsakanin ita da anni din.
Daga yanayin tsaiwarta da yadda take bin komai da wani irin kallo ta tabbatar ba alkhairi bane ya
kawota,don haka taci gaba da abinda takeyi din ba tare data ce komai da ita ba.
"Yace gashi nan...." Ta bata amsa tana sake binta da kallo tamkar a tsorace,sannan ta qarasa ta dauki
plate dinta ta koma kusa da annin ta naniqe ta zauna tana ci gaba da satar kallon maamah din.
Da sallama ya shigo falon cike da kamalar nan tasa dake shimfide saman fuskarsa,sanye yake da
jallabiyya ruwan qasa,kansa sanye da qaramar hula tashi ka fiya naci.
Amna da anni ne suka amsa sallamar tashi,yayin da maamah ta dubeshi kadan kafin ta dauke kanta
"Mariya ce?,....bismillah......zauna mana" Ya fada yana zama kujerar dake daura data anni. Kamar tace ba
zata zauna ba,to amma kuma zaman yafi kamata tayin,don tanason daga qarshe ta gasa masa
maganganun da indai ya haifu zai fara janye jikinsa daga dukkan wata mu'amala ta fu'ad dama
rayuwarsa gaba daya,yabar mata 'ya'yanta kamar yadda kowacce uwa keda iko da nata yaran.
"Muna lafiya.....ina fata kuma lafiyar ko?" Gyara zamanta tayi sosai tana dora qafarta daya kan
daya,sannan ta saka idanunta sosai cikin nasa
"Wajenka nazo hamza" Ta fadi kanta tsaye,abinda yaja hankalin anni kenan tadan daga kai ta dubeta,sai
kuma ta saukar tana son kwashe hankalinta sam sam daga kansu.
"To ai gani.....Allah yasa lafiya" Fuska ta qanqance tana dubansa idanunta a ciki.
"Al'amarinku yana bani mamaki hamza yana kuma dauremin kai.........duk duniya ban taba ganin inda
ake irin haka ba sai a kanku,hankaka mai da dan wani naka?......amma mu ajjiye wannan batun......tunda
kun zab lallai sai na zama maqasqanciya a gabanku akan 'ya'yana?......ba laifi don komai da ka gani a
rayuwa lokaci ne.....kuma iyaka gareshi......" Ta furta qasan ranta tana hangen iya adadin lokacin da ya
rage musu wanda alaqar uwa da uba zata wanzu a tsakaninsu.....da tazarar lokacin da alaqar zata juye
zuwa alaqar gagarumin abokin adawar da duk duniya fuad din zai wayi gari bashi da abokin adawa irinsa.
Burinta shine ta bude idanu taba tsabtsar gaba da adawa mai qarfin gaske ta qullu tsakaninsu......irin
adawar da zata bawa kowa mamaki ta kuma shiga sahun tarihi......tabbas saita fanshe dukkan wani
baqinciki da suma cusa mata......hakanan ba zata qyale ba sai sunyi aman duk wani da sukaci daga cikin
arziqin fuad......koda kuwa wannan gidan da suke ciki yana cikin jerin sahun mallakar fu'ad din.
"Wai nikam hamza.......ban sani ba ko cikin duhu ne a sannan?......hadaka da kuma gamayya kukayi da
ubansu fu'ad yayin samuwar cikinsu?,ma'ana tare kukamin cikinsu ko kuwa?" Ba alhaji hamza kibiya
kadai ba,hatta anni dake zaune daga gefe ba tare da shiga shirginsu ba sai data cira kanta da sauri
maganar tana dukanta
"Subhanallahi.......innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Alhj hamza ya fada zallan mamaki yana saukar
masa,idanunsa akan fuskar amna wadda ta yunqura tana miqewa ba tare data tsaya daukan plate din
abincin ba saboda yadda maganar ta girmimi kunnuwanta.
"Mamaki kukayi?,to ai ba abun mamaki bane duba da yadda kuka qanqame min rayuwar 'ya'ya hamza"
Ta kuma fadi cikin izza ba shakka ko d'ar a cikin idanunta.
"Mariya cikin hankalinki kike kuwa?" Anni ta gaza jurewa ta fada tana kafeta da idanunta. Wurga
kallonta tayi zuwa ga annin
"Shin mene marabar dambe da fada mariya?,ai hauka nau'i nau'i ne.....nakin ina kyautata zaton ta
wannan fuskar yazo"
"Kamar yadda cutarwarku tazo da sigar yaudara da damfara ba.......na rantse da Allah a yau inda fu'ad
yana a faqirinsa bashi da komai da tuni kun watsashi shi da dan uwansa........."
"Kaman yadda zamantowarsu halittar da zaki iya mora ta sanya kika dawo cikin rayuwarsu ba?....bayan
kin watsar dasu a sannan kina zaton su din ba masu amfani bane,nauyi ne kawai a wuyanki?". Anni ta
maida mata amsa ta hanyar katse numfashinta bacin rai yana fara nuna alamun tasiri cikin muryarta
"Ya isa aminatu......ban yarda ki sake cewa wani abu ba" Alhaji hamza ya fada yana daga mata hannu. Ya
gama karantar akwai abubuwa masu tarin yawa a bunne cikin zuciyar maamah din,biye matan da annin
zatayi shi xai bata damar furzar da maganganun da idan suka qyaleta basu tanka mata ba har ta mutu
saidai ta mutu dasu a cikinta.
Dole ta ninke dubban maganganun da suke tsinkulinta a rai kawai don ta bawa abban
girmansa,amma bawai don abinda take da shirin furtawa itama ya qare ba,ta kauda kai tana hadiye
fushinta ba tare data sake jefa baki a maganarsu ba
"Ka gaya masa ya bini.....domin kuwa duk duniya ba wanda akace aljannarsa tana qarqashin qafarta face
ni.....komin lalacewata......ka taimaka ka sakar masa mara ya rabu dani lafiya kaman yadda na tabbatar
ka rabu da naka lafiya......ka shaida masa yazo ya bani kudin dana buqata a hannunsa.......bawai alfarma
nake nema ba......ka gaya masa dole ne yayimin...." Tana kaiwa nan ta miqe tsam,idanunta akan anni da
tayi kaman batasan da wanzuwarta a wajen ba. Taso ace annin taci gaba da ja,don tana da tarin
maganganun da takeso ta amayar mata
"Wallahi duk d'an da ya hana uwarsa bacci.......shima bazai huta ba" Ta furta tana juya hankali kwance
tana barin falon.
Shuru ne ya biyo baya,duk kuwa da cewa ta gama ta kuma fita daga gidan ma gaba daya
"Hasbunallahu wani'imal wakil" Alhaji hamza ya furta gauraye da wata ajiyar numfashi me nauyi
idanunsa na kallon waje daya.
Baisan wanne irin abune yake dawainiya da mariya ba......baisan kuma wanne girman laifi
sukayiwa rayuwarta haka da take musu kallon wasu manya manyan abokan adawarta ba. Anni batace
komai ba kaman yadda shima bai buqaci tace ba,tanata qoqarin sarrafa bacin ranta da ganin ta hadiyeshi
ba tare data barshi ya mata tasiri ba
"Bansan ina yayi ba.....mun rabu dashi a dazu kan zai shiga wajenta" Ta amsa masa a taqaice. Karkacewa
yayi ya ciro wayarsa daga aljihun jallabiyyarsa ya soma trying number din fuad din.
Sosai yayi nisa cikin tunani,a haka idan ka ganshi zaka dauka bacci yakeyi,saidai ba ko guda daya.
Wasu mintina ne daketa wulga masa tsakanin bacci da ido biyu wanda a ciki baisan ainihin abinda yakeyi
ba
A silent wayar take,amma hasken da take fitarwa ya ratsa rufaffun idanunsa a cikin duhun dakin.
Kamar bazai bude idanun nasa ba amma sai ya budesun a hankali yana saukesu akan wayar. Yayi
tsammanin ya kashe duka layukan,sai a sannan ya lura guda daya ya kashe. Sunan daya gani saman
wayar ya sanyashi sauke qafafunsa a hankali yana maida hankalinsa a kanta,ya miqa hannu ya daukota
daga inda take ajiye yana qoqarin dagawa.
Sallama yayi amma muryarshi ta maqale,yadanyi gyaran murya sanda yajiyo muryar abban yana
masa sallama
"To abba" Ya amsa masa a ladabce. Remote ya laluba ya dauko ba tare daya tashi a gun ba ya maida
hasken dakin. Take yayi tarwai da haske kaman yadda ainihin dakin yake
"Allahumma la sahla illa ma ja'altahu sahla.....wa'anta taj'alil hazna iza shi'ita sahla" Ya furta muryarsa
can qasa,yana jinsa gaba daya ba kuzari,tun daga zuciyarsa har zuwa gangar jikinsa.
Bai wani bata lokaci ba ya sauya kayan jikinsa sannan ya wuce sassan annin. Sallama yayi
hankalinsa na kaiwa fuskar anni. Tun bai zauna ba jikinsa ya bashi akwai wani abu,don ba kasafai kake
ganin fuskar annin a haka ba. A nutse ya qarasa shiga ciki,kai tsaye kuma ya nufi inda Alhaji hamza
yake,wanda bai motsa ba daga wajen tunda maamah din ta fita ta barsu.
"Bismillah.....zauna" Alhaji hamza din ya masa nuni da kujerar dake kusa dashi. Sanda ya zauna din ita
kuma anni ta miqe da zummar barin wajen,abban ya maida dubanshi kanta
"Zama kema zakiyi......ina zakije?" Duban abban tayi,kaman zatayi magana sai kuma ta fasa,ta koma ta
zauna ba tare data sake cewa komai ba.
"Muhammadu" Abba ya kira sunanshi kai tsaye,abinda ba kasafai hakan ke kasancewa ba. Mamakin ya
hanashi amsawa saidai ya daga kai kawai yana duban abban.
"Muhammadu ya ina yabonka sallah zaka kasa alwala?" Abban ya sake fada idanunsa still akan fu'ad
din,tausayinsa kuma yana ratsa zuciyar abban.
"Me dame mariya tace maka tana da buqata wanda bakayi mata ba?" Ya masa tambayar Kai tsaye don
sauqaqe masa wahalar tunani.
"Abba.....ba wani nauyi ko haqqi daya kamata na bawa maamah wanda bana bata shi......bana tunanin
akwai wani abu da ya zama nauyi ko haqqi da ubangiji ya doramin wanda na gaza dauke mata shi". Har
cikin zuciyarsa abban ya gamsu da wannan,saboda shi kansa ganau ne bawai jiyau ba akan hakan
"Na sani Muhammadu......amma don me yasa idan tana da buqatar kudi daga hannunka kake hana
mata?". Sam baima kawo wannan zancan bane,sai ya sauke boyayyar ajiyar zuciya yana sauke kanshi
qasa.
"Me yasa kusan ko yaushe matsalarka da ita akan tana neman kudi ne ka hanata?,bayan Allah yayi maka
wadatar da zaka iya bata ko nawa ne Muhammadu?" Ya qarashe maganar ta sigar tambaya idanunsa a
kanshi,can qasan ransa yana mamakin abinda ke kawo musu matsala akan abinda yasan ya jima da fin
qarfinsa.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 60
"Ka sani cewa......duk d'a aljannarsa tana qarqashin qafar iyayensa?,kuma haramunne jayayya dasu bare
su buqaci abu aqi ayi musu?"
"Na sani abba.......amma bazan iya bawa maamah ko sisi ba". Sosai maganar ta bawa abban mamaki,har
anni dake zaune daga gefe itama ta daga kai tana kalleshi
"Akwai abubuwa masu yawan da baka gama saninsu ba abba akan maamah......akwai boyayyun sirrikan
dana ajewa cikina abba.......akwai wasu abubuwa masu yawa wadanda ba zasu fadu ba......amma koma
meye cinta shanta lafiyarta dama suturarta wani abu ne da bazan taba iya hana mata su ba ko don
albarkacin haihuwa da Allah ya bata........amma batun kudi abba........bazan iya bata ba"
"Dalili?,dalili nakeso naji Muhammadu" Abba ya sake tambaya cikin tsananin mamaki. Bai taba
umartarsa da abu ba ya saba.....sai gashi s yau yana qoqarin bijire masa.......tabbacin akwai wani
qaqqarfan dalili da kuma hujja kenan
"Abba...." Ya kirayi sunansa yana jin nauyin abinda zai furta din. Shurunsa ba abinda zai harfa tsakaninsa
dashi sai gurguwar fahimta,bayaninsa din kuma bawai abu bane me dadin ji ko sauraro ba.
"Zan bayar abba.....zan bata amma bawai don zuciyata tana so ba......"
"Kirashi yanzu yanzu" Ya sake bashi umarni kai tsaye. Dole ya fidda waya ya turawa sadiq din saqon
umarnin fidda kudaden,sannan ya aje wayar yana duban abban
"Zai sanya mata in sha Allahu". Ajiyar zuciya abban ya sauke. Shi kansa yasan akwai qalubale masu tarin
yawa cikin rayuwarsa,to amma ko meye zaiyi yana yine saboda kyautatuwar rayuwa da kuma gobensu.
Kamar yadda ya saba lokaci bayan lokaci baya gajiya da yi musu nasiha dukkaninsu,yanzunma
nasihar ce dai yayi masa.
Haka kawai sanda yake barin falon yaji hankalinsa bai kwanta ba. Muddin maamah tazo gidan to
ya tabbatar akwai wani abu maras dadi daya biyo baya. Ko mene kuma ya farun yasan babu me gaya
masa cikin gidan,daga amna sai musaddiq wanda baya gidan.
Yana takawa a farfajiyar gidan yana lalubar number amna din. Bugu daya ta daga tana amsa
sallama a nutse
"To hamma" Ta amsa masa tana sauke plate din hannunta data gagara cin abincin ciki. Wayar tabi da
kallo har yanzu muryar matar tana amsa kuwwa a kunnenta. Maganganunta sun girmi
kunnuwanta,batasan komai a kanta ba amma tana ganin rashin kirki qarara daga dukkan wani motsi
nata.
A tsaye ta sameshi idanunsa saman qananun shukokin dake bawa wajen iska me kyau da yanayi
me dadi
"Zauna" Yace da ita yana nuna mata kujerar dake gabansa tare da qoqarin karantar fuskarta. Ba musu
din ta zauna tana jin jikinta yana qara sanyaya daga kallon da taga yana yi mata
"Akwai baquwar da tazo gidan nan dazun?" Ya tambayeta yana kallon tsakiyar idanunta. Kallonsa itama
tayi sai tayi qasa da kanta tana tuna gargadin da anni tayi mata
"Ba ruwanki da abinda tazo ta fadi,wannan ba abinda ya shafeki bane.....ba'a gaban kowa kuma akayi ba
saike kadai...... Kada na soma jin zancan nan ya fita" Gargadin annin kenan bayan ta bar falon ta isketa a
kitchen.
"Ehnnnn......kina nan sanda ta shigo na tabbatar......akwai wasu abubuwa data cewa anni da abba?" Ya
sake tambayarta yana kallon fuskarta. Ba zata iya kallonsa kuma tayi masa qarya ba......hakanan ba zata
iya saba maganar anni ba,don haka ta zabi sunkuyar da kanta ta kuma girgiza masa kai. Qaramin
murmushi ne ya subuce masa wanda ba komai cikinsa sai bacin rai
"When kika fara yiwa hamma qarya amna?" Tambayar tasa saita rudata gaba daya,taji bata da sauran
zabi illa ta shaida masa gaskiya.
Tambayar farkon data jefawa abban ita ta sanya fuad jan kujera shima ya zauna wani nauyi yana
saukar masa. Ya ilahi.....wannan wacce irin jarabawa ce?,me yasa UWA take jin tasu jarabawar rayuwar?.
"Tashi kije" Ya bata umarnin daya sanyata miqewa da sauri tana barin wajen.
Tafin hannunsa ya sanya yadan daki goshinsa yana lumshe ido. A mizanin hankali da tunani da
sanin ya kamata......yayi zaton maamah zata kasance ne cikin sahun farko na mutanen da ko kansu sukan
sanya a gaba suka yanka ba zata ce komai ba.
****A hankali take takawa cikin layin zuciyarta na bugawa a hankali a hankali. Bugun zuciyartata ne
batasan meye ainihin dalilin faruwarsa ba. Tsoron ganinsa takeyi ko kuma shauqin ganin nasa?.
Tun daga wancan ranar daya aike mata wasiqa ta qarshe bata sake jinsa ko kuma ganin motsinsa
ba,har kawo yau da suke shirin cinye satin gab daya a kuma shiga sabon sati.
"Assalamu alaikum" Sautin sallamar daya sanya zuciyarta wani irinn bugawa ta ba zata,mamaki kuma da
tsoro suka hanata amsawa saboda yadda taji alamun muryarta a shaqe take. Kasa waiwayawa tayi har
zuwa sanda ya tako yana cimmata a inda take,ya zagaya kuma yana yiwa kansa matsaya a gabanta dab
da ita. Yanayin kallon daya rutsata dashi ya hanata janyewa baya kaman yadda takeyi a duk sanda ya
tsaya kusa da ita kamar haka
"Banga alamar kinyi kewata ba......inacan soyayyarki zata kasheni?" Ya furta yana karyar da wuya tare da
komawa kalar tausayi ainun.
"Ciwon sonki" Ya fada wani mayaudarin murmushi yana subuce masa. Nasararsa yake hange muraran
daga idanun yarinyar,ya tabbatar yana dab da cika burinsa......yana kuma gab da daukan fansa.
"Bakiyi kewata ba huda sam sam" Ya sake fadi yana kalmashe wuya idanunsa cikin nata,yanason ya sake
dasa mata dafin da zaiyi wahalar gogewa daga ranta. Yanason ya cimmata sosai,ya kuma nutsar da ita
cikin tafkin qaunarsa fiye da yadda yayarta ta jefa masa qugiyar da har yanzu ya gaza zameta daga
ruhinsa. Baya jin akwai wata mace da zata iya kashe masa qishirwarta. A kanta yakejin komai kuma ita
kadai zata iya sama masa da wannan nutsuwar.
Saidai kuma ya karanci hakan wani abu ne da bazai taba samunsa ba.....don haka gwara yayi
daukan fansan da zata gwammace bashi rayuwarta yayi yadda yaga dama da ita.
"Don Allah me kyau kice wani abu mana" Ya fada yana marairaice mata
"Nayi kewarka mana....." Ta samu kanta da furtawa. Yadda ya fidda idanu yana gwada mata mamakinsa
ya sanyata jin kunya gami da mamakin kanta. Wani abu ne da yake faruwa da ita karo na farko a
rayuwarta da bata taba tunanin zuwansa a nan kusa ba
"Da gaske kike?" Ya fadi har yanzu idanunsa a waje,sai tasa hannunta kawai ta lullube fuskarta dasu tana
sakin qaramin murmushi,abinda ya sake fidda kamanninta sosai da sabreen.
"Don Allah yau daya ki bani aron mintunanki biyar" Ya fadi yana hade hannayensa waje guda. Mintunan
biyar din da yake sanya ran a cikinsu zai qarasa dashen da ya dauko.
"Don Allah karkice aah,bazan sake neman wata alfarma ba daga wajenki ba daga wannan" Ya sake
maganar yana qara marairaicewa da kyau.
Rabuwa biyu zuciyarta tayi,wani sashe na zuciyar tata yana cewa ta bashi damar.......yayin da
wani sashen kuma yake cike da tsoro,tsoron da kusan kullum a cikinsa take.
Batasan yadda akayi ya shammaci rayuwarta har ta soma sabo dashi take kuma jin wasu baqin
abubuwa a kansa ba,irin abinda bata taba jinsa akan kowa ba,koda kuwa cikin duniyar mafarkinta ko
kuma hasashe.
Cikin qasa da mintuna biyar din daya dauka ya qarasa wargaza duk wani tunani nata. Sanda take
takawa zuwa gida dauke da kalamansa masu nauyi.......ji ta dinga yi duniyar tamkar ita daya ce mace a
ciki......dama haka zukatan dake da masu furta musu kalamai masu dadi sukeji?. Yau daya ta gasgata
kalaman daya taba furta mata
"Har yanxu ke yarinya ce.....ba zakisan dadin rayuwa ba sai kinso kin kuma bada dama an
soki......kowacce rai tana da buqatar wanda zai sota.....a lokacinne zaki karanci martaba da darajarki da
kuma zamowarki cikakkiyar mace duk da qarancin shekarunki.
Hannunta takai tana shafa qaramar wayar daya bata wadda ke dauke da layi da kuma number
dinsa. Ita kanta batasan adadin yawan roqon da yayi mata ba kafin ya karya zuciyarta ta aminta da
karbar wayar ba
"Zanyi tafiya me nisan xango,a qalla zanyi watanni biyu ban saki a idanuna ba......bazan iya jurar rashin
ganinki ba......" Kai take girgizawa a tsorace
"Yaa sabreen......"
"Ita kike tsoro?,zanje na nema dama a wajenta,kada ta rabani da abinda raina yakeso,zan roqeta ta barni
na dinga jin muryarki....."
"Baka da hank......" Taji bakinta ya subuce da fadi.....sai kuma ta yiwa kanta waigi daga furta abinda tayi
niyyar fada din a mugun tsorace. Yaa sabreen din da kullum kwanan duniya cikin kwatanta mata ta
kaucewa sauraren kowanne d'a namiji har sai ta isa minzali?,yaa sabreen din da bata lamuncewa kowa
mu'amala dasu ba komai kusancin dake tsakaninsu?,shine a yanzun yake neman kai kansa da kansa
gabanta?.
"Huda......zan iya komai a kanki.....zan kuma iya komai saboda ke,ni kadai nasan zafin sonki da nakeji a
raina.....don Allah ki karbi wayar nan......muryarki kawai xanji,daga gaisuwa idan kinso ki kashe wayar" .
Ido ta zuba masa a mamakance jikinta kuma yana yin sanyi,wai dama haka soyayyar take?. Qwallar data
gani shimfide a idanunsa suka karya duk wani qwarin gwiwa nata,kafiya da kuma dagiya,ta karbi wayar
ba tare da tana da masaniyar ta karbi shiryayyen abu da zai wargaza musu rayuwa ba dukkaninsu......
Sake dafa wayar tayi sosai,qasan ranta tana jin qarin tausayinsa yadda yake faman marairaice
mata,da alama soyayya ba qaramin kamu tayi masa ba. Dama wannan itace soyayyar?,dama haka
akeji?,dama haka take iya canza mutum daga ainihin yadda ka sanshi?.
Ita kanta mamakin kanta takeyi yadda ya iya canzata gaba daya cikin qanqanin lokaci haka,amma
kuma hakan fa yana nufin nan da shekara daya ko biyu kenan aure zatayi?. Tayi aure kuma yana nufin
tabar yaa sabreen?,tabar nadra tabar haneefa?.
To wai ta yaya ma zata fuskanci yaa sabreen din da shi?,tace mata me?,bayan tsahon tasowarta
idanunta basu taba gwada mata yaa sabreen din tana soyayya ba da kowa ma ballantana aure?,kullum
zancanta yadda zasuyi zuzzurfan karatu kuma su zama wasu a gaba......wannan qudurin zai cika kuwa?.
Eh.... Wata zuciyar ta bata amsa daga wani gefan
"Shi karatu ai baya hana aure......kaman yadda aure baya hana karatu" Ta tuna da wata hira data jiyo
'yammatan ajinsu sunayi,abinda ya sanyata sakin murmushi kenan dai dai sanda take sanya qafarta cikin
falon nasu.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 61
Dai dai lokacin sabreen din ke aje wayar mashkur wanda ya sanyata a lissafin yadda komai zaya
kasance.
Shine mutum na farko daya matsanta mata da son ta bishi wani guri wajen garinsu. Da fari yaso
ace dubai suka wuce,saidai tayi duk wata hikima tata ta kansile tafiyar da a baya ya tayar dayi musu
shirinta gadan gadan. Baisan wace ainihin sabreen ba.....shi yasa ya gaza fahimtar dukka wadannan
shirmen basa gabanta. Taqi kadan take jira ta yasar da qwallon mangwaro ta huta da quda.
A matse take.....kuma cikin matuqar buqatar kudaden saboda aikin ayshatu data tabbatar gab
zuciyarta take ga kaiwa ga matakin da zata daina moruwa. Ko a jiya data ziyarci gidan jikinta yayi
sanyi.......ta kuma sare sosai da yanayin jikin nata,har sun fidda rai da ita a wunin ranar,amma da yake
shi rai idan yana da sauran shan ruwanshi a gaba to tabbas fa sai ya sha.
Motsin shigowarta ba tare da sallama ba ya sanyata daga fararen idanunta ta zubesu a kanta.
"Meye hakan kuma yau?" Tayi mata tambayar tana duban fuskarta wani abu yana darsuwa a ranta.
Sai data danyi jim kadan sannan ta amsa mata,ta bude labulen ta shigo,sabreen ta bita da kallo
can qsan rabta wani abu yana kai kawo
"Sannu da gida" Ta fada tana nufar hanyar dakinsu,don sam ba'a sake take ba,Allah Allah take ta samu
waje ta yiwa wayartata ajiya me kyau. Tasan halin yaa sabreen din qwarai da gaske,tana da mugun fikira
da saurin dago wani abu dake a boye,a yanzun haka kallonta da takeyi din gani takeyi kaman tana kallon
wayar ne tarwai bisa idanunta.
Bata iya amsa mata ba,tadai bita da kallo har zuwa sanda ta wuce dakin. Janye dubanta tayi daga
bakin qofar dakin tana sauke numfashi. Bataso taji kokwanto ko shakka ko kadan akan 'yaruwarta......to
amma haka kawai jikinta yake bata wani yanayi daban wanda bata saba jinsa ba akan huda din.
Duk da tasan ba kowa a dakin amma hakan bai hanata kallon gabas da yamma hagu da dama na
dakin ba kafin ta ciro wayar daga aljihunta,ta kuma daga katifarsu daidai inda tafi kwanciya ta jefa
wayar. Tana dagowa sabreen na daga labulen dakin ta shigo hade da sallama.
Wani mummunar faduwa gabanta yayi,ta amsa da sauri tana kuma waiwayawa,sai suka hada
idanu da ita. Tsoronta ya qaru,ta dinga ji kamar ta ganta ne sanda take ajiyar.
Kanta da taga ta dauke shine abinda ya bata relief,ta sauke boyayyar ajiyar zuciya ta fara fidda
uniform din jikinta.
"Na'am" Ta sake amsa mata tana sakin rigar uniform dinta data kama zata fidda.
Idanunta ta zube mata,kafin tace komai haneefa da nadra sun shigo,wanda already sun rigata
dawowa harma sun sauya uniform dinsu zuwa kayan gida
"Kuje falo a samu plate a juye yasha iska,gani nan fitowa" Ta amsa musu tana binsu da idanu har suka
fice kafin ta maida dubanta ga huda
"Zo nan huda" Ta umarceta tana ci gaba da karantarta. Ba musu ta ajjiye dan kwalin hannunta sannan ta
tako ta zauna a inda sabreen din tayi mata nuni.
Zuba mata idanu tayi tamkar yau ta fara ganin fuskarta,abinda ya sake sanya ma huda fargaba da
shakku
"Kinsan na tsani nayi tambayar meke faruwa?,akwai matsala?......a bani amsa da babu komai....bayan
kuma da matsalar.....akwai kuma abinda yake faruwar" Ta qarashe maganar idanunta har yanzu cikin na
hudan.
Har cikin qashinta taji tambayar tata tamkar taba hango komai tar tar,saidai kuma wani sashe na
maganarsa ya bata qwarin gwiwa tare da hikimar kaucewar tuhumarta
"Tunda har akwai tsoron yaa sabreen a ranki,bai kamata ki bari a yanzu tasan muna tare ba,har sai mun
sake shaquwa da junanmu.....ta yadda koda ta tashi rabamu,tausayin yadda mukeson junanmu zai
sanyata ta haqura......akwai lokacin da na ware da zamu sanar mata......kinga koda kuwa na girme mata
nesa ba kusa ba.....amma dole nayi mata biyayya kema na tayaki yi mata biyayya ko ba haka ba?" Wasu
daga cikin kalamansa da a yau suka sake sanyawa ta sake masa. Yadda ya mutunta mata yayar da duk
duniya bata da abu mafi girman daraja irinsa.....bata jin zata kasa sonshi a ranta.
"Me yake faruwa huda......kome qanqantarsa kada ki boyemin" Ta furta tana kallonta.
Kanta ta girgiza tana narke fuskarta
"Me kika gani yaa sabreen......?" Itama kanta ta kada zuwa gefe guda gami da cije lips dinta na qasa,daga
qasan zuciyarta ana gaya mata lallai akwai wani abu da ba dai dai ba.
"Canji nake hangowa dan kadan huda......wanda kowanne canji cikin rayuwa daga kadan kadan yake
farawa" Ta amsa mata kai tsaye ba wani kwana kwana.
"Ba komai yaa sabreen fa.....idan ma akwai din ni bazan boye miki ba"
"Kin tabbata?" Ta jefa mata tambayar da wani nannauyan sauti dake tabbatar mata tambayar me girma
ce dake dauke da tarin fassarori da ma'anoni.
"Shikenan" Sai ta miqe itama tana daukar daya wayar tata wadda ita ta shigo da ita dakin.
Mika'il takeson tabowa.......tana da buqatar fara kawar dashi daga layin,koda kudin visa passport
da bill na asibitin ta samu daga gareshi,idanma so samu ne ya zamana komai ya fita daga jikinsa,ta yadda
duk abinda zai samu daga bangaren mashkur din zai zamana tamkar ribar qafa ce.
Akwai abubuwa da yawa da yake list dinta wannan karon da takeson yi,wanda kuma yana da
buqatar muquden kudade. Akwai mutane da yawa data kwana biyu bata gansu ba,tanason a wannan
karon ta jiqa kowa yadda ya kamata.
Kaman yadda ta saba kebe kanta a dukkan lokaci irin haka da ya shafeta. Yanzunma can farfajiyar
gidansu ta wuce bayan ta rabbatar ta sallamesu da dukkan abinda ya kamata. Me home work yana yi,me
bita da hada haddar da zaya bayar a islamiyya ma yana nashi.
JIB ta kira,kamar ko yaushe layinta layine na musamman da ita kadai ke kiransa dashi,hakan ya
sanya baya missing call,don muddin yaga kiran yasan akwai abu me muhimmanci.
Gaisuwar ban girma yayi mata kaman yadda suka saba sannan suka shiga tattaunawa kai tsaye
akan ayyukan da takeso ta gama dasu
"Ka sani,ba kasafai nakeson dadewa da mutum ba.....nafison nayi na gama a wuce gurin ya sake sabon
lale.....ciwon aishatu shine abinda yafi dagamin hankali najeeb......banason sanadiyyar wani ayshatu ta
rasa ranta......inason sama mata lafiya tare da mata tanadin rayuwa da zata manta abinda ake kira da
tsanani talauci ko wahala". Can qasan ransa yake hadiye wani abu,yana cika da mamakinta ako
yaushe,tana yawan sanya ranta da kanta a risk,bawai don saboda jin dadinta ko walwalarta
ba......aah......tana yin komai ne kawai don jin dadin wasu.
"Zamu kammala da izinin Allah......amma a wannan karon indai komai yayi kyau,adadin kudaden an
samesu daidai ya kamata kema ki inganta rayuwarki sama da yadda kike a yanzu". Dan qaramin
murmushi ne ya subuce mata,har jib yana iya jiyo sautinsa kadan
"JIB.....kune a gabana......har yanzu inajin mutanen dake tare dani ban kaisu matakin daya dace sukai
ba". Zuciyarsa ce ta karye girmanta na dada qaruwa a ranshi
"Ko yanzun ma me ya rage?,kinyi mana komai,tunda muna iya tsaiwa da qafafunmu......mu ya kamata
mu tallafeki kikai inda ya dace kikai din.....kusan dukkanmy burinmu ki samu nagartaccen miji......"
"Mubar wannan maganar jib yanzu" Ta katse numfashinsa. Murmushi kadan ya saki,shima kansa yasan
ya taba inda batason aje. Sau tari yakanyi mata uzuri......koda shine yaga abinda ta gani,yaji kuma abinda
taji ba shakka iya hukuncin da zaima rayuwarsa shine nisantar kowacce diya mace,saidai kallo daga
nesa,indai ba qaddara me qarfi da zata hada tarayyarsu guri guda ba.
"Zakibi mashkur abuja bayan mun gama da mika'il" Ya furta a nutse bayan shurun daya gifta a tsakani na
wasu 'yan mintuna
"Itace hanya guda daya mafi sauqi da zamu kammala komai hankalinmu kwance......na sani baki taba bin
kowa ko ina ba......amma a yanzun zakije,na miki alqawarin ba abinda zai faru,zan baki kariya da support
harki dawo,zan bi bayanku idan ta kama......kwana daya tal zaki bani zan kammala aikinsa.....mashkur din
nada tsananin wayo fiye da yadda kike tunani......amma kuma kinsan kutsa kai asusun mika'il yafi na
mashkur hadari da kuma tsauraran matakai da sai an masa shiri na gasken gaske?" Shuru tayi tana son
fasa maganganunsa daya bata su a cure. Kanta har ya soma dan hargitsewa,sai ta gyara zamanta kadan
tana cewa
"Ka rudar dani jib......mashkur nada wayon da lallai sai an bishi qafa da qafa kafin cimma
nasara......mika'il sassauqan wayo ne dashi......amma nasu account din yana tattare da tsaro sosai haka
ne?"
"Exactly boss lady" Ya fada yanason jefa raha cikin zancan. Ya jefawa fuskarta murmushi kadan kuwa,sai
taja dan qaramin tsaki
"A ajjiye wasa jib.....na soma gajiyawa da wadannan hadarurukan......inason muyi babban aikin da zan
huta nima hakanan na kula da rayukan dake gabana da kyau"
"Haka nakeso miki nima......bari na qara miki wani bayani kadan......mika'il yana riqe da ragamar babban
account din dake mallakin wani kamfanin sarrafa diamond......kamfani ne ne matuqar qarfin jari da
huldodin kasuwanci da qasashe daban daban.......kusan rabin kudin wannan kamfanin asusunsa mika'il
yana da access dashi.....hakanan duk wani kudi da zai shiga ko ya fita yana da access da hakan.....a
bincikena na lura yana wadaqa da kudin yadda yakeso,saidai kuma yana bi ta hanyar lura da saka
tsantseni ta yadda ba lallai a gane hakan ba,saboda mahaukaciyar riba da matsiyatan manya manyan
kudaden da kamfanin ke samu a kowacce rana....."
"Matsiyata.....manya manya?" Ta jefawa jib tambayar. Qaramar dariya ya saki
"Sorry......maqudan kudade"
"Okay......naji kana amfani da wasu kalmomi ne.....eheeen......kaga kenan komai zaizo mana akan
daidai?"
"Haka nake tunani......amma ki bani kwana uku,zan duba yadda zamu kutsa cikin asusun.....amma shima
dole ku hadu a ranar Koda na awa daya zuwa mintuna talatinne......ki sassauta riqon tsaurinki kiyi kaman
kin sakar masa komai....."
"Mtseewww....ya isa don Allah" Ta dakatar dashi,don zuwa yanzun abubuwan sun fara barin kanta,tana
ji kawai lokaci ya tunkarota da zata maida kai sosai ga 'yan uwanta. Dukkansu girma suke qara yi,kuma
suna da buqatar attention dinta sosai fiye da wanda take basu a baya.
"Shikenan......cikin kwanaki ukun zaki iya jina koda wanne lokaci,kibar wayar a bude,ki kuma fara shirin
zuwa abujan.....nima zanyi nawa shirin"
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 62
Tunda ta tabbatar ta fita zuwa farfajiyar gidan ta rufe qur'aninta,ta kuma miqe da hanzari ta
wuce zuwa cikin dakinsu.
Cikin mintuna qalilan ya cire dari darin da take na amsa wayarsa da takeyi cikin dakin. Tun tana a
tsaye tana kai kawo da kuma leqe tsakanin labulayen dakin har ta koma ta zauna sosai a gefen gadon
tana sauraren kalamansa dake da wani irin dadi suke kuma sake samun matsugunni me kyau a zuciyarta.
Yadda dukka kalamansa suke a tsaftace,ba wani kalma ko furuci maras kyau ya sanya take sake
jinsa sosai cikin ranta,wani bangaren na zuciyarta kuma yana yabawa kamalarsa da kamewarsa.
Ba wani abu me muhimmanci da zaman zaiyi mata,don haka ta yanke duka tunanin tana miqewa
daga inda take din tana nufar cikin gida don komawa dakinsu.
Tun daga nesa kadan dab da qofar da zata sadaka da ainihin tsakar gidansu ta hangi hadiyyan. Ta
ganta sarai zance takeyi,wanda dama takanyi din lokaci bayan lokaci.
So samu tabi ta wata hanyar da bazata hada numfashi da ita ba,to amma kuma babu
hanyar,saidai tabi zabi guda daya daya rage mata,ta koma ta zauna ta jirata har ta gama zancan tabar
wajen. Wannan abunne kuma takejin ba zata iya ba,duk abinda ta niyyaci ko nufaci yi ba kasafai take
bari dalilin wani ko wata ya sanyata ta juya da baya ba.
Tunda ta doso gurin ta fuskanci hankalinsa ya dauku a kanta. Ba baqon abu bane a wajenta saurin
gane motsi ko manufar d'a namiji a kanta daga kallo daya tak. Dauke hankalinta da idanunta tayi daga
wajen kamar bata san da zamansu ba tana wucewa ciki.
"Wannan 'yar gidanku ce itama kenan?" Ya maida hankalinsa ga hadiyya yana tambayarta wadda tuntuni
idanunta suna a kanshi,cikin wani irin banzan kallo da bacin ran yadda yake kallon sabreen din
"Eh 'yar nan dince.....sai akayi yaya kuma?" Ta bashi amsa a matuqar fusace har sabreen dake gab da
wucewa tana ita jiyota.
Kanta ta girgiza kawai tana sakin siririn murmushin nan nata maras sauti me dauke da tarin
ma'anoni masu yawa. Itakam daga hadiyya har dukkan wani gajan baqo da zayazo wajenta bata tunanin
akwai wanda ya isheta kallo a cikinsu.
"Ina kuma hudan?" Sabreen ta tambaya tana kallon sararin da tabar hudan a zaune kafin fitarta
"Ta shiga daki" Haneefa ta bata amsa. Labulen daya sakaya qofar shiga dakin tabi da kallo
"Ban sani ba wallahi.....naga dai ta shige" Nadra da aka miqawa tambayar ta amsawa sabreen cikin
rashin taqamaimen amsa
"Tun yaushe ta shiga din?" Ta sake tambayar nadra wannan karon qasa qasa.
"Baki jima da fita ba" Ta bata amsa itama da yanayin yadda tayi mata tambayar. Bata son saka ko darsa
wani abu a ransu,don haka tadan sake rantabrana kallon nadra
"Rufe littafin data bari a bude din" Batayi gaggawar shiga dakin ba don kada ta barwa zuciyar yaran wani
hasashe,saita koma ta bude fridge ta dauko ruwa,ta qarasa gaban first aid box dinsu dake ajiye cikin
falon t dauki paracetamol ta taka zuwa dakin.
Daidai sanda ta shaqi wani sassanyan numfashi daya cika fal da farinciki da kuma shauqin
soyyayya,daidai lokacin ta daga labulen dakin tana takowa zuwa ciki.
Mutuwar kwance tayi sanda idanunta suka ga shigowarta,sai ta kasa ci gaba da maganar da taso
ci gaba da yi. Tana iya jinsa yana cewa
"Hellooo.....my love.....hello" Amma ta kasa kowanne motsi. Duk sautin maganarsa qwaya daya ji takeyi
kamar zata saki fitsari,don tana ganin yadda sabreen din ke matsowa tsaf zata iya jin sautinsa.
"Me kikeyi a kwance bayan sallar magariba?.....kuma na barku ne kuna karatu?" Ta mata tambayar tana
kafeta da idanu,gami da zama saman drawer dake tsakanin gadajen nasu. Shuru yayi daga inda yake
zaune yana bin sakannin da suka kwashe da ita akan waya suna qara gudu,yana kuma sauraren sautin
muryar sabreen dake ratsowa ta cikin wayar zuwa kunnuwansa tare da sake tuna masa abubuwa masu
yawa da suka shude tsakaninshi da ita.
Numfashi taja ta sauke,lokaci daya yadda zata sauya daga ainihin yanayinta yazo mata,saita bata
fuska
"Banajin dadi ne". Inda hankalinta cikin jikinta yake a lokacin ba shakka babu abinda zai hanata jiyo
sautin fitar murmushinsa.
Ko iya hakan yana gwada masa samuwar matakin nasara daga gareshi. Ta yadda ya bibiyi diddigin
rayuwarsu.....a yadda bincike ya fito masa.....basa iya boye mata komai.....komai girman laifinsu ko
gaskiyarsu.....komai tsanani ko maslaharsu.....ba wani abu da suke iya lullube mata shi,yau gashi ya fara
taka matakin nasara......ta koya qarya saboda shi.
"Me yake damunki haka nan da nan?" Cikin qwarewa wajen iya bankado abinda ke lullube ta tambayeta.
Tambayar data sanyashi jingina bayansa da kujera yana jiran jin amsa ta biyu
"Kaina ne yake ciwo" Sai ya tsinci muryar sabreen din tana bada amsar da hudan ce ya kamata aji haka
daga bakinta.
Yadda ta bada amsar ya sanya huda daukewar numfashi daga jikinta na wucin gadi,tare da sanya
Naseer tattara hankalinsa akan wayar,kadan kadan fargabar kada ya zamana ta gano meke lullube tana
son saukar masa.
"Ga magani tashi kisha" Ta sake cewa da huda tana miqa mata kofin ruwan dake hannunta tare da
satches na maganin.
Ruwan da maganin duka tabi da kallo,ta fara motsawa kadan sannan ta miqe da sauri ta zauna
tana sakin wayar. Santsin pillow din ya sanya ta zame ta kuma sulale ta sauka a gefen cinyarta saita
matsa kadan tana qarasa danneta.
Ci gaba tayi da dubanta har zuwa sanda ta balla maganin tasha,sai ta miqa hannu ta karbi
rayuwar ruwan da maganin itama ta balla ta sanya a bakinta tabi da ruwa
"Ba abu mafi sauqin fade irin ciwon kai.....amma ki sani,yawan kiran sunansa yana iya jawoshi koda babu
shi a wajen" Ta fadi tana qarasa sauke idonta a kanta.
Tsoro da fargaba ya sake cikata,saita lumshe idonta tana son dasa gaskiyarta a zuciyarta
"Nima zamana kenan na jishi ya saukar min,na dauka nadan lokaci ne xai sauka idan na kwanta"
"Allah ya sawwaqe" Ta fada a taqaice tana takawa a hankali hadi da ficewa daga dakin.
Wata ajiyar zuciya ta sauke tana fidda idanunta waje,tana iya jin yadda bugun zuciyarta ke kai
kawo wanda ta tabbata tsoro razani da kuma firgici ne ya haifar mata dasu.
*****Tsakanin asabar da kuma lahadin yana da isashe lokacin da zaiyi shirin komawa bakin ayyukansa
zuwa litinin,wannan ya sanyashi maido da dukan ayyukansa da suka tsaya sakamakon tafiyar da yayi.
Shi kansa yasan satin da zasu shiga din ba satin zama bane,babu hutu sam a tattare dashi. Aikine
me yawan gaske,don bayajin zai zauna ya huta har sai yakai ga gacin kammala komai ya kuma bude
kamfanin da a yanzu shine cikar burinsa.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 63
Sassanyan yammaci ne dake bada wata irin iska me dadin shaqa da samar da nutsuwa ga
zukata,hakan ya sanya zaman wajen yayi masa dadi ,wanda tun bayan sallar azahar ya zauna a nan din.
Yau din zama sukayi sosai da mu'allim,wanda shi yake kula da bangaren masu buqata ta musamman da
kuma neman taimako. Ya karba list na mutane masu yawa,ciki harda list din anni dana maamah wanda
ya jima yana kallonshi.
Sunaye na mutane barkatai,wanda yafi kyautata zaton an shirya sunan ne kawai an kuma shigar.
Ya karba takardar da zummar zai duba din,don hatta da numbers na wayoyinsu dake a jiki kallo daya yayi
musu yaji sunfi masa kama da lambobin bogi.
A yanzun ya gama shigar da komai cikin laptop dinsa da kusan zaiyi wahala ka ganshi ba ita. Tana
dauke da muhimman bayanansa da kuma sirrika sosai a ciki.
A yanzu da yake zaune yana karbar kira ta kai tsaye ta cikin system dinsa. Video call ne da daya
daga cikin kamfanin narka gold da wankeshi daga qasar china,farouq ya tako yana isowa farfajiyar.
Kujera yaja ya zauna,sannan ya fidda wayarsa yana duba saqonnin WhatsApp da tun daxun ya
sauka da zummar zai koma din. Hira sosai suka shiga yi da fannah,don kusan duka saboda ita din ya hau.
Jifa jifa yana mata gajeran voice note don kada ya janye hankalin fu'ad da baqonshi.
A nutse ya kammala amsa kiran,yayi disconnecting sannan ya maida dubansa ga farouq. Idanu
yadan zuba masa,yana mamakin yadda yakejin dadin soyayya gaba daya,wai shin mene a cikinta har
haka da take iya maida mutum wawa ne?.
"Ya dai?" Yaji muryar farouq din yana katse masa tunaninsa
"For what?" Farouq ya katse masa magana yana maida masa tambaya murmushi dan kadan yana fita a
fuskarsa
"Yadda mutum me hankali yake komawa kaman soko.......wannan abar farouq It doesn't make sense
wallahi" Ya fadi iya gaskiyarshi,gaskiyar da har saman fuskarsa zaka hangeta kwance quru quru.
Dariya ce sosai ta qwacewa farouq har yana duqawa,abinda ya sanya fu'ad tsaiwa ya zuba masa
ido yana kallonsa.
"To abun kuma ya fara cin qarfina,to be sincere ka fara bani tsoro sama dana baya.......nafi tunanin kuma
yanxun bawai aljana bace ta aureka ba,tunda koda aljana ce saida soyayya ai ko?"
"Kai ka sani qaton banza" Fu'ad din ya fada yana jifansa da wata harara data sake sanyawa farouq ya
fashe da dariya,don irin wannan hararar kawai yake iyayi masa idan ya quleshi ya kaishi bango.
Qoqarin daidaita nutsuwarsa yayi don kada ya jawowa kansa jagwal ko yaqi bashi hadin kai akan
batun da yazo masa dashi,ya sani sarai kadanne daga aikinsa ya murje idanunsa,musamman yanzun da
har ya shiga gonarsa ya kuma tsokaneshi.
"Mu ajjiye wannan batun.....ina nan dai inayi maka addu'a.......na saka a duba mana ticket zuwa abuja
Saturday in sha Allah......already ma nayi payment zai mana printing ne kawai"
"Bazanje ba" Ya bashi amsa kai tsaye yana qoqarin shutting down system dinsa idanunsa saman screen
din.
"Sai na tafi ni kadai.....amma kuma idan ta tambayeka,zan bata labarin ka saba Alqawarin da mukayi da
kai ne" Yakai qarshe yana zuba ma side na fuskarshi idanu.
Shuru yayi kawai bai sake cewa komai ba,wanda alamu ke nunawa farouq zaiyi wahala yace
bazaije din ba. Sau tari shuru a wajensa alamu ne na accepting abubuwa,idan baya so kai tsaye zaice
baiso kuma bazaiyi ba kaman yadda yanzu ya fada mishi da farki,yana sane kuma ya sanyo zancan cika
alqawarin......don ya sani shi din mutum ne da ba abinda ya tsana irin qarya sam sam,idan kanaso kaga
tunzurarsa ko fadansa to kayi masa qarya.
"Ya ake ciki maganar ginin?" Farouq ya sanyo masa maganar da yasan yanzun itace a gabansa sama da
ko wacce. Sai kuwa ya qarasa kashe system din ya rufeta yana dora fararen idanunsa akan farouq din.
"Ending month dinnan nake sanya ran gini zai kammala,sai preparation kawai na budewa wanda shima
banaso ya wuce watanni biyu.....duka engines da sauran kaya next week zasu iso in sha Allah" . Kai
farouq yake jinjinawa,yana matuqar yabawa da hazaqa da qoqari irin na fu'ad din.
Tun farko yasan idan don ta shine bazai iya ba......don haka ma ya saki wannan ragamar kawai ya
miqawa fu'ad din,don tunda shi ya faro barota shine zai iya. Qaramin murmushi farouq din ya saki,fu'ad
ya dage masa gira alamun tambaya
"Ba komai.......kawai na tuna temple run dinka ne......rigimammen dan bautar qasar da yaje garin wasu
ya musu barna.....ya kuma gudo da abinda suke ta buri da nacin samu......Allah inda a zamanin yaqe yaqe
ne zakayi barna da yawa fa" Maganar dole ta sanya murmushi kubcewa daga fuskar fu'ad,ya zauna sosai
yana sake duban farouq
"Mazantaka a zuciya take farouq......sannan dukkan namiji muddin zai amsa wannan sunan dole kalmar
TSORO ta fita daga dabi'arsa......bai halatta ba sam sam namiji ya zama me tsoro ba..... Idan hakan kuwa
ta kasance a matsayinsa na shugaba kuma jagora,dole al'amura su lalace..... Adinga ganinsu kuma ba'a
yadda suke ba".
Duk da tsananin gajiyar dake a jikinta bayan dawowarsu daga wajen boka DURGUJI amma hakan
bai sanyata zama ta huta ba bare akai ga batun kwanciya. Kai kawo kawai takeyi tsakanin kitchen da
dakunanta cikin sabgar dafawa da saukewa. Wani tsari da takeson fara qirqiro dashi a yau din,don shine
hanya guda daya da zata samu ayyukan da aka tsara mata su tafi yadda takeso.
Ta bata lokaci sosai tana son tuna wanne abinci da wanne abinci sukafiso ta dafa musu lokacin
quruciyarsu?. Da qyar ta dinga tuna wasi abubuwan da suma shafesu saboda yadda ruhi da zuciya suka
jima da yin nisa daga rayuwarsu dama komai daya shafesu.
Tayi lissafin abubuwa guda hudu duk da tasan sunfi hakan,saidai sauran ta barwa ranta zata nemi
ganin ma'aikatansa da yake yawan rayuwa dasu don samun wasu amsoshin. Anni ce tasan wadda zata
samu amsar kai tsaye daga gareta,saidai zuwa yanzun tana jin cewa tafi qarfin anni ballantana ta sake
neman wani abu daga wajenta akan 'ya'yan da ita tayi cikinsu ta kuma haife abinta. Alwashi taci......tana
nan kuma riqe dashi......hakanan ba zata runtsa ba ba kuma zata huta ba har sai ta samu cikar wannan
alwashin nata.
Tana aikin masu aikinta suna mamakin shigarta kitchen yau da kanta. Duk kallon da suke binta
dashi bata samu nasarar tantancewa ko kuma kula ba,saboda hankalinta yayi matuqar nisa akan
maganganun da suka tattauna da durguji.
_"sau daya nakewa mutum aiki na gama dashi.....muddin kuma nayi aiki baici ba yana da wahala na sake
na biyu indai ba sa'a ka taka ba......aikinki me hatsarin gaske ne......duk abinda kikaji ko kika gani kada ki
wuce wata guda kacal baki dawomin ba"_
Ita batun sake aiki da rashin sakewar duka ba damuwarta bane,tunda ta riga data sani kudi suke
juya akalar kowa su kuma sauya tunaninsa. Muddin zata zube masa kudi ta tabbatar duk taurin kansa sai
ya sake waiwayarta. Kawai abinda yake damunta a yanzu shine yadda zata samu dawowar hankulansu a
kanta,ta yadda cinsu da shansu zai dawo qarqashinta,wanda wannan shine abu guda daya tal da zai
sanya aikinta ya tafi yadda ya dace.
Tana kammala white rice sai ta kasa haquri ta fita a kitchen din. Dakin gadonta ta wuce ta samu
saman sofa bed ta zauna tana latsa wayarta. Number fu'ad din ta fara kira,daidai sanda yake zaune suka
ci gaba da tattaunawa da farouq yana nuna masa tsarin taswirar ginin kamfanin.
Fararen idanunsa ya daga yana azawa saman wayar. Zubawa wayar idanu yayi yana kallon yadda
sunan ke wucewa ta saman screen din. A duk sanda zaiga shigowar kiranta sai yaji wani abu tun daga
qasan ransa har tafin qafafunsa. Inda yana da iko bazai daga wayar ba sam sam,to amma wata fuskar tafi
gaban mari
"Ina zuwa" Yace da farouq yana daukan wayar ya daga ya saka a kunnensa.
Cikakkiyar sallama tayi da kwantacciyar murya da zai iya cewa ya manta rabon da yajita daga
bakinta,wani abu guda daya sake jan hankalinsa,saidai bai hanashi amsa sallamartata ba hadi da dorawa
da fadin
"Ka wuni lafiya kai da dan uwanka?,tunda har yanzu ban cancanci a kullum naga lafiyarku ba......hasalima
kamar kuna mantawa ne da rayuwata" Yadda tayi maganar ya taba ransa kadan,yaji sautin da amon da
ya jima baiji daga gareta ba
"Kiyi haquri ba haka bane" Ya maida amsa wani abu yana kai kawo a ranshi
"To idan ba haka bane yaya ne Muhammadu?,kamanhar yanzu kun kasa manta abinda ya faru ne kawai"
Idanunsa ya lumshe kawai yana saurarenta. Zuciyarsa nadan qara bugun da takeyi yana jin wani abu
sosai can qasan ransa da kuma wani sashe na zuciyarsa
"Idan zaku iyayimin alfarma,inaso ana gama sallar ishai ku shigo kai da musaddiq....inason ganinku duka
ku biyun"
"In sha Allah" Ya amsa mata kai tsaye. Wayar na a kunnensa har ta yanke Kiran,sai shima ya zame wayar
daga kunnensa yana kallon screen din.
Sanda ya daga idanunsa sai suka hada ido da farouq,murmushi farouq din ya sakar masa kawai.
Har yanzu bai taba saka baki ko shiga lamarinsa da maamah ba,infact ma shi bai taba masa magana a
kanta ba,ko yaushe shida sadiq suna qoqarin kiyaye iyakokinsu ne.
Wani irin murmushi ta saki bayan ta ajiye wayar idanunta akan qofa tana jin wani farinciki yana
shigarta. Nasara ce a kusa take shanshanarta......kuma jikinta yana bata komai yana kusa da qofarta.
Plan dinta guda uku ne qwarara,ta fara da wannan na farkon,idan yayi aiki shikenan,idan baiyi
ba zata wuce plan B,idan shima yayi aiki shikenan,idan kuma shima baiyi ba tana da plan C......wanda
shine tsororuwar shiri mafi tsauri da tauri.....plan din data tabbatar zai yamutsa hazo iya
yamutsawa........ita kuma zata saki dukkan wata iyaka da ikon da Allah ya bata don ganin tabbatuwar
plan din da kuma wanzar dashi.
Ranta fes,Zuciyarta wasai ta ajiye wayar ta koma kitchen tana shirye shirye shirye gadan gadan.
Haka kawai yakejin yanayinsa wani iri,jikinsa da zuciyarsa dukka ba'a sake suke ba,a haka ya shirya
cikin Moroccan abaya ne sulbi ya wuce zuwa sallar magariba.
Kafin ya isa masallacin suna hanya shi da farouq musaddiq da saddiq suka biyo bayansu.
Wannan din wata kyakkyawar al'adarsu ce da anni ta renesu a kai. Muddin suna garin ko suna
qasar,hakanan ba wani babban uzuri ko aiki bane ya riqesu a kamfani,to zaka samesu a gida duk inda
magariba tayi. Kwata kwata basusan yawon dare ba,farouq ne ma medan sha'awar fitan daren,to sukan
fita jifa jifa su zaga a mota su dawo. A nan zasuyi sallar magariba suyi ishai,suyi dinner tare me uzuru ya
wuce nasa uzurin.
Sanda yake sabule tattausan flip flops din qafarsa yace da musaddiq ba tare daya waiwayo ba
"Bayan ishai ku shirya kaida saddiq zamu shiga wajen maamah" Dan kallon yayan nasa kadan
yayi,kaman zai magana sai kuma ya fasa ya amsa da to.
Tun bayan magariba ta sallami kowa tare da kafawa kowa sharadi da dokar bataso kowa ya sake
tako mata parlor sai gobe idan Allah ya kaimu.
Ta duba doormat din bakin qofar falon yafi sau goma daga zamanta,ta kuma tabbatar komai yana
nan intact kamar yadda ya kamata ace ya kasance din,sai ta koma ta zauna tana sauya tashar Tv din
zuwa mbc Bollywood bawai don tana jin dadin kallon ko yana burgeta ba,dukkan hankalinta yanzu da
nutsuwarta shine takowarsu cikin falon,su zauna kuma su cika cikin su da abinci da abin shan da ta
tsumashi ta kuma tanadashi musamman saboda su.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 64
Saddiq da musaddiq dinne a gaba shi kuma yana biye dasu a hankali a hankali,hakan ya sanya suka
dan masa tazara kadan. Wayar Mika'il yake amsawa,wanda yakeso ya tabbatar komai ya zama daidai
zuwa ranar Monday da zai koma office. Yanason ya gabatar masa da dukkan wasu mu'amala na kudi da
banking ya samu bayan tafiyar tasa,komai na shige da ficen kudi.
Yana wayar ne amma hankalinsa yana kan saddiq da musaddiq,tamkar 'yan biyu kamar yadda
kowa yake musu kallo hatta da makarantun da sukayi. Suna hira abinsu ne cikin wani irin shaquwa da
jituwar jini. Malam saidu ne ya bude musu qofan da kanshi,ya rusuna kuma yana miqa masa gaisuwa sai
ya gyada masa kai hadi da daga masa hannu saboda wayar da yakeyi din,ya taka a nutse yana bin
bayansu.
Dab da zasu isa steps din da zasu sadasu da ainihin falon yaji gabansa yayi wani mummunar
faduwa
"Zamu qarasa anjima" Yace da Mika'il a gaggauce yana katse wayar ba tare daya jira amsarsa ba
"Kai saddiq" Ya furta da muryar da taja hankalin maamah dake falon,wadda dama dukkan tunaninta
yana fa farfajiyar gidan tana sauraren kowanne motsi.
"Saddiq kuma?" Ta tambayi kanta da kanta a mamakance,sai ta tuna kuma bata da sauran lokacin
batawa,don muddin ta bari wani bayan yaran nata ya taka wannan shirin akwai matsala,don haka ta
zabura tayi zumbur ta miqe ta kuma nufi bakin qofar falon da sassarfa.
Wancakali tayi da doormat din,ta sanya hannu ta dauke abun da yake qasan,sannan ta finciki
tsintsiya dake ajiye a can wani gefe daban ta fara tattara sauran abubuwan da suka rage.
"Kunyi addu'a ne?" Ya fada yana tsaresu da idanu duka su biyun. Juna suka kalla shi da musaddiq din
"Hamma ai daga masallaci muke" Saddiq din ya fada dukkaninsu suna sauke qafafunsu daga saman steps
din da suka fara dorawa
"Kuyi addu'a kafin ku shiga.......haka musulunci ya koyar damu,kome zakayi akwai addu'ar da akeyi
masa" Ya fadi idanunsa akan musaddiq
"To hamma" Suka fadi sannan suka maida qafafunsu kowa bakinsa yana dan motsawa.
Da kallo ya bisu zuciyarsa cike da wani wasi wasi da baisan daga inda ya samo asali ba. Sosai
hankalinsa yana kan musaddiq da ya tabbatar baisan komai akan shirin maamah nason raba tsakaninsu
da iyalin alhaji hamza ba. Shi kansa abban baisan komai ba akai,shi daya yake juya maganar tsakanin
qirjinsa da zuciyarsa.
Dan ja sukayi suka tsaya sanda suka sameta duqe tana tattare wani abu da basusan meye shi ba.
Ta daga kai tana dubansu,wani irin bacin rai ya cika mata zuciya fal.
Ta yaya banda sun raina umarninta zata ce tana buqatar ganinsu su biyu su rakito mata wani?.
Fushin yanason yayi galaba a kanta amma tanata qoqarin danneshi. Yanzun ba lokacin nuna fushi bane
ko fada..... Lokaci ne na sauke kai da maida komai ba komai ba muddin nasara take da buqata,wannan
shine abinda hajja ta gaya mata.
Dole ta qirqiro murmushi tana cewa cikin nuna kulawa a garesu gaba daya
"Maraba da 'yan samari na" Saita zubda abun cikin kwandon shara ta kuma taka zuwa ciki tana fadin
"Ku qaraso mana". Sai da suka fara shiga sannan yabi bayansu yana kula da hagu da damansu
"Ina ma'aikatan suka barki kina shara?" Fuad ya furta da nutsatsiyar muryarshin nan yana zama hannun
kujera hannunsa goye a qirjinsa yana kuma qoqarin karantar komai dama motsin komai dake a falon.
Dan murmushi ta saki tana zama saman daya daga cikin kujerun alfarma dake falon
"Ina buqatar kebewa da 'ya'yana,nayi sirri dasu irin na uwa da 'ya'yanta,shi yasa na sallamesu yau da
wuri". Maganar tata sai ta kasance kamar ta jefi tsuntsu biyu ne da dutse guda,don haka saddiq sai ya
rusuna kawai yana gaidata.
"Lafiya alhamdlh saddiq......ya mutanen gidan?"
"Zataji in sha Allah......hamma zan qarasa,saikun fito" Idanu fuad din ya zube masa,yayin da maamah ta
bata fuska tana cewa
"Ina kuma zaka daga shigowarku ko zama bakayi ba?". Dan murmushi yayi yana saukar da kansa qasa
cikin girmamawa
"Gida zan qarasa,jibi zamu koma company ban kuma gama shiryawa ba,kinsan kuma hamma......bazai
dagan qafa ba idan aka samu kuskure" Tabe baki tayi kadan ta yadda ba lallai bane su fuskanta,qasan
zuciyarta kuma cike fal da baqinciki da bacin rai,amma kuma a fili saita saki murmushi
"In sha Allah" Ya fadi yana waiwayawa gefan musaddiq ya bashi hannu yadda suka saba yana yin gaba.
Shiru falon ya dauka sanda saddiq ke ficewa,cikin ranta take gayawa kanta da kanta saura kadan
komai yazo qarshe.... .watan watarana saidai ya gifta katangun kamfanin ya ratse ya wuce ta
bayansu,komai na wata dama ta shiga cikin kamfanin baida ita.
Sai daya kammala ficewa tsaf sannan ta maida dubanta garesu,dukansu ta fahimci kamar
hankalinsu baya tare da ita,don haka ta danyi gyaran murya,gyaran muryar daya sanya dukansu suka
dubeta,sai ta saki musu murmushi.
Amsa gaisuwarsu dukka su biyun tayi,a yau sai take jinta kamar a aljannar duniya,sai takejin
kamar burinta ya gama cika duk da an samu matsala a karon farko,amma akwai tafiya ta gaba,ta
tabbatar ba zasu tsallakewa abincinta ba.
Tanaso a yau tasan abubuwa masu yawa game da rayuwarsu,tanason tasan adadi da zurfin
dukiyar da kowannensu ya mallaka,koda batasan duka ba,tanason ta karanci kaso me tsoka.
"Ina fatan zaku cire komai daga zuciyarku,kuci gaba da kallona a matsayin mahaifiyarku,komai zai wuce
mu fara gina sabuwar rayuwa tsakanina daku.....ina buqatar 'ya'yana a kusa dani kamar yadda kowacce
uwa take da buqatar 'ya'yanta. Inaso na kasance daku tamkar komai bai faru ba,nayi alqawarin baku
farinciki da kariya kaman yadda kowacce uwa ke bawa 'ya'yanta" Ta qarashe maganar cikin matuqar
raunin zuciya da karyewar murya kamar wadda ke shirin sakin kuka.
Ci gaba da dubanta fu'ad yayi mamakinsa yana qaruwa. Tunda ta fara magana baiji inda tace tayi
nadama ba......nadama koda qwaya daya akan abinda ta yiwa abbansu ba,su din basu da buqatar ta
nema yafiya ko afuwarsu,tunda itace ta haifesu,tayi silar kowasu duniya.....ba wani abu da zasuyi mata
wanda zasu saka mata da iya wannan aikin......amma kuma abban fa?,kota manta cewa itace silar
komai?,ta manta itace silar faruwar komai?. A yanzun ya Fatimid tafi buqatar hankalunsu a kanta da
abinda suka mallaka sama da nadama neman afuwa ta zahiri da yafiya daga mutumin da aka zalunta
wanda yanzu haka yake kwance a qarqashin qasa.
"Banaso ku dinga nesa dani suka nesanta kanku dani,bani da wani abu dana mallaka a yanzu sama
daku.......ina zaune ni kadai,idan mutuwa ma nayi kenan saidai kuji labari daga wajen bare?" Ta maida
tambayar kan fuskar musaddiq. Kanshi ya girgiza mata yana sauke kan nasa qasa. Har yanzu idanunsa da
sauran tunaninsa sun kasa goge masa komai,ballantana hammansa daya tabbata komai yana rubuce ne
a allon zuciyarsa. A duk sanda ya kalleta sai ya tuna ruwan data watsa saman fuskar majinyacin
mahaifinsu sanda ya buqaci ta bashi ruwa,shine ya zame masa rumfa yaje ya kwanta a samanshi da
zummar kareshi saboda sanyi da yadda ya jiqe din sosai,a sannan ta taka ta fice a dakin hankalinta
kwance tana waqe waqe abinta.
"Don Allah koda abincin dare ne ku kasance tare dani ko na safe... Ku bani koda awa daya kowacce rana
mu zauna ni daku nasan na haifi 'ya'ya nima kamar kowacce uwa.....don Allah" Ta sake fada da muryar
roqo sosai,raunanniyar muryar daka iya sauko da tausayi a zuciyar wanda baisan manufar me magana
ba.
"In sha Alla" Kawai fu'ad din ya furta. Ya sani koma me zaice yanzu ba maslaha zai kawo ba,ba kuma zata
taba fahimta tunda akwai banbancin manufa a tsakaninsu. Kowanne a cikinsu abinda ya ajjiye a
zuciyarsa daban.
"Muje ga abincin dare can na shirya muku.....abinda nasan kunfi so sosai" Ta fada tana murmushi ranta
yana mata dadi da yadda suka karbi request dinta suka amince da xuwan nasu.
Ba wanda ya musa mata,suna dai binta da ido da kuma hankulansu har xuwa sanda ta jawa
kowannensu kujerar zama tana fadin
Serving nasu komai da komai tayi,tana yi tana jansu da hira tare da qoqarin tuna musu wani abu
na daga quruciyarsu. Shidai fu'ad idanu ne kawai nashi ba tare daya iya maida komai ba,har ta kammala
tana fadin
"Gashinan kowa ya dauki nasa". Duban abincin yayi da kyau,gaskiya ta fada batayi kuskure ba,a baya
baida abincin da yakeso irinsa,amma tun daga ranar data dafa abincin cikin gidansu,ta kuma yiwa
mahaifinsu haramiyar abincin a sanda yake kwance yana jinya.....yunwa take sake take rawa wajen
galabaitar dashi,ta hana masa abincin,abinda yayi silar kwanansa da yunwa,tun daga ranar har kawo yau
bai sake saka irin abincin a bakinsa ba,daga ranar ya fita a ransa,fita ta har abada wadda har yau bai sake
dawowa zuciya da rayuwarsa ba.
"Shikam hamma ai maamah yanzun wannan ba cimarsa bane......nima kuma kin manta dama ba kasafai
na fiya ci din ba?" Musaddiq ya fada yana shafa kanshi idanunsa cikin na maamah din.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 65
Wani abu ne yaso ya tsaye mata a rai,tunzura takeso tayi amma kuma tana gayawa kanta ba
yanzu ba......idan ma basuci na yau ba ai na gobe yana nan,muddin kuma zasu ci gaba da taka qafarsu
cikin gidan yau ko gobe nasara tana nan tare da ita.
"Yaushe Muhammad ya daina ci?" Ta yiwa musaddiq tambayar sai kuma ta maida dubanta ga fuskar
fu'ad din a mamakance,saidai kuma sanda suka hada idanu dashi sai komai daya faru a wancan ranar ya
dawo mata a take,amsar tambayarta ta fita kamar budewar shafukan littafi.
Wani abu taji me nauyi wanda sam baiyi kama da kunya ko nadama ba,tabbas a baya din don ba
cikin daidanta take ba.....ba yaran bane a gabanta ballantana abinda ya shafesu da har zata lura da meye
ya damesu da wanda bai damesu ba.....amma tabbas sai yanzu ta tuna,tun daga ranar yake bar mata
kwanonta gaba daya yadda ta zuba.
"To amma bai kamata ace bakuci komai ba koda lemo ne" Ta sake fadi tana jan jug din gabanta tare da
qoqarin raba kofunan ta zuba musun kada ya zamana komai da komai ma tayi asararsa a yau din.
Idonsa still a kanta,ya miqa hannu ya jawo gorar ruwan daya tabbatar a kulle take ya soma
budeta,qarar budewar ya sanya ta daga kanta zuwa gareshi tana dubansa
"Ruwa kuma muhammadu?,ga lemo dai" Ta fada tana tura masa wanda ta zuba
"Maamah dare ya soma yi.....idan kuma dare ya fara bana iya cin komai...." Dubansa ta sakeyi kadan sai
kuma ta dauke kanta tana qirqiro murmushi
"Kowa time table zai bani na abinda yakeso yaci kullum har sati guda koma sati biyu.....masu girki na
musamman zan ajiye muku.....burina naga kun kusanta dani......na maida tsohuwar alaqar dake a
tsakaninmu" Ta qarasa maganar tana duban cikin idanunsu.
"Fu'ad" Ta sake kiran sunansa,ya daga fararen idanunsa da suka fara rusuna saboda gajiya da zama a
wajen,sam baya jinsa comfortable sam sam
"Me yasa kabar musaddiq tare da farouq......duk da ba laifi bane.....amma kaman zaifi cancanta ya
kasance tare dakai qarqashin naka kamfanin" Shuru ya biyo baya na second uku,sai ya maida idanunsa
ya kulle yana jan boyayyen numfashi. Shikam yayi imanin ba zata canza ba,ya tabbatar abune me wahala
da girman gaske da zai sauya mata hali farat daya. Wannan ya sanya kowanne taku ko motsi nata yake
sanya masa ayar tambaya,wani lokaci idan tayi wani move din sai yaji gaba daya kanshi ya juye yana
tambayar kansa anya da gaske maamah din itace uwa ta asali a garesu?.
"Kowanne bawa da abinda yafi shaawar yi yafi qwarewa a rayuwarsa......yadda abba ya ginemu shine
kowa ya dauki zabinsa da ra'ayinsa a rayuwa muddin bai kaucewa hanya ba....inda kikaga farouq da
musaddiq su suka zabi wannan sashen duk kuwa da cewa tare da farouq mukayi gwagwarmayar samar
da abinda na gina din a yanzu.....ba wanda ya zaba masa ko ya tursashi gashinan maamah ki tambayeshi"
Juyawa tayi tana duban musaddiq ranta duka a jagule,bata son kowa ya rabi fu'ad a duniya idan ba dan
uwanshi ba,batason kowa yasan sirrin dukiyarsa idan zaiyuwu sai ita daya,wannan tunanin ya sanya ta
yanke shawarar sanya ido me tsananin a alaqar fu'ad din da amna......don ba zata taba yarda amina ta
dauki d'iyarta ta qwaquma masa ba su qarasa nadeshi.
"Shikenan,Allah ya taimaka" Ta fadi tana sauke numfashi bawai don ta haqura a zuciyarta ba. Kawai tana
ganin tunda komai yana kan turba bai kamata ta bata lokacinta tana dogon zance dasu ba,lokaci kadan
take jira ta soma bada umarnin wanda zai shiga ko ya fita daga rayuwarsu.
"To yaya sunan surukar tamu musaddiq?....koda wasa baka taba attempting kawota ta gaida mamarka
ba?" Ta yiwa musaddiq tambayar tana dubansa da murmushi,cike da zaquwa da son jin kalar matan da
suke shirin kawowa rayuwarsu. Wani babbab abu da yake cikin tsarin abubuwan da takeso ta yiwa
garambawul idan damar da take tsimayi ta samu,tanason surukanta su zama qarqashin ikonta fiye da
yadda hajja ke juya nata mulkin a gidan.
"Minal bata iya zuwa ko ina,daga makaranta sai gida.....zata zo wataran in sha Allah". Ba haka takeson ji
ba,don haka ta gyara zamanta tana sake sakin fuskarta
"Aah wataran yaushe kenan?,ina buqatar ganinta mu tattauna ka shaida mata mamarta nason
ganinta......" Ta fadi din don da gaske tanason ganin wace ita?. Zuwan nata kuma a nan ne zata samu
amsoshin tambayoyib data tabbatar ba zata samesu daga bakin musaddiq ba.
"In sha Allah" Ya fadi a taqaice yana auna yadda abun zai kasance.
"Kai kuma fa?" Ta waiwaya tana duban fu'ad daya tattara hankalinsa duka saman wayarsa tamkar ma
baya jin abinda suke fadi. Gajiyayyun idanunsa dinnan ya daga ya kalleta,sai kuma ya maida dubansa ga
musaddiq. Kan musaddiq din a qasa yana satar kallon fu'ad din ta qasan idanunsa,boyayyan murmushi
nason qwace masa.
Debe kallonta kacokam tayi ta maida kan musaddiq tanason sake samun tabbacin hakan
"Kamar yaya kenan?" Satar kallon fu'ad yayi sannan ya dubi maamah,yayi qasa sosai da muryarsa,duk da
yasan dole ya jishi don yana da wannan baiwar ta kaifin ji
"Ba wata budurwa.....tsoronsa ma suke......ba wadda take iya tararsa maamah tace tana sonshi"
"Very good" Ta fada qasan zuciyarta. Tsananin farincikin da taji ya bayyana har saman fuskarta,tadan
danne tana hada rai
"Garin yaya?.....har yanzu halinka dinnan bai canza ba?" Ta watsa masa tambayar . Karon farko kenan da
magana kwatankwacin wannan ta taba hadasu,don haka ya rasa ma da abinda zai bata amsa illa cewa da
yayi
"Lokacin lokaci na ne,yana kuma tafe" Ta bawa kanta da kanta amsa a zuciyarta,amma a fili sai tace
Duka hirar ba wani armashi gareta ba,amna haka suka sadaukar da lokacin har zuwa sanda ta
basu izinin tafiya sukayi mata sallama suna ficewa.
Suna tafe ne kawai suna dosar gidan,daga shi har musaddiq din ba wanda yace da dan uwansa
komai. Sai da sukazo mabanbantan qofofin sassansu,fu'ad din ya murza key yana bude qofarsa yace da
musaddiq
"Shigo ciki ka zauna muyi magana" Ba tare daya dubeshi ba,ya gama budewa ya shige musaddiq din yabi
bayanshi.
Zaune kawai tayi tana duban kwanukan abincinta da suka barta dashi,banda ruwan gorar
dukkaninsu ba abinda suka taba ko qanqani. Lemon data zuba ta turawa musaddiq din ma tana saka ran
zaiyi koda kurba daya ne amma baiyi din ba shima sai ya buge da shan ruwa. Ta fahimci yana bin sahu
tare da matuqar kwaikwayo ga fu'ad,iya wannan ya isa ya bata amsar cewa,muddin ta samu fu'ad ta
samu musaddiq......wanda kuma wannan din shine babban qalubalen da aikin data sake amanna ba
qarami bane.
Furzar da iska tayi me zafi daga bakin ta,kusan komai data tsara ya wargaje babu shi,dan abinda
ta amfana dashi daga zuwan nasu bai taka Kara ya karya ba.
Akwai damuwa sosai a ranta da take da buqatar abokin tattaunawa,don haka ta sauka daga
dining area din zuwa ainihin falon ta dauki wayarta ta lalubo hajja.
"Musaddiq" Ya kira sunanshi kai tsaye sanda yake zaune saman wata qawatacciyar kujera da irinta
qwaya daya ce tal cikin falon.
"Na'am" Ya amsa masa. Shuru kaman bazaiyi magana ba,sai kuma ya zauna sosai yana goye hannuwansa
a qirji
"Inaso ka zama me takatsantsan sosai......inaso kuma ka zama me kula.....bazan hanaka zuwa gidanmu
ba duk sanda kake da muradin hakan......amma kayi aiki da hankalinka da kyau......yanzun kai ba yaro
bane.....ba wannan musaddiq din da ko yaushe sai hammansa yana gefansa bane don ya kula da abinda
zai cutar dashi ko ya amfaneshi bane.....abubuwa sun yiwa hammansa yawa......kula da rayuwarsa yana
hannunsa".
Wadannan kalaman na hamman su suka dinga juyawa cikin kanshi. Duk da bai fito qarara ya
masa bayani a bayyane ba,amma kamar yadda yace din shi ba yaro bane yanzun,hakanan shi a karan
kansa hankalinsa ya fara dauko masa wasu abubuwan a iya zuwansu gidan yau kawai.
Haka kawai ya kasa bacci a daren,har yanzu musaddiq baisan ainihin wace maamah din ba. Iya
matakin da idanuwan basira da hankalin musaddiq kadai ya kaishi bai sadar dashi da ainihin wacece
maamah ba........meye zata iya yi?,da wanda ba zatayi ba.......dole koda a fakaice ne ya sake nesantashi
da tunkudeshi daga dukkan abinda yake ganin zai iya zama cikas a rayuwarsa.
Bugu biyu tak hajja ta dauka,hakan ya yiwa maamah dadi,sai ta miqe da wayar tana nufar
bedroom dinta
"Aah inadai shirin tashi.....labaran ne ya zaunar dani muna lissafin abinda kamfaninsa ya samu na
shekara". Ido maamah tadan fiddo cike da mamaki
"Kamfaninsa fa?,yanzu lissafin shima tare kukeyi?". Dan qaramin murmushi me sauti hajja ta fidda tana
aza hannunta saman kan budurwar dake kwance saman cinyarta tana amsa waya itama
"To meye a ciki?,nice uwarsa fa?,akwai wani abu da suka isa su boyemin?,koda cikin gidajensu akayi abu
koda da darene da safe kuwa rana bata bullowa bansan komai ba......ke banda ma ina taka birki ma wasu
abubuwan......ai hatta sunnar aure da matansu sai sanda na bada iznin a yita,kuma idan anyin sai an fada
min"
"Ke?.....zauna kina wasa da lamarin yaran yanzu,kina sake musu hanya sai linzaminsu ya koma hannun
matansu,keda wahalar raino da daukan ciki amma wata ita keda d'an,kin zama 'yar kallo,sai abinda tace
a tsakuro a sammiki.....tun daga kan yahaya na fara daukan izina.....ban kuma zauna ba har yau har
magajin gobe" .
Duka mamaki ya gama kashe maamah,amma kuma bayanan hajja din sai suka gamsar da ita,ta
kuma yarda cewa gaskiya ta fadi,gashi yanzun ita tana fafutukar karbar 'ya'yanta daga hannun wata ma
tun basuyi aure ba?.
"Yanzun ya ake ciki?,komai ya tafi dai dai ko?" Ajiyar zuciya maamah ta saki tana maida hankalinta ga
hajjan
"Hajja ba abinda sukaci fa?.....duk wahalar nan kin ganni da kayana suka barni....."
"Haka nake gayawa kaina......kana iya target din abu amma shekara goma gaba kake hangowa.....zamu
zuba dasu in sha Allah......wannan karon banga abinda ya isa ya hanani ko ya dakatar da burina ba" Ta
fadi har qasan zuciyarta tana jin confidence akan wannan.
"Sirrin samun nasararmu dama itace jajircewa naci da kafiya". Hajjan ta qara mata qwarin gwiwa.
Sun tattauna sosai har na kusan mintuna talatin kafin su yanke kiran. Hajjan ta sauke wayar wani
murmushi na fita daga fuskarta,tadan tsuke bakin ta lissafinta yana tafiya da nisa sosai.
"Mommy ga adeel zaku gaisa" Budurwar ta fadi tana daga kanta daga saman cinyarta hadi da miqa mata
wayar. Sai data kalleta sannan ta amsa wayar ta sanya a kunnenta.
Ba yabo ba fallasa ta amsa gaisuwar nashi,ba jimawa sukayi sallama ta miqawa yarinyar wayar
tana kallonta. Kallon hajja kawai a garesu yana da fassarori,don haka tayi masa sallama ta katse wayar ta
ajiyeta a gefe tana kallon hajjan
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 66
Itama duban momyn nata take yi,ta sani tabbas momy din nata tana matuqar ji da ita.....kaman
yadda ta sani taci buri sosai a kanta. Duk da hakan tana da buqatar qarin haske a maganarta,don haka ta
motsa kadan
"Momy.....wanne irin buri ne?,ta yaya zan iya sallamar dukkan kuma wadanda muke tare dasu yanzu?"
"Bance ki sallamesu yanzu ba,tukunna dai.....amma dai abune da kika sani cewa.....ke din ba kalar
qananun maza bace....ban haifeki don wani me jaririn arziqi a hannunsa ya aureki ba.....plan dina kuma
idan lokaci yayi zakiji....don ku yaran yanzu kwata kwata bakusan me ake nufi da sirri ba".
*****Ta jima zaune gefan gadonta tana juya wayarta a hannu. Mikail takeson kira,ta kuma shirya
haduwarsu kaman yadda ta tsara zata kammala da babinsa ta kuma rufeshi kwata kwata cikin
shafukanta kamar yadda ta binne maza masu yawan gaske. To amma haka kawai duk sanda tayi
attempting na kiran nashi sai taji kaman kada ta kira din.
"Ya cancanci ya fuskanci komai......ya kuma cancanci kowanne irin hukunci,jin kunyar mara kunya asara
ce!" Ta sake jin wani sauti daga can qasan zuciyarta yana rada mata maganar har zuwa kunnuwanta.
Danna kiran tayi,ta kuma tattara dukka nutsuwarta akan wayar tana sauraren yadda Kiran ke
tafiya kai tsaye zuwa layin mika'il din.
A kasalance yake shiryawa,kasancewar daren jiya ya shawu. Duk da ya tsagaita shan ma,bai wani
sha yadda yakeso ba,saboda ya sani safiyar yau din litinin tana cikin ranaku masu muhimmanci da zai
gana kai tsaye da CEO. Mutum na farko kaf rayuwarshi dake masa wani irin kwarjini,kwarjinin daya
tabbatar yana da alaqa da kamewarsa......da yadda fara'a ko murmushi sukayi nesa da fuska dama
rayuwarsa gaba daya.
Ya jima yana so ya shiga rayuwarsa fiye da matsayinsa,amma kuma ya gaza samun wannan fuskar.
Mutum ne da idan ya zauna aiki kawai,baya daukan wata magana da ba cikin aiki take ba,kamar yadda
baya daukan wasa ko kuma wargi.
Yadda dukkan ma'aikatan dake aiki qarqashin kamfanin suke da iyakoki......haka nan dukkan wata
magana da zaiyi dakai akwai iya adadin lokacin da yake baka.
Qarar wayarsa ta ja hankalinsa sanda take saka links na rigarsa,sai ya dakata cak daga abinda
yakeyi din cikin tsananin mamaki yana kallon wayar.
"What a wonderful day" Ya fada qasa qasa yana daukan wayar ya zauna gefan kujera. Wani mamakin
yana sake kasheshi da idanunsa suka tabbatar masa eh itace take kiransa
"Yau kuma da kanta?,da wanne irin sa'a na tashi?" Ya yiwa kansa tambayar yana daga kiran ba tare daya
tsawaita dogon tunani ba.
Kamar kowanne lokaci tayi masa sallama wadda shikam ba kasafai yake iya tunawa da ita ba. Sai
yadan daburce kadan kafin ya amsa sallamar ya dora da fadin
"Good morning queen....nayi kira nayi kira har na gaji anqi a dagamin waya.... Kwatsam sai gashi na
tsinci wani abu da ban taba kawowa zai faru ba".
Murmushi ta saki kadan wanda ko kusa da gefen zuciyarta bai kai ba,yayin da shi kuma
kunnuwansa yaji kaman zasu narke da fitar sautin sassanyan murmushin nata. Kowanne tsiga na jikinsa
sai ta shiga tashi
"Da gaske!" Ya fada da wani irin murna daya kasa boyuwa yana fidda idanunsa waje
"Kamar?" Ta jefa masa tambayar da zazzaqar muryartan nan,don wajen da takeso azo kenan tana
tunanin kuma ana gab da zuwa din,saidai ita ba zata iya requesting ba har sai ya nema da kanshi
"Mu hadu yau.......don Allah kada kicemin aah". Shuru tayi cikin salon jan aji,kaman bataso
"Please mana.....please,kice to" Ya fadi murya a raunane cike da fatan samun amincewarta
"Shikenan"
"Oh god......" Ya sake fadi yana dukan kujera da hannunsa,yana kuma ji duk duniya ba wani d'a namiji da
yakaishi sa'a yau dai a duniya. Yana nashi bidirin amma nata qasan zuciyar a quntace. Wani mugun
tsanarshi take ji da haushinsa. Da gaske wannan din dabi'arsa ce bazai kuma taba canzawa ba,ko shin
mata nawa ya lalata da kalar wannan mummunar dabi'ar tasa?.
"Bansan da wanne irin yare zan gode miki ba....amma zakiga godiya a aikace har saikin rasa da meye zaki
maye min gurbin hidimata a gareki......tabbas zan ninka darajarki.....zan daukaka martabarki a idanun
duniya......zan maidake tauraruwa cikin mata....zan miki ado da gold irin adon da sai 'yar gata...."
"Thank you......thanks" Kawai tace dashi don tanaso ya dakata daga zubo wannan dogon sharhin nasa.
Tana tausaya masa a daren yau irin barnar da zatayi masa,ta tabbatar wadannan maganganun da yake
jerowa a yanzu saisun koma sumbatu.
"Zan shiga company akwai lissafin da zamuyi da boss dina.....duk inda la'asar yayi koda bamu gama ba
zan dauki excuse......zan kama mana daki a Bristol,zan tura miki details da komai da komai".
Baki ta tabe tana jin wani haushi yana cikata. A daren yau bashi ba,hatta da boss din nasa saita
sakasu a lissafin da babu fita. Tanaji a jikinsa ma shi da boss din basa zaiyi wahala idan ba zamuje ta
tadda muje mu ba. A yadda yakan bata labarinsa lokaci bayan lokaci......irin kudaden da yake wasa dasu
da kuma shekarunsa talatin da bakwai a duniya amma ace ba macen aure?,to idan ba sheqe ayarsa
yakeyi ba me yakeyi kenan?.
Ture wannan tunanin tayi daga zuciyarta don a halin yanzu bashi da amfani,abu guda daya ta sani
ba sassauci,kuma a yau din takeso mika'il ya zama tarihi cikin rayuwarta,shi kuma ta bashi darasin da zai
sanya rayuwarsa tayi laushi da kyau.
"Ina fata kasan rule din.....zaka rigani isa gurin da wasu mintuna......kuma bana buqatar kowa yasan
muna tare ne da kai"
"Dukka dokoki da qa'idojinki kisa a ranki an gamasu......ranki ya dade.....da zaki bani dama da kin fadi
inda zan aiko driver ya daukomin ke.....don bana buqatar kiyi wahala" . Wani sirrintaccen murmushi ta
saki
"Na maka uzuri saboda baka jima cikin rayuwata ba bare ka fahimci wacece ni......zanzo da kaina,bana
buqatar kowanne driver"
"As you wish.....saidai zan saka kudin transportation.......please karkice min aah" Idanunta ta lumshe
sannan ta budesu,har ta fara gajiya da dogon hirarsa
Ajiyeta tayi gefe tana furzar da iska daga bakinta. Inda ace dukka haka mazan aure suke ba shakka
a jiya da kunnuwanta basu jiye mata abinda taji ba saman dogon layin masu lalurar ciwon zuciya dake
dakon ganin likita......tabbas da idanunta basu gane matan auren da hawan jinin bacin rai da baqincikin
d'a namiji ya jefa musu hawan jinin daya juye musu zuwa ciwon zuciya ba......da bataga matar data
yanke jiki a wajen ta fadi ba......wadda daga qarshenta gawarta aka fitar a asibitin 'yaruwata na kuka
dukka sanadin baqinciki namiji.
Ita kuwa me zatayi da aure?......wanne tsautsayi ne zai kaita damqa rayuwarta hannun d'a namiji
guda daya yayita hajijiya da rayuwarta ba gaira ba dalili?.
Abubuwan data gani din dasu ta kwana,su suka yita yiwa kunnuwa da idanuwanta gizo,kuma suka
hanata komawa duba ayshatu.....suka kuma sanyata jin ta matsu ta kora mika'il mashkur harma da
ya'aqoub din daga rayuwarta gaba daya.
Kafin tabar wajen taji alamun shigowar saqo. Koda ta duba alert ne daga banki da sunan mika'il
wanda ya sanya mata 1mil a matsayin kudin mota kawai. Ta juya wayar a hannunta,ta sake juyata,sai
kuma ta saki siririn tsaki tana ajeta a gefe.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 67
Kamar kowanne lokaci,yakanyi breakfast dinsa ne a sassansa,saboda duk wani abu da zaiyi
breakfast dashi yasha banban da cimar mutanen gidan. Wannan ya sanya ya aje cook dinsa daban
wanda yasan tsare tsare na cimarsa. Koda a ranar baida ra'ayin cin abincin cikin gidan,nashi cook din zai
masa irin abincin da yayi dai dai da ra'ayinsa,zai shiga ne kawai ya taya anni zaman cin abincin.
Yau din ranar litinin ne daya tsara abubuwa da yawa da zaiyin. Bakwai da mituna goma sha shida
ya murza handle na bedroom dinsa ya soma takowa a nutse zuwa ainihin parlor dinsa.
Yayi wani sassanyan kyau cikin tsadajjen yadin Qiviut fabric me tsananin taushi da kuma rashin
nauyi,daya daga cikin favourite yadiddikansa duk da tsadar da suke dashi amma baya jin wannan. Metro
blue ne da yayi matuqar haska fatarshi,ya kuma fidda sura haiba da cikar kamalarshi.
Fuskan nan a dinke kaman ko yaushe,wanda kusan duka safiya anni ko abba ne ke jefa murmushi
a kanta,sai kuma fitinannenshi farouq musamman idan a sassan ya kwana,to fa kafin su rabu kowa ya
wuce wajen aikinsa sai ya addabeshi har ya zare wannan yanayin daga kan fuskarsa din..
Yau din budadden takalmi ya sanya,abinda ya bawa zara zaran yatsunsa daman fitowa kenan cif
da cif cikin takalmin da ya soma zareshi daga qafansa sanda ya iso dining area dinsa.
"Good morning sir" Cook din nasa daya kasance yaren igala ya furta cikin girmamawa yana rusunawa
"Fine sir...." Ya amsa masa yana matsowa da sauri gami da kama aikinsa na serving nasa komai. Wannan
kuma shine ya bashi daman duba wayarsa da yaji tana vibration,wanda kusan koda yaushe idan zai
kwanta bacci yana barinta ne a hakan gudun takura.
Sunan daya gani ya sakashi dan furzar da iska kadan daga bakinsa. Duk da cewa a yadda suka
rabu jiya bayajin yau zata kira ta assasa wata matsalar ko damuwar,shidai baisan me yasa duk sanda
zaiga kiranta hakanan ba sai wani abu ya tsirga masa ba.
Daidai sanda Ameh yake barin gurin ya daga wayar,ya ajeta daga gefansa bayan ya sakata a
handsfree yana jawo mug din da ya zuba masa dafaffiyar madarar da aka watsa mata turmeric guda
guda,wannan yadan sauya mata kala zuwa yellow kadan.
"Barka da asuba" Ya fadi cikin nutsuwar nan tasa. Murmushi ta saki daga daya sashen,cikin son nuna
zallar kulawa tace masa
"Barka kadai.....kira nayi naji lafiyar d'ana ya ya tashi?,na kira dan uwanka wayarshi a kashe,ina fatan
komai lafiya?" Kaman ko yaushe,duk wani motsi nata yana masa banbarakwai,yanzun ma haka ne,sai ya
aje mug din yana hade hannayensa waje daya
"Mun tashi lpy alhmdlh.....da fatan kema haka......musaddiq ban fita cikin gidan ba tukunna,bamu hadu
dashi ba". Fuska tadan yamutse,amma bata bari sautin muryarta ya canza ba
"To yayi ba damuwa.....amma ya kamata dai ace kasan kwananshi da tashinsa......banason yadda kuke
nesa nesa da juna fa?".
Sai yaji maganar kamar ta saukar da murmushi cikin zuciyarsa,murmushin dake nannade da
mamaki,amma sai ya basar
"Ina tare dake maamah" Ya amsa mata tana duba agogon hannunsa da kuma qaramar wayar dake ajiye
a gefe,wanda kiran saddiq yake shigowa
"Cewa nayi bari nayi muku tuni,dinner by 8pm yau......ina fatan zaku cikamin burina na kasancewa tare
daku duk dare?". Idanunsa ya sake lumshewa,tsananin rashin gamsuwa da tsarij yana tsarga masa. Da
can da waye da waye taci gaba da kasancewa duk daren a sanda ta tattarasu ta baiwa duniya
kyautarsu?. Bayajin a stage din da ake kai yanzun zai yarda da ita ko ya gasgatata. Furucinta da kuma
alaqarta da hajja harira ba zasu taba barin zuciyarsa ta nutsu da ita ba
"To yayi na gode.....sai na ganku" Ta fadi tana yanke kiran. Wayar yabi da kallo,har tayi maganar da tafi
damunta,ta fadi kuma dalilin da ya sanya ta kirashi suka kammala wayar baiji addu'a guda daya daga
bakinta ba.
Yaja numfashi me nauyi yakaishi xuwa cikinsa,ya tabbatar babu yadda za'ayi anni ta
kirashi......walau yana qasar nan ko yana wata qasa su kammala maganar su bata bishi da kyawawan
addu'o'in da ko yaushe yake jinsu har cikin tsakiyar zuciyarsa ba. Addu'a da tsaftaccen niyya da kuma
manufa na alkhairi.
Hasken wayar ya sanyashi maida dubansa gareta,sai ya daga itama ya sakata a handsfree yana
sake janyo mug dinsa yaci gaba da kurba
"Gani nan......Moses ya qaraso?" Ya tambayeshi yana bude daya plate din dake gabansa
"Okay.....get ready" Ya fada yana katse kiran tun kafin saddiq din ya katse nasa.
Kamar kowacce safiya,ya shiga wajen annin cikin nutsuwa mutuntawa da kuma qaunar daya
tabbatar daga ubangiji take....irin qaunar da yayi imanin Allah ne ke sanyata cikin zukatan bayinsa aduk
sanda yakeso. Ta gyara lullubin laffayarta tana masa addu'a,addu'ar data sanya rauni me yawa a
zuciyarsa,raunin da yaso nunawa har sanda yake cikin motar da dagashi sai saddiq sai driver,sauran
guards suna gabansa wasu a bayansa cikin wata motar ta daban.
Wacce irin rayuwa ce hakan wai?,wanda zai hafoka daban?,wanda zai gina maka rayuwa da
kyakkyawan fata da kuma addu'o'i daban?. Wannan shine abinda ya dinga yi masa yawo akai,har daga
qarshe ya samu ya yakice komai a ransa kafin su isa kamfanin.
Kamar kowanne lokaci isowarsa cikin kamfanin kadai yakan sanya kowa shiga hankalinsa. Hakan
kuma yana da nasaba da rashin daukan wasansa da yadda yake daukan komai da muhimmanci. Wannan
ya sanya duk wanda ke aiki dashi yake shiga taitayinsa yake ajiye komai a gefe sai idan ka fita wajen
kamfanin.
Babban office ne dake dauke da kusan sashe biyu a cikinsa,wanda kusan kowanne sashe zaman
kansa yakeyi. An qawatashi cikin tsari da nau'in kalolin da yafiso ya kuma fi ta'ammali dasu. Komai cikin
tsari yake da tsananin tsafta tamkar wankewa da gyarawa kawai akeyi ba tare da ana shiga ba.
Yadda mamallakin office din ya zama na daban,haka office din nasa ya zama na musamman.
Hularsa ya zare ya ajiye su saman mulmulallen table din yana hadawa da wayoyinsa da system
dinsa daya karba daga hannun ahmad,wanda shike jigilarsa tun daga sanda zai shigo kamfanin har ya
fita.
Idanunsa na ga wasu files daya tarar saman table din,amma kunnuwansa na sauraren bayanin
taheer.
"Ina mika'il?" Yayi tambayar hankali kwance yana daga wasu takardu dake gefe
"Bai qaraso ba tukunna" Saddiq dake qoqarin kashe tab din hannunsa ya bawa fu'ad amsa.
"Alright.....trading manager da laboratory technician.....su da sauran staffs dake qasansu dukka ka shirya
mana meeting.....one hour thirty minutes kawai,akwai meeting da zanyi da sababbin ma'aikatan da
muka dauka kafin nayi wannan tafiyar"
Daya bayan daya yake duba duka aikin daya bari da wanda suke zaman jiransa. Wadanda yake
buqatar qarin haske ya turawa saddiq komai ta email nashi,don shine yake da alhakin kula da komai
daya shafeshi,kaman yadda komai din sai ya biyo ta hannun saddiq din kafin ya iso gareshi.
Duk da cewa yasan shi din mutum ne da baya saba lokaci ko karya magana,amma hakanan ya
samu kansa da duba agogonsa.
Yau din gaba daya hankalinsa baya a jikinsa,yana jin cewa yau zata kasance babbar rana a gareshi
wadda zata kafa tarihi cikin rayuwarsa da kyakkyawar yarinyar da ya tabbatar koda cikin bariki samun
irinta abune me wahala.
Duk da 'yar hira da tattaunawa dake gudana tsakanin ma'aikatan hankalinsa shi ba'a wajen yake
ba yayi nisa wajen wassafa yadda zai rayu da ita,yayi nisa wajen tsara yadda zai more rayuwarta da
kyau.....ya kuma yi nisa wajen tsara yadda zai jiqata da kudi.....yadda zai sake maidata tauraruwa.....da
kuma yadda zai maisheta abar kallo.
Muddin ya sameta yayi imanin zaiyi zarra cikin duniyar bariki,zai kuma tayar da hankulan abokan
adawa da yawa,hakanan zai zama wani na daban daya mallaki babe din da baijin akwai sauran irinta.
Miqewar da ma'aikatan sukayi daga saman kujerun zamansu dake zagaye da kyakkyawan table ya
sanyashi dawowa hayyacinsa. Miqewa ce taban girma ga CEO din nasu,wanda yake takowa cikin hall din
cike da takunsa dake sake nuna zallar kamala da nutsuwar da Allah S W T ya hore masa.
Lafiyayyen kwarjinin nasa dake sake saka kowa shiga taitayinsa yana kwance saman fuskarsa.
Basu zauna ba har sai daya basu izinin zama sannan shma ya zauna din.
Yadda suka saba gabatar da meeting irin wannan haka suka fara yanzun ma. Mataki bayan
mataki,matsayi bayan matsayi. Yana biye da bayanan kowa ta sigar da idan ka kalleshi a haka zata
tsammaci kaman baya fahimtar bayanan,don babu system ko abun rubutu ko daya a hannunsa,illama
yatsun hannunsa daya sarqe cikin juna yana kallon duk wanda bayani yazo kansa.
A gaban mika'il din akwai mutane da sai sun kammala miqa nasu bayanan kafin azo kanshi. Duk sai
yaji ya matsu,tamkar ya nemi a daga masa qafa tukunna ya fara gabatar da nasa bayanan. To amma ko
giyar wake yasha yasan hakan bame yuwuwa bane,don waje ne da ba'a daukan irin wannan wargin.
"Ina neman afuwa,lokacin da na tsara zamu zauna din ina ganin kamar sai mun wuceshi.....zamu sake
qara awa daya zuwa biyu......akwai me wani uzuri kaman na abinci?,shiga bayan gida da sauransu?". Yayi
maganar cikin harshen turanci da wani irin daddadan accent,karyewa da lanqwashewar halshensa kawai
ya isa ya gaya maka gwani ne wajen iya yaren.
Cikin rashin jin dadi mika'il din ke rarraba dubansa akan fuskokin staff's din,yana cike da fata da
burin samun wanda zaice yana da uzuri shima ya zama na biyu da zai furta haka. Saidai kaman yadda
zuciyarsa ke raya masa ba wanda ya nemi wannan excuse din,hasalima daya daga cikinsu cewa yayi
"Koda duka awanninmu na yau zaka qarar sir mun sadaukar maka dasu" Sauran suka shiga gyada kai.
Kowannensu da wani irin qawa zuci da qauna ta gaske yake zaune dashi,duk da ba'a rasa qananu
matsaloli da kowacce tafiya bata rabo dashi,amma ya gina wani irin qaunarshi a zukatansu da
sadaukarwa me tarin gaske,wanda shi kansa baisan ya gina din ba. Saidai kuma abune sananne,duk
wajen da ake samun kulawa tausayi da kyautatawa dole qauna ta biyo baya. Fada ce ta ma'aiki,an gina
zukata abisa son wanda ke kyautata musu da qin wanda ke munana musu.
"Alright.....na gode" Ya fada da salon daya sake sanyawa kowa nutsuwa da qaunarsa a zuciya.
Boyayyar ajiyar zuciya mika'il din ya saki,gumi yana fara tsatsatsafo masa. Yafi kowa son samun
kusanci da jadda......yafi kowa son ganin yafi kusancin dashi,yanaso yafi kowa samun fada da dama,don
haka shi yafi cancanta ya nuna zallar biyayyarsa ga boss din ba wasu ba,don haka ya saki wani murmushi
"As you wish sir.....mu duka muna qarqashin cewarka ne". Kadan fuad ya waiwaya ya kalleshi,sai ya
gyada masa kai ba tare da yace komai ba.
Gyara zamansa yayi saman kujerar kamar tana mintsininsa ne,yana jin kamar babbar asara tana
shirin samunsa ne,kaman zai rasa wannan babbar damar ne a yau,wadda muddin ya rasata din baisan
ranar da zai sake samunta ba. Sake danna wayarsa yayi ta kawo haske,lokacin da suka tsara zasu hadun
yana dab da cika.
Wajen SMS ya shiga,ya rubuta gajeran saqo ya tura mata,idanunsa suna kan wayar yana fatan
samun amsa daga wajenta,duk da kuwa yasan abune me wahalan gaske.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 68
Tunda suka dawo daga makarantar hankalinta yana kan wayar,dama kawai take nema da sabreen
din zata fita ta samu ta fidda wayar. Ta tabbatar yayi kiranta har ya gaji,yanzun haka qila yana cike ne da
kewarta.
Sunyi hira me tsaho dashi jiya cikin toilet,wanda ta dinga mamakin yadda yasan wasu abubuwan a
kansu,saidai amsar daya bata ta cire dukkan wani zargi nasa daga ranta
"Indai zakiyi mamakin yadda akayi nasan rayuwarki huda ashe son da nake miki ma baikai nan ba......kina
wasa da kalar soyayyar da nakeyi miki ko?" Idanunta ta lumshe har cikin zuciyarta tana jin a yau din
bayan yaa sabreen din ta sake samun wani barin zuciyar wanda ya damu da rayuwarta ya kuma damu da
damuwarta. Har yake iya sanin wacece ita a rayuwa ba tare data sani ba saboda tsananin son da yake
mata
"Inason na daukeki daga gidanku huda.....na killaceki daga rayuwar da kike ciki......na hana kunnuwa da
idanuwanki ji ko ganin duk wani mummunar kalma duk don saboda yaa sabreen....". Ta riga tayi amanna
yasan komai kawai a kansu har akan sabreen din,don haka sai ta lumshe ido zuciyarta tana karyewa
"Ba rayuwar da tafi rayuwar aure daraja da martaba a wajen mace.....qila idan yaa sabreen dinki taga
zakiyi aure itama tayi" Ya fada cikin salon karya harshe dason nuna yadda zuciya ta karye,saidai a gefe
guda yana sone kawai ya cusa wani kakkaifan abu a zuciyarta.
"Banji dadin shaidar dana ji daga bakunan mutane a kanta ba.....don nima a yanzun ina daukarta kamar
yaya take a gareni".
"Muyi kowacce magana dakai amma banda ta yaa sabreen,don zuciyata me rauni ce a kanta,ita din
komai namu ce....."
"I know huda.....i know,but inason na killaceki huda na daukaka darajarki.....inason ta silarki ya sabreen
dinki ta zauna waje daya,ta samu martaba irinta....." Sai kuma yayi shuru bai qarasa ba,shurun da itama
hudan da zuciyarta ke mata zugi ta zabi yinsa.
"Zamuyi waya anjima idan kin samu lokaci.....i so much love you....please take care" Ya fadi yana katse
kiran ya barta da yawa a hannu.
Zare wayar tayi daga kunnenta jikinta yana yin sanyi. Kenan kowa ma yana dora tuhuma akan yaa
sabreen?,kowa ma yana da zargi a kanta?. Idan dai har Hameed da yake baqo a unguwar dama
rayuwarsu gaba daya zai iya samun wani abu a kanta to ya kenan sauran jama'a suke kallonta?.
Shin gaskiya Hameed yake fadi?,tayi aurenta kawai ko hankalin yaa sabreen dinta zai dawo
daidai?. To shin me yasa yaa sabreen din ba zata zauna kaman kowacce mace ba?. Me yasa bayan ta
samu kudaden da sun isa ta riqe musu rayuwa?.....me yasa ba zata haqura ba?....me yasa?,meye
dalilinta?,idan a baya tana da hujja tana da dalili yanzun meye dalilinta?.
Wadannan tarin tambayoyin su suka dinga yi mata kai kawo,sannu a hankali sai taji kaman tana da
ja akan sabreen din,tana kuma qalubalantarta duk da harshe ko aikinta bai nuna ba....... Amma tun daga
sannan can qasan zuciyarta wutar hakan tana ruruwa sannu a hankali.
Kamar wadda ke ciwon jiki haka ta dinga aiwatar da komai. Duk da tana da daukan lokaci wajen
wanka da shirinta amma a yau din sai abun ya sake ninkuwa.
Ta gyare gashinta ta kuma dameshi cikin band madaidaici,ta gama shafa cream dinta na
musamman dake qarawa fatarta glowing cikin kowanne yanayi,amma kuma saita kasa ci gaba da yin
komai.
Bata taba ayyukan da suka tsaye mata a rai takejin ta takura ba irin aikin Mikhail dana mashkur
da cikin qarshen satin nan zata yishi. Batasan dalili ba......amma ta alaqanta hakan da canzawar salon
aikin. Ma'ana kowannensu zata kasance dashi cikin dakin hotel daga awa daya har zuwa sanda aikin zai
kammala. Shin tana da tabbacin kubuta daga hannun miyagun kurayen da dama dama suke nema irin
wannan?,mutanen da suke kallon diya mace cikin idanuwansu da wani irin duba kwatankwacin duban da
mayunwacin zaki kewa nama a yayin da sukayi arangama?.
Tana zaunen amma tana lura da yawan shige da ficen da huda keyi tsakanin falon zuwa dakinsu.
Kaman zatayi mata magana sai kuma ta basar,don tana da wani irin dabi'a nabin komai da idanu har sai
sanda ta samu cikakken hujja ko makama a kanshi.
Qarar yar siririyar wayar da tasan kiranta na dabanne shine ya dauki hankalinta. Wanda ta zata
din shine kuwa,Jib ne,sai ta daga kiran tana rage volume na kiran.
"Hello jib?" Ta furta daidai sanda huda ke ficewa a dakin. Samun kanta tayi da jan qaramin tsaki can
qasan ranta. Jib?....ko waye kuma da wannan sunan?,zai iya yiwuwa wannan shirin da takeyi ma fita
zatayi,kuma wajensa zata je,idan mace da namiji suka kebanta a waje daya kuma me zai biyo baya?,idan
taje gurinsa me zasu aikata?..... Tambayar data yiwa kanta kenan ta qarshe data sanya bugun zuciyarta
qaruwa,saita samu kanta tana saurin dakatar da kanta daga wannan tunanin tana furta
"Yaa sabreen ce fa?" Idanunta ta lumshe tana son sake jaddadawa kanta eh.....ya sabreen ce,amma wani
sashen kuma yana qoqarin maidata baya.
"Yadda kika tsara abun bazai yiwu ba sister.....dole ya kasance kuna tare nan da awa guda......mafi kyau
kuma ku isa wajen tare koda xaku shiga ta qofa daban dabanne......don na bincika a yanzun kamar suna
dakin meeting da boss dinsu..... Meeting din kuma zai zamana sun tattauna muhimman abubuwa.....na
lissafa zasu soma lissafi na kudaden da company ke dashi a qasa......zasuyi musayar documents da
bayanai,zaa tashi ba tare da sun kammala ba don bayanan yana da yawa,kuma owner na kamfanin jadda
baya saba lokaci......wadannan bayanan da zasu kasance tare dashi ina da buqatar wasu abubuwa a ciki
da zasu sauqaqamin kutsa kai cikin account din muyi aikinmu da wurwuri mu gama.......inaso kuma aikin
na gamashi ne a daidai lokacin da masu kula da komai nasu suka tafi hutun fitowa daga meeting
din....idan zaiyiwu ki samu kaiwa office dinsa,akwai wani ajiyayyen code cikin files na office din da zaki
ciromin,kin fahimta?"
Dukkanin bayanan sa ta fahimta ta kuma gamsu,to amma kimarta fa?. Bata saba yin magana ta
dawo ta warware ta ba
"Kada kiyi tunanin komai.....wannan ce rana ta qarshe tsakaninki dashi.....kuma wadannan sune awannin
qarshe da aishatu keda chance na tsallakewa siradinta".
Wayar ta aje a gabanta kawai tana kallonta tare da tunanin da yadda zata sake requesting wa
mika'il din su kasance tare tun yanzu?. Kaman ana jira ta yiwa kanta tambayar saiga shigowar saqonsa.
Tana duba saqon tana jin sanyi da yadda komai yazo mata a sauqaqe. Duk da hakan ya faranta
mata amma saita ajiye wayar bayan ta gama dubawa,ta miqe kawai ta isa wardrobe dinta tana laluben
suturar da zata dace da jikinta da kuma yanayin.
Shurun nata da rashin samun amsarta ya qara masa yawan rashin sukuni. Ya dinga duba wayarsa
duk bayan wucewar wasu mintuna,har sai daya kasa jurewa ya sake tafa massage dij har sau biyu ya tura
mata a jere.
Saqon ya shigo mata sanda take daura agogon hannunta ne,tun taga sunan tasan shine,bata bi
takai ba sai data gama daurawar,ya qara barima a kunnenta tayi Rolling mayafin Turkish dress din,ta
kuma jawo kimono din kayan da suke zuwa tare da shirt me dogon hannu da skirt din ta aza saman
kayan sannan ta dauki wayar ta bude tana maida masa amsa
Sai data maimaita karanta saqon kusan sau hudu,tana mamakin yau itace da kanta zata turawa
wani d'a namiji saqo da yayi kama da wannan?. Ji tayi kaman ba zata iya turawar ba,ta aje wayar saman
madubi tana furzar da iska daga bakinta
"No way out" Taji zuciyarta na gaya mata,dole ta tura muddin tanason cika mission din. Tana so ta rabu
ne da mikail.....ba kuma zata iya barinsa salin alin ya wuce hakanan ba,sai ta miqa hannunta ta sake
bude wayar,ta danna send sannan ta maida wayar ta ajiye.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 69
Bayan maimaita karanta saqon da yayi,har sai data kaishi ga murza idanun nasa don ya tabbatar
daidai ya gani ko kuwa akasin hakan?.
Jikinsa har rawa yake wajen maida mata reply,har bai lura da yadda Muhammed jadda ya zuba
masa idanu ba yana karantar yanayinsa.
"Mr mika'il" Ya kirayi sunansa da husky voice dinsan nan dake ratsa zukata su kuma maida hankalin
mutum zuwa jikinsa.
"Yes.....yes sir" Ya fada adan daburce yana qoqarin tattara masa nutsuwarsa bayan ya tabbatar da isar
saqon zuwa wayarta. Bawai address kawai ba,harda code da zata samu zarafin bude office dinsa ta shiga
ta zauna tayi tsimayensa.
Murmushine ya subuce mata da ganin yadda ya bata komai in details. Ba wani shakka ko
kokwanto. Wato shi namijin bariki akan mace susutacce ne?.....sannan fiye da rabin maza ta fuskanci ba
kasafai suke iya mallakar kansu ba idan batu ake na mace. Wani zaka hangi fuskarsa cike da kamala
amma muddin aka raba masa mace a nan dukka rauninsa yake bayyana. Bai tsoro shakka ko kwanton ita
din fa baquwa ce cikin rayuwarsa gaba daya?.
"Good job mika'il" Ta fadi murya can qasa tana forwarding ma JIB komai.
"Kana tare damu?" Muhammad jadda ya sake jefa masa tambayar yana dage girarsa dukka biyun
"Yes.....yes sir" Ya fadi yana sakar masa murmushi don ya amintar dashi. Idanu yadan tsareshi dashi
kaman meson karantar wani abu,wanda duka duka cikin mintuna biyar ya dauke idanun yana cewa
"Bismillah" Tare da maida idon nasa saman farar takardar gabansa da daya daga cikin ma'aikatan ya
gabatar.
Sai da yayi namijin qoqarin daidaita nutsuwarsa sannan ya fara gabatar masa da komai daki daki.
Sai data buda qaramar handbag dinta ta tabbatar ta sanya komai a ciki sannan ta fiddo dubu
biyu a ciki ta miqawa huda dake tsaye a gabanta
"Masu kamfanin pure water zasu kawo ruwa....ki basu wannan idan sun kawo.....naso saikun wuce
islamiyya kafin na fita.....amma it's urgent.....kiyi qoqari ku fita da wuri kada kuyi latti"
"A dawo lafiya" Ta fadi bayan ta karbi kudin. Qasan ranta fal farinciki,a yau din zatayi hira da hameed
yadda ranta keso,don zata saitawa su nadra hanya zuwa islamiyya ne ita kuma ta baje kolin soyayyarta
yadda ranta yakeso.
Gaban haneefa ta qarasa tana sakin murmushi,itama haneefa din murmushi ta saki,hannunta ta
dora saman sumarta data cirewa dankwali. A kullum fuskar haneefa ba wanda take tuna mata dashi sai
umminsu. Akwai shaquwa da sabo me tsanani tsakaninsu.......amma duk da haka saida mutuwa tayi
aikinta ta raba tsakaninsu.
"A dawo lafiya yaa sabreen........amma yau kam sabuwan teddy nakeso ki sayamin"
"Ke kuwa ki rasa abinda zaki zaba sai Teddy?" Nadra ta fada tana qyalqyala dariya
"To madam tsokana.....ba ruwanki" Sabreen tayi hanzarin katse nadra data wuce daki tana ci gaba da
dariyar tsokana din hadi da yiwa sabreen a dawo lafiya.
Tana takawa don fita daga layinsu ta isa bakin titi amma tunanin qannen nata ne a ranta. Batason
ko kadan yadda kullum sai ta fita ta barsu,wani lokaci su fita tare saidai su rufe dakin,harma wasu
lokutan su rigata dawowa. A yanzun huda tafi tsaye mata a rai,tunda har ta cika shekara sha biyar ta
shiga ta sha shida tana da buqatar sanya idanunta a kanta,don mataki ne da komai daga nan yake
farawa daga rayuwar yarinya. Duk da inda ace ita din me gata ce,ita dinma tana buqatar kulawa ne tare
da qarasa rainon tarbiyyarta.
Ko kusa ko alama bata lura dashi ba,don tayi nisa a tunaninta,sai muryarsa taji daga gefanta.
"Um uhmmm......sai ina kuma haka?" A nutse ta waiwaya tare da sake rage yanayin tafiyar tata tana
kallonshi.
Tsaf yake kallonta,ya turo hula gaban goshinsa yana mata wani irin kallo. Idanunta ta dauke don
bata buqatar yanayin kallon da yake binta dashi. Ta sani haushinta yakeji qwarai,tun waccar ranar data
hanashi kudi. Wannan duka ba damuwarta bane,don idan da sabo ta saba,sai ta watsar da wannan
batun kamar kullum tace dashi
"Ras na wuni.....ko kin dauka zan mutu ne saboda kin hanani kudinki?,to kisha kuruminki 'yar
nan......cikin satinnan da yardar me duka arziqi zai fashemin......sunana zai fantsama a duniyar masu
arziqi......daga sama'ila zan koma alhaji ismai'il sha maka Allahu". A mamakance take kallonsa,tadai sani
bashi da wata sana'a data wuce caca,kuma muddin ka jishi yana lissafin maquden kudade irin wannan to
wata caca za'a buga kuma yake sanya ran zai cinye.
"Akul naji bakinki.....dani dake ai dan juma ne da dan jummai... Ke har gwara ni duk tsiya".
Kanta ta dauke tana hadiye wani abu daya tsaya mata a wuya,bata sake tanka masa ba sai ta fara
takawa tana barin wajen. Har tayi taku hudu qwarara ya qwala mata kira da ainihin sunanta
"Aminatu" Dakatawa tayi don ba zata iya ci gaba da tafiya ba,ba'a canzawa tuwo suna,duk duniya kawu
sama'ila ubanta ne.
"Ke wato baki jin ko dar idan an miki gugar zana ko?,to miqomin wani abu nan,ki rubuta shi a lissafi duka
cikin satin nan zan biyaki" Ya fada yana miqa mata hannu tamkar ya bata ajiya. Idanu ta xuba masa,sai
kuma ta sanya hannu tana sauke jakarta daga kafada,ta zuge ta fidda dubu dubu guda hudu ta miqa
masa.
Karba yayi yana juyasu alamun a raine suke a wajensa,sai ya yatsina fuska
"Ki rasa abinda zaki ban sai wannan?,kai Allah ka dawo mana da arziqinmu za'a sha kallo wallahi......"
Daga haka ya juya yana cusasu a aljihu tare da barin gurin bai kuma sake bi takan inda zataje din ba.
Kasa ci gaba da tafiya tayi har sai daya bacewa ganinta,ta kada kai ta na yin gaba kamar kullum
zuciyar nan cike da nazarin rayuwa . Tun daga rasuwar mahaifinsu har ta mahaifiyarsu bai taba miqo
komai yace musu gashi ba wai don su rayu.....amma ita ba zata iya qirga ko lissafa adadin sau nawa ya
karba daga hannunta ba,kuma a raine,ba godi bare na gode.
Ya riga ya bata shaidan da zata nuna na cewa shi take nema,wannan ya sanya bata samu matsalar
shiga kamfanin ba tun daga gate din farko gate na biyu,ta zarce zuwa main entrance,ta ratsa reception
da sauran guraben da kamfanin yake dashi kai tsaye kuma ta isa ga office din.
Tayi amfani da code din ya kuma bude mata successful. Ta tura qofan a hankali kamar me tsoron
shiga qaramin murmushi na sauka saman fuskarta
"Quda a wajen kwadayi akan mutu" Ta furta qasa qasa tana sanya qafafunta cikin office din. Har ta fara
takawa sai kuma ta tsaya cak tana wurga idanunta sassa sassa na qawataccen office din da aka narka
kudi akayi masa wani irin lafiyayyen tsari me daukan hankali. Tabbas tasan babu yadda za'ayi guri irin
wannan ya rasa CCTV camera,indai kuma hakanne ta yaya zata iya gudanar da komai ba tare data samu
wata matsala ba?.
Dan wani abu cikin kunnenta ta matsa,muryar JIB ta bayyana,sai ta danja da baya kadan ta raba
qafa tsakanin office din da veranda din da jerin gwanon office din yake don bataso ta fito gaba daya ko
ta shiga gaba daya don kada camera din ya samu damar nunata
"Ni dakai duka bamuyi tunanin CCTV ba jib?".
"Haka ne......wasu lokuta dama kece ke mana hasshen irin wadannan abubuwan......ba matsala
bane,manyan kamfanoni irin wadannan akwai irin cameras din da suke amfani dasu,katseshi ba zaiyi
wahala ba nasan takan irinsu sosai......yanzu ki tsaya daga nan inda kike...kafin ki shiga ki gano mana
daga wanne saiti camera din yake shikenan kawai"
"Okay....."
"So kaji komai tsakaninmu kenan bayan sirri ne?" Ta fada cikin dan salon zolaya da wani lokaci takeyi
masa. Dariya ya qyalqyale da ita kadan yana fadin
"Tuba nake....Allah yabar soyayya". Sai kawai ta saki murmushi kadan tana tura qofar hadi da sake
qarewa office din kallon tsaf.
Cikin qasa da minti goma ta gano komai suka kuma katse sadarwa da tsaida aikin camera din. Da
dan hanzari ta ajjiye hand bag dinta. Tanaso tayi komai ne ta gama kada damar ta subuce mata yazo ya
shigo.
Sai data tattara dukka hankalinta da nutsuwarta ta karanci inda komai yake ajiye a office
din,gudun kada ta taba wani abu ta kasa maidashi daidai inda yake hakan ya nuna masa alamar tayi
masa bincike. Hatta da biro dake ajiye qwaya daya tal saman teburin sai data karanci a yadda yake ajiye
din,ta dauka ta kuma gwada maidawa ta tabbatar ya zauna kaman yadda aka ajiyeshi. Wayarta ta
fidda,ta sake yiwa office din qaramin video komai da komai sannan ta maida wayar jakar,ta kuma shiga
aikin bincika komai daki daki.
Baya ga abinda suke nema taga abubuwa da yawa cikin office din,irinsu condom dake nuna mata
lallai riqqaqqen dan bin mata ne,taaba irin masu tsadar nan da sauran abubuwan maye. Abinda ya sake
darsa mata mugun tsanarsa kenan,wutar kuma ta tabashin ta hanyar kwakwashe masa komai tana sake
ruruwa cikin ranta. Ya zama dole ta durqusar dashi,durqusarwar da bazai sake tashi ba.
Maida komai tayi kaman ba wani abu daya faru a office din,ta tattare duk abubuwan da take
nema din tayi musu ajiya ta musamman cikin jakarta. Hatta da wani qaramin ledar cake da akaci aka
barshi sai data tabbatar ta maidashi yadda yake,ta gyara rolling dinta da kyau tana sauke numfashin
samun nasarar kammala komai ba tare daya dawo ba.
Maqoshinta taji ya bushe tana da buqatar ruwa,sai ta taka tana nufar kyakkyawan fridge din dake
girke waje daya.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 70
Turus tayi tana kallon yadda aka maqare gidan farko na fridge din da wasu kalan kwalabe da bata
saba ganin irinsu ba. A hankali take dubasu har ta fahimci kwalaben na meye?.
"Innalillahi" Can qasan harshenta. Sai kuma taja jikinta baya a hankali tana matsawa daga jikin fridge din
don batajin zata iya shan wani abun sha daya fito daga fridge din komai halascinsa.
Zuciyarta ke qara bugawa da tsanarsa haushi da kuma takaici. Shikam mikail dame
zaiji?,abubuwan ai sunyi masa yawa,sun masa yawan da batasan wanne a ciki zai iya dauka ba. Kaman
ana son bata amsar tambayarta sai qofar tayi qaramar qara alamun ana budeta ne,ba jimawa ya
bayyana cikin office din yana dubanta da murmushi
"Am so sorry dear......ina fata banyi keeping naki da yawa ba......boss ne idan ya tashi aikinsa tamkar
engine.......baya gajiya,na samu na kubota da qyar".
Idanunta ta dauke daga kan files din da yake rungume dasu,wanda ta tabbatar a cikinsa sauran
bayanan da take nema suke. Ta kalato dukkan dauriyarta ta jefeshi da qaramin murmushi
"Wow......serious?" Ya fada da wani irin zumudi da zakwadi yana qarasowa gabanta dab da ita ya zauna
har yana neman hade gwiwoyinsu guri guda. A dabarance ta miqe da sauri,sai ya bita da kallo. Taji a
jikinta yana kallonta ne don haka ba tare data juyo ba tace
"Oh....okay to dear" Ya fada yana dora files din saman table din cikin ransa yana qissima yadda a yau din
zai gwangwaje,a yau din zai kashe duk wata qishirwa tasa dake damunshi a rai.....a yau zaiyi morewar da
bayajin ko daren amarcinsa zaiyi wannan.
Gaban madubij toilet din ta tsaya tana sauke numfashi idanunta akan fuskartata. Muryarta can
qasa tace
"I know.....zanyi iya qoqarina......amma please kada kice zakiyi halin hawainiyar nan taki" Dan murmushi
ta saki,yasan halinta sarai,koda nawa aikin zai basu idan ta motsa mata tana iya cancel dinsa
"Zanyi qoqarin nima" Ta amsa masa tana kunna famfo sai ta bige da daura alwala.
Mutum hudu ke biye dashi sanda yake takowa cikin veranda din idanunsa saman takardar dake
hannunsa yana sake karanta abinda take dauke dashi. Can qasan zuciyarsa akwai wani kokwanto da
mamaki,kusan zaman yau da suka fara yi da mikail wanda ba'a qarqareshi ba saboda quracewar lokaci ya
karanci kamar hankalinsa ba gurin yake ba sam sam. Yana karance da kuma bibiye da motsinsa. Duk
muhimmanci da girman takardar a wajen kamfanin gaba daya amma har ya iya mantota cikin dakin
taron,wannan ya sanya ya yanke biyoshi da kanshi ya kawo masa don ya sake alamta masa
muhimmancin takardar.
"Wait here" Ya fadi a nutse ga mutanen dake bayanshi yana sanya code na qofar office din Mikhail din ta
bude ya murza handle din yana turawa can qasan ransa yana jin kamar bai kamata yayi hakan ba ba tare
daya nema izinin shigar ba. Duk da kowanne office a qarqashinsa yake amma bai shiga office din
kowa,hakanan baya taba bada damar a bude maka office muddin baka nan,amma haka kawai yau din
yaji yayi hakan.
Sanda ya murda handle din yake shigowa da sallama cikin husky and deep voice nashin nan,dai
dai sannan itama ta bude qofar toilet din ta fito tana qoqarin maida rolling na mayafinta.
Idanunsa kan mikail daya miqe a rude cike da tsananin mamakin ganin boss din nasa yau da
kanshi a office dinsa gabansa yana faduwa,yayin da nata idanun suke kan fu'ad fuskar fu'ad din tana
dubansa qasan ranta tana jin kamar tasan wannan fuskar.
"Keep it......." Ya furta da wani irin yanayi idanunsa cikin tsakiyar qwayar idanun mikail wanda hakan
kadai ya isa ya gaya masa wani gargadi yake aika masa da kuma muhimmancin da takardar ke dashi
"In sha Allah sir" Ya amsa yana karbarta da hannu biyu. Juyawa yayi da zummar ficewa a office din,dai
dai sannan idonsa ya sauka a kanta. Idanunasu suka gauraya waje daya,sai tayi saurin zare dubanta daga
kan fuskar tashi gabanta yayi wani irin faduwar da batasan meye dalili ba.
Dan zuba mata ido yayi na sakanni tamkar zaiyi magana,sai kuma ya fasa,ya juya ya kalli mikail
sannan ya maida dubansa kanta sai kuma ya juya yana ficewa a nutse daga office din.
Wata wawiyar ajiyar zuciya ya sauke. Allah ya sanya ba zuwa yayi ya samesu cikin wani yanayi
ba da dukka sauran gaskiyarsa da yakeson tabbatarwa boos din a yau babu ita.
Yasan an jima ana kai masa tsegumin halinsa,amma kasancewar shi din ba mutum bane me
daukan qananun maganganu ya sanya abun bai wani tasiri ba.
A yadda yake jinsa a dan rude sai yaji yana buqatar giya don daidaita nutsuwarsa. Ya tafi zuwa
fridge din yana fadin
"Boss......bashi da sauqi kwata kwata,idan har wani kuskure ya faru tsaf zaka rasa aikinka,a wajensa
wannan din ba wani abu bane me wahala".
Batace dashi komai ba kaman yadda bata kula da abinda ya dauko yakw sha ba,ta qarasa wani
sashe na dakin ta tayar da sallah kawai don lokacinta ya shiga.
Tunda ta tayar da sallar har ta idar yaba zubawa cikinsa barasa. Sanda ta sallame din saita
kafeshi da idanu kawai. Ranta cike fal da mamakin yadda dan adam da hannunsa zai dinga durawa
cikinsa abinda yasan zai cutar dashi?.
Waiwayowa yayi sai suka hada ido. Ta hade fuska da kyau tana miqewa
"Banason wannan abar sam... Muddin kanason mu kasance tare kuwa saidai ka rabu da ita" Tayi
maganar duka tana jin wani iri har cikin ranta
"Am sorry dear.......indai wannna ne kada ki damu na ajiye".
Tana maida takalmin qafarta tana tunanin yadda zata samu ta duba takardar da boos din nasa ya
kawo masa yanzu?.
"Na tsani shaye shaye" Ta bashi amsa kai tsaye,amsar data sakashi sake zaro idanu
"Duk kyan nan naki babe?,kinsan yanzun macen bariki bata gama cika ba sai ta hada da cakewa?". Ido ta
dan rufe kadan tana budesu,kalmar MACEN BARIKI da yayi amfani da ita a kanta tana mata quna sosai
cikin rai
"Cikar wannan kyan naki babe ki dinga taba wani abun da zai sanya ki dinga jin kanki very high......Ni zan
dauki nauyin baki komai mai tsada wanda ba kowacce yarinya ce ta isa ta samesu ba......sai irinku matan
da kuke da gata a wajen partner dinsu......like kaman wannan giyar.....bata bugar dani,saidai nayi bacci
na awa daya shikenan idan na farka zan jini fresh......please ki koya sha ko kadanne akwai dadi,saikin
gwada zaki gayamin" Yayi maganar yana qoqarin sake zuba wata a cup da alama kuma ita yake da niyyar
baiwa idan ya zuba din.
Tsam ta miqe tana jawo jakarta dake a gefanta tana ratayawa
"Zan wuce gida" Da sauri ya diro daga saman kujerar da yake kai
"Haba babe.....me yayi zafi?,bayan baki cikan alqawari na ba......kinsan dakin nawa na kama mana a
Bristol kawai saboda yau?" Idanunta ta juya tana ajiye numfashi
"Banga alamun ka dauko wannan hanyar ba......kana yimin maganar abinda babu shi a tsarina.......baka
iya saukar baqo ba sam......na nema abun sha kana min sharhin da lokacinka yake ci maka......idan
lokacin dana diba ya cika zan tafi koda ba komai daka samu"
"Ba za'ayi haka ba" Ya fada da hautsine jin zaiyi asaran abinda ya qwallafa rai a kai,ya ajjiye komai na
hannunsa ciki harda takardar da yanzu yanzu aka jaddada masa muhimmancinta yayi hanyar fita daga
office din.
Wannan shine ya bata cikakkiyar damar qarasawa,ta fidda wayarta tayi snapping takardar ta
turawa JIB kai tsaye ta share komai ta koma mazauninta tana jiran dawowarsa.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 71
Kai tsaye ya wuce saman sofan dake ajiye bangare daban na office din yana zame takalman
qafarsa. Already sunyi sallan azahar bayan fitowarsu daga hall din,don haka ya maida bayansa kadan ya
jingina da sofa din.
So yake ya huta kadan kafin ya fita yaje yaga baqinsa,to amma tunani ya hanashi hutawar,don
maamah ce ta fado a ransa,sai ya fidda waya yana kiran musaddiq idanunsa akan agogo yana qirga
yawan awannin da suka rage da zasu maidasu gida su duka. Ko kadan bazai bari musaddiq yaci gaba da
mu'amala da gidan maamah haka kai tsaye ba,ko mu'amala da dukkan wani abu daya shafi gidan game
da abinci ko abun sha ba. Don sam hankalinsa bai kwanta ba bazai kuma taba kwanciya ba,don ta kashe
dukkan wani abu da zai bashi nutsuwa tattare da ita.
"Zamu dan jima yau,saboda akwai sabbin fertilizer da aka muka fitar,zamu gabatar dashi ga manoma"
Katse wayar yayi yana sanya hannu zai jawo file din daya shigo dashi sai kuma abun ya fado masa.
Ya tsaya cak yana juya ganin da yayi mata. Daga toilet ta fito,jikinta duk damshi da lema da yake nuna ta
taba ruwa,to me yakai mace office din mikail?.
Ya jima yana jin maganganu iri iri akan mikail din,to amma shi din ba mutum bane ke daukan
qananun maganganu shi yasa bai taba bi takai ba. Hakanan bai fiya zafafa bincike da bin al'aurar mutum
ba. Amma yau haka kawai yaji maganganun da yakeji a kanshi din yana dawo masa.
Muqamin da Mikhail yake dashi a company din bashi da alaqa sam da hada hadar jama'a karbar
baqi ko mu'amala dasu ballantana yace harkar kasuwanci ne ya kawota wajensa.
Qaramin tsaki yaja yana qoqarin watsar da maganar. Ta iya yiwuwa irin watsatsun 'yammatan nan
ne dake yawon bin maza office office dinsu don kawai son abun duniya. Muddin ko haka ne shi bazai bari
wannan ta faru cikin kamfaninsa ba. Dukiya yake nema ta halal me cike da albarka,dole duk wanda yake
qasansa ya kiyaye dokar Allah lokacin mu'amalarsu,bayan kuma mutum ya fita daga kamfanin saura ya
rage nashi.
Zancen ya maqale a ransa duk da ya bude file yana dubawa,qananun shekarun daya fuskanta
tana dasu su sukafi tsaye masa a ido duk da ba qare mata kallo yayi ba,yana tsoron kada ya zamana
yaudarota yayi ya kawota office dinsa?. Wayarsa ya zaro ya laluba number saddiq da ya baro a first floor
yana ganin ma'aikatan da suke da buqatar dauka kafin shi ya gansu yayi final interview dasu.
Ringing biyu ya daga,sai ya zauna sosai ya sake tambayarsa inda yake duk da yasan a inda yake din
"Alright......kasan me nakeso da kai?" Ya tambayeshi yana shafa baqar kwantacciyar sumar dake gefan
fuskarsa zuwa habarsa
"Aah hamma"
"Mikail......ina buqatar kowanne motsi nasa daga yanzu ya zama ana min monitoring nasa"
Sosai wannan aikin da hamman ya bashi yayi masa dadi,don ya jima yana ganin abubuwan zargi
masu yawa tattare da mika'il din,to amma baida cikakkiyar hujja da zai gabatarwa da hamma,shi kuma
hamma koda kana da hujja sanda zaka gaya masa magana sai ya bincika ya tabbatar da gaskiyar
maganarka.
Minti talatin ya sake duba agogonsa. Yana shirin miqewa saddiq din ya shigo,ya gabatar masa da
komai ya ajiye masa duka takaddun
"Well done" Fu'ad ya fadi bayan ya tabbatar da komai ya tafi daidai.
"Kira me sunan malam.....wanne time ya bawa mutanen nan?" Ya gayawa saddiq daya kasance executive
assistant dinsa wani lokaci ya juya ya zama P.A dinsa,har muqamin me sunan malam dinma yana hawa
wato scheduling coordinator ma gaba daya.
Hularsa ya dauka da agogonsa daya jiye a gefe,ya qarasa ya sanya takalmansa daidai sanda
executive Porter dinsa ya shigo
Shi ya dauki sauran kayan da yasan zai iya fita dasu din,yabi bayansa,yayin da musaddiq ya tsaya
don ya qarasa killace komai ya kashe sauran electronics dake kunne,don yasan ba lallai su sake dawowa
ta kamfanin sai kuma gobe.
Yana fita suka hadu dame sunan malam din,sai yabi bayansa suna takawa a nutse yana gaya
masa sauran schedule dinsa na yau duka
"Amma sir.....sai nakega kaman abubuwan sunyi yawa.....ko akwai abinda zaa rage ko a sauyashi a kaishi
gobe?".
Kansa ya girgiza sanda saddiq ya matso yana scanning keycard jikin designated elevator din da shi
daya yake amfani dashi cikin company din.
"Kada ayi cancel komai.....zamu kammala in sha Allah komin dare.....make sure kowanne ka sanar masa
da exact time da zamu hadun"
"Yes sir" Me sunan malam ya fada yana bawa guards dinsa waje,daya daga cikinsu yayi gaba don
tabbatar da lafiyar elevator din duk da anyi keeping nata waje daya kuma don saboda shi,muhammad
jadda yabi bayansa sauran guards din suka shiga hadi da saddiq.
Cikin ransa ya shirya sake maida kanshi busy fiye da kima,bama wai shi kadai ba,hadda musaddiq
don kaucema duk wani tsari da plan na maamah har sai yaga iya inda gudun ruwanta zai kaisu. Ya shirya
sadaukar da dukka lokacinsa ya tafi dashi a aiki fiye da yadda yakeyi a baya,duk da ko a bayan shi din ba
wani cikakken lokaci gareshi ba. Sau tari anni tana yawan yi masa fadan yana tsaurarawa rayuwarsa da
yawa,ya kamata ya fiddawa kansa lokaci da zai dinga hutawa. Bashi da wani time qwaqwara daya ware
don yaje hutu,idan ka ganshi yana hutawa to tabbas umra yaje wadda duka duka baya haura sati daya
yake dawowa.
Suna yawan ware qarshen kowacce shekara suje dukansu suyi umra,daga nan abban ya zaba musu
qasashe guda biyu dake da wani tarihi cikin addini ko rayuwa suje su qarashe qarshen shekararsu a can.
Sau tari shi din baya tafiya tare dasu,saidai ya biyosu daga baya,wanda ana kammala umra dinsa yake
dawowa kan kamfaninsa,bai fiya binsu tafiye tafiyensu da suka tsara ba.
Direct suka nufi private parking garage dinsa wanda aka tanada kawai saboda ajiye motocin da yake
kai kawo da kuma hidima dasu. Wajene da yasha banban da sauran duka parking lot na company
din,wanda aka qawatashi aka kuma cikashi da tsaro na cctv da kai kawon security.
Dukka sauran guard nashi suna tsaye suna jiran qarasowarsa. Isowar nashi yasa da sauri CSO dinsa
ya qaraso ya bude motor din da zai tafi a cikin ta ya matsa yana bashi guri,ya shiga saddiq yabi bayansa.
Sanda motocin ke motsawa suna barin wajen zuwa ainihin hanyar da zata sadasu da gate na farko
na kamfanin,daidai lokacin ya gyara zamanshi yana bude wani guri a side na kujerar da yake kai don ciro
earpiece da zaiyi using nasa wajen amsa kiran daya shigo wayarsa.
Kaman fitar kibiya idanunshi suka fada parking lot na sauran staff da suke da matsayi na biyu cikin
kamfanin. Kan mikail idanunshi suka fada,ya bude mata murfin motar yana jifanta da wani mayen
murmushi,yayin da nata fuskar yake kadaran kadaham tana sanya jikinta cikin motar
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 72
Zare Idanunshi yayi daga kansu yana jin wani quna a ransa.
"Tun yaushe mikail yake irin wannan abun?" Yayi maganar a hankali ba tare da yayi tunanin saddiq zai
jishi ba. Dan dubansa sadiq din yayi kafin ya rusunar da idanunsa
"Hamma yana dan taba harkokinsa dama,amma kuma banajin a cikin company,yanayin komai ne a
wajen company"
"Idan har a wajen company yakeyi in zanyi wani abun bazai wuce tunasar dashi kawai da gyara masa
kuskurensa da take wuyan kowanne musulmi,ya kuma wajaba a kansa ya zama dole a addini da wajen
ubangiji yayi akan dan uwansa musulmi a sanda ya fahimci kuskure ko gyara cikin al'amarinsa.....amma
kuma muddin yana shigo min da wasu abubuwa da basu dace ba muhallin neman halal dina.....lallai lallai
zan dauki mummunan mataki ne a kansa". Yayi maganar da sound din da zai nuna maka da gasken gaske
yake.
Tunda suka shiga motar take jifanta da wani irin narkakken kallo. Yanaji jikinsa yana macewa kasala
yana saukar masa kamar ko yaushe idan yasha barasa,shi yasa yaso ta bashi hadin kai ko hannunshi
yadan fara kaiwa jikinta guraren da suka tsone masa idanu amma ta qiya. Yana kuma tsoron suna isa
Bristol zaiyi wahala baiyi baccin nan nasa ba na wajibi,wanda muddin baiyishi ba bazai iya hasala komai
ba yadda ya kamata.
Ta gaya masa tana da qa'ida da kuma dokokin da dole ya kiyayesu muddin yanason rakiyarsu tayi
tsaho. To sai yaga hanzarin ma na meye?,ya qyaleta mana?,don dai jiran awa daya kacal me zai cishi?,shi
da ta tabbatar masa a yau din wuni guda tana tare dashi?.
"Babe......muddin a yau kika bani hadin kai yadda na jima ina mafarki.....zan baki fara sheet da ba komai
a ciki ki rubuta komai da yazo kanki kike burin mallaka......idan nace komai ina nufin komai fa,komai
tsadarsa ko yawansa.....ina tare da lalitar jadda diamondchore" Ya fadi yana sakin qaramin shu'umin
murmushi,don ya hango irin barnar da ganimar da kwasa cikin account din.
Kadan tadan dubeshi sai ta dauke kai,tana maimaita sunan kamfanin da tun shigarta ta tabbatar
ba qaramin kamfani bane gama gari da kowa ya saba gani ba......to amma sai taji ba abinda ya burgeta
tattare dashi. Ta tabbatar tunda har mamallakin kamfanin zai danqawa mutum irin mika'il ragamae
tasarrufi da dukiyar kamfanin duk kanwar ja ce,ba yadda za'ayi mikail din ya dinga irin wannan
fantamawar yana wasa da kudadensa ba tare da masaniya ko daurin gindinsa ba.
Ta yaya ma cikakken namiji kamar wannan daya mallaki dukiya ke dimbij yawa,kadarori kala daban
daban ciki harda private jet amma ya gagara aure?,bayan a shika shikan aure bai rasa komai ba?.
Qaramin tsaki taja qasan ranta hoton fuskarsa yana dawo mata tana jin kimarsa da haushinsa suna
kwaranyewa daga idanunta,saboda haka batajin daga shi har mika'il sun cancanci tausayawa.
"Bakice komai ba" Mikail ya fadi yana dan waiwayowa ya dubeta kadan,don tsananin rudewa da
firgicewa cikin farinciki da dimuwa da yake ganin wasu matan a ciki idan ya musu irin wannan albishir din
sam sam baiga koda kamannin haka a wajenta ba
"Idan kuma hakan baiyi miki ba ki zabi kome kikeso a rayuwa......indai zaki bani rayuwarki zan baki komai
da kike da buri" Ya sake fada cikin qoqarinsa nason gamsar da ita kalamansa.
"Baka da damuwa" Ta amsa masa cikin salon miskilancin nan nata,don maganganunsa sun fara
isarta,bata fiya son doguwar magana ba.
Juya kalmar ta bashi rayuwarta takeyi cikin ranta. Har yanzu ta kasa sabawa da kalaman maza 'yan
bariki,har yanzu mamakin wannan halittar ta d'a namiji ta kasa sakinta,su koda yaushe kansu
sukeso?,kansu suka sani?,ko yaushe yaya zasuyi su samu jin dadinsu daga wajen 'ya mace?,ba tare da
sun damu da yadda tata rayuwar zata kasance ba?. Basu da wannan asarar,suna iya sanya qafa suyi fatali
dake duk sanda wannan halin nasu ya motsa na BUTULCI,aurenki sukeyi ko zaman bariki kuke?.
Tayi imanin halin D'A NAMIJI A JININSA YAKE,dan kunama ne shi da gaske,tana kyautata zaton
babu wani d'a namiji da bashi da wannan halayyar,saidai na wani ne ya d'ara na wani kamar yadda take
gani take kuma kan gani din. Wannan hasashe da karatun da tayi musu shike nesanta zuciyarta kullum
daduniyarsu,takejin ba abinda yafi dadi a wajen mace irin ta rayu ita kadai ba tare data raba kowanne
namiji cikin rayuwarta ba bare ta bashi wani matsayi da zai zameta lalura qunci ko quna nan gaba cikin
rayuwa.......gwara ta rayu ita daya shine zata zama me cikakken 'yancin da bata dame bata mata rai.
Nisa da zurfin da tayi a tunani ya sanya har suka iso Bristol bata sani ba. Yayi parking na motar ya
fito yana takawa da qyar saboda yadda jikinsa yake qara nauyaya,ya zagaya side din da take zaune ya
bude mata qofar sai ya miqa mata hannu alamun ta taho.
Hannun nasa ta kalla sannan ta kalli fuskarsa. Ta gama ganin zallar mayen giyar da yasha yana
narkewa a jikinsa
"No need" Ta fada tana girgiza kai sannan ta dauke dubanta daga kanshi.
Baya yaja kadan yana furzar da iska daga bakinsa. Gulmarta yakeyi a ranshi,jin kanta yayi
yawa,tana da wata izza da wani irin jan aji da kamewar da bai taba gani a wajen matan titi ba sai a
kanta,amma ba komai,yaci alwashin a yau dinnan sai ya banbance mata aya da tsakuwa,dukka wannan
jan ajin garawar da wahalar dashi data dinga yi sai ya fansheshi a yau.
Tana gaba yana bayanta kamar ma ba tare suke ba har suka wuce ciki. Bata sake gasgata da
gaske yayi booking ba......da gaske lamarin namiji abune me bada mamaki da daure kai ba sai da suka
shiga babban dakin daya kama musu,wanda duk kwana daya a yadda ta gani cikin jadawalinsu naira
dubu tari takwas da hamsinne. Komai an jere na kayan abinci,isowarsu kawai ake jira. Ya fada saman
lafiyayyen gadon da yafi kama da gadon da ake shirin cin amarci a kai yana dubanta qasa qasa.
"Komai da kike buqata akwai an tanadeshi.....amma inajin sai kinyimin alfarma na matse baccin nan ko
na awa daya ne cakal.....kiji dadinki yadda kikeso.....idanma akwai wani abu da kike da buqata ga waya
can ki musu magana zasu kawo miki" Yayi maganar muryarsa tana maye ita kanta,da alama baccin yayi
mugun cin qarfinsa.
Sanda ya miqe yana shirin sabule wandonsa da riga sai ta kau da kanta tana jin yadda zuciyarta
tayi wani irin bugawa. Irin wadannan abubuwan take gudu shi yasa bata taba yarda ta biyo kowa wani
kebantaccen waje ba,sai gashi haka kawai jib ya takura mata sai tabi mutum biyu don samun cikar
aikinsu.
Yif taji ya koma ya fada saman gadon,koda ta maida dubanta sai taga bai iya cire komai a jikin
nasa ba,kawai kokawar banza ya gama yi ya koma ya fadi cikin bacci.
Minti goma qwarara ta bashi sannan ta taka ta isa gabansa. Yayi sadidan a baccinsa,taja da baya a
hankali tana jin faduwar gaba tace
"Okay" Ta fada tana jin sanyin jiki da faduwar gaban da batasan dalilinsu ba.
Ganin mintuna arba'in suna niyyar shudewa ba wani labarin nasara,ga mikail yana motsawa
lokaci bayan lokaci ya sanyata magantuwa
"Wannan aikin yayi tsauri da yawa adda.....akwai tsauraran matakai da shinguna masu zafi a kai,yanxun
haka abinda na soma fahimta kamar wani abu ya fara alerting nasu anason musu kutse cikin asusun
nasu" Ya fadi shi kansa kamar yanajin qarfin gwiwarsa yana son sarewa. Duk inda ya zaci zai samu
nasarar balla account din nasu da dukkan hanyoyi da dabaru amma sai yaga abun kamar ya wuce nan.
Daidai lokacin da yake tsaka da meeting da investors din da suka jima suna da shaawar sanya
hannun jarinsu a kamfaninsa na jadda diamondchore resources da yake a lagos da kano.....da kuma
sabon kamfanin da yakeson yabude din a yanzu na jewelry da sauran dangin kayan ado da qawa na
mata.
Daga saman system dinsa wani abu ya fara harbawa. Alamace da take nuna masa DANGER. Sosai
ya zubawa alamar idanu,sannan da hanzari ya jawo system din gabansa ya soma bibiyar abun
"What?,scammers?" Ya furta qasan ransa,sai ya kalli baqin nasa yana miqewa tsaye gami da daukan
wayarsa
"Excuse me" Yana daga musu hannu tare da takawa a hankali yana matsawa nesa dasu. Sadiq dake can
nesa dashi ya kira
"Call the security team na kamfani......ka gaya musu akwai alamun shirin yin kutse su kula".
"Done" Ya fada kaman yadda ya saba gaya masa. Juyawa yayi yana komawa wajen baqinsa,ya koma
mazauninsa ya zauna yana jawo system din gabansa.
Hankalinsa ya raba biyu,yana saurarensu yana kuma duba yadda suke samun progress na sake
kutsa musu. Alama ta qarshe daya gani ta sanyashi lumshe idanunsa hadi da ture system din gefe kadan
ya maida dukka hankalinsa dari bisa dari akan baqinsa.
"Done adda!......done,millions of naira sunyo dropping" JIB ya fadi da wani irin sautin farinciki,yana jin
sukuni yana ratsashi na samun cikar mafarkin mutanen da suke rayuwa ruhinsu a jikkunansu.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
Page 73
"Zan iya tafiya?" Shine abu na farko data tambayeshi ba tare da tabi takan adadin kudin da suka
samu cira ba
"Yes adda.... Zaki samu me napep a corner farko na street din yana jiranki gudun samun delay". Katse
kiran kawai tayi,ta miqe tana daukar jakarta ta jefa wayar hannunta da sauri tana dan duban yadda
mikail yaketa motsawa,alamar koda kowanne lokaci yana iya farkawa,saita wuce kai tsaye ta bude qofar
ta fice.
Sai data tsaya da lobby din ta daidaita nutsuwarta da kyau gudun zama suspect a idanun security
na hotel din,sannan ta fara takawa a nutse tana qarasa ficewa.
Hankalinsa a tashe yake dawowa wajen fuad din,yama gaza kiransa a waya kaman yadda shi ya
kirashi a daxun.
"Na sani.....jeka jirani mu qarasa mu wuce gida" Ya dakatar dashi ba tare da ya barshi yace komai ba. Da
dan mamaki sadiq yake dubansa ganinsa zaune hankali kwance. Duk da yasan yafi gaban hakan amma
wannan din ba qaramin abu bane da ya kamata ya ganshi haka a zaune calmly ba yana tattaunawa da
investors,to amma bashi da sauran zabi illa juyawa ya tafi din kamar yadda ya buqata.
Tana tafe a hanya tunane tunane cinkus cikin kanta da qwaqwalwarta. Haka kawai taji ta kasa isa
gida,sai kawai ta bawa me napep din umarnin suna da wajen da take so ya kaita.
Guri ne very quite,ba cikar jamaa,kuma kowa sabgan gabanshi yakeyi. Hakanan gurin yana da
yalwa da fadin da zaka zauna a guri wani ma da yake nemanka bai ganka ba. Order din lemo da ruwa
kawai tayi don batajin zata iya cin komai. Batasan me yasa ba.....ba yaune karon farko da haka ta fara
faruwa ba amma wannan din yanason tsaye mata gami da sanyayar mata da jiki.
"Eh ba shine na farko ba......amma kuma yafi kowanne nauyi da girma......baki taba samun kudade masu
tsananin kauri da yawan wadannan ba,sannan kamar an shiga lalitar wadanda baki taba koda magana
dasu ba.....kaman akwai nasu haqqin a ciki". Wani sashe na zuciyarta ya fara tunasar da ita. Wanda qarar
ring na wayarta ya katse mata tunanin.
Sunan titi data gani shi ya dauke hankalinta daga dukkan tunanin komai,ba jinkiri ta daga wayar
suka fara magana
"Komai ya qare in sha Allah" Ta bawa titi amsa a taqaice saita katse kiran. Dukka karsashinta taso dawo
dashi,ta fara lalubar wata number da jib ya bata.
Ayyuka biyu tayi a wajen da suka qara kashe mata kusan awa daya da rabi. Ta tura dukkan abinda
mutumin ya buqata don yiwa titi aishatu da dan rakiya daya visa na fita qasar india da ita da komai da
komai da zaa buqata na asibiti lafiyarta da sauransu wanda ya lashe maquden kudin da suka ninka kudin
da akayi hasashen zaa kashe din. Abu na biyu kuma ta zauna ta datse ta share ta kuma sake toshe
kowacce hanya ko kafa da zata sake sadata da mikail.....sai data tabbatar ta sanya kowanne shinge da zai
nesantata dashi nisa na har abada sannan ta tattare komai nata tana fita daga wajen.
_hmmm,anya kuwa kayan Muhammed fuad jadda zasu tabu 'yammata?,to muje zuwa dai muga yadda
wasan zai kaya FUAD dinne keda nasara?,ko SABREEN?_
Karo na farko a rayuwarta da taji shigowar sabreen cikin gidan dama dakin gaba daya amma ta
shareta kamar ma bataji ba. Tayi lakur saman gadon tana ci gaba da kwanciyarta.
Hirarsu da hameed yau ta dasa mata abubuwa da yawa cikin zuciyarta dangane da yayartata. Tayi
amanna ta kuma yarda hameed mutumin kirki ne na qwarai,daga yadda yake yawan mata nasiha da
wa'azin ta kare mutuncinta......ta guji yawace yawace da yawan fita barkatai.....don duk yarinyar data
fiya fice fice,qafafunta basa zaman gidan tabbas akwai ayar tambaya a kanta ko taqi ko taso,alamar
kamewa ga mace shine ta lazimci zaman gida.
A yau din ayoyi qwalli biyu da hadisai guda biyu suma daya karanto mata sunja hankalinta. Itakam
hameed yayi mata,a yanzu dukka burinta shine tayi aure......tayi aure ta matsa daga rayuwar da take
sake Fahimtar yaa sabreen din tana yi.....ta auri hameed tayi nesa daga cakwakiyar gidansu.....baqaqen
maganganu zallar gori da habaice habaice. Ta tabbatar zata samu irin rayuwar da takeso daga wajen
hameed,zai killaceta kaman yadda yake fadi din.
Tayi mamaki sosai da taga qofar tasu a bude,sanda ta shiga kuma falon sai ta tabbatar akwai wani
a ciki,sai ta aje jakar hannunta ta kutsa uwar dakin.
Gaban gadon hudan ta qarasa tana kiran sunanta. Da farki sai tayi banza kamar bataji ba,har sai
data saka hannu ta yaye bargon da take ciki
"Lafiya qalau" Ta samu kanta da bata amsa kai tsaye. Wani irin mamaki yaso kasheta a tsaye,amma sai ta
cinye wannan. Hudan a yanzun ta fara zama budurwa,shekara sha biyar ta fara hawa bigiren kaiwa
yammatanci,tabbas zata iya faskantar canje canjen halaitada dabi'u a tattare da ita kaman yadda ta
tabaji mamanta ta fadi a sanda take cika tata shekara sha biyar din,wanda a yanzun shekara biyar daidai
kenan
"Idan har lafiya lau huda me zai hanaki zuwa makaranta kuma uhmmm?". Kamar ta bude bakinta ta gaya
mata aure takeso,kamar ta bude baki tace ta bawa hameed ita,kamar tace mata ta gaji da ganinta
kullum tana fita babu sahihin inda take zuwa,ba makaranta ba ba kasuwa ba,amma sai tace
"Allah ya kaimu" Ta juya zuwa sashen kayan sawarta tana fidda kayan jikinta don sauyawa da wasu. Can
qasan ranta zuciyarta ta kasa samun nutsuwa,sake gaya mata takeyi
"AKWAI MATSALA.....DOLE KI NINKA SANYA IDANUNKI" da wannan tunanin ta kammala canza kayan
sannan ta juya ta koma falon don duba me dame akayi da bata nan.
Da kallo ta bita har ta fice,sai taja qaramin tsaki qasan ranta zuciya da shaidan suna ayyana mata
ko dame dame ma tayi sanda ta fitan?,caraf kuma wani sashe na zuciyartata ya kwabeta.
*D U N I Y A TA*
*_H U G U M A_*
PAGE 74
Kaman kowanne lokaci ya bawa kowa daman yayi order na abinda yakeso qarqashin kulawar sadiq
da shike handling kusan komai.
Shi daya ya ware kansa a wani table da corner na daban,ya fidda system dinsa da ya sanya sadiq
dauko masa ita. Ranshi a tsananin bace yake,amma kuma yana da wani irin abu,ya iya boye fushinsa
idan yaso,ya iya kuma danne abinda yake damunsa,dole da rayuwa sun sanyashi iya controlling anger
dinsa.
Yana da matuqar sani da zafi gami da kaifi ta bangaren computer.....ya koma da baya daga baya
cikin karatunsa,ya zabi computer science ya kashe lokaci akai har sai daya zama qwararre kuma cikakke
akan fannin,saidai ba kasafai ayyuka da cushewar abubuwa ke bashi daman practicing karatun nasa
ba,amma komai nasa zaka sameshi a tsare da burbushi da alamu dake nuna yasan kan computer sarai.
A nutse ya soma bin komai daki dai cikin matuqar qwarewa tare da sanin makamar komai. Ba
jimawa musaddiq ya iso wajen,sai yayi masa alama yayi joining sadiq kawai. Juyawa yayi yana matsawa
daga wajen don tunda ya ganshi a hakan ya bawa system nutsuwarshi yasan akwai abinda yakeyi me
amfani.
Ya samu sadiq din yana waya wanda ya kasa jurewa ya kira security team din da kansa. Ranshi a
bace shima yake wayar,duk da abincinsa dake ajiye gabansa baiko bi ta kansa ba. Dan zuba masa ido
musaddiq yayi kafin ya zauna,jikinsa kuma yana bashi lallai akwai wani abu. Jawo tray din yayi yana bude
komai tare da warware spoon da fork din dake nade cikin tissue,ya sanya musu cikin abincin ya saita
musu komai saidai still hankalinsa yana kan saddiq din.
Kusan mintuna goma sha biyar da isowarsa kafin ya kammala wayar,ya kasheta ya ajiye yana jan
tsaki.
"What's going on?" Musaddiq ya jefa masa tambayar yana dage giranshi. Cup din daya zuba musu ruwa
ya jawo yana kurba
"Scammers......hackers.....me ma zance ne musaddiq?". Idanu musaddiq ya waro waje yana kallon sadiq
"A'ina?Meye ya faru?"
"Sun diba maquden kudade daga cikin asusun company dazu........security team dinmu sun kasa aiwatar
da komai......hamma fu'ad kuma baisan wanne matsaya ya dauka ba.....duk da nasan bazai qyale ba
amma sai naga kaman ya dauki abun da sanya.....ina dai kyautata zaton yanzun yakebin kadin abun
kamar ba kudi masu yawa aka diba ba" Saddiq yayi maganar yana maida hankalinsa ga fu'ad dake dan
nesa dasu wanda baya iya ganinsa sosai da sosai
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" Musaddiq ya soma maimaitawa yana rasa abun fadi kwata kwata.
Sannu a hankali ya soma bude idanunsa har ya gama budesu gaba daya
"Wayyo......." Ya furta yana miqewa sosai saman gadon yana jin yadda kanshi da idanunsa sukayi fresh.
Komai ya sakeshi kenan,babu wani sauran burbushin giyar a tattare dashi,komai kuma zai tafi daidai
yadda ya dace.
Idanunsa ya fara wurgawa cikin dakin bai ganta ba,sai ya barwa ranshi tana toilet ne tana
shiryawa,don haka ya jawo wayarsa yana yana duba time
"Kai!" Ya fada a mamakance ganin irin baccin da yayi na kusan awa uku maimakon awa daya kacal
kaman yadda yace zaiyi. Jikinsa ya danyi sanyi ganin yadda baccin yayi tsaho,zuciyarsa ta raya masa
yarinyar nada wani irin aji da wahalar samu tamkar tarwada cikin ruwa,anya zata zauna duka wadannan
awannin tana jira?.
"Da kuwa na tafka babbar asara" Ya furta a sarari gabanshi yana faduwa,sai ya jiye wayar ya miqe da
hanzari ya nufi toilet din.
Duka bandakin ya duba ba ita ba alamar ta,sai ya fito ya soma duba dakin har zuwa balcony dake
gaban dakin,lobby da sauran gurare,hakanan ya dawo zuciyarsa na harbawa da tsananin baqincikin
kufcewar wannan damar a garesa
"Wai me yasa ma nasha barasa duk da sunan farinciki?,wannan tsinannen baccin......" Ya katse zancan
bayan ya zauna gefan gadon yana dafe kansa da hannayensa bibbiyu.
Yadan jima a haka yana karatun asarar da yayi,da kuma wassafa yaushe zai sake samun irin
wannan damar?.
Tsaki yaja sanda yaji wayarsa tana qara. Ya waiwaya yana duban me kiran,john ne chief of
security team.
"Ubanshi zan masa......ya barni naji da asarar da nayi" Ya fada a sarari yana rejecting kiran.
Sake kira yayi bayan sakanni biyar kacal,hakan ya sake qufular dashi,don daga yanzu har wayewar
gari har kwana uku bayajin zai huce daga asarar da ta sameshi.
Sake rejecting yayi,bai haqura ba ya sake kiransa a karo na uku. Wannan karon da niyyar cuccusa
masa ashar ya dauki wayar,tunda a tsakaninsu kar tasan kar ne,saidai yana dagawa ya jefeshi da
tambayar data sanya ya shiga tunani
"Kana tare da wayarka kuwa?,kasan me yake faruwa?,bakasan anyi kutse account din kamfani ba?". Dif
wuta ta dauke masa,sai kuma ya bude bakinsa
" Kai john banason iskanci.....ka sanni na sanka,idan giyarka ka shawo ka daina gigin kirana ka bari ta
sakeka tukunna,wayata tana hannuna......kuma ba wani abu daya faru,na sani fa ka dade kana harin
muqamina,to qaryarka tasha qarya......in kanaso sai ka jira sai sanda matsayina ya qara daukaka a jadda
company sai ka shiga takarar neman tsohon matsayi na" Daga haka ya katse kiran yana mitar shi baisan
abinda yake damunsa ba zai qara masa damuwa.
Yankewa yayi kawai ya kirata ya lallasheta ya kuma sake shawo kanta,tunda kudin kwana biyu ma
ya biya,ya samu ko wuni dayan gobe tayi masa tunda ya tabbatar ba zata taba dawowa a yau ba.
Saqon da idanunsa suka gane masa daga banking da kamfanin nasu ke ta'ammali dashi ya kusa
sanya gudawa da fitsari duka yanke masa lokaci guda. Yayi wani mugun gigicewa sanda ya shiga saqon
idanunsa suka haska masa adadin kudaden da aka zare daga asusun.
Wani irin abu yaji yana tsirga masa daga kowacce kafa ta gashi dake jikinsa. Gangar jikinsa yakejin
kamar ba tashi ba ballantana ayi batun qafafunsa su samu daman iya daukansa,don haka sai kawai ya
sulale ya zube ragwab a wajen yana jin kamar numfashinsa zai qwace masa.
Ko sanda ya duba time na faruwar abun,da sanda John ya fara kiransa sai kawai ya saki wayar ya
dora hannu saman kai yana fadin
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Da qarfin gaske,wanda kalmar ma sam batazo bakinsa ba sai sannan.
Yana dire kalmar farko hawaye suka fara bin kuncinsa. Daidai sanda kuma kira ya shigo wayar tasa
abinda ya sanyashi zabura kafin yakai dubansa ga wayar.
Sir sadiq daya gani a rubuce ya sanya fitsarin dole kubce masa duk kuwa da yadda yaso ga riqeshi.
Ya shiga uku ya lalace,yasan tunda yaga kiran saddiq din magana ya gama isa kunnen boss. Da wanne
baki zai kare kansa?,idan suka buqaci kuma ya biya a ina zai samu?,ta ina zai samosu?. Yayi imanin koda
danginsa zai siyar bazai hada wadannan kudaden ba.
Zuciyar dake da Allah a cikinta......hakanan zuciyar dake da yawan ambaton Allah ce kadai ke
samun nutsuwa a sadda bala'i ya durfafo ta,don haka dukka wata dabara da kuma nutsuwa sukayi qaura
daga gareshi.
Ya dinga zirya yana kai kawo,ya kasa aiwatar da komai,ya kuma kasa kamo bakin zaren komai. A
haka lokutan sallah duka suka shude masa,hakanan qarar kiraye kirayen mutane suka yita shiga
kunnuwansa suna fita ba tare daya iya rabar inda wayar take ba.
Duk wani kira da zai shigo wayar tsoro yake bashi,baya qaunar koda rabar inda wayar ma take
gaba daya.
Sai kusan bayan sallar ishai ya iya fusgo tunanin baiyi sallah ba,ya miqe yana hada hanya ya nufi
toilet don cire jiqaqqen wandon jikinsa daya jiqe da fitsari ya dauraye jikinsa ya kuma daura alwala. Har
a sannan sam tunaninsa bai kawo masa sabreen ba,ya mance sam sam da itama saboda tsananin
rudanin daya shiga.
"Don't call him again......ka barshi,inason naga iya gudun ruwanshi......kafin sannan ni na gama nawa"
Fuad yace da sadiq wanda ke shirin sake kiran mikail din karo na biyu
Kusan tare suka yiwa juna sallama ita dashi,sai suka amsawa juna sannan tace
"Nace dai Allah yasa lafiya......daga ku har abbanku yau duka kunyi dare a waje"
"Lafiya lau anni.....ayyuka ne suka riqemu,wasu al'amura kuma suka taso wadanda su suka shagaltar
dani daga kiranki"
"Babu komai......kada ka damu,tunda dai dukkaninku kuna lafiya to alhmdlh......farouq yace min kuna
tare da musaddiq ko?"
"Ameen ya hayyu ya qayyumu" Ya amsa mata zuciyarsa na sake cika fal da qaunarta da qarin ganin
kimarta. Tana taka muhimmiyar rawa qwarai da gaske wajen cike musu wawakeken gibi da ramin dake
zukata da kuma rayuwarsu.
Tun da aka kirayi sallar magariba ta gama shirya komai,sannan ta sallami masu aikinta kamar jiya.
Tsaf ta shirya cikin embroidery holland gold atamfa da keta sheqi da nuna ainihin tsadar sutturar. Tayi
kyau abinta,kai ba zakace itace ta haifi zabgegen saurayi irin muhammad fuad da musaddiq ba. Ita din ba
baya bace wajen iya kula da jiki da tattalin fatarta da dukkan abinda zaya qara mata lafiya da kuma
quruciya.
Parlor ta koma tayi zaune bayan ta kunna tv ta kuma saita tashar da take ra'ayi. Ta kame saman
daya daga cikin sofas din falon tana kallon hagunta da damanta. Kujerun take kallo,a ranta tana wassafa
ranar da zatayi gwanjonsu. Duk da tsadarsu da kudaden da aka kashe wajen mallakarsu sam ita bata
tuna wannan. Abu daya dake sake tsaye mata a rai shine,labarin katafaren ginin daular data samu cewa
yana yi cikin garin abuja. Batasan ainihin wacce unguwa bace,amma me kawo labaran ya shaida mata
cikin jerin unguwanni mafi daraja da tsada a garin abuje yake ginin,kamar yadda yakejin qishin qishin din
yana nan yana tamfatsa wani a lagos.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 75
K'aramar qwafa taja,muddin da gaske wannan villa din yake ginawa.....indai da gaske hoton da me
dauko rahotonta ya nuna mata fuad dinta ke ginawa.....to kuwa koda zatayi yawo tsirara ba zata taba
bari ameena da hamza su sanya qafafunsu cikin wannan daular ba.
Wayarta ta dauko ya kira hajja harira,a nan suka bata lokaci me tsaho suna sake tsara yadda
komai zaya kasance.
Batasan ma lokaci yaja haka ba sai da suka gama waya da hajja harira din. Ta kalli agogo tana
mamakin rashin shigowarsu gidan,fargaba na saukar mata na kada fa yau ma a maimaita abun jiya?.
Bata samu fuad ba,amma ta samu musaddiq,ya amsa mata da zasu shigo,don shima baisan fuad
din ya gama shirya yadda zasu cinye daren a waje ba.
Ci gaba tayi da duba lokaci mintuna bayan mintuna,saidai duk sanda ta kalli agogon sai ranta ya
sake baci,haka ta sake jawo waya da xummar sake trying number musaddiq amma ta kasa samunsa.
Ranta ya sake baci qwarai,dama ta sani samun number fuad ba abu bane me sauqi,sau tari xaka
iya kiransa ka kasa reaching dinsa,saboda ba da gama garin wayoyi yake amfani ba don dalili na tsaro da
kuma matakin rayuwa da yake kai dole yana buqatar tsari akan komai nashi.
Dukka number dinsa taci gaba da gwadawa,number ta qarshe data kira taji alamun kiran ya soma
tafiya,saita samu gefen kujera ta zauna tana furzar da iska me zafi daga bakinta ranta yana tafasa.
Kaman jira ake ya gama wayar wani kiran ya shigo. Kamar ko yaushe bayyanar sunanta saman
screen din fargaba da kokwanto yake sanyashi. To amma ba yadda ya iya,dole ya daga kiran ya mata
sallama kaman yadda yake a dabi'arsa.
"Wa'alaikumussalam.......me yasa har yanzu baku shigo bane fuad?,ka manta da alfarmar dana nema
kenan?" Ta fadi tana qoqarin tausar zuciyarta ta yadda kalaman zasu fita da taushi daga bakinta.
Komai qanqantar motsi tsakanin anni da maamah sai yaga tarin banbance babance. Da fari anni
lafiyarsu kawai takeso taji kafin komai......amma ita nata uzurin su shigo suci abinci shi ta fara
gabatarwa,abincin da ta tabbatar koda basuci a wajenta ba zasuci ako ina nema,amma kuma lafiya fa?.
"Ayyukane suka tsaremu yau dukkaninmu,yanzu haka ma wani guri zan qarasa......amma in sha Allah i
will do my best". Shuru ta danyi wuta tana dauke mata,yanzun qarfe tara harda rabi na dare,yaushe yaje
wani waje,yabaro gurin kuma yazo wajenta?.
" Okay,ina jira" Abinda ta fada kenan tana jin kamar ta bude masa abinda ke ranta. Bala'i da masifa
takeson lullubeshi dashi,to amma ko dazun suna waya da hajja harira sai data gaya mata
"Me garaje ba kasafai ya fiya cin nasara ba a dukka lamuransa,saikin saka haquri juriya da kauda kai
kaman bakiga komai ba". Wayar ta cillar gefe,ta hada tafukan hannayenta cikin fuskarta.
Wata irin tsanar anni da alhaji hamza tana mata masauki a zuciya tana kuma qara samun
hauhawa cikin ranta. Inama ace yau zata budi idanu taga babu su cikin rayuwarsu?,da kowacce dama
tazo mata yadda takeso.
Iya tafiyar da sukayi cikin motar bawai zaman shuru kadai yayi ba,zuciyarsa ta gama nisa akan
matsalar iya balla shingen asusun ajiyarsu har kuma a debi wani abun?. Ba shakka koma waye ya aikata
hakan yana da alaqa me qarfi da kamfaninsu,yana kuma da alaqa ta kusa kusa da mika'il. Dole ya
zamana yana da alaqa da mikail.....ko shi kansa mikail din ma gaba daya.
Dalili......dukan abinda zai basu daman yin kutse kai tsaye da samun nasara haka a sauqaqe yana
tare da mikail din. Dazu dazu ya danqa masa komai,cikin qasa da awa biyu kacal kuma ace komai ya
faru?.
"Muje gida" Ya bawa driver din umarni,wanda ba wanda ya binciki dalili tsakaninsu ukun suka sauya
akalar tafiyar tasu.
A tsaitsaye ya leqa anni sannan ya wuce zuwa sassanshi. Ya samu sassan nasa neat kamar ko
yaushe kaman kuma yadda yake buqata. Ba duhu ba kuma haske me yawa sai matsakaicin hasken da bai
fiya takurawa idanuwa ba. Ko ina qamshi yake fiddawa da wani irin moderate yanayi.
Takalmanshi ya sabule daga bakin qofa yana sauya wasu lausasan flip flops,daya daga cikin
hadimansa ya sunkuya ya daukesu yana adanasu cikin wani qawataccen ma'ajiyar takalma me daukan
hankali.
"Ku ajiye komai ku tafi,na sallami kowa.....sai da safe" Ya fadi musu yana takawa zuwa hanyar da zata
sadashi da wani dan corridor da zai bashi daman isa bangaren dakunan baccinsa.
Daga zuciyarsa har gangar jikinsa basu da wani karsashi ko qwari,to amma kasancewar zuciyar
jaruma ce ya sanya bata gaza ba,sai daya tabbatar yayi wanka yayi sallah ya sauya kayan jikinsa sannan
Kai tsaye ya dawo falon da babu kowa a cikinsa,saidai ya tabbatar security tako ina suna kai kawo cikin
gidan dama wajen gidan.
A nutse yake ratsa falon hannunsa zube a aljihun boxers din daya sanya tamkar wanda ya boyeshi
saboda jin sanyi ko baya buqatar aga hannun nasa. Light blue kalan kayan sun masa wani irin kyau,saidai
kuma fuskarsa tadan fada kadan wanda baya rasa nasaba da stress din yau daya tsinci kansa a ciki.
Dining ya wuce kai tsaye,komai yana shirye cikin tsafta. Bayajin a duniya bayan anni akwai wanda
yakai ameh sanin tsarinsa akan abinci.
Yasan duk abinda ya bude cimarsa ce,kuma abinda yakeso ne,saidai kuma bayajin akwai wani
sauran space da cikinsa zan dauki abinci,wannan ya sanya ya bude royal glass bowl din da tun bai bude
ba yana iya ganin abinda yake ciki.
Lafiyayyen fruit salad ne da aka samar dashi daga dukkan nau'in kayan marmari na nan qasar
dama wanda bamu dasu a nan din. Baya rabo da fruit sam,don haka masu shirya masa store da fridge
dinsa sunsan duk inda zasu samar masa da nauin fruit da cimar da yakeso din.
Bayashan coffee sai idan dole ta kama,amma yasan sirrin shan black tea da ake masa hadi na
musamman da abubuwa masu amfani ga lafiya irinsu cinnamon cardamom scent leaves da sauransu.
Da kansa ya shirya komai saman tray ya nufi wata yar kyakkyawar books shelves ta ainihin
gogaggen katako dake bangon gabas na parlor din. Hannu daya ya sanya ya murza wani abu da ba lallai
ka iya lura da zamansa jikinta ba,sai ya sakeshi yasa hannu ya juyashi take qofa ta bayyana daga baya
abinda ba zaka taba tunanin samuwarsa a wajen ba,ya taka ya shiga a hankali yana maida qofar yadda
take.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 76
Daki ne da yakan jima bai shiga cikinsa ba sai muhimmin aiki irin haka ya taso. Saidai duk da haka
komai a tsaftace yake.
Wani irin table ne na musamman ya jawoshi gaban main table dake dauke da nau'ikan na'urorin
computer iri daban daban,ya aza tray din hannunsa a kai,ya taka a hankali ya kunna kowanne lantarki
dake dakin,ya bada haske sosai. Komai na dakin bisa tsari yake,da nau'o'in kalolin green masu qarawa
idanu qwarin gani.
Idanunsa saman systems din daya kunna guda biyu yana jiran su gama saituwa. Kadan kadan kuma
yana kurbar black tea din da qamshinsa ke qara masa nutsuwa,kafin ya ajiye ya soma shan fruit salad
din,daidai sanda komai na system din ya daidai ta,sai ya sake jawo kujerarsa gaba yana bata dukkanin
hankalinsa.
Cikin tsananin nutsuwa da qwarewa yake bin komai. Ya kusa kashe a qalla awa biyu cikakku kafin
ya dakata,ya tura kujerarsa baya yana zubawa allon computer idanu yana duba abinda ya samu a tsahon
zaman da awannin da ya kashe.
Iska kawai yake furzarwa daga bakinsa,mamaki yana sake cikashi da samun bayanan duk da bai
qarasa samun ragowar baya nan ba,amma ko iya wadannan bayanan da zaman da zaiyi da mikail sun
isheshi samun kan komai. Ya dinga murza tafin hannunsa cikin na juna tamka ma jin sanyi,kanshi yana
sake cakewa.
"Jibril usman" Ya maimaita sunan idanunshi nakan sunan da bai samu damar samun ainihin fuskar
me sunan ba. Tabbas ko wayeshi din mayen computer ne,kuma qwarrare a sanin fanninta,saidai duk da
haka qwarewar tasa akwai saura,don akwao gurare da abubuwa daya gani wanda shi Jabril din da ya
samu rufesu to ba shakka shi kansa yanzun bazaikai ga isa ga bayanan ba. Qaramin masanin computer
zai iya saluting jibril,amma shi da mutane ire irensa zasuyi murmushi ne kawai,a karon farko kuma su
fahimci saura taqi kadan yakai inda ya dace yakai din.
Gefe daya ranshi ya sake ninka baci,duk wanda yaga aka zare kudin zaiyi tsammamin manyan
hackers gagarumai wanda suka gagari duniya system dinsu ta hadu dashi......wannan kadai ya isa ya sake
zaburar dashi lallai lallai yana buqatar yin garambawul wa security team dinsa,amma kafin sannan mikail
shine mutum na farko daya dace ya dauki mummunan mataki a kansa,saboda shi da kansa ya yiwa
tsaron company dinsu aiki,ya saka abubuwan da duk qwarewarka idan ba samun wani information
mutum yayi ba zai wahala ya samu isa ga inda suka samu isa din.
"Ina yaje?,waye ya bawa sirrinmu?" Wadannan sune tambayoyi guda biyu da yake buqatar ji daga bakin
mikail din. Kodai yaci amanar company......ko an nemi rayuwarsa an masa barazana....kota dalilin
sakacinsa bayanan sun fita.
Washegari kaman kullum,yabi tsarin jawadalinsa na kullum tun daga gida har zuwa office. Qarfe
shida da rabi yake kammala motsa jikinsa ya wuce wanka,idan ya fito yakan dan bar bathrobe jikinsa ya
karbi newspaper da magazines ya duba,yadan duba saqonnin email da WhatsApp dinsa ya hada da shan
ruwan duminsa ko dafaffiyar madarar shanunsa me tumeric. Sai bayan kammala dukka wadannan
hidindimun sannan yake shiryawa,yayi breakfast ya wuce office.
Kamar ko yaushe yau dinma bakwai da rabi ya fito daga toilet daure da bathrobe dinsa. Yanaso
yau ya fita da wuri ne fiye da yadda ya saba fitan. Don ko da safe daya tashi ya sami missed calls din
maama din kusan guda goma,wanda ya tabbatar tun na daren jiya ne.
Yawan kiran nata kadai da takeyi yana sake bashi tabbaci ne a kanta. Ya jawo wayar ya turawa
musaddiq text akan zuwa takwas ya shirya zai aikeshi wani guri,sai ya cire toilet slippers din ya sanya
wasu tausasan rufaffun takalma ya soma takawa yana fita don riskar parlor ya duba newspapers din yau.
Ba kowa parlor din sai ameh daketa zirga zirgar shiryawa ogan nasa dining,sai me sunan malam
dake zaune saman lallausan turkey carpet din da aka qawata tsakanin kujerun. Me sunan malam din na
daya daga cikin amintattunsa da basu da shamaki wajen samun daman isowa parlor dinsa.
"Morning me sunan malam.....mun tashi lpy" Ya amsa masa yana zama saman wata sofa guda daya data
banbanta da sauran duka kujerun parlor din yana kai hannunsa saman dan qaramin table din da aka
zube masa sabbin newspaper din bayan an kwashe na jiya.
"Lafiya alhamdulillah sir"
"Ma sha Allah" Ya furta yana bude page din farko na jaridar ba tare daya tsaya karanta bangonta dake
dauke da title na labaran ciki ba.
Labarin farko suka wafci idanunsa. Ya sake dawowa da baya bayan ya karanta layin farko da akayi
da manya manyan zane. Bai tsaya bata lokaci ba ya koma bangon don sake duba title din da ya
tsallakeshi a dazu. Tabbas duka abu guda suke nunawa cikin harshen turanci
Jaridar ya juya tamkar ma ya manta wanne gidan jarida ne suka kafe labarin. Sai ya maidata ya
ajiye yana dauko newspaper ta gaba.
Ita dinma kaman wancan,bangon farko abinda yake rubuce kenan a jiki,ya sake juyawa shima ya
duba gidan jaridar sai ya maidata itama din ya ajiye,ya sake daukan ta uku.
To ita dinma babu wani canji,duka dai labari guda daya ne,abinda ya bashi tabbaci da yaqinin
wannan shine labari na farko da zaiyi trending kenan yau a duniya kasuwanci.
Idanu kawai yaci gaba da zubawa rubutun kamar wanda kwanyarsa ta kasa gano komai,ya daga
idanunsa a nutse da suka fara sauya launi ya kalli ameh daketa goge dining din da kyau don kawar da
qura datti ko maiqo komai qanqantarsa daga muhallin cin abincin boss din nasa da ya sani da tsananin
tsafta da rashin son qura ko datti komai qanqantarsa
"Ameh......dauki waya ka kira sassan saddiq.....i wanna see him yanzu yanzu".
"Yes sir" Ameh ya amsa masa yana sakin komai,sannan ya gangara a hankali yana nufar inda wayar take
girke.
Daidai sanda ameh ya gama shaidawa saddiq saqon fuad farouq yayi knocking daga can first door
sannan ya turota a hankali ya shigo. Yana sanye da kayan motsa jiki da alama fitowarsa kenan daga dakin
motsa jiki na gidan,wanda dama kusan kullum shine qarshen shiga,fuad kuma na farko,saddiq da
musaddiq ke binsa daga baya.
Dauke yake da jaridu har guda uku a hannunsa,kallo daya fuad yayi masa ya karanci shima labarin
ya gani kuma shi ya shigo dashi. Fuskarsa a dinke ba walwala ya samu kujerar dake fuskantar fuad
din,wannan ya sanya me sunan malam ficewa ba tare daya gabatar da abinda ya kawoshi ba,hakanan
ameh shima ya wuce ta kitchen ya bulla ta baya yabar sassan.
"Tun jiya naketa qoqarin ganinka.....duk da dare yayi sanda kuka dawo nayita nemanka ban samu
ganinka ba........yanzu da safe kuma sai naga wannan" Ya fadi yana zube masa jaridun hannunsa. Binsu
yayi da kallo sannan ya maida dubansa kan fuskar farouq
"How comes fuad?" Ya furta tsananin bacin rai yana cin zuciyarsa. Kanshi ya motsa kawai yana girgizashi
kadan
"A lot of things farouq......bansan ma ta inda komai ya fara ba......na kuma rasa ta inda zan
kamoshi......inajin kamar ana warwaremin tunani na ne......da farko wawashe asusun kamfani ta sigar da
ba wanda zai iya yinta sai na kusa ko wanda yasan sirrin asusun......ina cikin aikin kamo zaren kuma sai ga
wannan......wannan fantsamar labaran tabbas shiryayyen abune koda kwashe kudin ba shiryayye
bane.......zakafi kowa fahimtar anyi ne don a yiwa kamfanin illa......ta yaya babban kamfani kamar namu
da yake da hannuwan jarin manyan 'yan kasuwar duniya ace saboda tsananin rashin tsaro har za'a iya
kutsa kai ciki a debe kudin mutane?......wanne tabbacin tsaro muke dashi da zamu baiwa dukkanin
wanda yake da buqatar kasuwanci damu?,wannan shine tuhumar da xamu fara fuskanta daga wajen
al'umma......waye ya fidda labarin cikin qasa da awanni uku,har ya zamana labarin da kowanne shafin
jarida suka maida bangon labarinsu?". Kai farouq ke gyadawa cikin zuzzurfan nazari,ya daga Idanunsa ya
sake duban fu'ad
"Shi kansa kwashe kudin nan baka tunanin aike ne?,ture ne?,kuma suna da alaqa da wanda ya fidda
labarin?". Mintuna kusan uku fu'ad din baice komai ba,kansa yana sake qullewa,sanda ya bude baki zaiyi
maganar sadiq ya shigo sanye da jallabiyya hannunsa riqe da system.
Kallo daya dukansu sadiq din yayi musu ya fahimci sunga komai,tun da sassafe kiraye kirayen
wayoyi suka tasheshi,kusan fitar labarin su suka hanashi fita motsa jiki tun daga sallar asuba daya koma.
Yana tunanin ta yadda zai iya sanarwa da fu'ad din abun,amma kuma yasan zai wahala awannin safiya su
wuce bai sani ba tunda shi din ma'abocin bin shafukan jarida ne.
"I hope abba baiji komai ba ko bare anni?" Fu'ad yayi tambayar tsananin fuskar farouq da sadiq. Junansu
suka kalla kafin farouq ya amsa
"Zai wahala abba bai sani ba,tunda kasan yana bibiye da kafafen yada labarai,annin dai ita zaka zatarwa
haka" Kai ya girgiza yana yin qasa da kan nashi,yasa hannunsa yadan shafi qasan wuyansa.
"Dole komai ya kasance cikin hikima da kuma tsanaki,hakanan for now dole mu zama cikin takatsantsan
da sanya ido akan kowa,faruwar wannan kadai ya sake gayamin tabbas akwai wasu qofofi dana bari a
bude......akwai wasu bayanai namu tabbas da suke fita.....akwai wanda kuma yake dauka yakai
din......sadiq " Fu'ad ya fadi yana dubansa
"Na'am hamma"
"Inaso kabar kowa a haka,kada ka sake amsa waya ko maganan kowa.....amma ka shiryamin meeting na
sirri,koda me sunan malam banason yasan da zaman.....ka tsara awannin da zamu zauna din zuwa
tashi,zai fara daga goma na safe har sai sanda na buqaci tashi......general meeting nake buqata"
"Okay hamma" Ya fadi yana sauke system din saman cinyarsa cikin qoqarin duba schedule dinsa na yau
yayi cancelling wasu ya kuma gyara time na wasu koda akwai yiwuwar zai iya gabatar dasu.
Sun jima da farouq a wajen suna tattaunawa kafin farouq din ya miqe ya wuce nasa sassan da
zummar shiryawa,don yanason ya bishi zuwa kamfanin.
Sai qarfe tara saura suka fito,kaman ko yaushe ya taka zuwa sassan anni. Kowacce safiya takan
zauna a parlor har sai taga ficewar kowa zuwa wajen sana'arshi. Yau dinma tana zaune cikin riga da zani
na lallausar atamfar super exclusive me ruwan sararin samaniya da ratsin ruwan ganye. Ta lullube jikinta
da tattausan mayafi dan turkey daya dace da atamfar,dukka hannayenta siraran awarwaro ne masu
daukan idanu da suka dace da fatarta da batayi komai na darajar kulawa nutsuwa da kwanciyar hankalin
da take ciki.
Kamar kullum kuma kaman ko yaushe ya duqa gabanta suna gaisawa. Yau din bata ja zance dashi
ba saboda ta karanci kaman gaggawar fitar sukeyi.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 77
"Na'am anni......akwai wani abunne?". Kai ta girgiza tana jin tausayinsa hakanan yana tsarga mata. Tasan
cewa akwai abubuwa da yawa da suke damunshi cikin zuciya,amma shi din wani irin mutum ne me
masufar zurfin ciki. Zai wahala kaji ya b'ara ko kaji kukanshi.
"Kaman akwai wani abu ko?" Ta jefa tambayar gareshi don batason fitowa kai tsaye ta Qureshi da
tambayoyinta
"Ba komai anni" Ya fada cikin bata tabbaci,don yayi imani ya nuna mata akwai damuwar,to yinin yau
gaba daya haka zasu barta cikin rashin sukuni.
Kai ta gyada ba don ta yarda ba,sai don tasan koma meye idan ya dace ta sanin shine mutum na
farko da zai fara gaya mata
"Ameen ya hayyu ya qayyumu anni,na gode" Daga haka ya juya yana fita. Har cikin ransa yakeji irin
wannan addu'o'in nata,duk kuwa da cewa bawai shi daya takewa adduar ba kowannensu ne,amma
yakanji a ransa kamar tasa ta dabance.
Bai shiga mota daga parking lot na gidan ba,sai yace su fiddo motocin su sameshi waje. Ya soma
takawa a nutse suna jerawa shida farouq suna tattaunawa kadan kadan har suka fito a gidan.
Sanda suka doshi gidan nasu yayi tsammanin farouq zai dakata daga yi masa rakiya amma sai yaga
yaci gaba da binsa har suka isa bakin gate. Sun gaisa da malam saidu cikin girmamawa sannan suka kutsa
kai ciki,guards dinsa guda biyu dake biye dashi suka dakata suna jiran fitowarsa.
Tunda ta wayi gari ta kasa tabuka komai,tana kwance kawai a daki tana kwancewa da saqawa
bayan doguwar wayar da sukayi da hajja harira. Anya kuwa nasarar da take sanya ran samunta zata
cimmata?,zata ma iya haqurin kwana ukun da bokan ya deba mata kuwa ba tare data koma ta sanar
dashi komai ba?.
Maida tunaninta tayi tana sarrafa shawarar da hajja hariran ta bata. Bata jin cewa shawarar
zatayi aiki har ta lanqwaso mata me babban suna yadda takeso?.....anya bazai zama doguwar hanya me
wahala ba?.
"Waye ne?" Tayi tambayar cikin izza sanda taji an nace da knocking mata qofar bedroom
"Nice hajiya.....yallabai ne yazo" Me aikin ta furta a qasqance
"Eh shine" Ta sake amsawa a ladabce. Cike da mamaki ta kalli agogo. Wannan ba shine lokacin da suma
saba shigowa gareta ba,me ya kawoshi yau da safe?,ko dukka cikin dabaru da salon son kauce mata ne?.
"Ina zuwa" Ta amsa mata sannan ta fara yunqurin saukowa daga saman gadon.
Tun daga nesa ta zuba idanunta a kansu,hira suke qasa qasa da wani irin kusanci da emotion da
zaka tsammaci su din tagwaye ne da ska rayu qarqashin mahaifa guda daya. Bata ga wani banbanci ba ko
kadan tsakanin danta muhammad jadda mamallakin kamfanin haqa da sarrafa diamond ba.....da kuma
farouq hamza kibiya me kamfanin saida tsabar abinci da taki ba!.
Meye ribar suna da yayi?,meye amfanin salon banbancin kasuwanci tsakaninsu muddin a idanu
zaka dinga hangar yanayin sukunin rayuwa iri daya tsakaninsu?. Kamata yayi ace ana hangen tazara
tsakaninsu,kwatankwacin tazarar dake tsakanin bawa da uban gidansa.
Wani irin abu yayi mata tsaye a wuya,amma dole ta saita yanayin fuskarta sanda ta isa gabansu
"Wato farouq kayi wuyar gani,har gwara sadiq ya fika kirki anfi ganinka" Dukkaninsu ba wanda zancanta
ya kwantawa,saidai kawai sun bita da irin yanayin da tazo musu dashi. Wannan faran faran sa sabuwar
maraba da iyalan Alhaji hamza kibiya sabuwa a idanunsu da basu taba ganinta ba.....koda kuwa sanda ta
dawo ta iske iyalinta cikin kyakkyawan rayuwa qarqashin jagorancinsu da tallafawar rayuwarsu.
"Wanne irin aiki ne ya riqeku jiyan kaida dan uwanka kuka saka halartar kira na?" Tayi masa tambayar
daketa cin ranta,don har xuwa lokacin bata gamsu wai aiki ne ya riqeshi ba
Yana murza yatsun hannunsa idanunsa samansu,zuciyarsa na wani irin motsa cikin yanayi maras
dadi. Koda yaushe maganarta babu komai ciki sai zallar son kanta a ciki......ba wani sauti alama ko yanayi
na kulawa ko nuna damuwa......ba wannan shaquwar da maganadisu dake tsakanin uwa da danta da har
zata iya karantar yanayin damuwa walwala ko farinciki da yake ciki,abinda dukka ta rasasu anni kuma ta
haye kansu ta zauna sosai.
"Yanayi ne na aiki da zai iya rutsawa dakai ako wanne yanayi ko lokaci" Ya amsa mata a taqaice don
bawa kansa kariya .
Duka duka zaman bai wuce na mintuna goma zuwa sha biyar ba suka wuce. Mintuna goman da
suke da matuqar tsada da daraja a wajensa......don ita din itace.....yana jin ya wajaba ko yaya ya bata
wadannan mintunan don tserewa tuhumar ubangiji.
Fadin ma yanayin daya kwana a cikinsa a wannan ranar dare har ya zuwa safiya bata baki ne. Duk
sanda ya waiwaya ya sake duba wayarsa sai ya dinga jin abun kamar mafarki......kaman baccin daya
kwanta shi yakeyi,kaman har yanzu idan ya farka zai samu komai ba gaske bane.
Daga sallar magariba har ishai saida safe ya hada da asuba ya ramasu. Gaba daya ya wani firgice
ya fita hayyacinsa a tsakanin. Ba abinda yake iya tunawa sai wanene Muhammed jadda da kuma irin
hukuncin da zai iya dauka a kansa.
Duk yadda yaso ma ya yiwa kansa hasashen ta inda zai fara kare kansa a gaban mutumin da a
fagen aikinsa baida maraba da zakin daya fito farauta sai yaga sam zantukan daya tsara ko kadan basu
hau kan saiti ba,basu kuma dace da hankali ba. Tsananin tsoron da firgicin ya sanyashi kashe wayoyinsa
gaba daya,saishi kadai cikin dakin tamkar tsohon mahaukaci.
Ba abinda kunnuwansa ke gaya masa sai sautin sallamar talauci cikin rayuwarsa,an debi kudin da
ya tabbatar baida abun biya koda kuwa zai saida komai daya mallaka shi da danginsa su koma yawo
tsirara.
Taku biyu yayi don shiga toilet ya rage gudawar da yake fama da ita tun faruwar abun idanunsa
suka fada kan dan kunnen.
Gabansa yayi wani mummunar faduwa sanda kwanyarsa ta haska masa wani abu lokaci guda
tamkar haskawar walqiya cikin duhun dare.
Tsugunnawa yayi ya dauki dan kunnen.....sai yanzu ma ta dawo kwanyarsa,sai yanzu tunaninsa ya
soma haska masa wani abu
"Fateema?" Ta maimaita ainihin sunan da shine nasa STAMP din data bashi.
Komawa yayi ya zauna saman kujerar dake daura da qofar bandakin yanason tuna yininsu na
jiyan a tare.
Yayi dukkan wani flash back daga qwaqwalwarsa zuwa zuciyarsa da kuma idanunsa,ba wani
motsi nata guda daya daya bashi alamun rashin gaskiya a tattare da ita
"To amma me yasa na farka na nemeta na rasa?" Ya jefawa kansa tambayar data sanyashi miqewa ba
shiri,ya jawo wayarsa da baiyi shirin kunnuwa ba ya kunnata,cikin ransa yana jin gamsuwar tabbas ita ta
aikata ko kuma tana da hannu wajen afkuwar komai.
Sanda wayar ta daidaita sai ya fara yunqurin kiranta,saidai a duk sanda zai kirata din sai
computer ta datse kiran ba tare da an masa bayanin komai daga danganci network ne babu a area din da
take?,ko kuma wayarce dungurun gum a kashe?.
Ci gaba yayi da gwada kiran babu qaqqautawa,har sai daya sare,energy dinsa yayi qasa,ya tabbatar
bazai cimmata a waya ba.
"Sai kayi tattaki ka sameta a inda take" Wannan shawarar ta sakashi zabura ya miqe,ya zura takalman
qafarsa a gaggauce,saidai yana daukan key din motarsa komai ya tsaya masa cak
"A ina take?,a ina kuma zaka sameta din?" Zuciyarsa ta jefa masa tambayar data kusa tsaida
numfashinsa
"Na shiga uku" Ya fada yana jin dukka jikinsa yana rawa
"Bansanta ba,bansan komai a kanta ba" Ya fadawa kansa da kansa idanunsa suna tara hawayen da babu
makawa sai da suka yiwa kansu qofa
"Garin ya akayi haka?" Ya sake tuhumar kansa da kansa,abinda ya sanyashi sulalewa ya zauna a wajen.
Yafi qarfin awa biyu zaune ya kasa hasalawa kansa komai,kafin daga baya wata zuciyar ta bashi
wata guntuwar shawarar data dan bashi nutsuwa kadan,har ya iya miqewa ya gyara rigar jikinsa ya
maida hularsa ya lalubi qofar fita.
Dukkan wani muhalli da yasan sun taba haduwa,cin abinci,shan ice cream,shopping da sauransu
ba wanda baije ba. Saidai duk inda yaje din dogon bayani ne maras fa'ida ko kuma alfanu,domin ba
wanda ya ganeta. Abinda bai sani ba shine......ita din tamkar tarwada take a cikin ruwa......tana da
matuqar santsi da idan taje waje zai wahala ka sake samunta a nan... Muddin taje waje dakai sau daya
ta kansile wajen kwata kwata cikin jadawalin rayuwarta,ba guri bane da take mu'amalantarsa ba a koda
yaushe ballanta fuskarta ta zama sanniya a wajen mutanen dake yawan xiyartar wajen ko kuma
ma'aikatansu ba.
Tun yana zagayawa da qarfin gwiwarsa har ya sare. Zuwa sannan yanajin zai haukace ne idan bai
gayawa kowa halin da yake ciki ba,don haka yana isa Bristol baiko koma dakinsa ba ya kira mato a waya.
Tazarar minti ashirin kacal ya iso,ya shigo dakin yana cewa
"Kai matsala ne dakai,wani lokacin sai ayita faman kiranka baka dagawa,tun jiya nake danna maka kira
kaqi dagawa......gobe ne za'a zauna cacar nan fa......"
"Shut up mato!" Ya dakawa mato din tsawa,don maganarsa a sannan daidai take da yana buga masa abu
me qara a kunne.
"Mato na hadu da 'yar damfara......na hadu da gagarumar barauniyar data yasheni tas......bama ni ta
yasheba tukunna......ta taba dukiyar kamfanin jadda ne!".
Zaro idanu mato din yayi waje yana janye jikinsa baya da sauri kaman yaga wani abun tsoro
tattare da mika'il din
"Anya yau bakasha barasar da kanka baya dauka ba?,kasan maganganun da kakeyi?,barauniya fa
kace,kuma macace?,sannan data tashi dukiyar Muhammed jadda ta kwashe?" Ya qarasa maganar
kaman zaiyi ruku'u. Ba kuma ruku'u din zaiyi ba,kawai yayi hakanne don ya samu damar ganin fuskar
mika'il dake zaune sosai,yanason kuma samun tabbacin maganar haka take ko kuma akasinta.
"Duk yadda kaji ka sake kuma fada hakanne" Ya fada a galabaice yana tsananta fatan samun mafita daga
wajen mato.
Ga mamakinsa sai yaga mato ya juya yana neman hanyar fita daga dakin. Da wani irin hanzari
mikail ya miqe ya damqo rigarsa yayi qarfin halin jawoshi baya sannan yasha gabansa
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 78
"Kai butulu......na dade da sanin alaqar bariki bata da riba.....kuma bata wanyewa lafiya
qalau.....amma inaso ka sani.....ni mikail baka isa ka gwadamin wannan halin ba saboda yadda kaci a
jikina,komai ka zama ta silata ne.....to ga hanya nan......kana iya tafiya......amma ka sani,wallahi.....wallahi
duk abinda zan shiga zan bada sunanka da tabbacin tare mukayi komai".
Ji mato din yayi kaman ya debo qarfe ya jibga masa saman kanshi,sai ya koma ya sulale ya zauna
"Ya zakayimin haka oga?,kasan tun safe naga qishin qishin abun?,ya baza jaridu da jafafen yada
labarai?,amma ban taba tunanin kaine a ciki dumu dumu ba?"
"Mune dai a ciki,kuma zanyi maka haka muddin kaima kayimin hakan". Ya bashi amsa kai tsaye yana
duban tsakiyar idonsa.
Wata wawiyar ajiyar zuciya ya sauke yana yin collapse. Nadama da dana sanin taba sanin mikail a
rayuwarshi tana sauko masa. Shikam ina zai iya tarar case da Muhammed jadda?,wanne ganganci ne ma
zaiyi saken da koda sunansa zai shiga list na sahun wadanda ake tuhuma.
Shuru yaci gaba da wanzuwa a dakin tamkar dukkaninsu ba xasu sake magana ba kafin mato ya
magantu
"Ita yarinyar wacece ita?,zaifi kyau kabi sawayenta ka bincikota ka damqawa jadda ita a sauqaqe su
tuhumeta". Wani banzan kallo ya watsawa mato
"Inda nasan ita din wace da ta yaya ma zan batawa kaina lokaci ina neman shawarar butulu
irinka?......tun haduwata da yarinyar na karanci tasha banban da sauran yammata dama mata gaba
daya.....tun daga yanayin kyau siffa da kuma jan ajinta......bata sake shallake tunani ba sai a yau dana
karade dukkan guraren da muka saba haduwa ko na saba ganinta amma na kasa zaqulota,......ta shafe
dukkan wani footprint nata,bani da sauran hanyar da zan iya lalubota".
Shuru mato yayi abun yana tsimashi shima. Duk iya yawan duniyarsa bai taba cin karo da abun
mamaki irin wannan ba.......duk budewar idanunsa da kuma son duniyarsa baiga gangancin da zai
sanyashi tunkarar fada ko jayayya da mutum irin muhammad jadda ba.....hakan daidai yake da saida
rai.....daidai yake kuma da Rungumar mayunwacin zaki. Amma irin wadannan maquden kudaden kuma
ace diya mace ce ta diba?.
"Me afkuwa ta afku yallabai.......yanzu lokaci ya qure ya kuma matse da zaka tsaya nemanta da bayyanar
da gaskiyarka.....don koda ka samota dinma ka gabatar musu da ita to ba shakka dole saika rasa
aikinka.....na tabbatar zasu sallameka ne". Wannan maganar ta mato ta sanya gumi tsatstsafowa mika'il.
Ya koma baya yana zama sosai tare da kamo habar rigarsa yana sharce gumin goshinsa.
"Don ubanka mafita nace ka bani bawai ka dinga haskomin makomata ba" Ya fadi da mugun tsaron ci
gaba da jin sautin xai rasa gurbin aiki da kamfanin jadda diamond rashi na har abada,bayan a nasa
mafarkin yana hangoshi ne wataran a kujerar CEO din ma gaba daya yana juya nasa kamfanin diamond
din.
"Mafita kam na samota......amma sai idan ka amince.......zaka juya hankalin kowa kayi wasa dashi.......ka
kuma binne batun kwashe kudin asusu ba tare da kowa ya fahimta ba".
Kaman an watsa masa ruwan sanyi haka yaji rahama tana sauka a zuciyarsa,baisan sanda ya
kama hannun mato ya riqe qam qam ba abinda bai taba yi ba tsakaninsu
"Dama za'a samu irin wannan hanyar na kasa yarda da ita mato?,maza gayamin......gayamin don Allah".
Hannunsa ya zame yana mamakin yadda yau masifa da bala'i suka sanya ubangidan nasa zama
maqasqanci a gabansa.
"Caca......a caca ne kawai zaka ciyo maquden kudaden da zaka iya cike babban gurbin da zai sauke fushin
me jadda daga kaso dari zuwa ashirin". Ido ya zubawa mato alamun me gama Fahimtarsa ba.
"Nasan baka gane ba ko?,me gida......kana da nasibin da muddin ka zauna teburin caca saidai ka kwashe
badai a kwashe ka ba,tunda kake baka taba zama teburin caca an cinye ka ba tsahon shekarun daka
dauka,saidai ma ka tashi da gwagwabar ribar dake lunka arziqinka.......wannan zaman da za'ayi a gobe
babban zama ne......akwai manyan gidadawan masu kudin da basu gama wayewa a sabgarba.....basu
kaika qwarewa ba,sun sanya mugayen kudade masu nauyi cikin cacar saboda romon bakan shigowarka
cikinta da nayi musu da yawan kudade masu nauyin gaske.......kudin da kowanne zai zuba ba qarami
bane me gida......kuma ina da tabbacin kaine zakayi nasarar wawashesu......ka zuba kudade sosai ka saki
jiki don ka sarqafo dukkan abinda zasu zuba.....bana jinka.....nasan da qwarewarka.....na kuma yarda
dakai".
"Nima na yarda da kaina" Ya fadi kai tsaye cikin confidence da kuma yarda da cewa lallai ba shakka
waraka tazo. Rungume mato yayi yana jin tsananin farinciki kafin ya sakeshi yana cewa.
"Muddin muka gama da wannan,na rantse da sarki Allah saina nemo yarinyar nan......saina nuna mata
cewa ita din ba komai bace cikin duniyar bariki,sai na bar mata tarihi,saina sanyata tayi danasanin
zuwanta duniya!!".
Tunda gari ya waye yake kwance kawai lamo,ita bame bacci ba hakanan ita ba idanunta biyu ba.
Su biyu ne a dakin tun bayan wucewar nadra da haneefa makaranta,tana daga parlor huda na cikin uwar
dakin qudundune a bargo da sunan bata da lafiya ba zata samu daman zuwa makaranta.
Ta shirya hakanne don tana sanya ran sabreen din zata fita ta barta a dakin kamar jiya,tasha hirar
soyayya da hameed dinta,wanda a yanzu duk duniya bata jin akwai sauti ko muryar da takai tasa dadi da
daraja.
Amma ga sabanin mamakinta yadda taga sabreen din kwance yana gaya matane ba lallai bane ta
fita ba yau din. Tayi tsaki cikin bargon yafi a qirga,tayi juyi daga hagu zuwa dama sau ba adadi. Tana iya
ganin yadda wayarta dake qasan filo keta haske alamun kiran hameed wato naseer ne yake shigowa
amma tsoro ya hanata dagawa.
A hankali a hankali ta dinga jin duk wata juriya tata tana qarewa,muradinta da burinta kawai shine
yadda zata samu taji muryar hameed dinta. Sannu a hankali ta dinga jin hirarsu ta jiya tana dawowa
_akan sonki bana tsoron kowa,zan kuma iya komai a gaban kowa saboda ke....zan iya sadaukar da komai
a kanki,zan kuma iya rabuwa da kowa,kefa?,zaki iya?,ki gwadamin wataran_.
Kalaman Hameed kenan ko yaushe a kanta. Muddin zai sadaukar har haka ita me zaya hanata ta
sadaukar?. Tambayar data yiwa kanta kenan,abinda kuma ya cire sauran dan tsoron dake ranta ta jawo
wayar ta daga ta kara a kunnenta.
"Har na fidda rai.....huda kina azabtar dani,kullum kafin na samu jinki sai nasha baqar wuya?,sai na shafe
awanni ina lalubenki?,bayan ni ko agaban waye bana iya wofantar dake huda?,koda waye a wajen zan
ambaceki zan kuma yi waya dake.....me yasa huda ni bazakimin wannan sadaukarwar ba?". Yadda yayi
maganar sai ya bata tausayi sosai,harma taji tana zargin kanta daqin daga wayar tasa tun dazu
"Allah huda idan aka wayi gari na mutu sonki ne ya kasheni" Duk wata tsiga ta jikinta sai data
zuba......son da yake mata wai da gaske ne har yakai haka?.
"Kina mamaki kuma kina musu ko?,kinason tabbatarwa?" Cike da quruciya da rashin sanin kan rayuwa ta
furta masa
"Eh"
"Nan da kwana uku xan dawo ya kama ranar Monday,zaki yarda na shigo makaranta na daukeki?.....zan
kaiki inda zan nuna miki zallar soyayyata a gareki ki ganta quru quru.....kin yarda kinaso ki gani tawan?".
Sai ta narke wuya zuciyarta na karkata gason ta gani din. Can qasan ranta kuma fal mamaki,tadai kusa
ganin wannan soyayyar da yaketa faman zuguiguita mata ita......ta kusa ganin soyayyar nan dai da takeji
anata magana a kanta.
"Zan miki tanadi na musamman,zaki gani da idanunki.....daga ranar nasan ba zaki sake musu shakka ko
kokwanto ba". Janta yayi zuwa cikin hirar sosai duk da sama sama take amsa masa a darare amma hakan
bai dameshi ba,sake jan ra'ayinta kawai yakeyi,yana kuma sake dulmiyata cikin kogin qaunarsa.
Kadan kadan takejin motsi daga dakin,to amma sai kunnuwanta sukafi tafiya zuwa tsakar gidan
gidan nasu. Don ta tabbatar huda bacci takeyi ko sanda ta fito,ta share wannan maganar tana dauko
wayarta ta lalubi number jib.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 79
"Allah dai yaja kwana hajjaju......our young hajiya" Jib din ya fadi cikin fara'a.
Karamin tsaki taja tana kauda zancan,haka kawai ita batajin komai akan kudin,bata kuma jin wata
walwala. Duk wani tsari da jib din yakeyi mata tana jinsa ne kawai,don nata lissafin duka ba'a wannan
bangaren yake ba.
Uwa uba shi Kansa jib din bataji ya tsarawa kansa komai ba,ita kuma yanzu su dinne a gabanta da
sauran yara marayun nan da take kwana dasu ta kuma tashi dasu cikin ranta.
"Ka sameni gidan marayun nan,zamu qaraso nida busari" Ta bashi saqon a taqaice
"In sha Allah" Ya fada mamakin halayenta suna sake ninkuwa a ranshi.
Kafin ta ajiye wayar tahau ta daya sim din data saba neman busari,ta tura masa saqo sannan ta
ajiye wayar tana dan furzar da iska daga bakinta gami da zubawa labulen qofar falon idanu kamar me
nazari akan yadda aka sarrafashi.
Kadan kadan ta dinga jin kamar dai motsinne daga dakin da kaman sautin murya a can qasa. Tun
tana basarwa har ta miqe,ta taka a hankali ta soma nufar dakin.
"Eh" Kalmar da aka fadi qasa qasa ta shiga kunnenta sanda ta yaye labulen dakin. Hasken daya ratso
falon zuwa uwar dakin ya ratsa blanket din da take ciki ya kuma alamta mata wanzuwar wani a dakin,sai
tayi wata mutuwar kwance zuciyarta tana tsananta bugawa ta latse wayar tana turata tsakanin katifar da
bagon gadon. Daqyar take iya hadiyar yawu saboda tsoro,tun yaushe nema aka shigo bata sani ba,kada
dai ace ta jima a tsaye tana jinta?,wannan tunanin kadai ya sanya jikinta jiqewa da gumi kamar an watsa
mata ruwa.
"Keda waye kike magana?" Sabreen ta jefa mata tambayar tana zube mata idanun nan nata masu kaifi.
"Magana kikaji yaa sabreen?" Shuru tayi dajin tambayar datai matan,sai ta girgiza kai alamun aah bayan
ta gama qare mata kallo
"Wannan gumin fa?,ko zazzabi kikayi ya sauka?" Ta sake jefa mata tambayar amma wannan karon da
salon son kamo abun farauta
"Eh.....eh nima haka naji" Idanunta ta maida ta lumshesu sannan ta bude. Ta gama bata hint,ta kuma
gama hada dukkan wasu abu da takeso,ta sanyata a ajujuwa kuwa tun daga sauyawarta zuwa yau,kuma
ta fadi a kowanne aji......tana jin sunzo matakin qarshe ita da ita,sai ta sake mata blanket din,ta juya tana
takawa a nutse zuwa inda take adana kayan wankanta ta diba tana fita a dakin.
Da wani malalacin kallon ta bita har ta gama ficewa,haka kawai taji kaman akwai wani abu ba
daidai ba
"Idan ma akwai.....idanma kuma ta gane aiba wan sabon Allahn kikayi ba" Wannan tunanin ya bata
qwarin gwiwa ta tabe baki,ta maida kanta filo tana jin yadda zuciyarta ke bugawa sosai,daga bisani kuma
ta koma tunanin hirarrakinsu da hameed kaman yadda ta saba.
Cikin qanqanin lokaci suka isa babban gidan kula da marayu,wanda yana cikin gidajen da suke
karban kaso mafi tsoka daga dukkan abinda ta samu.
A yau din kabakin arziqin data kai musu ya faranta ran kowa. Hakanan list da tayi na abubuwan da
zata aiwatar musun ya sanya kowa kokwanton anya da gaske take?. A duka shekarunta ina taga adadin
wadannan kudaden?. Ayyuka ne da zasu canza fasalin gidan gaba daya ya canza cimarsu harma karatun
yaran gidan. Tsari ne kuma data dauki sunayen 'yammatan ciki da suka isa aure suke da buqatar tallafin
kayan daki da kayan kitchen harma da suturar fitar biki. A ranar gaba daya gidan a yamutse yake da
tsananin mamakin ayyukan da tace zatayi din. Saidai daga bisani shigaban gidan ya basu nutsuwa ta
hanyar fadin
"Ta iya yiwuwa 'yar wani hamshaqin attajirin ce mu bamu sani ba ta bad da sawu,ko daga suturar jikinta
da fatarta zakasan cewa kaman hakan zai yuwu,kudai godewa Allah daya turo me dauke mana
damuwarmu koda yaushe,gashi a wannan karon bayan tallafin data saba bayarwa zata mana aikin da
mutanen dake da ikon yi masu yawan gaske suka gaza yi mana......zata mana aikin dana tabbata muddin
ya tabbata matsalolinmu masu yawa zasu kauce".
Ta yita share qwalla me yawa a hanyar komawa gida,yaran suna mata gizo cikin idanuwanta.
Wato maraya a wannan zamanin daidai yake da wani abu maras alfanu cikin al'umma muddin ba dukiya
aka mutu aka bar masa ba?,hankula da idanuwan al'umma duka sun toshe?,me arziqi shine mutum?,me
arziqi shike da amfani?,idan yau kana da abun hannu kowa qoqarin rabarka yakeyi?,kowa so yake ya
hada dangantaka dakai komai qanqantarta?,kowa so yake ace kuna da alaqa kunsan juna?.
Anya mutane a yau kuwa sunsan iya adadin bala'i da masifar zubar ruwan hawaye a idanun
maraya qwalli daya tak a garesu?,anya suna tunawa da girman haqqinsa da ma'aiki yayi gargadi da jan
kunne akai?. Bibo ta fado mata a rai,saita dinga juya kai kawai,matar tana daya daga cikin mutanen da
zasu azabtar dasu tsananin azaba inda Allah ya qaddari mutuwa ta dauke ummeensu a sanda suke
dukkaninsu qananu......arrahmanu arraheem ubangiji da baya hadawa bawa abu biyu......sai ya dauke
musu sanyin idaniyarsu a sanda ita nata hankalin da qarfin ya fara kawowa. Ya sanya mata qarfin zuciya
da kuma qarfin halin iya tare musu tashin hankali da masifa komai girmanta,ya sanya rainonsu da kulawa
dasu a hannunta tun bata wuce itama a raineta ba.
(YAKE BAIWAR ALLAH!....tabbas riqo yana da wahala.....riqo yana da daci yana da nauyi,amma
kisani......DA KI RIQE YARO KI AZABTAR DASHI GWARA KI TUN FARKO KICE BA ZAKI KARBA RIQON BA yafi
miki sauqi da mafita har a wajen Allah muddin kikasan zuciyarki ba zata iya jure da kiyaye wannan
amanar ba.....AMMA WALLAHI
WALLAHI
WALLAHI kikayi kuskure kika karbi riqo don ki burge ko kada a zargeki,to wallahi idan nace KINA CIKIN
MASIFA ma kadan ne.....ba zaki san girman bala'i da kike ciki ba sai ranar gobe qiyama......hatta ubangiji
bayason kuka maraya shi da yayi kowa yayi komai ya kuma qaddara hukuncin maraici a kansa
IDAN KINSAN akwai maraya yanzu haka da kike banbanta riqonsa dana 'ya'yanki.....to ki gaggauta yiwa
kanki hisabi tun kafin ranar zuwan hisabin na gaske.......idan har kinsan akwai maraya yanzu haka a
hannunki.....to ki gaggauta gyarawa kafin ki barwa 'ya'yanki masifa da bala'in da zaiyita bibiyar
rayuwarsu,kiyi qoqari kifi qarfin wannan tsokar dake qirjinki wadda ake kira da ZUCIYA.....kiyi qoqari kifin
qarfin wannan maqiyin naki wato SHAIDAN.....Allah ya bamu ikon fin qarfin wadannan ababe guda biyu
ameen summa ameen).
"Kaini gidan malam" Ta fadiwa busari a nutse,wanda bai musa ko ya tambayi ba'asi ba ya karkata akalar
motar. Zuciyarsa shima cike take da farinciki,don yana cikin alherin tashi daga dan adadaita sahu,zuwa
mamallakin shago sukutum da guda a babbar kasuwar kantin kwari nan da sati uku kacal.
Kusan duk wanda ya kwana ya tashi a kamfanin yasan da faruwar komai. Yayin da sake fitar labarin
boyayyar badaqalar data afku qasa da wasu awanni ya sake sanya mutane da yawa na kamfanin mamaki
musamman wadanda basu san komai ba,basusan kuma abinda ake ciki ba.
Kowa da kansa da kansa ya yiwa hisabi,don shigowar boss Muhammad kamfanin ya sake sanya
kowa shiga taitayinsa. Masu zuba kunnen abinda zai faru da kalar matakin da zai dauka suka ci gaba da
sanyawa,yayin da a nasa bangaren ya nutsa cikin bincike tare da tattaunawa da taimakon dan uwansa
kuma shaqiqinsa farouq.
Ganawa ce takai tsaye kuma da mutum na farko bayan shigarsa kamfanin da sukayi da manager
din banking da yake mu'amala dashi,wanda suka iso su uku da biyu cikin nasu ma'aikatan. Hankalinsu
kusan yafi na fuad tashi,don sun sani ba qaramar nasara bace ace kamfani kamar wannan yana da asusu
dasu,hakanan kuma....gagarumar asara da faduwa ce ace a yau ya rufe account dinsa dasu sanadiyyar
wannan.
"Baku da laifi sir......coz kusan sai aka shigar da komai da ake buqata da zai bawa mutum damar
accessing da account din sannan kuka bada damar fitar kudin......inda kuskuren yake shine......amount
din da aka fidda din ya cancanci ace anyi alerting namu kafin a bada daman fiddashin.....saboda akwai
hanyoyin da mukebi wajen fidda kudade masu nauyi irin haka........kuma kun san da
hakan......anyway...sakacin security team namu yafi na kowa.......sai kuma ma'ajij company da yake
number one" Ya qarashe maganar yana komawa ya zauna sosai yana gyara wuyan suit nashi.
"Hamma......mun gaza samun mikail har yanzu mu shaida masa zaman da za'a yi yau din". Kansa ya
gyada
"Kar damu dashi......idan inason ganinsa ko ina ya shiga zan sanya ne a kawomin shi.......but nafison ya
kawo kansa da kansa in a legal way.....ka rabu da nemansa"
"Okay" Ya fadi cikin gamsuwa. Ya yadda da hamman nasa,ya sani ba ordinary mutum bane
tuntuntuni......bayajin a yanzu ko farouq zai gaya masa wayeshi saboda kaf gidan yafi kowa kasancewa
dashi cikin awanni masu yawa. Fara aiki dashi ya sanya kullum kwanan duniya yake sake shiga ransa.
Baisan haka hamman nasa yake da shiga rai ba sai yanzu......baisan haka kyakkyawar mu'amala take
yawo a jininsa ba sai yanxu da aiki yake hadasu adadin awanni masu yawa.
Hannu ya miqa ya karba file din da suka iso masa dashi na dukka bincike da nasu bibiyar da sukayi.
Kusan wasu guraren abubuwan da suka bincika yazo daidai da nasa,wani gurin kuma sun kasa accessing
information din jibril wanda shi a yanzu haka yana da komai. Abu daya ya kasa yarda dashi shine......jibril
bashi kadai yayi wannan aikin ba.....dole akwai wani a tare dashi......wanin kuma yana qarfafa zargin
muddin ba mikail bane da kanshi ya dauki duka information din ya miqa musu da zummar cin amana
ba......to na jikin mikail ne wanda yake tare dashi.
"Mr Joshua mamallakin bankin yana miqa jajensa......yanzu haka yana hanyar zuwa kowanne lokaci,da
fatan zaa karbi baquncinsa". Wani abu me kama da murmushi kawai yayi yadan dage kafadarsa,sukayi
sallama dashi ya fice.
Iska me zafi ya fitar a bakinsa,ya miqe yana zare suit din jikinsa na saman ya ratayeta a muhallin
da aka tanada don ratayewar. Ya duqa yana zare takalmin qafarsa hadi da magana da saddiq
"Good......yanzun security team kawai nakeson gani,kayi cancel sauran staffs......infact ma banason susan
da zaman.......ina da buqatar binciken sirri a kansu don dole mu nemo me fidda mana information......ka
gayawa me sunan malam immediately after meeting inason ganinsa"
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 80
"Done" Ya fada kaman yadda ya saba. Daga kai farouq yayi ya kalli saddiq din
"Kalleshi kaman mutumin kirki........ya addabemu cikin gida......sai yazo company sai ya zama wani me
biyayya.....thank god da Allah ya hadaka da fu'ad......da nine da tuni ka kusa sakamin hawan ruwa" Ya
qarashe maganar yana daukan gorar ruwan da fu'ad ya dauko musu saman table yana mamakin yadda
qananun hidima na cikin office yake yi da kansa,duk da cewa yana da qarfin ikon da ko taka qasa yace
bazaiyi ba akwai masu yi masa.
"Bakasan mutane da yawa da suka fiya wasa ba suna da wani boyayyen talent?".
"Talent a wajen wa wai?,wannan?,kawai dai Allah ya tattaro mana shi da taimakonka" Ya fadi yana bude
murfin ruwan. Bai amsa ba fu'ad,yadai saki siririn murmushin da ba lallai ka iya fahimtarsa ba yayi
bismillah can qasa ya soma zuqa a hankali.
Kafin yakai ga dire cup din kira ya ratso wayarsa,saddiq yafi kusa da ita don haka yace
"Kai dauki kace mata lokacin aiki ne yanzun" Kai fu'ad ya girgiza da sauri yana aje ruwan. Wayar ya miqa
masa,ya sake duba kiran sannan ya daga
"Ban tambayeki ba amma kina raina amna.....wani muhimmin abune ya taso.....kiyimin addua,ki gayawa
anni ma idan tazo sallan dhuha tayimin addu'a.....but karkice mata wani abu ne ya taso,just kice munyi
waya nace tayimin addu'a during salat of dhuha".
"Hala rival dina baya kusa hamma......yaji da kunnensa sunan dai nawa ne"
"Karki bari na dawo gida na iskeki....." Saddiq dake gefan fu'ad ya fadi da sauri. Kai ya daga fu'ad din ya
jefa masa harara
"Sorry sir" Ya fadi yana shafa kansa. Abun ya yiwa amna dadi,yana iya jiyo qaramar dariyarta har ya katse
kiran.
"Baka hasko komai game da mikail ba?" Farouq ya jefa masa tambayar sanda yake qoqarin duba wani
saqo daya shigo system din nasa daga department na wanke dukka diamond din da aka haqo don
tabbatar da kyansa da ingancinsa.
Fararen idanunsa kewayayyu da hasken system din ya qara haskewa ya daga ya dubeshi na wasu
sakanni sannan yace
"Kai me ka hango?".
"Guy din bashi d gaskiya kwata kwata.....and ina kyautata zaton yana da masaniya akan komai koda bada
saninsa akayi ba".
"It's true.....ni tun tafiyarka South Korea na karanci abubuwa masu yawa game dashi,bamu samu zama
bane yadda naso har wannan abun ya faru......amma bari mu fita a meeting dinnan"
Wata irin zazzafar tattaunawa ce ta wanzu tsakaninsa duk wani dake under security team. Jiki da
zukata sunyi laqwas da wani irin tsoro da kuma firgici. Bacin ran da suka gani a fuskar boos din nasu ya
sanyasu cikin tashin hankali,domin kuwa wani abune da basu taba ganinsa a tattare dashi ba.
Dukka bayanan da suka bashi kusan yazo iri daya akan nasa da wanda baki suka bashi,saidai
akwai wasu sauye sauye cikin nasu
"Na baku 2days to find full details na dukka team din da sukayi wannan aikin......na tabbatar ba aikin
mutum daya qwal bane......team work ne tabbas!" Ya fadi yana doka file din saman table din da yake kai.
Zuciya da qwaqwalwarsa duka a zafafe ya dawo office,yayi nufin yin alwala don yayi salat dhuha
kaman yadda ya saba sai yaga lokaci ma duka ya qwace,duk da haka bai fasa daura alwalar ba saboda ita
kadai tana saka masa sanyi cikin zuciyarsa
"I need rest please.....duk meson ganina ka gaya masa sai after one hour......kayi shutting komai saina
nemeku" Yayi magana da mutanen dake tare dashi. Da daya da daya kowa ya fice har saddiq. Farouq ya
miqe a hankali
"Ina zaka kai kuma?"
"Zan bar CEO ya huta haka nan......da gaske brain dinka yana buqatan shuru na wasu lokuta".
"Ko zan huta da ganin kowa banda kai farouq" Ya amsa masa yana jingine bayansa jikin sofan da ya
canza mata siffa daga kujera ta koma qaramin gadon hutawa cikin sakan talatin.
"Na sani.....but now dai dole farouq yadan matsa kadan Shima.....zanje nayi waya da fanna......yau duka
ban kira naji lafiyarta ba". Kiran sunan fanna kawai da yayi ya sanya ya daga masa hannu ba tare da yace
masa komai ba,sai ya sake sakin qaramar dariya yana takawa
"Anyi zancan SOYAYYA zaka birkice.....bari na qara matsawa da hanzari......hala daya cikin matan naka ne
ma zasu kawo maka ziyara". Yayi zancan yana kaiwa qofa.
Maganarsa ta sanya fu'ad sakin murmushin dole duk da bai shirya ba,sai ya bude idonsa a hankali
yana bin bayan farouq da kallo har ya qarasa ficewa,ya maida idon ya rufe bayan ya saita security na
qofan nasa da wani qaramin remote a gefansa ta yadda babu me iya damunsa,duk da ya bada warning
ma reception nasa da kuma saddiq. Shi a wannan ire iren situation dinma idan har yace soyayyar zaiyi
baisan ta yadda zai fuskanceta ba.....baisan ma ta inda zai kwasota ba. Yasha ji daga bakin farouq rashin
bada kulawa da bada lokaci yana kawo macewar soyayya.....shi kam ya tabbatar wannan shine dalili na
farko da zai saka tasa soyayyar mutuwa murus. Ya tuna 'yammata biyu da farouq ya takura ya
hadasu.....abinda dukka ya rabasu dashi shine lack of caring. Sometimes ma mantawa yakeyi da
babinsu,koda kuwa ta hanyar tura tex bare kira bare aje gayin tattaki zuwa gidajensu. Da kansu suka
fahimta baida lokaci,suka kuma samawa kansu salama zancan ya mutu murus,shima suka shafa masa
lafiya.
A hankali kekenapep din ke gangarawa da ita layin gidan malam din,ya kuma tsaya daidai gidan.
"Na gode......kana iya tafiya,gobe idan Allah ya kaimu zan nemeka saimu qarasa komai,ka gaida ummaah
da kyau"
"Zataji in sha Allah....tace zatayi tattaki da kanta don miki godiya". Murmushi kawai ta saki tana sauka
daga napep din,idanunta kan muhallin da malam ke bada karatu. Ba jamaa wajen,ta kalli agogon
hannunta,da sauran lokaci akan lokacin daya saba xama,sai ta taka a nutse tana wucewa cikin gidan.
Kamar kullum ta taras da rumasa'u tana aikace aikacen gida,matar malam na daga rumfarta a
zaune tana tsince busashen zogale.
"Maraba da diyata" Ta fadi cikin fara'a da murmushi tana sauke farantin zogalen daga cinyarta gami da
karkade zaninta da ya d'an baci da kadan. Har qasan zuciyarta kuma tana jin dadin dawowarta da
wuri,ba kaman wancan karon ba data tafi ta jima bata waiwayosu ba.
Itama tata fuskar da murmushi tare da jin dadin yadda aka samu wasu halittu da suka damu da
rayuwarsu ta qarasa shiga cikin rumfar,bayan ta zame halfcover din qafarta
"Aah.....ina sauran jikokin nawa?" Ta furta tana duban bayan sabreen. Murmushi ta saki tana zama
saman shimfidaddiyar daddumar da matar malam din ta shimfide mata
"Ba daga gida nake ba gwaggo" Ta fada Kaman yadda taji rumasa'u tana kiranta wani lokaci.
"Kash.....to ai naso ganin kishiyata haneefa ne ai" Ta furta tana dariya tare da yunqurin miqewa
"To Allah ya yarda" Ta amsa mata tana bude fridge din dake ajiye a rumfar gaban falonta ta ciro mata
ruwan pure water me matsakaicin sanyi da lemon zobo,rumasa'u ta hado da kofi ta shigo mata dashi.
"Nima inata sanya ido naga huda" Ta fada tana murmushi. Kiran sunan hudan ma ya sanya hankalinta
dawowa kan huda din data barosu gida.
Zama tayi suna dan taba hira,tana son su sabreen yarinyar,wanda su kansu basusan dalili ba,saidai
ba ruwan ubangiji shi yakan sanya qauna da jituwa tsakanin bayinsa a duk sanda yaso hakan ya kasance.
"Yana nan,yadan fita ne kasuwa,amma da wuri yau din zai dawo,yana da karatun dare na manya da
yakeyi". Kai ta jinjina,tana jin dole zata jirashi har ya dawo,duk da tanason komawa gida da wuri,don a
yanzun hankalinta bai bata ta dinga nisan kiwo ba.
Jikinta da zuciyarta sun gaza samun nutsuwa sam sam akan huda,cikin jikinta takejin akwai wani
abu ba daidai ba.
Iya yadda tayi magana da ita dazun kawai ya isa gaya mata akwai wani abu,saita rufe babin
wannan tunanin tana maida hankalinta tsakar gida hadi da taya su gwaggo amsa sallamar malam din.
*Tsaye yayi kawai gaban madubi yana duban fuskarsa da kyau tare da son bawa kansa qwarin
gwiwa. Yana buqatar cikakkiyar nutsuwa da kuma qarin tattara dukkan wani tsohuwar fasaha da
qwarewarsa wajen ganin ya cimma nasara a cacar. Tunda yake bai taba caca mafi hatsari ba irin wannan.
Caca ce da zata iya zuwa masa da sakamako guda biyu......nasara wadda zata wankeshi daga dukkan
wani rudani da tashin hankali.....ko kuma faduwa wadda daidai take da daukan guduma ta kuma
tarwatsa rayuwarsa gaba daya.
Hasashen sunan faduwa kawai sanyawa zuciyarsa wani irin mugun bugu yakeyi,tuna sunan
FADUWA kawai sai yaji kaman qirjinsa zai tarwatse,don haka a yanzu da yake tsaye gaban madubin ya
daga murya don baiwa kansa da kansa tabbaci tare da qwarin gwiwa
"Ba faduwa a hanyata,tabbas nike da nasara......ni zan cinye!" Ya fadi da wani irin qaraaji yana sake
sanyawa ransa nasarar da gaske tasa ce.
Qofar aka dan qwanqwasa,ko ba'ayi magana ba yasan waye,don haka ya waiwaya yana fadin
Baice da mato komai ba ya bude gaban motar ya shige,mato kuma ya bawa motar wuta,ya
danna hon me gadi ya dage musu gate din suka fice.
"Ina fatan yau baka shawu ba" Mato ya fada yana sake bawa motar wuta saman kwalta. Harara ya
waiwaya ya maka masa kafin yace
"Mahaukaci ne ni?,idan nasha ta yaya zan samu isa ga abinda nakeso?,......zan shawu iya shawuwa
bayan mun dawo da talin himilin kudin da zan cike gibin asarata". Kai mato ya jinjina yana dan dukan
steering
" Inaji a jikina kam wannan nasarar tana hannuwanka......munkaila me da'ira?.....ka manta sunan naka
ne?". Wata wawiyar dariya ya saki,sunan da mato ya tuna masa ya sake jinsa cikin alfahari......wani
rubutaccen suna ne daya samoshi daga wajen abokan cacarsa. Muddin zai hau tebur din caca to ko kai
waye ka zama nama,baisan iya adadin abinda ya tara ba da dukiyoyin al'umma shekara da shekaru,sai
yau gashi dare daya wata qaqqarfar guguwa tanason yin gaba da tsohon arziqinsa?......inaaaa......ai
bazaya bari ba,sai inda qarfinsa ya qare. Iya sunan da mato ya gaya masa ya sanya masa qarin karsashi
tare da jin dokin isa wajen.
"Ni kaina inaji a jikina lokacin nawa arziqin ya gabato,don gagarumar caca ce ina gaya maka me
gida.......tsaffin 'yan caca za'a zuba wadanda suka sanya kudi masu ciwo......don Allah banda ganganci ina
tsohon hannu zai kara da sabon jini?,yaro masanin dabaru da siddabarun kayar da mutum?"
"Tsautsayi ne mato" Ya bashi amsa wani murmushi yana subuce masa,don nasararsa kawai yake hanga
muraran.
Tafiyar mintuna kadan suka isa gidan cacar,tun daga waje ya fahimci gidan a cike yake,abinda ya
sake tabbatar masa da maganar mato. Ya fito a motar yana murmushi suka jera da mato zuwa ciki yana
sake bashi bayani akan komai.
"Har gwara ya nemeni da wannan shurun da yayimin......shirunsa yana nufin komai mato......shi yasa
nake bidar nasara a wannan karawar.......daga nan wajensa zankai kaina ayi a gama......bani da tabbacin
a yanzun baida masaniyar inda nake.......tsaf yana sane da motsina duka zai iya yiwuwa". A mamakance
mato ke duban mikail,tsoron girman izza da qarfin ikon Muhammed jadda tana sake saukar masa,saidai
bai samu cewa komai ba suka qarasa ciki.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 81
Daga yadda yaga wajen ya sake amanna da maganganun mato din. Duba daya ya fahimci tabbas
masu tsohon arziqi da kudin caca ne,kuma da alama a yau din kowa cikin buri yake,hakanan kowa yayi
guzurin dukka wata dukiya da yake alfahari da ita.
Saura kadan dariya ta fashe masa,don dukkaninsu shi a nasa idanun kallon gidadawa yake
musu,kuma cinyayyu da zasu qare wasan cikin hasara da rashin nasara.
Su biyu rak ke zaune daga wata kwana cikin farfajiyar wajen. Kawu kenan,wato kawu sama'ila shi
da nasa aminin barau.
Cikin nutsuwa da shegen kwanyar da yake dashi yake karance mikail da idanunshi sunkai kan
kawo amma banda kan kawu din. A nutse yake karantar mukail,har zuwa sanda suka zauna da'irar da
za'a zuba caca ta farko.
"Me ka karanta ne sama'ila?,kayi shuru ko ka fasa ba zaka buga wasan ba?" Murmushi kawu ya saki yana
tura hularsa gaba.
"Tun bayan mutuwar yaya daya haramta min yin caca,ban qara zama gagarumar caca irin wannan
ba.....inaji a jikina silar arziqina ne yazo.....bazan zauna ba har sai naga iya nashi takun......baka ruftawa
wasa baka san yanayin hannun kowa ba"
"To me ka fahimta sama'ila?" Barau ya sake tambaya idanunsa akan yadda wasan ya fara tafiya
"Dan zamani ne fa wannan da zai kara da tsaffin 'yan wasa......gogagge ne kana kallonshi,kuma shima
qwararre ne da irin tasa qwarewar,wanda idan kowa baiyi takatsantsan ba komai zai iya faruwa"
"Ka zuba ido kawai kayi kallo" Ya amsa masa yana maida hularsa daga gaban goshi zuwa qeya.
A duk sanda yakeson samun nutsuwa ta qwaqwalwa da ruhi sararsa shine kwanciya,ya rufe
idanunsa yayi kuma shuru a waje da muhallin da ba hayaniya ko kuma motsin kowa. Ko yanzun hakan
yayi cikin office din,saidai qarar wayarsa ya sanyashi miqa hannu ya lalubota don yasan ring din na daban
ya sakawa kiran don kirane da yake buqatarsa
"Yes sir" Ya furta cikin girmamawa. Wayar ya ajiye,sai ya miqe a nutse ya zauna ranshi na wani
mahaukacin baci. Ga wani zargin ya sake shigo kasa akan mikail yanason kore uzurin da zuciyarsa keson
bashi. Muddin ya kuskura bincike yazo masa caca yayi da kudinsa na halal tabbas!,zai nuna masa ainihin
kalarsa......zai gane waye zahirin muhammad jadda. Dukiyar da aka tarata da gumin halak?,dukiyar da
ake takatsantsan wajen jefa haram a ciki komai qanqantarsa?,kudin ruwa da ruba dukkaninsu
haramtattu ne a cakudasu cikin dukiyarsa,amma yau din zanyi ganganci ko kuskuren zarar halalinsa ya
jefa a qazantaccen guri irin wannan?.
Tsam ya miqe,sai ya koma saman table dinsa ba tare daya sanya takalma a qafarsa,ya kunna
system dinsa ya tattara hankalinsa akai.
Karo na kusan goma barau ya kalli kawu sama'ila kaman yadda mato ke zaune yana murmushi
daga gefan mikail yana kuma tayashi lissafin maquden kudade da dukiyar da yaketa cinyewa ta abokan
bugunsa.
"Sama'ila?,dama wannan shine hasashen naka?". Murmushi kawu ya saki yana karkacewa kaman abun
ya masa dadi
"Gaskiyar kenan barau.....amma barshi ya gama iya tasa dabarar......uwayensa na nan zuwa su koyar
dashi darasi" Wata dariya barau ya saki bayan ya gama fahimtar abinda kawun yake nufi
"Yanzu naji batu,amma ta yaya muna da kai zaka bari wannan jaririn yazo gidanmu ya cimu wasa?"
Murmushi ya sake saki idanunsa akan mikail daidai sanda ya cinye alhaji wada miliyoyin kudi
"Talala ce me kaman sake.....barshi ya gama karbarmin kudaden tukunna da gidajen" Dariya barau ya
sake saki harda buga qafa.
Cikin awa uku ya daurewa kowa jijiya a wajen. Cikin tumbatsa da izza mato ya miqe
"Akwai wani sauran wanda zai kara da sarki?" Yayi shela yana ji a ransa sun gama da kowa,babu me
sauran motsi. Shuru ne ya biyo baya,sai ya sake maimaita tambayar yana duban kowa d'ai d'ai
"akwai" Barau ya fada da qarfin murya. Mato da mikail din duka suka waiwaya suna duban kawu dake
qurya,sai suka dubi juna tsakanin mato din da mikail
"Waye kenan a cikinku zai shiga?" Tsam kawu ya miqe yana nuna kansa
"Nine" Ido suka hada sai suka bushe da dariya tsakanin mato da mikail
"Qaraso mana dattijo....koda yake ba dattijo a nan......inajin akwai rabona a jikinka ne kaima.....ko giya ta
kwana daya na sha da canjinka". Boyayyen dariya kawun ya saki,ya fara takowa zuwa wajen kowa ya
zuba masa idanu yana mamakin qarfin halinsa,kamar ba'a gabansa aka cinye kowa ko ba amma shi zai
jefa kansa?.
"Dame zaka shiga?" Ya jefa masa tambayar a raine. Karkacewa yayi ya zaro wasu takardu yana dubansu.
Takardun dake dauke da sunan alhaji aliyyu ahmad zaki......mahaifi ga sabreen..... Takardar dake
matsayin mallakin magadan kuma marayan yaran da yayi Qundumbalar shiga cacar da ita,cikin jin cewa
zata ciyo masa tarin maquden kudaden da zasu zame masa silar arziqinsa gaba daya.
Saman teburin ya aza takardar yana kallon mikail,hannu ya sanya ya dauka ya duba ya karanta ya
kuma tabbatar original ce wanda gidan ya haura miliyoyin kudi
"Ashe.....kudinka baaba ai ya haura 'yan canji ma ai.......idan na samu nasarar cinye gidan nan
ko?,rusheshi zanyi na maidashi gidan shaqatawa,ayita shigomin da 'yammatan unguwa ina hutawa dasu
ina biyansu".
Wani abu ne ya cakewa kawu a rai,ya tsani zina,ya tsani harkar neman matan banza,kaman yadda
ya tsani shaye shaye,barshi kawai da cacarsa data zame masa masifa wanda dama tana da shiga jiki. Kai
tsaye yaji tsantsar cin fuska ce ya tanadeta zaiyi musu wannan ya sake aza wutar qaimi a zuciyarsa,ya
karkace kaman yadda yakanyi a yanayi irin wannan,ya kalli Mikhail da kyau
"Idan dai har ya zama mallakin naka kana da wannan damar" Ya bashi amsar da wani irin kakkaifan
kallon dake gaya masa kai tsaye na SAI NA BAKA DAMAR CINYE GIDAN SANNAN ZAKA AIKATA HAKAN.
Izza da jin cewa zai samu nasara akan kawun ya sanyashi ninka abinda kawun ya zuba shima ya
zuba cikin cacar aka fara buga wasan. Tashin farko kawun ya maido takardun gidan yayi tafiyar ruwa da
kudaden da mikail ya zuba,abinda ya jawo hautsinewar wajen,hankula dukka suka komo wajen,aka fara
yo dafifi,wadanda aka cinye suke alhini dukansu karsahinsu ya dawo,sai aka fara zuba sabon wasa.
Da daya da daya ya dinga zuba abinda ya ciyo kawu sama'ila yana kwashewa. Duk abinda ya zuba
kawun ya cinye shaidan zuciya da kuma mato saisu gaya masa ya sake zuba wani,zai iya yuwuwa ya
samu nasarar dawo da abinda aka cinye masa a baya.
Tafi tafi cikin qasa da awa biyu sai gashi yana tashi daga Mikhail me manyan kudi yana komawa
asalin mikail dinsa kaman yadda ya shigo wajen. Cikar awa biyu cif komai ya qare!.kawu sama'ila ya
wawushe duk wata kadara daya cinyo daga wajen wasu ya zuba!,ya koma tsurar yadda ya shigo musu a
wajen!.
Sowa ihu murna da tafi ya cika wajen,ainihin sunan kawu sama'ila na teburin ya soma dawowa
bakunansu wato DA BANBANCI!.
Kowacce tsiga ta jikin mikail zubawa takeyi. Idanunsa sun kada sunyi jazur,jijiyoyin kansa sun fito
rada rada. Sosai yakejin ya muzanta,ya toxarta. Ta yaya zai bari wani qaramin alhaki tsohon daya bashi
shekaru masu tazara ya kafa tarihi a kansa?,tarihin da muddin ya bari ya tabbatu a haka.....to ko shakka
babu ya xubar da kimarsa da kwarjininsa a idanun abokan cacarsa dake bashi wani irin girma. Karon
farko a rayuwarsa da wani yayi nasara a kansa,shi kuwa ta yaya zai bari haka ta tabbata?.
"Ga wasu kudaden na zuba.....azo a sake zama!!" Ya furta da qarfi,sautin daya sanya wajen yin dif aka
zuba masa ido.
Da sauri mato ya kalleshi,ya kuma ja hannunsa da qarfi yana dubansa qasa qasa
"Wanne kudi kuma ya rage maka indai ba motar da mukazo a ciki ba zaka saka?"
"Qyaleni mato.....bakajin habaicin da suke yada min?,dole na aje musu tarihi,dole sunan mikail suma yaci
gaba da wanzuwa a kunnuwansu da bakunansu da wajen cacarsu".
"Ragowar abinda aka bari a asusun jadda" Ya fada yana jin zuciyarsa ta qeqashe,kuma tabbas wannan
kudin xai dawo da sauran kudin da duka narke,duk kuwa da yasan mugun gangancin dake cikin aikata
haka.
"Anma yi" Ya amsa masa ba fargaba ko shayi saboda ya bawa kansa tabbacin shine keda nasara.
Wayarsa ya fidda yabi dukkan process yayi transfer kudin da suka rage zuwa account din wanda
zai ajiye kudin,idan nasara tasa ce ta dawo masa,idan ta kubce kuma dukka kudi sun tabbata mallakar
KAWU!.
Daidai lokacin da akayi alerting mutum biyu fitar kudin,sai fuad dake zaune yana bibiyar komai ya
lumshe ido yana sauke siririyar ajiyar zuciya,daidai sannan kuma kira ya shigo masa. Ko daya duba sai
yaga daga department din da aka kira ya daga yana cewa
"Just keep an eye on it,naga komai" Sai ya kife wayar yana maida dubansa ga allon system din yana
qoqarin tracking account na wanda aka sanya kudin.
*_TURQASHI....QAQA QARA QAQA,BAZANCE KOMAI BA😂😂.....amma akwai ZAZZAFAR TURKA TURKA
FA.....MUJE ZUWA_*
*HUGUMANKU CE*